MARYAMA

Page 54

by @ummufadeela01

54...

"Kan bala'i, mai wannan kuma ta dawo yi min a gida ni Sameera Allah ka dube ni, me wannan kuma nace,?"

Samira ta fada tana nuna Maryama dake tsaye a bayan Qaseem jikinta sai makyarkyata yake.

Gaba daya sai ta nemi rikicin da ta tanadar da nufin idan ya dawo zan gabatar mishi na fooling dina da yai na rasa,...

"Honey! me wannan yarinyar mai kama da sadaka yallar ke yi a nan bata koma gidan ubanta bane? ko dai dama akwai wani abu da kake boye min ne da ban gama sani da tantacewa ba?

Ya kamini shiru ina ta magana?" 

Samira ta fada ganin baice komai ba.

Kan Yarinyar da har zuwa yanzu bata san sunanta ba kuma bata fatan sani, ta koma hadi da nuna mata kofa a fusace.

Ke dan kaza kazanki bar gidan nan kafin in nuna miki other side of m..."

Cike da karsashi da yadda da shawarar da zuciyarshi ke bashi na lallai dole saika jajirce ka zama namiji a gidanka ya juyo ya kamata ya rike gam a jikinshi, "mai kike aikatawa hakane Sameera uhmyimm?mai yasa kullum kina girma amma hankalinki yana zama irin na yara?"

Zaro idanu sameera tayi bakinta yana rawa tace, "What?Honey!yau ni kake fadawa magana haka gatsau akan wannan mai kama da sulalalliyar karas din,wato so kake ka nuna min iyakata dan ban haihuwa a gidannan ba ko,?wato duk abun da kake fada min dama yaudarace ba har zuciy...."mukusss ta yi gami da hadiye sauran maganar tata jin saukar warm lips nashi saman bakinta,cike da kwarewa ya ke sarrafa bakinshi cikin nata ba tare da tuna cewa akwai wanzuwar wata halitta a bayansu ba.,tun yana yi dan ya rufe mata baki kawai har abun ya fara fin karfinshi,dole ya ciccibeta ya wuce bedroom nashi da ita.

Hannu na daura saman kaina duka biyu zan kurma ihu,sai kuma na fasa, hannun na mayar bisa bakina ina toshewa da duk wani karfi da Allah ya bani hawaye na rige rigen sauka bisa kuncina...A hankali na kai duqe kasa ina hada kaina jikin kujera wani kuka yana kwace min,tun ina kuka har wani bacci ya kwashe ni ban sani ba.

Tsawon lokaci suka dauka a dakin kafun suka fito,sun sake sabon wanka gami da canza kaya zuwa na shan iska,yana makale da ita gefen jikinsa a kokarinshi na ganin ya mantar da ita duk wannan tataburza dake faruwa wanda shi kanshi bai san a wanne mataki yake ba yanzu,sai dai a bangaren Sameera duk wannan abubuwa da yake mata bai rage ko da kaso daya cikin rashin kirkin da ta tanadarwa yarinyar ba sinki sinki wanda a yau ba sai gobe ba zata bar gidan nan komai dare kuwa.

Hango ta ya yi duke gaban kujera kanta daure bisa hannun kujerar da alama bacci take yi, sosai ya yi kokarin ganin bai maida hankali a kanta ba.dan gudun kar dan rarrashin da yai din ya watse,"Honey!muje kaci abinci" 

Peck ya bata a gefen fuska sannan ya zauna a kujera yana nuna mata gabanshi ya ce, I prefer here Sameera". Dining din ta wuce ta hado duk abin da tasan zai bukata ta kawo nan gabanshi ta dire...

Muryar shi ce ta tayar dani daga firgitaccen baccin da ya fara daukata,a hankali na kai kallona garesu cikin sa'a muka hada idanu dashi, da sauri na janye nawa idanun zuwa kasa.

