MASIFAFFAN NAMIJI

19

by @jamilaumarjanafty

MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty💞*

*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
Contact Hijabs Corner by Janafty for all kind of Qualitative hijabs for women of class.
*** ZARIA/KADUNA Natio wide delivery.

*019*

'"Cigaba da Charting sukayi Abdullahi na gayamata yadda yayi kewarta,Ita kuma tana Biye mai Tana mai Tabara da sangarta Ganin ta kunnoshi Da yawa yasa ta kashe Datan kawai ta sauka tana Sauke Numfashi.

Subai"atu Dake gefenta ta waigo Tana Kallonta Bayan itama Tagama Waya da Mahmud dinta Dayake suna katifa Daya ne a kasa matar gidan ta Shimfida musu,Makotan su Goggo Habiba ne,Ita kuma Zannira tana Bisa gado Ita da yarinyarta sai Jamila Diyar goggo Habiba da wasu baki Suna Dakin Uwargidan Dayake gidan Uwargida da Amarya ne,sakamakon Chan gidan Goggon Baki sunyi yawa Ba wajen kwana yasa Goggo tace Jamilarta Ta kaisu gidan Alhaji Isa din su kwana makotansu ne ana zaman Mutumci da karrama Juna.

Ganin Kallon Datake mata ne yasa Hafsah tace"Kallon fa..? Nanawa ne..? Subai tace"Ke zan Tambaya naga kingama Chart da Yayanmu kina ta Sauke Numfashi kodai kodai..?Cikin Sauri Hafsah tace"Kodai me..? Subai na Dariya tace"Kodai ana Bukatar Yayan Namu ne..? Wani Duka Hafsah ta Dakama Subai tana Fadin"Kefa yar iska ce. ? Mugun saka idonki yayi yawa kina waya da naki mijin ammh hankalin na wajena ko..? Sai na Fada masa Allah."

Subai na Dariya Tana Fadin"Yo yau naga ikon Allah Ina Laifina gani nayi kuna gama Mgana kin Hau Nurfafashi Dole na maganta.."Tafada tana kashema Hafsah ido Daya,Kafin Hafsah ta Bude Baki tayi mgana Wayarta ta Shiga kara Da Sauri Subai ta Saka Hannu ta Dauki Wayar ganin An Saka *HUBBY*❤️ yasa Tagane Abdullahi ne,Mirmishi ya kwace mata da Dariya tace Tana Kallon Hafsah.."Lalle Su ya Abdullahi manja...Ahe Hubby ne kuma.."Tsaki Hafsah tayi ta Fizge wayar Tana Fadin"Bai kai a kirasa da Hubbyn bane.? Ko me kika maidashi Yar rainin Hankali.."Ta karishe fada Tana Hararanta Dariya ta kama Subai tanayi Har tana kara kwanciya kan Katifar ita kuma Hafsah sai ta Juya mata baya ta Daga Kiran Kafin tayi mgana Taji Abdullahinta ya Saki kakkarfan Ajiyan zuciya Cikin Rudewa tace"Abban Amira me ya Faru..?

Shagwabemata yayi yana Fadin"Umh.Uhm bake bace..! Itama Cikin Tabaran tace mai"Ni kuma.?me nayi..? Ta fada tana wani karya wuya Kamar wata karamar yarinya,Baki kawai Subai ta saki Tana kallonta,Dagachan Bangaran Abdullahi yace"Ina ta Kiranki baki Daga ba...Zuciyata har ta Fara Zafi Hafsatuna.."Karya wuya Hafsah ta sake yi kafin tace"Afuwan Megidana..na dan Fita ne Shiyasa.."Cikin Kaguwa Abdullahi yace"Ina kika je kuma da wannan Daran..? Da sauri Tace"Ba fita nayi ba..Tsakar gida na Fita naje nayo Fitsari Kafin mu kwanta.."Ajiyar Zuciya ya Sauke yana Fadin"Kina ina ne..? Gidan goggo..?

Hafsah tace"A"a muna makotansu inda muka kwana Jiya..Chan ba wajen kwana Don ma yau an ragu wasu sun Bi amarya.."Abdullahi yace"Eh yanzu Muka gama waya da Umma take Fadamin ita da Inna Abu sun raka Amarya Malumfashi.."Hafsah tace"ai kam mu sai gobe zamu je mu ga Daki in Allah ya kaimu.."Yace Allah ya kaimu Plz Hafsatuna ki Dawo Goben Allah gidan yayi min Girma Ina jin kewarki Sosai.."

