HALINSA!

Page 02

by @salmaahmadisah

HALINSA!
©SALMA AHMAD ISAH 
Page| 02
Haka Rahama ta ture komai ta zage ta ci gaba da shirin bikinta hankali kwance, Anti da abin ya ci gaba da damunta ta kasa hakuri ta sanarwa daya daga cikin ‘yan uwanta. Wadda ita ce ke bata shawarar cewa tun da mahaifin yarinya, danginsa da kuma ita kanta Rahaman sun amince da auren to fa ba ta da ta cewa, abu daya za ta mata, shi ne ta mata addu’ar dacewa a gidan aurenta, tun da ba a san rabon ‘ya’ya nawa ne a tsakaninsu ba. Kuma Antin sai ta yarda da hakan, ta danne zuciyarta ta ci gaba da dagewa da addu’a a kan lamarin ‘yar tata, tun da mijinta bai goya mata baya a kan batun ba waye zai yi?
Duk wani shagali da Rahama da kawayenta suka tsara a bikin nan sun yi, kama daga ledies party, kamu, har da su chuda da yini da suka kasance dama su na al’ada ne. Umar ya sakar musu kudi sun yi komai, duk kuwa da ba ayi da shi ba, a ranar Asabat aka daura aurenta da Umar, washe gari kuma bayan sun yi yini da yamma aka kawo motocin da za su tafi da amarya. Rahama ta sha kuka, duk dauriyar Anti sai da ta zubar mata da kwalla, haka ma Abbanta da ya kamata ace shi yake lallashi, abinka da ‘yar fari, kannenta ma ba a barsu a baya ba, sun sha kukan rabuwa da ‘yar uwarsu. Haka aka dauki amarya a mota har zuwa garin Ngurun Jahar Yobe. Da yake tafiyar dake tsakanin Nguru da Hadejia ba wani nisa ne da ita ba, nan da nan aka kaita suma suka dawo, tun da can din ma gida ne, kuma sun barta a hannun ‘yan uwata ne. magariba tana yi duk wanda suka zo gidan karbar amarya suka watse, aka barta ita kadai, saboda Umar ya kira yace ba ya so ya dawo ya tarar da kowa a gidan, za su iya tafiya abinsu, ya gode da hidima.
Tun da ta shigo gidan aka ajeta a cikin dakinta, ba ta daga kai ta kalli ko ina ba sai da suka fita suka barta tana jan zuciya, domin har zuwa lokacin kuka take, kamar yanda ta ji wanda suka kawota suna ta yaba gidan haka yake,dakin ya yi kyau sosai, musamman da ya samu gudunmawar kayan furnitures masu kyau ‘yan ya yi. Hakika mahaifinta ya yi kokari wurin yi mata kaya daidai gwagwado, a matsayinta na auren fari a gidansu. Tunawa da gida ya kara karya zuciyarta, ta sake kankame jikinta tana sharar hawaye, ba a fi minti biyar da tafiyar ‘yan uwanta ba ta ji dirin mota a compound din gidan, hakan ke nuna mata cewar Umar din ne ya karaso.
Kara shiga taitayinta ta yi, tun da aka fara bikin har aka gama ba ta sa shi idonta ba, ko lokacin da suka zo daurin aure a bakin mutane ta ji cewar ya zo gaisuwar iyaye, amma ba ta gan shi ba, kai idan z ata iya tunawa ma rabonta da shi tun bikinsu saura sati uku, kuma shi ne kadai haduwarsu tun da aka saka ranar aurensu. Sai kuma haduwar da suka yi a baya kafin ma maganar aure ta shiga tsakaninsu. Dan haka ita yanzu ba komai ta sani a kansa ba, ba wai a matsayinsa na dan uwanta ba, a matsayinsa na shi Umar wanda a yanzu yake amsa sunan mijinta, wanda take sa ran za su yi rayuwar da ba ta san karshenta ba. domin a yanda ta fahimci amfanin alakar soyayya kafin aure, ana yinta ne domin a san halayen juna, ko ba dika ba, a kalla mutum zai samu bakin cewa ya san abu kaza kan spouse dinsa. Amma su fa?... 
