Page 10.
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*Zeey Kumurya*
10.
BRIGHT PENS 2026
YOTA ID 003
Bismillahir rahmanir rahim.
Zuba wa Ahayan ido Umma ta yi ta ce. "Ban gane ba? Me ya same ta? Ya na ga kamar ba ta motsi?" A rikice Rauda ta ce. "Ba ta yi Umma, kina kallon fa yadda Aunty Laure ta yi cilli da ita?" Yunƙurawa Umma ta yi har tana ƙoƙarin kifawa, a ɗimauce ta ce. "Na shiga uku! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Allah kar kasa yarinyar nan ta mutu! Allah ka tashi kafaɗunta." Miƙewa Ummi ta yi ta matsar da jakunkunan islamiyyarsu gefe tana faɗin. "Zama bai gan mu ba, ba tattaɓa ta za ku tsaya yi ba, ku kama ta mu kai ta asibiti da wannan kuɗin da aka ba mu." Adibibice Umma ta ce. "Na rikice ma ni, Yar Amana ce fa yarinyar nan, idan ta mutu ban san ya zan yi ba." Raudah da ke bin su da kallon mamakin da ma suna son Ahayan ɗin sun damu da ita har haka amma suke yi mata wannan cin kashin ta rafka tagumi, ita kanta ba ta taɓa zaton akwai watarana da abu makamancin wannan zai samu Ahayan ta damu ba.
Ranga-ranga suka fito da ita daga ɗaki, tsabar ruɗewa Umma ba ta saka hijabi ba akai kawai ta rufa shi, takalmi ma ba don Ummi ta lura ba wari da wari ta so sakawa. Raudah ta riga su fita don taro mai napep, a tsakar suka ci karo da Inno, turus ta tsaya ta bi su da kallo a sheƙe.
"Mene haka? Ina za ku kai ta?"
"Ba ta da lafiya ne, asibiti za mu je?"
Umma ta ba ta amsa.
Ƙugu Inno ta riƙe ta ce. "Ba shakka, sannu mai ƴa, to ga wanke-wanke can na tara shi ina jiran ta ta yi mini kafin Magriba, tunda ba ta da lafiya ai sai ɗaya a cikinku ta zauna ta fanshe ta, ta yi, da za ku ɗaɗe ku bar gidan saboda kawai wannan ƙasƙantacciyar ba ta da lafiya? Yarinyar da har yau ba mu san ubanta ba, ba mu san kowa nata ba, ba mu san asalinta ba." Yamutsa fuska Ummi da nauyi ya fara sagarwa kafaɗa ta yi, ji take kamar ta mangare Inno su bi ta kanta su wuce tsabar takaici.
"Ki yi haƙuri, za mu tafi mu biyu sai Raudah ta zauna ta yi miki."
"Ya fi dai, to kuma ba ki tambaye yi Yayan ba za ki fice? Ko zaman kanki kike ne ban da labar..."
Ƙamshin turaren da ta ji da takun tafiya ya saka ta haɗiye sauran maganarta ba shiri. Abba Adam ne cikin tafiyarsa mai kama da ta sarakai, yana sanye cikin ƙananan kaya kamar kodayaushe, idanunsa da suka rine suka yi ja ya fara cilla musu. Kai Inno ta fara sosawa cikin yaƙe ta ce. "Ƙanina, ka dawo? Sannu da zuwa." Bai amsa ba sai Ahayan da ya zubawa ido.
"Me ya same ta?"
Ummi ce ta yi caraf ta ce. "Aunty Laure ce ta dake ta ta yi cilla da ita kanta ya bugu da ƙofa, shikenan ta daina motsi."