Hafsah tace"Insha Allahu ko bamu Dawo gobe ba Jibi Tun Safe muna Tafe.."Ba haka yaso ba Dayake Goggo Habiba ne sai yace"Ok Allah ya kaimu ina Yaran nan ne..? Subai da Zannira..?

Hafsah tace"Ga Subai nan Zannira kuma Tana Ciki mu muna Falo ne.."Baki ya Tabe yana Fadin"Sai da safe...Ki kularmin da kanki kinji ko..? Hafsah tace"Insha Allah..kaima haka.."Dagahaka suka yanke Kiran Sai ji kawai Hafsah tayi Subai ta Fado mata tana Fadin"Ke daman Haka ya Abdullahi ya iya Rage murya yana Shagwaba..? Ashe dai ba Masifa kadai ya iya ba.."

Hafsah tace"Allah zan gayamai kina mishi Labe in yana Waya da Matarsa.."Da Sauri Subai tace"Rufamin Asiri Don Allah..Kada ki kara jamin wani Fadan Bayan wanda dazu nasha.."Dariya ta kama Hafsah itama Subai din Tana Tayata Kwanciya suka gyara Lokaci Daya Suna Cigaba da Hira Cikin Hiran ne Hafsah ke tambayan Subai Labarin yayar Mijinta nan take Fadamata Tunda Ummi tazo ta bata Hakuri kuma tace zata jama Uwanin kunni Shikenan Daga Lokacin ko Haduwa sukayi Sai dai Harara Daga nesa Hafsah ta gyada kai tana Fadin hakan yafi Gwara kowa ya zauna iya matsayinsa,Suna Cikin Hirar ne Barci ya kama Hafsah ganin haka yasa Itama Subai din tayi addu"ar Barci ta kwanta.

Washegari Tun  wajen 10am na Safe su Hafsah da Zannira da Subai sai Jamila da wasu Jama"ar suka Tafi malumfashi,Wajen azahar suka isa Dama anyi Danki wasu kaya ne suka Tafi dashi na kitchen sai akwatunan amarya da Sauran Kayan amfani Sun iske Su Umman Sadiq sunyi wanka suna ma Ta Shirin dawowa ne,Nan suka Hadu suka kara gyaran gidan Amarya Bayan sun gama Manyan su Umman Sadiq da Wasu Daga Cikin Dangin Babanta suka mikata gidan Surukanta Dayake ba Nisa da Gidan Da yaron ya gina chan suka Barta Daganan Tashar Mota suka kara samu zuwa Danja,sai Dare suka iso Goggo Habiba sai Hamdala take tana kuma Fatan Yadda komai ya gamu Lafiya yasa Baki su koma Gida Lafiya.

Washegari Tun 11pm na safe yan Zaria suka taso wajen 1saura na Rana suka iso Gidan Mama suka yada Zango Daman nan ne Daba,Yara suna ma iyayensu oyoyo,Sun Sauka ba Dadewa Zannira Auwal ya Rakata Tasha tayi Tashan Golf zuwa Kaduna taso ta bari sai gobe ammh Mijinta ya Hana Dole ta koma aranar,subai da Hafsah ne suka kai Dare,Inna Abu kuma Suna Sauka ta karisa Gida.

Da daddare Bayan Abdullahi ya Taso Daga wajen aiki ya Biyo,akuma Lokacin ne yace Mama ya yanke Hukunci aure zai yi ma Jidda sai Lokacin ya gayamata Abunda ya Faru Ranar da sukaje Daurin Aure,Jin Haka yasa Mama ta goyi Bayansa Umman Sadiq ne kadai tace A"a kada ayi gaggawa abari ta ida karatunta,jidda na Jin haka ta Fara kuka tana bama Abdullahi Hakuri sai da aka kai Ruwa Rana da Taimakon Umman Sadiq ya yarda zai barta ta Zana WEAC DA NECO dinta wanda sun kusa Farawa ammh da Sharadin in ya kara ganinta da wani Saurayi batare da Wa'adin Daya Dibarmata ya Cika ba wlh ko Shawaran su Mama bazai Nema ba sai dai taji Ya bada ita Sadaka ga koma waye kuwa Jin haka yasa ta Tsorata sanin Halinsa kaifi Daya ne, in yayi mgana baya Chanzata kuma in yace Eh toh eh din ne Har Abada.

