SOYAYYAR ZUCI

Chapter 15&16

by @deeyamerh10

πŸ’–πŸ’– SOYAYYAR ZUCI πŸ’–πŸ’– 
    (Love and Romantic story)
    Written 
 By
 Deeyamerh
07070647269
Page 15&16
Sosai Rabi'ah take ganin makirci kala kala,har sharri sai da Asiya ta kulla mata wai tana neman Sabeer,wanna abu yata da tarzoma ba kadan ba dan da kan sa Alhaji yasa aka kira masa Sabeer ya tambaye shi,shi kuwa a lokacin da aka tambaye shi sai cewa yayi a'a dan shi ko zaman gidan yanzu bai fiya ba,bare har wani abu ya shiga tsakanin su da ita,sai dai ita Asiyar dan tasha ne mansa yana ki shine tai masa wanna sharri.
Sosai Alhaji yaji dadi akan wannan batu da Sabeer yayi,inda ya rinka shi masa albarka akan fadan gaskiyar da yayi domin yasan Rabi'ah bazatai abinda aka ce ba.
Shi kuwa abinda yasa Sabeer yayi wa Asiya haka yayi,yayi ta bashi 10million zai yi birthday amma taki karshe ta ci masa mutunci har da haΙ—awa da Uwar sa wannan abin ne ya tsaya masa rai shiyasa yayi alΖ™awarin sai ya rama.
 Shiru shiru Asiya taji Alhaji Lamido ya saki Rabi'ah amma shiru, karshe ma abin kanta yadawo dan ba karamin ci mata mutum alhaji yayi ba duk da kasan ransa tsoranta yake ji.kukan makirci tasa masa akan karya yake mata Alhaji bebi ta kanta domin haka wai yake jin kamar ya sauke wani nauyi dake kansa.
Abu kamar wasa sosai soyayya dawo sabuwa fil tsakanin lamido da Rabi'ah,dan sosai ta dage da addu'a domin abin ba na lafiya bane,ita dai tasan yana sonta da kaunar ta amma ace lokaci daya mutum sai ya burkice, duk da bata shigo wa part din ta amma haka take satar jiki ta tufa masa addu'ar a cikin Paron da yake sha ta rufe ta bar gurin domin ance addu'ar makamin mumini.
sosai taga alfanun hakan domin kowa ko wata uku bayi yana sha ba sai gashi kamar korarre duk ya rame yayi baki,hakuri kuea ya bata shi har sai da tayi masa kuka sannan ya dai na batashi,haka yasa ta a gaba sukaje gidan su yabawa yan uwanta hakuri sannan yabawa dan uwan Rabi'ah 50million akan a kula da Abubakar tun ga secondary har zuwa University,sosai hakan yayi musu dadi duk da suna da kudin rike shi amma ko da ya girma za'ace mahaifinsa ne ya dauki nauyin sa.
Ba'a dade da da komawa normal Rabi'ah ciki ya bayyana sosai suke murna da wanna kyauta da Allah ya sake basu a lokacin da basuyi tsammani ba.
Kullum Rabi'ah cikin sallah da azumi take akan Allah ya kare mata ya'yanta Da mijinta, domin ranan da kanta taji su talatu suna zanjen wai sunji tana waya da bokanta kan azubar da cikin,wanna zance ba karamin daga mata hankali yayi ba,shiyasa ta dage da addu'ar ba dare ba rana.
Haka dai rayuwa tai ta gangara da dadi ba dadi,wanna lokacin ya'yan Rabi'ah Hudu uku maza daya macce wacce taci sunan Hajjiyar Lamido wato Amina suke ce mata suhaima.
Haka bangaren Asiya tana da ya'ya uku duk mata na.nan fa salon taku ya canja dan daga haihuwar Twins din Asiya komai ya fara jawa Alhaji Lamido baya dan kuwa ba'a kwana uku sai wani abu yasami dukiyar kafin kace meye kusan rabin abinda ya mallaka sun fara salwanta,nan fa hankalin Alhaji Lamido da yan uwan ya fara tashi domin lamarin kamar wanda aka sa masa hannu,a guda daya ne yake samun sauki idan ya Rabi Rabi'ah zatai tafada masa kalaman kwantar da hankali domin kuwa ita kanta juriya take dan abin ya fara bata tsoro sosai.