Murya kasa kasa Qaseem ya ce, "Sameera ki bata abinci plsss," da sauri samera ta kai dubanta gareta sarai ta kula da ita time da suka shigo palon, amma ganin yadda oga kwata kwatan ya share ne ya sata jin wani irin dadi dan haka itama ta fuske abin ta.Juyo da ganinta tayi gareshi yadda yayi da fuska ne alamar plssss ya sata sakin murmushin da bai kai zuciya ba ta mike tana kallon Maryama da still kanta ke kasa,ta ce, "ga can abinci sama zaki ci?"

"wanne irin zata ci kuma sameera?"muryarshi ta katseta tun Maryama bata ce komai ba,"zan tambayeta mana honey, idan bazata ci ba kaga an shiga hakkinta ai".

"No, this is not good for you" wasu hawayen na kara sharewa gami da girgiza kaina sannan na ce, "Na....Nak...Nako.Shiiii"harshena yana rabe kalmomin.mai kika ci kika koshi, abeg get up my friend" ya fada da tsawa babu shiri na mike na bi bayan Sameera da ta durfafi dining area tana ta karkada duwawu kamar tsohuwar karuwa.

Plate ta janyo ta zuba jollof na spaghetti da yasha kifi da veggies sai tashin kamshi yake yi,ko jariri aka ba abincin da Sameera ta zuba bazai koshi ba,ta ajiye kasa gami da tura plate din da kafartaa kiiiiiii har gaban Maryama, "ki zauna anan kasa kici abincin ba dan halinki ba,idan mazaunan mijina ya zauna a fili,wata bata da ikon zama a wannan wajen,what i mean is, baki da martabar zama a kujerar da mijina ke zama dan cin abinci".

Tabbas da ina da iko sai na bata amsar wannan maganar da ta min,amma sai na yi hakuri gami da danne duk wani abu da nake jin yana taso min,murmushi na kakalo a karo na farko cikin kwanakin nan na ce, "Nagode!"...Ki godewa Allah,ta fada gami da juyawa ta bar wajen.

Na kwashe akalla minti talatin ina tsaye a wajen ban samu zarafin zama ba balle inci abincin da ko kallo bai isheni ba,ganin tsayuwar ba mafita bace gareni na tako a hankali zuwa cikin palon kamar munafuka, duk idanu suka zuba min suna kallo na kafun Qaseem ya nuna min kujera "zauna zan muku magana" maimakon in zauna a inda ya nuna min bisa kujerar sai na rakube a gefe.

Gyaran murya yayi yana kallon Sameera ya ce, "Kamar yadda nace zan miki bayani abun da ya faru, firstly iam sorry wife for fooling you, na ce miki ina gida kin dawo baki sameni ba, secondly iam sorry again for compromise you, kince in driver ya kaita park, and ni da kaina na kaita har garinsu,bawai ina baki hakuri dan ke kike da ikon shimfida doka a gidana ba, a'a ina baki hakuri ne dan akwai fahimtar juna a tsakaninmu,abin da ya faru kuma ta sanar dani ita yar Adamawa ce, so shiyasa na yi sha'awar zuwa in gaida Modibbo you know na kwana biyu ban jeba da niyyar ina zuwa in dawo a yau din, amma aka samu matsala.

Gaba daya abun da ya faru a gatin su Maryama Qaseem ya sanar mata kana ya daura da fadin, "So munje wajen Modibbo da ita inda ya tabbatar min da lallai dole ta zauna a wajena for a mean time daga bangarenshi kuma zasu cigaba da bincikawa ko Allah zai sa a dace da ganin danginta, zamanta a can hatsari ne gwara ta yi nisa that's what happened," 


Juyo da kanshi yayi kan Maryama dake zaune jugum ya ce, "Maryama meet my lovely wife Sameera, zaku zauna tare na lokaci kadan and ki mata biyayya ki girmama ta yadda ya kamata kafun Allah yasa a gano iyayenki dan za'a fara bincike soon," idanunshi ya kara mayarwa kan Sameera da tayi suma wucin gadi yace, "Sameera you heard abun da nace well so ina ganin sai a gyara mata guest room din can ko kafun muga yadda zata kaya din.