Subai ta Fara Tafiya Gida Mijinta yazo ya Dauketa ita da yara Hafsah kuwa sai wajen 11pm na Dare Abdullahi ya kwasheta ita da yara zuwa Gida,Duk da Ranar ta gaji gata gajiyan tafiya gata Zirga zirga ammh Abdullahi bai Daga mata kafa ba sai da ya nuna mata yadda yayi kewarta kamar yadda yake Fadi,Washegari kuma Goggo Habiba ta kira kowa tamai Bangajiyan Biki tace kuma Tana nan zuwa Tamusu Bangajiya Dama kuma sun zo da Sakon Su Cincin dasu Dubalim wanda tace abama Mama ta Rabama wanda ya dace.

******

*After 3 Month..*

 
"Zuwa Lokacin Dai haka Abubuwa sukayi ta Gudana Da Dadi ba Dadi,Bangaran Hafsah da Abdullahi kuwa komai yana Tafiya Daidai Kusan dai yanayin na Abdullahi Watarana Dadi Watarana kuma Madaci Dayake Hafsah Ta Riga ta gama Saninsa Bata Biyemai ta Riga ta san Halin mijinta Baya son Raini yana son abashi Girmansa Shiyasa ta zama mai Biyayyah da Sadda kai,komai Cikin Taka TsanTsan take bata kaunar Taga tayi Abunda zai batamai Rai Ballatana Har wani Fada ko karafinsa ya Shiga Tsakaninsu.

Bangaran Sakina kuwa da Nazifi Babu Chanji sai Abunda ma yayi Gaban Nazifi ya Riga ya gama Fita Sha"anin Sakina ya ijiyeta a onesite,Ya kama Harkan gabansa ,Mganar neman Auransa kuwa Tunda sukeje Gidan Salisu Engr,bai kara komawa wani waje ba,Bawai ya hakura Da karin Auren bane a'a yana so sai zuwa gaba in yaga wacce zata iya Rikesa Ba kamar sakina Datayi ma Rayuwarsa Rikon Sakainar kashi ba,Yana son in zai kara Aure yayi Shi Don Allah da kuma yarda sunnar Manzo ta tanadar Baya son ya kara Tafka irin kuskuran Daya Tafka a Baya.

Ganin Ginin Abdullahi nata Nisa yasa Shima Nazifin ya Fara Gina Filinsa na Gaskiya tare da Taimakon Shawaran Abdullahi Data Baba wada,Sai kuma sukayi Tunanin gwara su koma Masters dinsu,kafin abubuwa su sake yi musu yawa Abdullahi dama Tun Tuni ya Turama Office dinsu Takardan yana so ya karo karatu kuma An Riga anyi approving din Requesting nashi shi bai maida kai ba,ammh mganar Nazifi yasa ya maida kai kan Karatun Dukkansu atare suka yanke Shawaran zasuyi,Tunda Dama Shi karatun Masters ba kamar Digiri bane ba koda yaushe kake Shiga makaranta ba,Wani Lokacin ma sai kayi Sati baka Shiga ba, Tunda Daman ga  ayyukansu da kuma iyalansu,Abdullahi ABU Zaria ya nema Shi kuma Nazifi sai ya nemi Kasu Kaduna State University  kuma Cikin ikon Allah Dukkansu suka samu kowa kuma abangaran Daya karanta kafin kace me har sun kamallah Registration sun Fara Karatu.