Kafin wasu lokuta abinda Alhaji Lamido ya tara duk babu su,duk wani ma kusancin sai da ya jajanta masa domin kamar ansawa dukiyar tasa wuta ne tunda ta fara ci bata tsaya ba sai da takwashe komai inda Allah ya tai make shi ya tsira da gidan da ke Abuja da wani karamin shago sai gidan da suke ciki a yanzu. Lokacin da Alhaji Lamido ya bude ido yaga ba shi da komai kowa ya gujeshi take ya yanke jiki ya fadi.
Da Temakon Allah da jajirciwar matarsa Rabi'ah ta tsaya tsayin daka gurin kula da shi da abinda a yanzu ya rage musu.kaff yaranta ta turaso Abuja gidan su ,duk sukai makaranta,domin idan ta barsu nan abun sai yayi masa yawa dan yanzu bashi da aiki sai tunanin kullum cin jininsa ya hau,sai da Rabi'ah tayi da gaske Sannan ya fara dawo cikin hayyacinsa.
Wata rana yana zaune da yamma a compand din gidan,dan yanzu ba inda yake zuwa,cikin nutsuwarta da suhaima ta dauko yazo kusa da shi tasa ta kujera ta zauna tana kallonsa duk damuwa tasa girmansa yasake fitowa sosai domin yasa damuwa a ransa a cikin hikima tace"Abban suhaima ka kasance mai godiya ga Allah domin ya baka arziki a Lokacin da bakai zata ba,ya kuma karba a lokacin da kake tsaka da jin dadinsu,duk abinda kaga yasamu bawa to Allah ya riga da ya tsara masa hakan tunkan yazo duniya,ka kasance mai godiya gareshi a duk lokacin da kasamu akanka,ka yadda da kaddara me kyau ko akasin haka shine cikar musulmi dan Allah"
Kallonta kawai yake yi yana jin wata kwalla na taruwa a cikin idanuwansa"Alhmdullah ala'nimatihi,Allah Nagode maka da Kabani komai kuma ka karbi komai sannan kabani wani arzikin da yafi wancan Rabi'ah hakika Allah ya karbe dukiyar da yabani Amma sai yabani arzikin da yafi na da domin samunki a kusa dani shine babban arzikin da Allah yasake bani,tabbas zan yi shela nace matata tafi ta kowa,dariya tayi sannan tace"kai Abban suhaima yau kuma yar zolayace a kusa kenan"?
 To Ni dai duk ba wanan"Yaushi suhaima zata dawo tunda dai sun gama secondary Gara tadawo gida ina kallon yarinya ta".
"Umm kaga masu hali iri daya jiya itama da muke waya da ita take mun korafin ita fa dawo zatayi kusa da Abbanta su kuma su Abdulrasheed Baffa yace sukuma kula da shagwan da yake can sbd wai kamar matsalar da kai take so yace mubari Muga yanayin kamun ludayin na su Amma yakace?.
Eh gaskiya Nima nayi wannan tunanin tunda Baffa da kansa yace haka to tabbas yaga wani abu dan Baffa baya fadin abu haka kawai ba bincike ce.
Sun dade suna hira da tattaunawa yadda al'amuran zasu kaya,sannan ta neme alfarmar da idan Suhaima tadawo zata koma makaranta domin yanzu ilimun macce yana da amfani ko ma bata morawa kanta da komai ba zaimata amfani gun 'ya'yanta.
Sosai yaji dadin kasancewa ta ita domin cikin hikima take nuna masa abubuwa sabanin Asiya da shi tunda abunan ya sameshi bayajin ma tayi masa addu'ar bare ta nuna a fuskama tasan me yake faruwa haka ma yaranta kaff shi be san me yasa bayajin son yaran a ranshi kamar sauran yaran.
Duk abinda suke akan idon Asiya kawai batajin abinda suke tattaunawa ne,Amma tun zaman su Sabeer da yashigo yake fada mata.
Hmm "kema mommy ki fita a sabgar matar nan kwata kwata ita bakye gabanta to kema ki kama kanki haba cewar Mubeenah.
Ke fa Dadina da ke baki da hankali yanzu kina ganin yadda makirar matarnan ta kwace mana Abba Amma kike fadawa Mommy haka sbd ke baki da kishi ko? Duk ita tajanyo mana wanna talaucin da muka shiga