CHAPTER 14
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA SHA HUƊU
Sufyan da ke barci shi kansa sai da ya farka a birkice, da sauri ya fito ya je ɗakin, ganin Farida ya yi tsaye gaban madubu tana ta sa hannunta tana gogewa, ganin abu ɗaya madubin ke nuna mata yasa ta sa hannu ta shafa kanta, ta ji wayam, ta ƙara dawowa girarta ma ta ji wayam.
Sufyan tsayawa ya yi cikin mamaki yana pretending bai san me ya faru ba ya ce, “Kambala’i abun har ya girmama haka kenan, wata sabuwa.”
Sai kuma ya kunshe baki yana dariya ta gefe, yana juyawa ya fita, Farida ko tashi bata yi, duk ta rikice, komawa kan gadon tayi tana fatali da zanin gado da filillanka da tunanin ko zata ci arba da gashin amma babu ko alamunsa.
Idanunta ya kaɗa ya yi jajur, hawaye ya fara ambaliya a fuskarta domin yadda ta ga kanta ko ita ba ta so ci gaba da ganin fuskarta a hakan ba bare wasu kuma.
Ba shiri ta fice daga gidan da yake sai an fara wuce gidan Inno kafin nasu, hakan yasa ta faɗa can kawai, tana shiga ta yi a rikice Inno sallah kawai ta ga mutum gabanta, kasa karasa sallamar da zatai ta yi, hannu na rawa ta fara,
“Salam-salam.” Ta fada tana daga kanta.
Ganin fuskar Farida da ta yi gira a shamule yasa ta gagara ganeta da sauri. Inno ta tashi jiki da baki na ɓari ta ce,
“Wa innahu Sulaimanu wa innahu bismillahi, mutum ko Aljan na bade na barbade.”
Ta karasa maganar tana kankame jiki da bango.
Kara fashewa da kuka Farida ta yi tana matsawa gun Inno,
“Nice fa Inno, nice.”
Inno na ƙara matsawa tana,
“Ke wa? Husumammiya, ki rasa wa za ki bi kaf dangi sai ni.”
“Inno nice Farida, haka na tashi na ganni nima yanzu, wallahi nice.” Farida ta fada cikin muryar kuka.
Inno ta ce,
“Ki ji tsoron Ubangijin sammai da kassai, ki fada mini gaskiya, bani shiga sabgar husuma kuma bana fatan ta shiga sabgata, wace ce ke zaki ce mini wai Faridatu ce, ina ganin fuskar mutum tankwal kaman an maka tuwon teba kice mini Faridatu ce.”
Farida ta miƙa mata hannu tana,
“Allah Inno tabani kiji.”
A hankali Inno ta miko hannunta ta riketa, da ta tabbatar lallai Farida ce sai ta yi ajiyar zuciya tana,
“Amma ke ko kwai husumammiyar Ɗiya, cikin asubar fari ki baro mijinki mai ya faru?”
Zame hijabin da ke kanta Farida ta yi.
Inno na gani ta dafe kirji da hannu tana,
“Me zan gani? Miye wannan? Kar ki ce mini kin shiga kungiyar asiri Faridatu.”
Farida ta ce, “Aa Inno, haka na tashi na ganni yanzu, kuma ni babban abin da ya ɗaga mini hankali ma shine ban ga gashin ba fa, babu alamar gashin a ɗakin ma kwata-kwata.” Ta faɗa a raunane.
“Ah, shikenan. Ma’askin dare ma ya kawo miki ziyara, don wannan aikin nasa ne, ba na kowa ba. Kuma dole a tashi tsaye, domin kila gidan naku ya ɗan samu matsala. Gun mai magani zamu nufa yanzu, bara su dawo daga Sallah. Karɓi wayata nan, kira mini Haruna.”
Inno sawa Farida ta kira mata Baba Haruna da Baba Shuaibu da su Mama, da Goggo Hansai, har Sufyan ma aka yi masa kiran gaggawa.
Gabaɗaya hankulansu ya tashi, don ba su san me ke faruwa ba. Shi ko Sufyan, zuciyarsa ta dunga bugawa, don ya gama ɗauka cewa Farida ta zo ta sanar da cewa ya yi mata aski ne.
Sai da kowa ya taru kafin Inno ta yi gyaran murya ta kirawo Farida ke cikin ɗaki.
Ta ce, “Ku kalleta ku ƙara me ta kallo.”
Kowa idanunsa a kan Farida, mamaki suke ganin yadda lokaci guda yanayin kamanninta ya ƙara sauyawa.