Cikin wannan Lokacin ne Jidda tayi Candy dinta Sai jiran Sakamako,Yanzu Zuwa gidan Mama sama sama ne Abdullahi baya samun Wani Lokacin kansa gana office ga na makaranta Shiyasa Wani Lokacin sai ya kwana Biyu bai je gidan Mama ba in ma zai je a gurguje yake zuwa ya Fito Shi kanshi Nazifin Sai yayi Sati Biyu Zuwa Hudu bai Shigo Zaria ba,wani Lokacin sai yazo Duba gininsa,ko kuma yazo gaida su Baba wada,Dukkansu yanzu basu samun Lokacin kansu Ballatana na iyalansu gwara ma Abdullahi yana Bama Hafsah da Iyalansa Kulawa daidai gwargwado,Nazifi kuwa Bai Damu ba Sakina na Abuja sai tayi Sati uku bata Lekosa ba Shima bai damu ba yana ta karatunsa ya maida kansa Busy,In Sakinar bata zo ba,baya Damuwa kamar baya Ita kanta ta sani Domin ko Masters din Daya Dora bai Gayamata ba sai da tazo Tagani tayi mamaki Sosai ganin yanzu Nazifi ya Daina Damuwa da Lamarinta kamar baya Shi kuma ya maida kansa Busy ne saboda samun Saukin wasu abubuwan kuma ya samu Yanzu bai Cika Son Damuwa da wata Sakina ba Azumi yake Litini da alhamis,in tazo ta bashi ya karbi Hakkinsa in bata bashi ba baya Matsama kansa wajen nema,Ganin haka yasa Sakinar ta Fara Shiga Taitayinta ta kan dawo Bayan Sati Biyu ta kwana uku Zuwa Hudu kafin ta koma Ammh Duk da Haka Bata Dada Nazifi da kasa Da zuwanta da Rashin Zuwanta Duk Daya yake Daukansu saboda bata da kunya Har da Complain ta Faramai da Zargin Cewa ko ya Fara neman mata ne Ranar yayi Dariya kamar zai kwanta a kasa Abun ya Bashi mamaki bai iya ce mata Komai ba kawai ya Fita batunsa aransa kuma ya Jinjina Rashin kunyar Sakina yaTabbatar ma kansa Duk Iskancin Datakeyi Shine ya sakarmata Shiyasa ammh Daya Fahimci Fita Batunta Shine Matsala sai ya nuna mata Shi yama Fi son tayi Rayuwar Yancinta Domin Cikar Burinta ba Damuwa Tun Sakina na Mamakin Nazifi har ta Daina Har Bincike ta saka akayi mata ko yana Bin mata ne..? Ko kuma Aure zai kara ammh bata sameshi da Ko Daya ba sai tayi Tunanin Kila Shima ya Fara gane Abunda Ta Dade tana nuna mai ne.

****

Ana Cikin Hakane Sai ga Mahaifiyar Jidda ta Diro Nageria wato Hajiya Sa'adatu wacce ake Kira Hajiya Sa"a,Hajiya sa"a Irin matan nan masu son Abun Duniya da Budewar ido suna Rabuwa da Mahaifinsu Abdullahi ba yadda iyayanta basu yi ba da Kartaje Saudiya neman kudi ta Zauna Tayi auranta taki,dama kuma Mahaifinsu ya Rasu Sai mahaifiyarsu ne kadai ga kanwarta Lariya dama su Biyu Ta Haifa.

Wata kawarta ta mata Hanya tatafi Chan Saudiya wajen Shekara ashirin kenan Tun Bayan Data yaye Jidda,Tunda kuma tatafi bata Dawo ba Har Mahaifiyarsu ta rasu ammh Sa"a bata Zo ba,Har Akayi bikin Lariya bata zo ba,sai da ta Shekara wajen Biyar achan kana aka Fara Jin labarinta ayadda tace Zuwanta da Shekara Uku tayi Aure ta auri wani Balaraban data Fara mai aiki agidansa Matarsa ta rasu,Daga baya kuma sai ta Rika aiko da sakon kudi da kuma kaya ga Lariya tana Saidawa Dama asalinsu yan Zaria ne a anguwar Samarun zariya,Dayake kuma Basu da wasu Dangin Duk sun kare sauran kannem Mahaifiyarsu ne kuma sun Fita batunta Tunda sukace karta je Saudiya takaranci Taje suka Fita Sha"aninta,Sai Gidan Babansu wanda Duk sun kare sai wani kanin babansa kadai ya Rage Baba isuhu sai ya"ya da jikoki, Lariyace ke kare mata tana Fadin Aure tayi achan ammh ba wanda ya yarda da Ita.

Bayan Shekara da Tafiyarsu Kawarta da suka Tafi Tare ta Dawo da Tarin Dukiya ita take Fadama Lariya irin kudin da Hajiya sa"a tayi da kuma Riban Datake samu wajen sana"arta Ita kanta Lariyar ta samu Abun Duniya Sosai na Dogayen Rigunan da Sa"ar take aiko mata Dashi Tana Saidawa kafin kace ma Sa"a ta maida kanwarta mai kudi,ana kuma Cikim Hakane Allah yayi ma Mijin Lariyar Rasuwa kuma bata Taba Haihuwa ba kawai sai ta koma tana zaman kanta Bayan an bata Gidan data gada na zaman Takaba,ta koma Chan tana Cigaba da sana"o'inta Kuma suna mgana da Sa"arta ta waya ita ta bata Shawaran ta Fara Fita Dubai tana Saro kaya kada kudaden su Darkane a hannunta da wannan Shawaran tayi amfani Lariya ta Fara zuwa Dubai saro kaya kafin wani Lokaci sunan Lariya mai kayan Dubai ya Fara Shahara,shekara Biyu Tsakani ta Biya kudin Hajji taje Saudiya achan suka Hadu da yar"uwanta Hajiya Sa"a bata iya ganeta ba saboda yadda ta Sauya ta Chanza kuma Tabbas Tana cikin Daula Rayuwa Domin Tana auran wani Mai kudi ne Balarabe ammh Baya som Haihuwa kuma sai da sukayi da Sharadi Kafim auransu suka je aka Juyama Sa"a mahaifa ita kuma saboda Tarin Dukiya ta yarda ta Aureshi baDomim komai ba Saboda tana so Ta gina da kanta kafin ta rabu dashi ta koma Nageria ta Dauko yarta su Zauna tare.