"Kan babban b**a ub****n" 

Sameera ta lailayo zagi ta maka, Honey kasan mai kake fada kuwa, ta yaya zata zauna a nan, danginta ma basu karbeta ba sai kai ga sodangi ko, me ka hada da ita da zamu riketa,? bazai yiwu ba, shi Modibbon mai ya hana shi riketa duk girman gidanshi da za'a kakaba maka jarab..."

"Sameera!!!!"ya fada da wani irin karfin da saida gaba daya gidan ya amsa,take fuskarshi ta sauya, ya koma mata tamkar wani zaki, "kada ki yadda ki kara ambatar iyayena cikin wannan lamari balle ki aibanta minsu, idan nace kada ki yadda, i mean even by mistake kar ki yadda, ko dan kinga ina lallaba ki ne, mind your self ba wai tsoronki na ke ji ba, i just respecting you the way you respect me, kar in kara jin such talk daga bakinki, if not zaki ga the other side of me.

Magana karshe wannan yarinyar zata zauna damu na wani lokaci "daga haka ya wuce fuuuu ba tare da ya kalli kowacce daga cikinsu ba.

Baya baya Sameera ta yi ta zube bisa kujerar tana dafe kanta, lallai ta tabbata wannan yarinyar ta zame mata bakar kaddara,dan tunda take da Alqaseem tsawon shekaru ba'a taba samun daga murya a tsakaninsu ba, Maryama ma takurewa ta yi waje daya tana kuka.

Ganin tunanin ba mafita bane bayan wani lokaci ta mike tsam ba tare da ta ga gefen da maryama ke zaune ba ta nufi dakin Alqaseem.

Tun shigowarshi dakin ya kwanta rigingine bisa couch dake gefen gadonshi hannunshi guda daya ya daura bisa kirjinsa, dayar kuma ya dafe goshi dashi, daga haduwarshi da yarinyar zuwa yanzu abubuwa dayawa sun sameshi, "anya zan iya?" ya tambayi kanshi,hakan ya yi dai dai da shigowar kira kan wayarshi, da kyar ya daga ya kara bisa kunnenshi ya lumshe idanu,daga daya bangaren Imran ya ce, "ango kasha kamshi ango baka laifi".

"Stop joking Imran, ina cikin damuwa matuka wallahi, anya zan iya kuwa? taya zan sanarwa Sameera wannan labarin, wallahil azeem bazan iya ba, kai kasan halinta, and babban tashin hankali na ma shine yarinyar, taya zan breaking mata news dinnan, taya zan sanar da ita an daura mata aure ba tare da izininta ba, taya zan sanar mata cewa yanzu matsayin matar aure take kuma matata..?"

"Qaseem kasan dai Modibboba ba zai aikata abun da ba dai dai ba, so ina ganin ka hadasu kawai ka sanar musu idan bomb din ya tashi lokaci daya shikenan.."

"Kai ina, imposs......" maganarshi ce ta katse sakamakon banko kofar da Sameera ta yi a cike da tashin hankali dan har wani irin kumfa bakinta ke fitarwa tana kallonshi ta ce, honey waye matar taka? 

Ai ni na sani dama, nasan dama kuna munafurtata ne, nasan babu yadda za'ayi ka dauko mace wai da sunan ka tsince ta a dubai, dama can akwai kulallaliyar da kuke kullawa" bisa mamakin Qaseem a hankali take maganar kamar ba samera ba, 

Dakata kiji sameee...Shiru yayi yana kallonta ganin ta fashe da dariya, dariya ta ke yi harda rike ciki kana hawaye yana sauka kan fuskarta, sameera! ya kira sunanta saidai bata amsa ba ta fita a guje hakan yasa ya mara mata baya shima a guje, ganin sun fito da gudu ne yasa Maryama dake zaune har lokacin mikewa itama zata gudu, amma taga fitt Sameera ta shige kitchen....