Kafin ta datse zaren tunanin da take sakawa ta ji kawai an bude kofar dakin da take ciki, kasanceear ta bawa kofar baya yasa ba ta iya kallonsa ba, sai takunsa da take ji, wanda ke sanar da ita cewar ga shi nan yana shigowa cikin dakin. Bai yi sallama ba, hakan ke nuna mata cewar yanda yake a wayar ma haka yake a zahiri, kafin ta sake wani tunani ya karaso inda take, kafin ta yi wani yunkuri har ya zauna kusa da ita, abin ya zo mata a bazata, sai ta dan matsa gefe kadan gabanta na faduwa, Umar ya bita da kallon mamaki.
“Ke! Miye haka?”
A karo na farko, ta karfafi kanta, sannan ta kai hannu ta janye mayafin dake rufe a kanta, ta kalli fuskarsa, zaune yake kusa da ita sosai, kusan da ta yanda ta haddace kammaninsa fiye da da. Kallon mamaki yake mata hade da bacin rai.
“Ba ki da lafiya ne?”
Tambayar da ya sake yi ce tasa ta sauke kanta da sauri tana goge idonta, sannan a hankali ta girgiza masa kai.
“To ki tara yadonki wuri daya, bana son shirme!”
Jiki a sanyaye ta gyada masa kai, tun dai ta riga ta karbi cewa haka halinsa yake. Ledar dake hannunsa ya aje kusa da kafafunta. 
“Ga shi kazar amarcinki ce, ki ci sai ki zo ki sameni a dakina!”
Yace, sannan ya mike tsaye yana baza babbar rigarsa, ya juya zai fita ta daga kanta ta bi shi da kallo, a cikin ranta ko tambayar kanta, yanzu da aka yi auren ma ba zai sauya yanda yake mata magana ba? sai da ya fita daga dakin, sannan ta tashi ta cire kayan jikinta, ta sake watsa ruwa, sannan ta sauya kaya zuwa PJ riga da wando masu tsayi ta saka turarr, sannan ta saka hijabi a samansu, kasanewar garin ana dan sanyi. Ta dawo jikin gadonta ta kalli ledojin da ya aje mata dasu, a ranta take cewa, dama ita kadai ya kamata ta ci ban da shi? har ta zauna a bakin gadonta za ta taba ledar, sai kuma wani tunani ya fado ranta, rashin kyautawa ne ta cinye ita daya ba tare da shi ba, kuma wannan ranar farin cikinsu ce tare da shi, dan haka bai kamata ta yi komai ita kadai ba. dan haka sai ta yanke shawarar daukan ledar ta fita daga dakinta, tsaye ta yi a falon tana kallon yanda ya hadu tun daga gininsa har zuwa kayan da ke ciki, kwalla ta ji tana shirin zubo mata, domin tunawa da gida, da kuma kokarin da iyayenta suka yi, kofa hudu ce a cikin falon, ba ta san wacce ce ta dakin nasa ba, dan haka ta fara da bude ta kusa da dakinta, ganin karamar katifa kawai shimfide a cikin dakin ya tabbatar da ba nan ba ne, ta nufi ta gaba, ta bude bakinta dauke da sallama, cikin sa’a kuwa sai ta ga nan din ne, kamar dakinta, shi ma wannan din si well furnished. Ganinsa zaune a bakin gadon, yayin da rigarsa babbar rigarsa da kuma hularsa aje a gefensa. Daga shi sai wandon shaddar kayan da kuma singlet, waya ce kare a kunnensa, kuma ko sallamar d ata yi ma bai amsa ba, karasawa cikin dakin ta yi, ta maida komar ta rufe, sannan ta soma takawa ciki a hankali. Ta dan tsaya daga gefe tana jiran ya gama wayar da ta lura ta kasuwanci ce, sai d aya gama wayar sannan ya kalleta.
