MARYAMA

Page 43

by @ummufadeela01

Shigowa sukayi su uku Imran da Qaseem sai wani tsoho mai cike da kamala da dattako da taji sun kira da Modibbo...Modibbo malamin Qaseem ne,tun yana dan shekara biyar aka kawoshi almajirci wajen modibbo,ganin irin kankantar shekarunsa ne yasa modibbo shigar dashi cikin zuriyarsa a lokacin Imran shima yana dan shekaru biyar kuma shine jikan Modibbo na farko dan babban danshi hakan yasa tasu ta zo daya, tun daga lokacin ya zama dan gida jar zuwa gama karatunshi ma bai koma kauyensu ba daga da yake yana sha'awar boko malam bai tauyesu ba ya saayasu da sauran yara, har Allah ya basu sa'a suka gama suka zama wani abu, yanzu haka Qaseem yana aiki da hukumar tattara kudaden shiga ta nageria ce.Shikuwa Imran babban likita ne a nan Yola duk abun da uba ya kamata ya samu a wajen da na gari, Modibbo yana samu wajen Qaseem sai da aka fara turashi kasashe ne ma ya rage zuwa amma da duk bayan wata biyu sai yazo, matarshi Sameera kuwa a unimaid maiduguri suka hadu lokacin tana digiri aji biyu shikuma yana masters aji biyu haka Allah ya hada soyayyarsu har sukayi aure, yanzu kimanin shekaru goma amma Allah bai basu haihuwa ba,kuma bai taba damuwa ba.

"Alqasimu wannan ce baiwar Allahn da ka bamu labari yanzu a waje?" kara rusunar da kai Qaseem ya yi yace, " itace, Allah ya baka yawan rai".masha Allah, yanzu bari muci abinci sai muga yadda za'ayi da al'amarinta.kai Imrana kaita bangaren ku ta samu su Husna su debe mata kewa sannan ka yi kiran iyayen naka gaba dayansu maza.

Da to Imran ya amsa sannan ya ce da Maryama ta taso su wuce ya samar mata abokai, ba tare da ta cire hijabin dake jikinta ba ta mike jiki a sanyaye ta bi bayanshi, yayinda Qaseem kuwa ya bita da ido, ahi kuwa Modibbo ya bishi da ido.

Bayan kamar minti ashirin wannan palo ya dinke da jama'a yayan Modibbo manya uku sai kannenshi su biyar da kuma Qaseem da Imran kasancewarsu manya jikokin gidan, abinci suke ci kala kala da aka kawi daga kowanne sassa na gidan sai fura da nono da ya zama al'adarsu duk dare sai ansha ta.

Bayan gama cin abincin yara masu jiran sudi suka tattara kwanukan modibbo yayi gyaran murya da fadin akwai magana muhimmiya da zasuyi dan haka kowa ya nutsu dan su tabbata ba maganar wasa bace.
" Dazu bayan mun gama daukar karatun magariba kwatsam naga danku Qaseem babu zato, to ba zuwan nashi bane al'amarin da ya zo dashi ne ya girgizani, ko da dai ya fadamin ina ganin tunda gashi kusa damu sai ya sanar daku da kanshi.

Kara yin kasa Qaseem ya yi da kai ya fara basu labarin haduwarshi da Maryama a airport da abun da ya faru da kuma labarin da ta bashi sannan ya karkare da labarin abun da ya faru bayan sunje garinsu Maryama babu gidansu babu yan uwanta da kyar ma suka sha dan harin rayuwarta ake.

Kusan gaba dayansu suka hada baki wajen fadin "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un". Yanzu menene kuke ganin mafita?' cewar modibbo wanda kasnacewarshi babba bai sa shi zartar da hukunci a gidan komai kankantarta har sai ya ji ta bakin yan uwanshi."Duk hukuncin da ka yanke dai dai ne" kusan dukkansu suka fada, sai ya dubi yayanshi yace kufa ,"babban danshi mustapha ne yace, "Duk hukuncin da kayi shi nedaidai Ranka ya dade, amma tunda ta bakinmu ka nemi ji, ina ganin a nemi mutum daya a hadasu suje can nijar din tunda tace daga can iyayenta suka fito, ta yiwu can suka koma dan rayuwat ya mace a ko da yaushe yana bukatar kasnacewa karkashin wani namiji, walau ubanta, ko danta, ko kuma mijinta,duk sadda aka samu kuskure zakaga rayuwarta ya shiga garari".

Kusan kowa ya yi na'am da shawaran amma Qaseem ya katse musu tunani da fadin, "amma wani hanzari ba gudu ba ranka ya dade, ta ce min fa bazata iya gane kauyen nasu a nijar ba,dan tun tana karama ake zuwa da ita dan haka bazat iya tuna ko da sunan garin ba...Dukkansu sun jinjina lamarin tare da fara tunanin wani mafitar.Modibbo yayi karfin halin fadin ina ganin kawai tunda har Alqasimu ya fara kawai ya idar,sannan na tabbata hakan zai zamto masa sadaqatul jariya insha Allah,dalili kuwa shine..........Tsawon lokaci Modibbo ya dauka yana magana da kawo dalilai masu yawa daga qur'ani da hadisai, sai dai tun lokacin da ya fara maganar Qaseem ya ji kanshi yayi wani irin sarawa giriiiimmmm sannan a hankali fara daina fahimtar abun da dattijon wanda yake matsayin uba a gareshi yake fada...Alqasimu kaji abun da nace shin ka amince?" kamilalliyar muryar Modibbo suka ratsa dodon kunnenshi cike da dimuwa ya dago kanshi yana kallon gaba daya occupant na palon da suma shi suke kallo, babu abinda Modibbo zai nema a duniya da Qaseem zai kasa mishi matukar ba wai ya sabawa Allah bane,sai dai amincewa wannan bukata tamkar yasa wuka ne ya farka ledar data hana ruwa cin gidanshi, tamkar ya sa bindiga ne ya tarwartsa duk wani farin cikin gidanshi..."Modibbo kun wuce neman shawara ko roko a wajena,duk abun da zaku aikata lallai ku aikata a kaina bisa umarni ba shawara ba, ku din iyayene na haqiqa a gareni.