Hanya ya ba su don su wuce, da sauri suka shige don a zaƙe suke da ma, har sun kai soro suka ji yana faɗin. "Ku shiga motata." Hangame baki Inno ta yi amma ba ta ce komai ba, wani kallo ya yi mata ya ce. "Ki kira ƴarki, ki shaida mata duk abin da ya biyo baya ta shirya ɗauka." Daga haka ya fice ya bar ta da baki a sake cikin tsananin al'ajabi, yana nufin wata banzar bare ta fi jininsa kenan?" A fili ta furta. "Mijinta ma kaɗai ya ishe ka, ban da lalacewa wata can za ka bi baya ka bar ƴar yayarka uwa ɗaya uba ɗaya? Sai ka ce ita ka san abin da ta yi mata" Ta ja ƙwafa tare da faɗin. "Ke kuma azaƙwaiƙwai uwar magana za ki dawo ki same ni ne, sai na haɗa miki jini da majina na ga mai ƙwatar ki." Daga haka ta nufi ɗakinta cikin ƙunar zucin ɗaukar su da Abba Adam ya yi a motarsa, motar da ko ita ba ta taɓa shigar ta ba.
Suna tafiya Umma na kwarara masa godiya, shi dai bai tanka mata ba har suka ƙarasa wani private hospital, Raudah ba ta samu napep ba har suka haɗu da ita a titi suka ɗauke ta.
Da sauri aka karɓi Ahayan aka shige da ita, bayan tsahon wasu mintina Likitan ya fito ya kira su office ɗinsa, ya yi musu bayanin abin da ya samu Ahayan da yadda suka shawo kan matsalar, ya ba su list na magungunan da za a siyo mata, Abba Adam ne ya karɓa ya biya kuɗin komai sannan ya tafi.
Suna shiga ɗakin da Ahayan take Umma ta saki ajiyar zuciya, ta ƙarasa gaban gadon da sauri ta kama hannunta ɗaya, a sanyaye ta ce. "Allah ya ba ki lafiya." Ummi ta amsa da Amin tare da faɗin. "Ashe kina son ta har haka Umma? Ban taɓa zaton za ki yi irin wannan gigitar ba don Ahayan ba ta da lafiya." Girgiza kai umma ta yi ta ce. "Uhm, ba za ki gane ba Ummi." Jiki a mace Raudah ta ce. "Ni dai daga yau ba zan ƙara yi mata wani rashin mutunci ba, don da ta mutu ban san inda zan gan ta na nemi yafiyarta ba." Idanun Ummi akan drip ɗin da aka saka wa Ahayan ta ce. "Allah dai ya sa mu dace, mun baro Sabira ita kaɗai a gida, kar ta dawo ta yi ta kuka." Umma ta ce. "Komawa za ku yi ai tunda sun ce ba yau za su sallame mu ba ku haɗo mana abubuwan amfani da za mu buƙata, sannan ku samu waya ku kira Babanku ku sanar masa." Amsa mata suka yi zuciyoyinsu cike da tausayin Ahayan da take ta sharar bacci.
****** ******
Duk da Sauban bai kwanta da wuri ba amma haka ya tashi da sassafe saboda suna da meeting a gurin aiki, ba san zuwa yake yi ba, don dai Dad ya matsa masa ne. Yana ɓaɓɓata rai ya fito daga part ɗinsa ya nufi part ɗin Dad. Lokacin Mom tana zuba masa abincin breakfast, shi kuma yana ta waya akan sabgoginsu na siyasa.
Sallama ba ɗabi'arsa ba ce musamman a gidansu, amma ganin Dad ya saka ya yi ta ciki-ciki, a tare suka amsa masa, Dad ya ci gaba da maganar da yake yi yana bin shi da kallo. Bayan ya gama wayar ya dube shi a tsume ya ce. "Sauban!" Baki ya tura gaba kamar ƙaramin yaro ya ɗago ya kalle shi, don daga yadda ya kira sunansa ya san faɗa ne zai biyo baya.