Komai Hajiya sa"a ta samu to Na Jidda ne,Kowani sako zatayi ma Lariya akwai sakom Jidda,ita kuma Lariya bata mika Sakon ga Jidda saboda tataba zuwa gidan Sau Daya da kayan Sakon da Hajiya sa'a kema Jiddan Ammh da Mama ta karbi kayan da ta sake komawa sai ta maida mata da kayan tace Yayansu yace baza ta karba ba Abun ya bata mamaki ammh sai bata Fadama Sa"ar ba bata so Hankalinta ya Tashi,Sai ta Cigaba da ijiye komai awajenta Tana Jiran sai Hajiya sa'ar ta dawo sai ta Fadamata komai acikin Hakane har Ita Lariyan ta Gina katon gida ta tare to da zata taren sai tazo ta Roki mama Ta bar Jidda taje shine data kwana bayan ta Dawo Abdullahi ya Fara fada Sosai saboda Gaskiya ana Rade raden wai Hajiya sa"a karuwanci take a Saudiya tana Turoma Kanwarta kudin Tana kasuwanci bama haka ba Tarbiyan mace bata  mace bace sai Tsayayyan Namiji ballatana Jidda Datake da Bala"in Rawan kai da Fi"ili.

Ashe itama Hajiya sa"a tana aiko da Kudi ana Tamfatsa mata, wani katom Gida a chika gari,ta Hannun Hajiya Lariya,Domin tana Shiryan Shiryan Dawowa ne,cikin Lokaci kadan Dayake da kudi Ginin gida ya kamallah aka saka komai na alatun Rayuwa achan Saudiya Hajiya sa"a tana so ta Tsinke Auranta da wannan Balaraben kuma sai abu ya gagara suka Fara Hayaniya Domin yace shi bazai sake ta ba,tayi tayi ammh kuma yaki Dole Dawowarta Nageria ya samu Tsaiko sai da ta Shekara 20cir kafin ta Sako kafarta acikin kasarta ta Haihu Shima Dalilin Rasuwar Mijin nata,bata baro kasar ba sai da aka Raba Dukiyarsa aka bata nata sauran kuma yan"uwansa da ya"yansa suka Raba Ita dai Saudiya ta mata komai na Rayuwa Shiyasa data Dawo Nageria bata ci Kaichio ba sai ma Cigaba tana Tunanin Data zauna acikinta Allah kadai yasan ya Rayuwarta zai kare a wulakance.

Tana Dirowa Hajiya lariya taje ta Daukota Direct gidanta suka Wuce already dama Hajiya lariya ta samo megadin dake gadin gidan Bayan kwama Biyu kuma da Dawowar Hajiya sa"a,Ta sa Hajiya Lariya ta samo mata yan aiki Guda Uku Biyu yan Matasa Daya Tsohuwa sai da tayi Sati Daya da Dirowa kana ta Shigo samaru Cikin Sabuwar Motarta Kiran Jeep,wacce Tun Tana Saudiya ta Turoma Lariya kudi ta Siya mata,Lokacin data isa Babbam Gidansu,kafin afara wata mgana ta Dinga musu barin kudi Sai kika ji bakin kowa Tsit,Baba Isuhu ne Duk da Haka sai da ya maganta,yayi mata Fada Sosai ta kuma Rantse da Allah Aure tayi ba zaman karuwanci ba, Gidansu  Mamansu kuwa duk irin Cin mutumcin da suka Tanadar mata ta Rufe bakinsu da kudi Matansu kuma ta basu Tsaran kayayyanki Bayan kwana Biyu kuma ta Dawo ta saka aka Buge garun gidan aka sauya na zamani ta kuma ta Bisu da kudi Domin su ja jari sai kaji baki Shuru sune mai ke Yada ai Sa"a aure Tayi achan Saudiya kuma Daman tazo musu da Hotunan Auranta da mijinta sun gani kuma sun yarda cewa auran tayi Duk da dai mutanan anguwan suna ta gulman yawon iskanci Taje bata damu ba yanzu kawai Burinta bai wuce ta Dauko yarta Jidda ba wacce Rabonta da ita Tun Sadda ta yayeta.

