Page 52
⚡MARYAMA⚡
52/53....
"Jama'a gata nan, shegu dangin jaraba ga dayar ta dawo"shine kawai abun da ummar Umaimah ke fada tana cigaba da cakumar Maryama,da hanzari oga zubairu ya ja Qaseem yana kara jadadda mishi ya kwaci Maryama fa su bar wajen nan tun kafun lokaci ya kure musu, kan kace me wajen ya fara dinkewa da mutane baka jin komai sai hayaniyar Jama'a..
"Shikenan Qaseem kana zamanka lafiya gashi yau ka kawo kanka da kanka mahallaka"zuciyar Qaseem ta fada mishi, tuna gargadin da wannan mutumin ya mishi ne ya sa shi zagawa ta daya bangaren inda wannan mata mai suffar mahaukata ta rike wuyar Maryama kuma babu wadda yayi yunkurin kwatar ta a wajen,hannu daya yasa ya fincike hannun matar daga wuyarta,gefe guda Maryama ta fadi tana wani irin tari dan ba karamar shaka ta mata ba,baki ya bude da niyyar tabbatarwa wannan mata batabda hankali amma sai maganarshi ta katse sakamakon wasu gungun matasa da suka tunkaro wajen kallo daya zaka musu ka fahimci shaye shaye ya rigada ya gama yiwa rayuwarsu illa, ko wannensu dauke da makami kamar sanda,adda da sauransu...
"Innalillahi" zubairu ya fada yana dafe goshinsa, da sauri ya rarumo hannun Maryama wacce tana gama tarin ta kara tunkarar Umma idanunta sun bushe qam babu alamar digon hawaye tana tambayarta ina Innata ina Hamma Jay?da sauri ya cusa ta gaban motar yana kokarin rufewa wadannan matasan suka iso, "Ina take mu far mata,ina take mu kaddamar mata" wani wawan zabura Qaseem ya yi ganin sun tunkari motarshi, bisa jagorancin umma,a tamanin ya kama handle din zai bude kenan, rimmm yaji saukar Wani mukeken sanda a mukamukinsa, rumtse idanu ya yi da karfi yana ci gaba da bude motar da yake jin yanda suke ta farfashe gilashinta a kokarinsu na ganin sun ciro Maryama,ya tabbata zuwa lokacin bayan wannan motar ta tashi daga aiki dan ruwan sanduna da tasha,..Kara mai karfi Maryama ta saki lokacinda ya samu nasarar shigewa motar zuciyarshi cike da mamakin mai yasa babu wadda yayi yunkurin taimakomsu sai zubairu kawai shima a tsorace yake? sai dai zuciyarshi ta bashi amsa da cewa "kowa gudun rayuwarsa yake".
Cikin zafin nama ya kamo Maryama ta kwanta lufff a jikinsa sakamakon wani sara da daya daga cikin mutanen ya kawo mata bayan ya fasa glass din gefen da take, by mistake ya dan samu gefen hannun Qaseem kadan,cike da kidima ya yiwa motar key ya zabure ta da mugun speed da gudu yaran suka bishi suma, da hannu daya yake driving din hannu daya kuwa na rike da Maryama da ta zama kamar mutum mutumi ita bata duniyarmu kuma bata wata duniyar tana dai tsaka tsaki.
Sosai yake sharara gudu har suka fito bayan gari inda ya tabbatar da sun rigada sun tsere musu sannan ya ja wani irin wawan birkin da ya dawar da ita hayyacinta,kanshi ya daura bisa steering yana maida numfashi sama sama tare da jin irin azabar da mukamukinshi ke mashi na sandar da yasha da kuma yankar da aka mishi duk da bai shiga sosai ba, amma yana digar da jini.
Sai a lokacin Maryama ta samu damar fashewa da wani matsanancin kuka tana kiran Innarmu ina kika tafi kika barni?...(Maryama ke bakiji shakkar tafiya ki barta ba,dan ita ta tafi ta barki laifi ne?).
"Zaki rufe min wannan bakin ki fada min inda zan kaiki ne ko sai na jefar da ke a nan na yi wucewata?".
Qaseem ya fada a fusace yana dagowa gami da watsa mata wani irin kallo da ta kasa fassara shi.Ina zan kaiki yanzu dare yanayi, dole ne in koma abuja a yau dinnan.
"Ina ne gidajen sauran relatives naki!"ya fada cikin daga murya ganin bance komai ba sai kuka da na ci gaba da yi.
"Bana da kowa yanzu,I have no body sun tafi sun barni suma".Na fada da wani irin murya mai karya zuciya.
Kamar ya baki da kowa?da ga sama kika fado ne?ina ne relatives naki suke malama i have to go back inda na fito yau dinnan,"ya fada da kaushin murya wanda ke nuna yana jin haushinta sosai zuwa yanzu.
"Sai dai ko in koma wajen Ummar su Umaimah kilan ta fada min inda su Innarmu suka tafi,ko kuma in samu Umaimah a gida ita nasan bazata guje ni ba".Na fada muryata tana rawa.