"Mene ne wannan a kanka?" Dad ya faɗa a tsawace sannan ya juyar da kallon shi ga Mommy ya ce. "Hajara kina kallon yaron nan da wannan banzan askin amma kika bar shi?" Ɓata fuska ta yi ta ce. "Haba Excellency, mene ne a cikin wannan askin? Zamani ne fa ya zo da shi, please ka bar yaron nan ya yi rayuwarsa yadda yake so don Allah." Rausayar da kai Sauban ya yi yana jin ƙaunar Mom na ƙara mamaye zuciyarsa, a kufule Dad ya ce. "To ba a gidana ba, ba zai yiwu muna faɗi tashi da ƙoƙarin inganta rayuwar al'umma a kullum musamman matasa amma ni nawa ɗan yana abin da ya ga dama ba, ka je ka aske shi tas, kar na sake ganin ka da shi." Wani irin waro ido Sauban ya yi, kamar zai yi kuka ya ce. "Dad jiya-jiya fa na yi, please ka bari ko five days ne ya yi mana."
"Ba zan bari ba, wallahi Sauban zan saɓar maka, wato har yanzu ba ka daina ire-iren wannan rashin jin ba ko?"
Da sauri Mom ta ce. "Alhaji!" Hannu ya ɗaga mata, hakan ya sa ta haɗiye sauran maganarta. Ya dubi Sauban fuska a tsuke ya ce. "Tashi ka bari guri!" Miƙewa ya yi yana kumbure-kumbure. Mom ta ce. "Sorry Son, me kake so na zuba maka ka ci?" Kai ya girgiza yana cika da batsewa. Girgiza kai Dad ya yi ya ce. "Ka dai yi azkar ɗin safe ko?" Bai yi ba amma haka ya ɗaga masa kai.
"To zauna ka karya, sai ka tafi office ɗin, M.D ya ce mini 8:30 za ku shiga meeting ɗin, kar ka yi late please kamar yadda ka saba."
Kai ya gyaɗa masa ya zauna suka karya tare, Mommy kamar za ta ba shi a baki ko ta mayar da shi ciki don ƙauna, shi kuma sai ɗage hanci yake a dole Dad ya ɓata masa rai. Ya riga su tashi bayan ya jaddada wa Mommy maganar mai aikinsa, ta ce yau in sha Allah za a kawo. Sallama ya yi musu ya tafi, har ya kai bakin ƙofa Dad ya ce. "Kar ka manta da addu'ar fita daga gida." Bai juyo ba ya amsa masa tare da barin parlourn.
"My Senator gaskiya kana takurawa yarona." Mom ta faɗa da iya gaskiyarta.
"Ba takura ba ce Dr, kula ce kawai da kiyaye haƙƙin da Allah ya ɗora mana a kansu, shi kaɗai Allah ya ba ni ɗa namiji, kuma a zamanin nan da muke a yanzu maza sun fi wuyar tarbiyyanyarwa, shi ya sa nake saka masa ido sosai don ganin bai kauce hanya ba."
Kai kawai Mom ta jinjina ba don bayanin nasa ya wani shige ta ba, don ita lokuta da dama yadda mijin nata yake abu kamar bai waye ba mamaki yake ba ta, abokansa duk ba sa irin wannan abubuwan akan iyalansu, barin ƴaƴansu suke su wataya son ransu a duk ƙasashen da suke so, amma shi ya ƙi ya dunkume mata ƴaƴa duka a gida, karatu ne kaɗai ya bar su duk suka yi a a waje.
Duk da jiya da daddare Dad ya dawo amma da safen nan ya kuma yi mata sallama ya koma, da ma ya zo duba su ne kawai kamar yadda yake yi duk lokacin da ya samu faraga tunda ita ta ƙi bin shi su zauna tare a can ɗin.
Bayan ta raka shi ta koma part ɗinta ta zauna a parlour ta ɗauki wayarta ta kara a kunnenta, ringing uku aka ɗaga tare da sallama.
"Sai a yi ta kiran ku ƙi ɗagawa akan kari, kin san abubuwan da na bari na kira ki kuwa?"
Ta faɗa cikin izza ba tare da ta amsa sallamar ba.
Daga cikin wayar matar ta ce. "Ki yi haƙuri Hajiya, ina waje ina aiki ne shi ya sa." Tsaki Mommy ta ja ta ce. "An samu mai aikin?" Ta ce. "A'a ana lalubawa dai, za a samu in sha Allah."
"Amma dai na faɗa miki sauri ake ko? Idan ba za ta samu ba na nema a wani gurin."