Lokacin Datama Hajiya Lariya mganar kan tana so su Shirya su Shiga Cikin Zaria Wajem marikiyar Jidda tana so ta karbota Aranar ne ta gayamata komai ta kuma nuna mata Uban kayan Data ke aikoma Jidda da bata kaimata ba, sai dai ta ijiyesu,Hajiya sa'a Haushi ya kamata Tana chan Tana Tunanin Rayuwar yarta ta inganta ammh Shine za"a gayamata mganar Banza Ko Dawowarta Rabin Tsarabanta na Jidda ne Har Mota ta bada Odar a kawo mata so take ta Inganta Rayuwarta Sosai yadda Zata ji Dadin Rayuwa Ba kamar ita data sha Wahala ba.

Cikin Bacin Rai Hajiya Sa'a ta kalli Lariya tana Fadin"Wani irin Shanshanci ne wannan Lariya.? Shine kika Boyemin wannan Abun mai matukar muhimmanci..?Kin fa san cewa Komai da nakeyi Duk Dukiyar dana Tara saboda Jidda ce na Dawo ina so na inganta Rayuwarta amatsayina na mahaifiyarta Tunda Tun dana Haifeta bayan na yayeta bata kara Jin Dumin Uwa basai dai na ganta a Hoto wanda kike Turamin,sai yanzu ammh kuma kika Boyemin wannan Abun mai girma..?

Hajiya Lariya Ta rausayar dakai Tana Fadin"Kiyi Hakuri Yaya Abunda yasa ban Fada miki ba Tun Lokacin bana so a Hankalinki ya tashi ne.."Wani Wawan Tsaki Hajiya sa"a ta Saki kafin tace"Ita Karimar ce tafada miki cewa Bazasu karbi komai ba..? Ko ta manta ni Sa"a ni na Haifi Hauwa"u da Cikina..?Tafiyata Saudiya ba Dadewa naji Labarin mutuwar Alhaji Usman wake Daukan nauyin yata..? Nasan Tana chan tana Shan wahala ya zama Dole yau ba sai gobe ba naje na Dauko yata ta Dawo Hannuna Har Abada.."

Hajiya lariya tace"Ba ita bace taki karba Cewa tayi yayansu yace Jidda bazata karbi komai Daga wajenki ba Domin bata Bukatarsa.."Hajiya sa"a tace"Yayansu kuma.? Waye kuma yayansu..?

Hajiya Lariya tace"Oho ina na sanshi Banta ba ganinsa ba ammh ai na gayamiki na zan tare a sabon Gidana naje da kaina na Roki karimar sanna ta  bari Jidda Ta Biyoni Dare yayi mata sai ta kwana baki ga yadda ta kirata tana mata Fadan ta Dawo gida yayansu na Fada ba, Danaga Jiddan ta Rude ne yasa na Tambayeta wanene sai take Fadamin wai ko yayansu wama..? yauwa Abdullahi tacemim kamar Shine Babba inaga shi ke Dauke dasu gabadaya Domin Jiddan na gayamiki makaranta mai kyau take kuma bata Cikin Wahala gaskiya.."


Hajiya Sa"a ta koma Ta zauna Dabas Tana Dafe kai kafin tace"Inaga Yaron Matarshi ta Farko ce daman naji labarin Yana da Babban yaro namiji Shima ba"a gidan taHaifeshi ba Shiyasa ban sanshi ba..."Hajiya lariya tace"Nima dai ban taba ganinsa ba


Hajiya Sa"a tace"Ki Shirya muje Gidan...Ko da Karfin Dukiya data Sharia sai yata ta Dawo Hannuna ina so na Jiyar da ita Dadin da ban Jiyar da ita ba A baya ba..."

Daga haka Tatashi tana wani Taku Mazaunanta na Juyawa Ta Shige Cikin kayattacen Bedroom dinta Hajiya Lariya ta Bita Da kallon Tsausayin ganin Ta Cikin bacin Rai.


Littafin Masifaffan Namiji  free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai Completed document  1k ne biya ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar.
Ko tuntuɓa ta wannan lambar ***



*Janafty*