"Inane gidansu Ummar yake?" ya tambayeni da sauri.Da hannu na nuna mishi baya sannan nace "itace muka bari a can ai".
Zaro ido yayi yace, "Wannan mahaukaciyar matar?" hawaye na cigaba da wanke min fuska na ce, "Tana da hankali Ummarsu Umaim...."
Katse ni yayi ta hpanyar daka min tsawa da fadin "to sauka kije tunda tana da hankali" ga mamakinshi handle din ta kama zata sauka kuwa, cikin fusata yayiwa motar key ya kara figarta da dan banzan gudu, babu shiri Maryama ta saki handle din ta dawo baya baya ta fada gefen damtsen hannunsa dake digar jini kadan kadan har lokacin, "ouchhh,it hurt" ya fada da dan karfi dan abun yazo masa ne unexpected.
Kara tasowa na yi sakamakon tudun da muka hau na bugu da kujerar da na ke zaune bisa, rumtse idanu nayi ina addu'ar neman sassauci daga rabbi. Gudu kawai yake ba tare da ya kara kallon ko gefen da nake ba har muka dawo yola lokacin rana har ta fadi...Wani anguwa da ban sanshi ba naga mun shiga,zuwa yanzu ya rage karfin gudun da yake yi a hankali yai parking motar gefen wani babban gida,ba babba a gini na zamani ba, babba a fadin fili dan shi kadai kawai ya cinye layin anguwar ta gefen gabas,daga waje kana iya hango part part dake gidan masu yawan gaske a kalla zai kai part goma a hasashe, sai babban masallaci dake manne da gidan da wani babban varanda mai girman gaske dake dauke da allauna jeri jeri wanda ke alamta lallai wannan gidan malamai ne kuma ana daukar karatu a ciki.
Imran ne ya fito daga cikin gidan dalilin kiran da Qaseem yai mishi na cewa ya dawo, "Subhanallah, mai ya sameka a hannu haka,? kafin ya bashi amsa idanunshi ya sauka akan motar shi da akayiwa dibar albarka "Innalillahi,Qaseem hatsari kuka yi ne?" girgiza kai Qaseem yayi da fadin, "Plsss Imran muje nearest chemist a min dressing na wajen nan its paining.
Ohk hanzarta muje, you know dole yai ciwo ai, idan ka samu accident sai ka bar motar a can ai ka hau motar haya, amma ga ciwo kuma ka kara driving har tafiyar 1hr?.
"Ka kaita wajen Innayi before mu wuce"sai a lokacin Imran ya lura da Maryama dake tsaye so innocent tana ta jujjuya fingers dinta, bai ce komai ba dan yanayin da abokinnasa ke a ciki, ya yafito wani almajiri cikin almajiran dake wajen suna ciccika butoci da ruwa dan magariba ta kawo kai.
"Salmanu ka kai wannan wajen Innayi kace mata bakuwar Qaseem ce, munje wani waje muna zuwa yanzun.
Maryama ba tayi musu ba tabi bayan yaron dan taji gaba daya abin da suke tattaunawa a kai,sai da ta shiga ta raina kanta, dan duk girman gidan a waje ta ciki ya fi shi girma tamkar anguwace idan ka shiga sai ka samu gidaje a ciki,ko wanne bangare da kofar shigarshi,direct sashen da yafi kowanne girma yaron ya kaita, har cikin wani madaidaicin palo da babu komai cikinsa sai shelfs dake shake da takardu na addini da kuma lallausan carpet da ya zagaye palon kana tabkeken tvn bango dake makale,shikenan abinda ke palon wata yar dattijuwa ce fara sol duk da jikin tsufa amma zaka fahimci irin hasken da take dashi, zaune gefe bisa dardumar Sallah hannunta dauke da casbaha, tana azkar na yammaci "Innayi inji Hamma Imran in kawo matar nan wai bakuwace suna zuwa." yaron ya fada bayan sunyi sallama a palon.Katse azkar din Tsohuwa Innayi tayi tana fadada murmushinta tace, "lale maraba da ke ,shigo mana" karasowa cikin palon Maryama ya yi a dan diririce ta rakube gefe ta zauna tana gaida Innayi, bata dade zaune ba aka fara kiraye kirayen sallar magriba,dan haka ta bukaci buta da bayi dan ko sallar la'asar batai ba.
Alwala ta dauro bayan Innayi ta hadata da wata yar jikarta da ta kawo abinci daga sashensu ta nuna mata toilet, wani dardumar ta bata gami da hijabi ganin dan gyalen dake kanta.
A nan suka gabatar har isha, wajajen karfe bakwai da rabi ta jiyo sallamar su daga bakin kofar, da farko har ta fara fidda ran cewa ko dai ya ajiyeta ya gudu ne, sai dai zuciyarta na karyata hakan dan a wajenta shidin mutumin kirki ne mai taimako dan Allah.