MATAR GIDA PAGE 32
MATAR GIDA 032
SHUUKRAN/022
P32
Inda ta saba ajiye abinci duk sanda ta kawo ta ajiye basket da take riƙe da shi daga haka ta yiwa Ɗalha sallama ta fita daga parlourn,bayan fitarta ta ne Ɗalha ya tashi ya buɗe wormer ɗin yaga dafaffen doya ne da miyar jajjage sai dafaffen kwai,sai ruwan lipto da aka cika cikin filas ɗin ruwan zafi ba tare da ɓata lokaci ba ya yi sarving kansa saboda sosai yake jin yunwa yanka biyar ya cire na doya da kwai biyu ya zuba ruwan lipto cikin kofi,zama ya yi nan ƙasan parlour ya fara cin abinci bayan ya gama ci ne ya ji wani irin bacci ya sauko masa lokaci guda,tashi ya yi ya nufi ɗakin Unaisa ya tarar har sannan bata tashi ba,shiga ɗakin ya yi ya fara tashinta,buɗe ido ta yi tana kallonsa cikin kwantar da murya ya ce ''tashi ki yi wanka ki ci abinci sha ɗaya ta yi'' banza Unaisa ta yi masa tare da gyara kwanciya ta cigaba da bacci Ɗalha bai hakura ya shiga kiran sunanta, sarai tana jinsa amma ta yi masa banza idanunta rufe kamar mai bacci,numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''pls ki daure ki tashi ki yi wanka babu kyau zama da najasa'' cikin muryar bacci Unaisa ta ce ''dan Allah ka ƙyale ni na ƙara hutawa da anjima zan tashi'' babu yadda ya iya haka ya ƙyaleta ya fita zuwa ɗakinsa bayan shigarsa ɗaki kwanciya ya yi saboda sosai yake jin bacci hakan yasa ba tare da ɓata lokaci bacci mai nauyi ya dauke shi,a can wajen Unaisa kowa karfe sha ɗaya da rabi taji yunwa na neman hallakata, gaba ɗaya ta nimi baccin ta rasa babu shiri ta tashi ta dauki doguwar rigar da ta yi sallah ɗazu ta zura kafin ta wuce bathroom ta surka ruwan ɗumi ta yi tsarki ta wanke jikinta daga haka ta fita daga ɗakin,bata tsaya ko ina ba sai parlour zama ta yi ta sarving kanta doya ba abincin ta bane hakan yasa ta ciri yanka uku kawai ta zuba miya sannan ta sawa kanta kwai biyu,ruwan lipto rabin kofi ta zuba kafin ta fara ci,bayan ta gama ci ne ta tashi ta wuce ɗaki ba tare da ta gyara wajen ba,plate ɗin da ta ci abinci da wanda Ɗalha ya yi amfani da shi duk ta bar su zube a parlour,kwanciya ta kuma yi tare da ɗaukar wayarta ta kunna data rabon da ta yi online tun jiya da dare ita da take kusan kwana tana chating da gari ya waye karfe tara ta sake hawa online amma yau ita ce har sha biyu bata yi online ba,daukar wayar ta yi bayan ta kunna data saƙonni sun fara shigowa murya can ƙasa ta ce ''to Allah..ya zan yi tun da na yi aure yanzu aiy hawa online barkatai ba nawa bane hidimar miji da gida ma ta ishe ni'' daga haka ta shiga group ɗinsu ta fara gaisawa da mutanen ciki,Unaisa ta dauki sama da awa guda tana chating kafin daga bisani bacci ya dauke ta
Karfe ɗaya da rabi na rana Ɗalha ya buɗe idonsa da ya masa nauyi,har sannan idonsa cike yake da bacci,a hankali ya sauke ƙafarsa ƙasa,miƙa ya yi tare da ambaton sunan Ubangiji daga haka ya shiga bathroom ya dauro alwala nan cikin ɗaki ya gabatar da sallar azahar bayan ya idar da sallah ya dauki a ƙalla mintina ashirin zauna yana tasbihi tare da addu'a kafin daga bisani ya shafe addu'a ya mike tsaye tare da linke darduma da ya yi sallah a kai,bayan ya gama linke darduma ne ya samu waje ya aje daga haka ya fita daga ɗakin zuwa ɗakin Unaisa,bakinsa dauke da sallama ya shigo ɗakin ganinta ya yi kwance kan gado hannuta riƙe da waya tana chating yadda ta buɗe kafafunta ta rufa jiki da bargo ta ƙure gudun AC haka ma fanka ɗakin ya dauke wani sanyi,ga labulaye ɗaki sake hakan yasa ɗakin yin duhu kaɗan harda yanzu ɗin rana ne,Ɗalha ya yi mata sallama a karo na biyu sai a sannan ta amsa sallamar har sannan hankalinta na kan wayarta waje Ɗalha ya samu ya zauna yana ƙare mata kallo yaga gaba ɗaya hankalinta bayan wajensa chating ɗinta kawai take ta na murmushi numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya jefo mata tambaya inda ya ce ''kin yi sallah?" idon Unaisa kan waya ta ce ''ban yi ba'' Ɗalha ya ce ''ya kamata ki tashi ki yi sallah yanzu karfe biyu ta wuce ta mintina biyar'' Unaisa ta gyara kwanciya ta ce ''ok zan tashi yanzu zan yi'' ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauki kafin ya ce ''ya kamata ki tashi yanzu sai ki ga an kira la'asar'' ba tare da kallon inda yake ba ta ce ''daman jiran la'asar nake da an kira sai na tashi na haɗa