"Za a samu Hajiya in sha Allah, anjima za ki ji ni da yardar Allah."
"To kin dai riƙe irin wadda na ce miki ko? Bana son yaran ƙauyen nan masu ɓaki kamar suna wanka da kwalta, su zo su yi ta ɗumame wa mutum gida da warin ƙashi, yarinya za ki samu tashin birni, wadda ba su da ƙarfi suke neman abun yi, irisu ya fi so."
Da azarɓaɓi matar ta ce. "Tom shikenan Hajiya in sha Allah, za a samu irinsu ba ɗaya ba ma sai ki zaɓi wadda za ta yi a cikinsu."
"Ya fi dai." Mommy ta faɗa tare da katse wayar don kira sai shigowa mata yake yi.
***** *****
Washegarin da Amare da angwaye suka tare Saudat ta ci burin more baccin safe, amma tana cikin bacci Mama ta ɗaka mata duka.
"Tashi ki kimtsa ki kai wa su Zubair abincin kari, ga aiki bajaja a gida amma kin zo kin ƙule a cikin bargo."
Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune tana karanto addu'ar tashi daga bacci, ta ji daɗin bacci sosai don kanta ya yi mata wasai, wayarta ta lalubo ta duba lokaci ta ga har tara ta wuce.
Wanka ta fara yi haɗe da alwala ta fito ta shirya, duk yadda Mama take azalzalar ta amma sai da ta yi sallar walaha sannan ta fito, don ta san ko ta dawo bai zama lallai aikin da Mama ta ce yana jiran ta ya bari ta samu lokacin yi ba.
Bayan ta karɓi kayan abincin ta fice, a bayan layinsu gidan Zubair ɗin yake, shi ya sa take takawa da ƙafarta, ta zo daidai kwanar gidan motar Sauban ta taho a fafare kamar yadda ya saba, rikicewa ta yi ta rasa ina ma za ta yi don motar ta zo daf da ita, wawan burki ya ja a fusace tare da sauke glass ɗin motar ya zabga mata wani mugun kallo. Numfashin da ta maƙale ta sauke a hankali tare da sakin ajiyar zuciya, don ta gama saddaƙarwa sai motar ta buge ta, kallon mamaki ta yi masa, don shi ne ya taho ba bisa ƙa'ida ba amma ya tare mata hanya ya yi shiru kamar mai jiran ta ba shi haƙuri.
"Idiot." Ya faɗa tare da jan tsaki ya mayar da glass ɗin ya zuge.
Dole sai da ya jira ta wuce sannan ya tayar da motar ya ci gaba da tafiya bayan ya bule ta da ƙura.
Murmushin takaici Saudat ta yi, ba yau ta saba karɓar cin mutunci daga gurin al'umma ba, amma idiot ɗin da ya kira ta alhalin shi ne ba shi da gaskiya ya ɓata mata rai ya kuma ba ta mamaki, duk da ba abin mamaki ba ne fuskantar haka daga gurin ƴaƴan masu da shi, don motarsa da kamanninsa da shigarsa sun tabbatar mata ba ƙaramin ɗan hamshaƙai ba ne.
Ta daɗe tana buga gate ɗin gidan kafin Yaya Zubair ya zo ya buɗe mata daga shi sai singlet de gajeren wando. Ƙasa ta yi da kanta ta ce. "Ina kwana yaya? Ga breakfast in ji Mama." Ba yabo ba fallasa ya ce. "Wuce ki kai ciki." Ta saka kai ta shiga shi kuma ya mayar da ƙofar ya rufe.
A parlour ta tsaya tana ƙare masa kallo don jiya ba ta samu ta zo ba, tun kafin bikin su Yaya Mardiyya suke ta sintirin ganin gidan amma ita ba ta taɓa zuwa ba. Ganin ba kowa ta yi wa kanta mazauni tana yaba haɗuwar gidan da kayan da aka zuba wa amaryar a cikin ranta.
"Babe, waye ne da sassafen nan?"
Amaryar Yaya Zubair ta faɗa tana fitowa daga ɗaki, daga ita sai wata bingilar rigar bacci iya gwiwa, kanta babu ɗankwali.