“Ya za ki zo ki tsaya mini a ka Rahama?”
Da sauri ta dan matsa ta dan difana mazaunanta a bakin gadon tana ba shi hakuri, zaman data yi kamar ace kett! Ta fice da gudu, ya sake kare mata kallo, duk ta wani cikwui-kwuye a cikin dogon hijabinta.
“Fita za ki yi ne?” ta kalle shi da mamakin maganar. “Wannan hijabin fa?”
“Oh, sanyi nake ji”
Ya sake jifanta da wani kallo. Shiru babu wanda ya sake cewa komai, sai ta aje ledojin dake hannunta a kasa.
“Wannan fa?”
Ta sake kanta a hankali ta furta.
“Na ga kamar bai kamata na ci ni kadai ba ne”
Mikewa tsaye ya yi, sannan yace.
“Bana jin yunwa, za ki iya ci ke kadai!”
Ta bi shi da kallo har ya shige bayi. Ta sake kallon ledar, a ranta tana fadin ni ma ai ba yunwar nake ji ba, dan haka ba zan ci ba. tana zaune a bakin gadon har ya fito ba ta snai ko wanka ya yi oho, ta ma fi tunanin ko alwala ya yi, tana jiran ta ji ya ce ta zo su yi sallah, kawai sai ta ga mutum ya naimi bakin gado ya kwanta daga can bangaren yana fadin “Wayyo Allahna!” irin ya gaji din nan, ta soma bisan da kallon mamaki, domin shi ya gama shirin yin bacci abinsa.
“Ki cire hijabin nan Malam Rahama, ki zo mu kwanta!”
Baki sake tace.
“Ba za mu yi sallah ba fa!”
T fadi domin tuna masa, domin wata kila ya manta ne, amma ya za a yi ma yace ya manta da abu mai muhimmanci irin wanna?. Kansa ya dan daga daga kan pillow ya kalleta idonsa daya a kanne wanda yake nuna tsanain gajiyar da ya yi hade kuma da tambaya a fuskarsa.
“Sallahr me?”
Ba ta san daga ina wata irin faduwar gaba ta taso mata ba, amma ta jita har cikinta, mamaki ya kasheta, domin da gaskiyar cewa bai san wace sallah ba ce har a cikin muryarsa da kuma fuskarsa.
“Sallahr da fiyayyen hallita ya koyar da sabbin ma’aurata su yi a darensu na farko, ba ka sani ba?”
“Mts!”
Guntun tsaki ta ji ya ja, sannan ya sake juyi bisa gadon, ya kifa kansa a cikin pillown.
“Allah yasa ba dole be ce”
Idon Rahama ya ciko da kwalla, da gaske bai sani ba, ta fada a ranta, sannan ta yi kokarin hadiye kwallar dake kokawar zubo mata.
“Ba farilla ba ce, amma yana da kyau ace mun yi domin samun albarka a sabuwar rayuwar da za mu fara!”
“Ai shikenan tun da ba dole ba ce, da Allah Malama ki zo ki kwanta, na gaji wallahi!”
Wannan kwallar da take ta son shanyewa ta sakko mata, ta sa hannu ta shareta, cikin raunin murya tace.
“Dan Allah Ya Umar ka daure ta tashi mu yi sallahr nan, raka’a biyu ce, idan mun kammala sai mu yi addu’a”
wannan karon tsakin da ya ja mai tsayi ne.
“Me yasa kika cika gardama ne Rahama?”
Ya tashi zaune, ya kalleta.
“Dan Allah!”