Ta zame mata hijabin da ke kanta.
Salallami ne ya kaure a falon, ana kallon-kallo.
Har a lokacin gaban Sufyan bugun tara-tara yake.
Inno ta ce, “Ince dai duk kun ga abin da ya faru? To, ma’askin dare ne ya kawowa Farida farmaki a daren jiya, ya wuwusheta tas gashi nan har ya fara sauya mata kamanni.”
Ta yi shiru ta numfasa kafin ta ci gaba da faɗin, “Ni babbar damuwata nafi tunanin cikin da ke jikinta suke hari. Kamar na sani na je na sa aka fara yi mata rubutu, ashe abun babba ne, sai an tashi tsaye. Don haka wajen mai magani zamu nufa yanzu-yanzu, ba bata lokaci, ayi wa tufkar hanci.”
Numfasawa Sufyan ya yi yana hamdala a zuciyarsa, ganin cewa ya kaucewa faɗawa cikin tuhuma.
Kawu Hamza ya ce, “Lallai wannan ba abin wasa bane yoo, tunda suka fara dawo da ita kamar namiji a zahiri, a abaɗinin ma xasu iya aikatawa kuma su kwashe abin da ke cikin.”
Abba Shuaibu ya ɗaga kai yana kallon Sufyan ya ce, “Ni fa ban wani yarda da zancen ma’askin dare ba. Ko aljanu, nafi tunanin cewa wannan yaron ne ya yi mata wannan aika-aikar.”
Sai a lokacin hankalin Farida ya fara dawowa jikinta. Ita ma ta fara zargin ko abin da ta yi masa ne ya rama. Sai kuma ta tuna ai da shi ne, zata ga gashi ko ya yane akan gadon, kuma ma zata iya jin motsinsa.
Maganar da Inno ta yi ne ya katse mata tunani.
“Kamar ya Shuaibu? Ta yaya zai iya yi wa matarsa haka?”
Abba Shuaibu ya ce, “Zai iya mana, tunda damar ba son auren yake ba.”
Inno ta taɓe baki.
“Kai ko Shuaibu, akwai son tada husuma. Ta ina Sufyanu zai iya wannan aika-aikar? Ai sai aljannu. Batun ma bai son aure ai bai taso ba, tunda ya iya maka mata ciki.”
Caraf Goggo Hansai ta cafe maganar,”Sosai ma kuwa Inno ai cikin shine shedar ana zaman so da kauna.”
Inno ta ce,” Ahto Wannan zancen ya kau, dama can munafurci ne. Kuma ma Faridatu, ina ce mini ki kai baki ga ko gashin ba da kika tashi?”
Farida ta girgiza kai.
Inno ma girgiza kai ta yi tana cewa, “Yoo, to ka ji dai. Sune kaɗai ai suke hakan, suna cire wa mutum gashi a jiki take suke cinyewa. Don haka ni na kiraku ne in shaida muku cewa a tura malamai ayi sauka a ɗakin nan, sannan yanzu zamu nufi wajen mai magani, kuma kai Sufyanu da kai zamu tafi saboda kaima a bincikaka.”
Ta ƙarasa maganar tana kallonsa.
Goggo Hansai ta ce, “Ai kuwa kinga ma sai mu je wajen Malam Iro abokin aljan na can Yalwa.”
Inno ta amsa da, “Tabbas kuwa Hansai, lamarin ai sai shi dama ku tashi mu je.”
Duk zancen nan da ake, Baba Haruna bai ce uffan ba. Tashi ya yi shi ma yana faɗin, “Allah ya kyauta,” ya fice.
Sufyan ba dama zillewa haka ya ɗauko motarsa zai kai su. Bayan Farida ta je zata zauna da su Inno, Inno ta kore ta tana cewa,
“Ni fa wannan munahincin naku ne bana so. Ki wuce ki je ki zauna gefen mijinki. Al’amuran banza kawai. Yoo, soyayyar nan ai ita ce rayuwa, wa zai hana ku yi ku morewa ranku fa.”
Goggo Hansai ta amsa da, “Ahto, sai su ta wani kumbiya-kumbiya.”
Haka ta je ta zauna gefen Sufyan a cikin motar. yana yi mata wani munafikin murmushi, ita kuwa haɗa rai ta yi tana galla masa harara.
Suna isa ƙauyen Yalwa, suka shiga wajen Iro, abokin Aljan.
Yana ganin Farida ya ce, “Wanga ɗiya ce mara lahani ko?”
Inno ta ce, “E, Malam, har ka ganeta ashe.”
