SOYAYYAR ZUCI

Chapter 17&18

by @deeyamerh10

πŸ’–πŸ’– SOYAYYAR ZUCIπŸ’–πŸ’–
   (Love and Romantic story)
 Written 
  By
 Deeyamerh
07070647239
Page 17&18
"Dallah kurufe mun baki yan kutumar uba kawai kubar naji da abinda yake damuwa na a'a wllh yadda natsani mutuwata haka na tsani matarnan Amma zanyi magainta kwanan duk wanna rawar kan zata dai nashi".
Sakin labulan window tayi dakinta tayi waya ta dauka wa, lambar Asabe ta kira sai da takira kusan sau uku sannan a Asabe ta daga dan tunda tai Wa Dan rashin mutunci ta fita a sabgarta dan ko banza taci riba da idan lakaci yayi zata gane me yake nufi.
Hello Asabe me yayi zafi haka ba kira ba zuwa eh?shiru tai tanajin me Asabe ke ce mata,"Kinga Ni duk ba wannan ba yanzu ya za'ayi a koma gun wani Bokan dan aikin Boka dungurun baya wani dadewa yanzu so nake akashe shegiyar matarnan wllh ".To kawai kizo gobe muwuce kema kin san kudi ba matsala bane kedai kawai goben kizo".Tom shikenan.
Ko da suka je gunsa ba wani a take so a yiba illa kawai a haukatar da Rabi'ah ta shiga duniya tayi nisa da gida,tafi so ya ganta tana yawo akan bula.kai idan da dama kawai a kasheta kuwa ya huta,Dariya Boka matsito yayi yace"baxamu iya kashe ta ba domin tana da rukwan addu'a kullum cikin tsarki take ko da kuwa bata sallah.
Amma tabbas zata hauka ce kamar yadda kika so dan haka kikoma gida ki kawo mana gefen dan kwalinta kiyanko kadan ki kawo sai bukata zabiya Sannan zamu fadi abinda Aljani ke so,shin kin yadda zaki cika alkawarin da ake so?
".Eh Boka matsito".
Maza kutashi kufita da baya da baya la'ananu kawai.
Haka suka kama hanyar koma wa gida,jikin ta duk ciwo yake domin sbd gwajan-gwajan hanyar kyauyen.
Tunda tadawo take neman hanyar da zata samu hanayar da zabi domin samun abinda yake so.tana cikin wanna tunanin taji tsayiwar mota,da sauri ta fita dan tafison duk abinda ake yi ashi a gabanta.wa zata gani?
Wata matashiyar budurwa ce wacce bazata wuce sa'anin su Mubeenah ba,sai dai wanna tafiso kyau,gayu,ka cikikar Diri tafiso haske sosai domin bakakene,
Tunani ta ke shin wacce wanna haka
Jin yarinyar tana kwalawa Abba kira da Ammey tagane wacce dan Wllh ita duk a tunaninta ai yaran Rabi'ah duk sun mutu ashe tana da kyakkyawar yarinya irin haka.
Da gudu yarinyar tayi ciki gun Ammey a hanyar shiga part din suka hadu rungume juna sukai dariya yar budurwar tayi tace"Ammey nayi kewarki ina Abbana"?
Kin bari kishigo ciki ko dan ki huta idan yaso kinga Abban naki ya Ι—an fita ne.
Bata rai yarinyar tayi tace"Amma Ammey kinsan zanzo ba sai ki fada masa kada ya fita ko ina. "Yanzu dauko akwatun naki sai mu kara sa daga ciki".
Sosai farinciki yake bayya ne a kan fuskar yarinya domin kagani kasan tana son mahaifinta.sosai ta huta dan ranar ita tayi musu girki inda Allah ya temake ta gidan su ba'a sakaci da abu biyu Addini da harkar girki,shiyasa bata damu da kowar suhaima can ba domin batasan zata samu tarbiya fiye da ita.
Sunsha hira sosai kafin Abban ya dawo,shima kana ganinsa kaga farinciki akan fuskarsa domin Allah ya halintasa son ya'ya shiyasa yake ji idan zai kashe musu duk abinda ya tara bai fadi ba.
Yasha surutu gun suhaima Dan duk yadda sukai rayuwa a abuja sai da taga masa,sosai yaji dadin irin tarbiya da kula da ake akan yaransa,sai girma da kimar ta sake karuwa a idawunasa.
Ba wanda Abba ya fadawa washe gari yasa Abokinsa ya nema wa suhaima gurbin katuru a inda yar da take wato Fatima,ba'awani dade ba yasamar mata gurbin karatu a jami'ar Bayero University hatta course din da Fatima yake shi suhaima aka samo mata Medicine.