Ta sake yi masa magiya cikin hawaye. Ba dan ya so ba sai dan magiyar da take ta yi masa, sannan ya tashi suka yi sallahr, addu’ar ma ita ta koya masa yanda zai yi, da abin da zai ce. Daga nan ya tashi ya kabe rigarsa ya koma kan gadon ya kwanta tare da fadin idan kin gama sai ki zo ki kwanta. Addu’o’inta ta yi. Ta jima zaune a wurin tana fadawa Allah, kan ya bata kafadun daukan wannan nauyi da ta daukowa kanta, ya bata damar iya sauya halin wannan bawa nasa. Jiki a sanyaye ta koma daya gefen gadon, ta kashe hasken dakin ta kwanta tana ta sauke ajiyar zuciya, can ta ji hannunsa na lalubenta a kan gadon, hakan ya tabbatar mata da ba bacci yake ba, yana yin nasarar lalubota ya janyota, sannan ya cire hijabin da tun dazu yake cewa ta cire shi, Rahama ta rufe idonta tana naiman sassauci daga wurin Allah kan halin da za ta fuskanta a wannan sabuwar rayuwar.
*
A hankali take sharar kwalla hade da jan zuciya, idanuwanta a rufe suke, kuma ba wai bacci take ba, idonta biyu, tana tuna kalar abin da ta fuskanta a cikin darenta na farko a gidan Umar ne. tunanin abubuwa da yawa sun cika mata kai, tambayoyi masu yawa suna yawo a cikin kanta, a yanda take jin labari a bakin kawayen ta da suka yi aure hakika wannan abin da farko sai cin wahala sannan akwai ciwo, amma ba ta san me yasa take jin ita nata ciwon ya fita da ban, domin a yanda ta ji ana wasa kafin komai ya faru, ita kuma hakan bai faru da ita ba, Umar just do it the way he want, bai damu da tana cikin ciwo ko azaba ba. kuma da komai ya lafa babu sannu ko guda daya. Yanzu ma tsakinsa ta ji ya tashi a cikin shirun dakin.
“wai ke a kan ki aka fara aure ne? da Allah malama ki mini shiru, kin hanani bacci, idan ke ba za ki yi baccin ba za ki iya tashi ki koma dakinki!”
Kukanta Rahama ta hadiye, ta koma yin na zuci, sai ruwan hawaye da yake sintiri a kuncinta, yanda ta ga rana haka ta ga dare, har asuba ta yi, ta dauka idan asuba ta yi zai tashi ya fita sallah, ita ma wata kila ta samu kwarin guiwar tashi ta gyaran jikinta, amma shiru! Sai sautin munsharinsa da ya cika dakin!. a hankali ta mika hannunta ta taba shi.
“Ya Umar!”
Shiru, ta sai da ta kira shi sau uku, sannan ya farka.
“Lokacin sallah ya yi!”
Tsaki ya ja mai tsayi, sannan ya sake juyi da fadin.
“Da safe zan yi!”
Hadiyewa komai ta yi, domin ya kamata ace batun rashin addininsa ya daina bata mamaki. Da kyar ta yi karfin halin tashi, sannan a daddafe ta koma dakinta, ta fada bayi, ta zauna a kasa, ta sha kukanta ta koshi, sannan ta samu ta yi wanka, ta taimaki kanta sosai, a nan ta san samu sauki, sannan ta fito ta yi sallah, ta zauna a kan dardumar, tana hawaye tana hadawa da addu’a. zuwa yanzu ta fahimci inda ta kawo kanta, kuma tana cikin halin ba gudu ba ja da baya, dole ta fuskanci wannan kaddarar da duk karfin da za ta iya, ta sani cewar Allah ba ya dorawa bawa abin da ba zai iya ba, dan haka ita ma za ta iya cin wannan jarabawar.
``````````
Wannan littafin paid book ne a kan 700, free pages ba su da yawa, dan haka tun yanzu za ku iya fara yin payment, ta wannan account no. din da zan rubuta a kasa.
5487270431
Salma Isah
Monie point