Ya karkace yana faɗin, “Yoo, mu da mun sansu, sun sanmu ai. Daga shigowarta na gane, kuma idanunta ma kaɗai abun tuhuma ne. Amma dai fara faɗo mini damuwarki, ɗiyar nan.”
Farida ta rattaba masa komai da ya faru.
Ya tambaya, “Waye mijinta?” Aka nuna Sufyan.
Ya girgiza kai irin ya girmama lamarin nan kafin ya gyara zama yana faɗin, “Tabbas sune suka yashe miki gashin kai da gira, kuma lallai abun da yasa su yi miki hakan shi ne suna kishi da ke. Ma’ana, wannan ƙaramin balaraben mijin naki suke so, saboda sam ko daga ido ma ai baki dace da shi ba. Yoo, ba don an faɗa mini ba, ce nake daban ya zo shi akwai yiwuwar su zo a sigar sa ma su yi wannan barnar.”
Daga kai Sufyan ya yi yana kallon Iro abokin Aljan, domin kallon da yake yi masa kamar ya san gaskiya.
Inno da Hansai suka girgiza kai a tare. Inno ta ce, “To yanzu ya kenan, Malam?”
“Ah, babu damuwa fa. Ai mun saba caskalewa da su. Za a haɗa mata magunguna ne na wanka da na sha. Ta kiyaye ta bi su ba tare da wasa ba. Ina tabbatar muku da cewa zasu kauce su bar ta. Shi ma ɗin kuma za a ba shi magani, domin suna nan birjik suna bibiyarsa.”
Inno ta taɓe baki.
“Haba, ko da na ji, ai ni nasan lamarin nan da hannunsu ne dumu-dumu ciki.”
Haka ya tara musu wasu kayan itace da ganye. Da aka tambayi kuɗin sadaka sai ya ce dubu ɗari.
Jiki na ɓari Inno ta ce Sufyan ya bayar.
Sufyan ya kalle shi ya ce, “Hamsin za a bayar. In za ka karɓa, ka karɓa.”
Iro, Abokin Aljan, ya zaro ƙananan idanunsa yana kallon Sufyan.
“Kai ɗan nan, ahir ɗinka! Kuɗin sadaka ne, ba na wani abu ba. Kuma aikinku babba ne, musamman kai. Kwana zan yi ina yi maka addu’a kala-kala, yo kai da aka yiwa lulluɓan bargo ma ka kawo wargi sai a yaye.”
Inno ta ce, “Kai ko Sufyanu, ka bayar mana. Ai lafiyarku ta fi mana komai.”
Sufyan ya ce, “Inno, to ku je kawai. Zan sallame shi.”
Su Inno na fita, Sufyan ya ce,
“Me kake nufi ne?”
Iro Abokin Aljan ya buɗe Idanunsa yana kallon Sufyan ya ce,”Ka ganni nan? To kar nake kallonka, kawai na bullo musu da hakan ne domin a zauna lafiya, wannan aikin ba na aljan bane naka ne.”
Kifi-kifi da idanu Sufyan ya yi. Zufah ta keto masa.
Ya ce, “To yanzu ni dai Don Allah karka tona mini asiri ni zan iya kara maka ma.”
Iro Abokin Aljan ya sheke da dariyar mugunta, “Da ka ce baka ji Ɗan nan, ajiye ka fice min da gani.”
Ajiye masa kuɗin Sufyan ya yi har zai fita Iro Abokin Aljan ya dakatar da shi, “Amma fa ka yi a hankali da ita akwai boyayyun lamura a tattare da ita, kasancewarta hakan akwai abun da Allah ke nufi.”
Sufyan ya ce, “Kamar me kenan?”
Dariya Malam Iro ya yi ya ce, “Nima ban sani ba, sai anjima ko.” Ya karasa maganar yana juyawa.
ficewa Sufyan ya yi yana hamdala aransa da asirinsa bai tonu ba. Don ba karamin taimako Iro Abokin Aljan ya yi masa, hakan ganin bayanansa ma wasu kariyane da zasu sa ba za a yi tunanin tuhumarsa ba.
Ganin ya kulle hanyar da zata janyo a zarge shi, hakan yasa ya ji daɗi sosai a ransa.
Suna cikin mota zasu koma gida, karar saƙo ne ya shigo wayar Farida.
WhatsApp ta buɗe, ta ga hoto ne Sufyan ya tura mata, hannunsa ɗauke da almakashi da reza a kanta. Tare da caption din,
“Biyan bashin da kika ci ne.”