Murmushi Saudat ta yi mata ta gaishe ta duk da ba za ta fi sa'ar Salma ba.
Wani banzan kallo ta yi mata tare da yatsine fuska ta amsa a wulaƙance. A lokacin Zubair ya dawo parloun, ta dube shi ta ce. "Wannan kuma daga ina?" Ya ce. "Ƙanwata ce, ba ki gane ta ba?" Ɗan jim ta yi ta ce. "Oh! Saude ko?" Ya ce. "E, Mama ce ta aiko ta ta kawo mana breakfast." Baki ta taɓe ta ce. "To ta cire tsumman jikinta ta gyara mana gidan, da ma ina ta tunanin yadda za a yi tunda Mommy ta ce sai an kwana biyu Mai aikina za ta zo." Hannunta ya kama ya ce. "Tom dear, yadda kika ce ai haka za a yi, sai ta dinga zuwa tana gyarawa kullum kafin mai aikin ta zo."
"Hakan ya yi, amma safe da yamma za ta na zuwa, because zan dinga baƙi na san za a dinga tara wanke-wanke sosai, ni kuma bana son kwana da dirty ko abu mai datti a gidan."
"An gama your Highness." Ya faɗa tare da kissing hannunta yana murmushi.
Ƙamewa kawai Saudat ta yi tana bin su da ido cikin al'ajabi, ganin suna ƙoƙarin shagala kamar sun manta da ita a gurin ta yi gyaran murya ta ce. "Zan koma gida Yaya."
Ashar ya danna mata ya ce. "Ba ki ji me ta ce ba ne? Ki cire hijab ki gyara mata gida, bana son wannan gidadancin naki fa, za ki ce wani za ki tafi a'a iska za ki bi, dalla Malama tashi!" Ya ƙarashe maganar yana buga mata tsawa. Ba ta kuma magana ba ta miƙe ta nufi inda take tunanin kitchen ne zuciyarta a ƙuntace.
Sai da ta gyara musu ko'ina Amarya na commanding ɗinta kamar wata uwarta, ga shi sai taɓara suke zubawa a gabanta, wadda Saudat ta fuskanci da gayya take yi, su suke yi amma ita suke bari da jin kunya, ga Yaya Zubair sai hantarar ta yake yi. Tana share hawayen baƙinciki ta baro gidan, bayan ta ƙudirce a ranta komai zai faru ba za ta ƙara zuwa ba, ta gaji, ta fara gazawa da ɗaukar wannan cin kashin da kowa yake yi mata.
A ƙofar gidansu ta tarar da mota a ajiye, ta zagaye ta, ta shige don ta tare hanya. Sai da ta tsaya a soro ta goge fuskarta sosai sannan ta ƙarasa ciki, direct bedroom ɗin Mama ta nufa, ta yi sa'a ita kaɗai ce a ciki tana waya, a gaban gadon da take kishingiɗe ta tsugunna tana ƙoƙarin danne kukan da yake son ƙwace mata. Bayan Mama ta gama wayar ta dube ta rai a ɓace ta ce. "Gidan uba kika tsaya da sai yanzu za ki dawo?" Ba ta ba ta amsa ba sai hannayenta da ta haɗe guri guda alamar roƙo, idonta na shatatar hawayen da ta kasa tsayarwa ta fara magana muryarta na rawa. "Don Allah Mama idan wani laifin na yi miki ki yi haƙuri ki yafe mini ki daina treating ɗina kamar ba ƴarki ba, ina son na ga muna hira cikin raha kamar yadda kuke yi da sauran ƴan'uwana, ina son ki dinga saka mini albarka kamar yadda kike saka musu, ina son mu dinga rayuwa mai cike da nishaɗi irin ta kowacce uwa da ɗanta, mene ne laifina don na zo a mummuna da za ki yi mini irin wannan tsanar, tsanar da ƴan'uwana suka gani a gurinki suka ɗora daga inda kika tsaya, a baya na ɗauka abin na ƙare ne, amma yanzu na ga kullum gaba yake yi, ku ku yi mini, mutanen gari su yi mini, sabbin shigowa rayuwarmu ma su yi mini, ya kuke so na yi? Rai da zuciya ne fa a jikina kamar kowa? Ina jin ba daɗi ina shiga damuwa, idan ban samu farinciki a gurinku ba a gurin wa zan samu? Ina kuke so na saka kaina na ji sanyi? Na ɗauka zan iya jurewa amma na ji na kasa, don Allah don girman Allah Mama ki sassauta mini, farincikin kowanne ɗa yana tattare da kulawar mahaifiya, ina tsoron gaba na yi aure ƴaƴana da mijina su gane ba ni da wata ƙima da daraja a cikin ahalina! Ki tuna Allan da ya yi ni shi ya so ya gan ni a haka, shi ya halatto ni a mara son rayuwar ƙawa da gayu, to mene ne laifina da na cancanci haka?" Ta ƙarashe maganar da wani irin kuka, jikinta har rawa yake.