gaba ɗaya azahar da la'asar sai na huta'' dafe kai Ɗalha ya yi cikin zuciyarsa yana karanto innalillahi wa'ina'ilahi raji'un can dai ya mayar da dubansa gareta ya ce ''tara sallah babu kyau ki daure dai ki tashi yanzu ki yi sai ki huta kafin la'asar'' babu shiri Unaisa ta yunƙura ta tashi zaune tare da ajiye wayarta kan bed side drower kafin ta mayar da dubanta garesa ta fara magana cikin kakkausar murya ta ce ''a gaskiya kana takura min a gidan nan kana damuna na faɗa maka zan yi sallah amma ba yanzu ba sai la'asar,amma sai damuna ka ke,ni gaskiya ba zan yi sallah yanzu ba sai la'asar zan haɗa gaba ɗaya,haba saboda Allah na yi ta magana ɗaya kamar karatu'' ta ƙare magana tare da ɗaukar wayarta ta yi kwanciyarta ta cigaba da danna waya
Tashi Ɗalha ya yi daga inda yake zaune ya je kusa da ita ya tsaya tare da naɗa hannu a kirgi fuskarsa babu alamar wasa ya ce ''tashi ki je ki yi sallah'' yadda ya yi magana ba tare da wasa ba yasa Unaisa ta sa kwayar idonta cikin nasa ganin babu alamar wasa a fuskarsa ya sa ta nuna masa fuskar wayarta cikin kwantar da murya ta ce ''kalla ka gani karfe biyu harda minti sha biyar, nan da awa ɗaya da wasu ƴan mintina za'a fara kiran la'asar kaga sai na haɗa'' fuskar Ɗalha haɗe ya ce ''yanzu za ki yi'' bata sake cewa komai ba ta aje wayar hannunta kafin ta tashi ta wuce bathroom ta yi wankan tsarki bata fita daga bathroom ɗinba saida ta dauro alwala kafin ta fito daure da towel ta tarar da Ɗalha zaune cikin ɗakin yana danna waya,binta ya yi da kallo yana mamaki sai yanzu ta yi wanka tun karfe goma cikin zuciyarsa ya ce Allah ya kyauta,bai so yi mata magana ba amma ya ƙasa jure kawai ya ɗago ya kalleta ya ce ''tun safe ba ki yi wanka ba? me ya hana ki wanka tun ɗazu?'' Unaisa ta murguɗa masa baki ta ce ''to aiy yanzu na tashi daga bacci,daga tashi na kuma ka shigo'' murmushi ya yi kafin ya ce ''da kin tashi kinga lokacin sallah ta yi kamata ya yi ki yi maza ki yi wanka ki yi sallah,amma sai kika kwanta kina danna waya'' cike rashin kunya Unaisa ta ce ''to aiy laifin ka ne'' Ɗalha ya ce ''laifi na da na yi me?" cikin tsiwa ta ce ''da ka hana ni bacci daren jiya ka yi ta azabtar da ni har safe,ko ban yi sallah ba Allah bazai tambaye ni ba kai Allah zai kama ka da laifi ba ni ba,tunda ba da gangan na ƙi yin sallah ba,ba ni nasa kaina cikin halin da nake ba'' Ɗalha ya girgiza kai yana ƙara mamakin rashin ilimin Unaisa idonsa kanta ya ce ''Allah ba zai tambaye ni ba,abinda na yi ibadah ce kema kuma kina da lada saboda haka ki bar wannan zancen'' taɓe baki ta yi tare da ɗaukar doguwar rigar da ta cire ɗazu kafin ta shiga wanka,daukar rigar ta yi da niyyar sa Ɗalha da duk wani motsin ta yana kallonta ta gefen ido ya yi saurin mayar da dubansa gareta ya ce ''me kuma za ki yi da rigar?" ba tare da kallon inda ya ke zaune ba tana kokarin sa rigar ta ce ''sallah zan yi'' gyara zama Ɗalha ya yi fuskarsa dauke da mamaki ya ce ''a'a ba dai sallah za ki yi rigar nan ba,tun jiya ki ke yawo da wannan rigar da kin cire za ki dauki zani ki daura'' shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan mintina ya dafe kai can dai ya tashi ya nufi inda Unaisa ke tsaye tana binsa da kallo baki buɗe,ita har ga Allah bata ga abinda ya yiwa rigar ba babu inda ta tafi da rigar daga ɗaki sai parlour to ta ina rigar ya yi datti?anya kuwa Ɗalha baya da cutar tsafta inba mutum me cutar tsafta ba ya za'a yi ta kwana uku tana sa riga ɗaya kuma bata fita ko ina da rigar ba ya ce ya yi datti a'a da sake tana nan tsaye baki buɗe Ɗalha ya tako har inda take yazo daf da ita tare da dafe kafaɗunta ya kwantar da murya ya ce ''look ke fa amarya ce kamata ya yi ki yi ta ado da kwalliya kina sa turare ko yaushe ki zama cikin tsafta'' hannu yasa ya karɓi rigar yana linke kafin ya ce ''pls ki duba wani abu ki sa amma banda wannan pls'' jinsa kawai Unaisa ta yi amma ta sani baza taɓa daina sa rigar ba saboda tana jin daɗin rigar ko ƙadan babu takura a ciki,kallonsa ta yi taga yadda ya kafeta da ido kawai ta ce ''shikenan bazan sake sa ba'' daga haka ta nufi inda saif ɗinta yake ta buɗe ta dauki wani riga da sikit na atamfa ta sa,bayan ta gama shirya kanta cikin riga da sikit ɗin ta tayar da sallah,sai a sannan Ɗalha ya fita dakin zuwa nasa
SHUUKRAN