Qaseem ya samu kanshi da furta wannan kalmar da bai san sadda ta subuce mishi ba...Madallah da karamcinka garemu Alqasimu, cewar Modibbo, yayinda Qaseem yaji bakinshi ya bushe qamas ya kasa furta komai.Kusan kowa ya yi na'am da hukuncin na Modibbo dan haka suka dan tattauna kagun gudanarda komai.Wani irin jiri ne ya fara dibarshi lokacinda yaji an shafa addu'a na watsewa daga taron ba tare da an nemi ji daga bakin ita yarinyar ba...Da taimakon Imran suka wuce bangarenshi, a palo suka tarar da husna Matar Imran din da Maryama dake zaune jigum bata fahimtar hirar da Husna ke ta zuba mata.gama cin abincinsu kenan da Husnar ta sa Maryama ci da kyar dan da farko kin ci tai.

A karon farko tun bayan da ya santa cikin tsukin kwanaki biyu rak,ya tsaya mata kallon tsaff, "she's beautiful,very very beautiful that you could'nt imagine"ya fada a ranshi still bai dauke idanunshi daga kan face nata that look so stranded ba.Har ya zauna daga cikin kujerar yana dafe kanshi da kiran sunan Allah,...Ras! rass!! rasss!!!haka gaban Qaseem ya yanke ya fadi a jere tunawa da Sameera da yayi, ko dazu sunyi waya kuma ya tabbatar mata yana gida and the worst part of it gobe zata dawo kuma jirgin safe zasu bi.Tun kallo daya da ta mishi bayan shigowarshi ta maida kanta kasa bata kara dagowa ba, sai dai tana jin yadda nashi idanun ke yawo a kanta...Gaba daya sauran hirar ya kare ne tsakanin Imran da matarshi, daga karshe ma mikewa yayi ya wuce bedroom dake mallakinshi a part na Imran din.

Wani single room dake kusa da bedroom din husna Imran ya ce da matarshi ta kai Maryama ta huta itama...Washe gari da tsananin ciwon kai Qaseem ya tashi,wanda rashin jirgi da zai tashi zuwa abuja da safe ya kara tsananta mishi ciwon, duk bulayin da zaiyi don samu koda ba direct bane bai samu ba sai jirgin yamma, wannan ne ya tsananta mishi ciwon kan ga shi sunyi waya da sameera lokacin da zata tashi ala dole ya kashe wayarshi dan a halin da yake a ciki bazai iya daukar ko wanne irin tashin hankali ba kuma,ko da Maryama ta yi wanka washe gari kayan Husna ta saka atamfa dinkin riga da siket sai dogon jilbab peach colour da ta sanya,sosai ta yi kyau dan ya boye kaso mai yawa na tashin hankalin da take ciki...Gabanta ne ya buga lokacin da Aka kirata wai tazo su wuce,.


Cike da rashin sanin takamaiman inda zasu wuce din ta fito da tunanin ko gidan zasu kara komawa suga ko za'a dace su Innarmu sun dawo,sai dai sabanin tunaninta bangaren tsoffin nan na jiya aka shiga da ita, bayan gaisuwa Modibbo ya fara yiwa Maryama nasiha mai tsayi da nuna mata muhimmancin yarda da kaddara a duk yadda tazowa bawa daga karshe yace suje Allah ya musu albarka,..Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki take binsu a baya zuciyarta na tariyo mata nasihar wannan tsoho wanda ta kasa gane ma'anarshi, bata kara tsinkewa ba saida suka isa filin jirgin sama taga da gaske fa shiga zasuyi nanne ta fashe da kuka tana tambayar Qaseem, "Ina kuma zamuje, a nanne kawai nake da yakinin ganin mahaifana dan Allah"

Da tasan halin da ya ke ciki bazata taba gigin mishi magana ba, amma sai ya daure yace yana kallonta, "Dubai zamuje,kin wuce ne ko sai na kakkarya wadannan kafafun naki mai kama da na sauro."

Cike da matsanancin kuka Maryama tayi gaba suna biye da ita a baya, "mr man sai ka bita a hankali fa, " cewar Imran yana kunshe dariyar dake cin cikinsa. "a'a da yakin duniya na uku zan bita" ya bashi amsa a takaice.Dariya Imran ya fashe da har yana rike ciki,..Saida yaga tashinsu sannan ya koma gida.

Wajajen bakwai na dare suka iso gidan nashi dake abuja a motarshi da ya baro a airport din, Sameera na goye da hannayenta a baya sai safa da marwa take yi a palon, tun isowarta ta kasa zaune ta kasa tsaye bata kara shiga tashin hankali ba sai da Ma'u ta tabbatar mata cewa tare da wannan yarinyar mai kama da sadaka yallar honey ya fita,tun jiya kuma bai dawo ba wani tashin hankalin kuma gaba daya wayoyinsa a kulle,"wato ni honey zai yiwa cin amana ko?" ta kara fada a karo na kusan million, a dai dai lokacin ya turo kofar gami da yin sallama a can kasan makoshi...

Carafff idanun Sameera da suka yi jawur tamkar zasuyi tartsatsinwuta ya sauka cikin na Maryama dake rakube bayan Qaseem kamar ace kyatt ta ari na kare, a tare zuciyarsu ya bada sautin dammmmmmmm......