Duk kafaffiyar zuciyar Mama amma sai da jikinta ya yi sanyi, ta yi shiru kawai tana kallon ta. Ba yabo ba fallasa ta ce. "Shikenan share hawayen, ki je falon baƙi kina da baƙo, idan kin dawo ma yi magana." Cak kukan da take yi ya tsaya, ta waro da idanunta da suka rine saboda kuka ta ce. "Baƙo kuma?"
"E, maza je ki wanke fuskarki yana ta jiran ki tun ɗazu."
Za ta kuma magana Mama ta katse ta da faɗin. "Ya ce yana sauri ki tafi kawai, ko mene idan kika dawo za mu tattauna, ki canza kayan jikinki ki saka mayafin da kika yi fitar biki da shi, ki saka turare ki gyara fuskarki." Kai kawai ta gyaɗa mata cikin mamaki gami da wani yanayi da ba za ta iya fassara shi kai tsaye ba.
***** *****
Tun Zeenat tana kallon falon da marmari har zaman ya fara gundurar ta, ta fara mamakin rashin dawowar Sita har wannan lokaci, agogon wayarta ta duba ta ga har shaɗaya na dare ta gota, tunanin ko ba lafiya ba ta fara yi, ta miƙe da zummar sauka ƙasa ta gano sai ta ji wata irin ƙara shuuuu mai saukar da razani kamar ana feshin wani abu, tsabar firgici ji ta yi kamar girgiza falon yake yi, a zabure ta fara kalle-kalle cikin tsurewa jin sautin yana ƙara yawaita, hasken falon ne ya fara raguwa da kaɗan-kaɗan, a hankali ta ga wani gefe na falon ya ɗaga gurin ya wawake, ba ta san gidan ƙasa ba, ba taɓa ganin shi ba ko a fina-finai, hakan ya sa ta ɗimauce ta saki wayar hannunta tare da ƙwalla ƙara, ganin mutum dogo ya fito ta gurin cikin baƙaƙen ƙananun kaya fuskarsa sanye da marks ya sa ta ji kamar fitsari na neman zubo mata, ja baya ta fara yi ilahirin jikinta na kyarma, wani irin tsoro ne ya ƙara lulluɓe ta.
"Na shiga uku! Ina mutumin nan ya kawo ni? Ina ne nan? Wane ne kai? Don Allah kar ka cutar da ni!"
Tunkarar ta kawai mutumin ya ci gaba da yi ita kuma tana ƙara yin baya har ta kai ƙarshen ɗakin, miƙa hannu kawai ya yi ya damƙo ta, ya shaƙa mata wani abu da ba ta san ko mene ba a fuska. Fitsarin da ya cika mata mara ta saki tare sakin gigitaccen kuka ta zube a gurin, warin abun ya saka ta fara jujjuya kanta tare da bubbuga goshinta da hannunta, so take ta yi magana amma ta kasa, ta ɗaga idanunta da ƙyar ta dubi mutumin da ke tsaye ƙyam a kanta ya zuba mata idanunsa masu ban tsoro, daga nan ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba.
*#Zeey Kumurya*
*#****