Ran da suhaima taji labarin tasamu gurbin karatun har kuka sai da tayi domin tana da burin cigaba da karatu.
Cikin Ikon Allah suka fara karatu inda gefe guda kuma kawance ya kullu tsakanin Fatima da suhaima domin kusan halayen su daya shiya jinin yazo daya,basu da wasu kawaye dan Bama sa suga harkar kuwa,ko da yake gara Fatima ita tana da kawa saudat Amma suhaima baya yadda yayi kawa da kowa ba iya Fatima ma ta wadatar.
Kamar ba Asiya a cikin gidan Alhaji Lamido domin ita dai bazaka ganta ba Amma zakaga su Mubeenah anci kwalliya an fita,Abinda yake bawa Alhaji Lamido mamaki shine baya iya tsawartar su Hassena duk abinda suke kamar yadda har yau bai taba tankawa akan zaman da Sabeer yake ba,Ashe Asiya duk ta kwalle masa baki,shiyasa baya iya cewa yaran komai sai dai ya bisu da kallo.
Duk wani abu da ake siyawa domin fara karatu a juma'ar Bayero haka akayiwa suhaima wanda Aboki kuma uba ga suhaiam domin a cewar baban Fatima suhaima ai yarsa ce dan haka yadda zai yiwa Fatima komai haka zai wa suhaima domin Alhaji Lamido yayi masa abinda bazai iya watsa masa kasa a ido ba.
Tare da Fatima suka fara zuwa makaranta inda Baban Fatima ya basu driver da zai ringa kai su makata Amma suhaima tace a'a zata tsaya a inda Allah yake so ya ganta,wanna abu tai sai takara girma a idon mutane family domin ta nuna halin tarbiya,sosai suhaiam take ganin soyayya da gata,idan ba makaranta ba to tana makale da Ammey dan ko gidan kakaninta bata fiya zuwa ba.
______________
Ranar Asiya nasarar samun yanko dan kwalin Rabi'ah domin a ranar suhaima ta wanke musu dan kayan da suka bata.
Basu kasa a gwiwa ba wajan kai wa Boka matsito wanna yankin dakwalin,"yana karba ya rufe ido yafara karanta wasu irin surkule kayan wajan mins 5 yanayi kafin ya bude idonsa mika mata yankin yayi yace ta juya baya tayi masa fitsari,ba kunya ba tsoron Allah Asiya ta waje gindini gaban boka matsito tayi fitsari, gama fitsari ta ke wuya yankin ya koma kurciya kawai ta tashi sama tai waje.
Jikin Asabe ta fada dan tsoro,wata dariya Boka matsito yayi yace"shigiya kinyi nasa akanta Amma kisani duk randa a shirin ya karye to ke zaki Hauka ce".hhhhhhh ya sake ke cewa da dariya
Bama zai karye ba ta haukace kenan"to yanzu boka matsito Meye ladan aiki"? Hhhhhhh dariya boka matsito ya ta cika gun yace"a cikin ya'yan zaki kawo mana wacce bataji Aljani barbero zaiyi ta rayyya da ita idan kuma ba haka ba to tabbas aiki zai dawo akanki.
Cikin rawar jiki tace "yanzu boka matsito dole sai yarinya ta bazamu kawo yar kishiyar yawa ba"?
Gimtse fuska yayi sannan yace"wanna yarinyar duk abinda zakiyi mata bazai taba cinta ba domin tana da wanda suke kare duk kan wani mugun abu da tai tabata idan kuma kika ce dole sai kinyi to mutuwa zaki irin da karnuka hhhhhhhhhhhhhh bace mun daga gani gobe kikawo mana abinda muka ce hhhhhhhhh.
Jiki na rawa suka fita,a hanyar komarsu ne Asiya take tambayar Asabe gaskiya ita bazata iya bada ya'yan ba.Kallon baki da hankali Asabe tai mata sannan tace"to wanna ke tasha fa danni nagama aikina ko kikai ko aiki ya dawo Kaki ah to.
sosai Asiya ta shiga cikin rudani,haka dai daga karshe ta dau Haseena takai wa Boka matsito ita.
hhhhhhhh kikace ke kamar yar iskace na'aniya,"Ke ya daka mata tsawa Sannan yace"maza fita da baya kikoma gida zatayi kwana biyu nan domin idan ba haka ba aikin bazai kammalu ba hhhhhhh
tana ji tana gani haka tafi rabar Haseena,idan bana kuka ba abinda takeyi domin Mommy batace nan zata kawota ba...