MAƘARƘASHIYA BY A'ISHA MB

Page 1

by @babyisha123

*🔥 MAƘARƘASHIYA🔥*




*WRITTEN & DIRECTED BY*
*A'ISHA M.B💞💞*.
*ZINARIYAR JAJIRTATTU*.



Na sadaukar da wannan page ɗin ga *Maman Ihsan da Malam Yusuf gumel* Muna matuƙar godiya da ƙoƙarin ku a gare mu, Allah ya biya ku da gidan Aljannah🙏🙏.

Sannan ina miƙa gaisuwa ta musamman ga waɗan nan mutanen abun alfahari na.
*Sadiya Ko'aje*
*Nainah KD*
*Hussaini Yusuf*
*Emilia*
*Basheer s Basheer*
Na gaishe ku duka, Allah ya ƙara dankon zumunci da qauna 😍😍😍.

*🌹BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*🌹

*Godiya su tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Mai rahama, Mai jin ƙai. Shi ne wanda Ya halicce mu, Ya azurtamu da ni'imominsa marasa adadi, kuma Ya ba mu ikon fahimta da basira. Duk wata hikima da baiwa daga gare Shi take, kuma gare Shi ne komai zai koma.*

*Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Shugaban Annabawa, Manzon Allah Muhammad (SAW), wanda shi ne hasken shiriya da abin koyi ga dukkanin al’umma. Wanda ya koyar da mu soyayya, haƙuri da imani, kuma ya bar mana kyakkyawan tafarki da muke koyi da shi har yau.*

*Ya Allah! Ka sanya wannan rubutu na ya zama mai amfani, ya zama abin da zai kawo fa’ida ga al’umma, ya zama haske ga zukata da tunani. Ka yi mana jagora a cikin tafiyarmu, ka sa mu kasance cikin waɗan da ka ke yarda da su. Kasa kalmomina su fito da hikima, ka shiryar da ni a hanya madaidaiciya, ka kuma yafe min kura-kuraina*

*Amin🙏*
 

*A wannan littafi, za ku tsinci ƙauna da tsana, gaskiya da ƙarya, amana da cin amana a cikin rikice-rikicen rayuwa. “MAƘARƘASHIYA” littafi ne da zai faɗakar, ya nishaɗantar*.


*Ku kasance tare da ni domin jin yadda labarin zai kasance*.



*MAƘARƘASHIYA ONGOING*
*PAID BOOK #500*




FREE PAGE1️⃣▶️2️⃣





      *NIGERIA LAGOS STATE*
     *MARINA ROAD*
   *FIRST BANK*


_______________________
Cikin babban hall ɗin bankin First Bank babu wani abu da ke tashi sama sai rawar zuciya, da kukan mutane. Wata ƙaramar yarinya ta riƙe hannun mahaifiyarta idonta cike da hawaye, yayin da dattijon da ke kusa da su ya kifa a ƙasa yana rawar jiki kamar mai zazzaɓi. Mata na kukan salati, maza kuwa kowannensu ya yi shiru cikin firgita, zuciyoyinsu na buga wa da sauri kamar ana buga gangar yaƙi.


A gefe guda kuwa, ɓarayi ne a tsaye cikin takama da izza. Dukansu sanye da mask masu launin baƙi, suna sanye da hand gloves riƙe da bindigogi.

Daga cikin su, akwai wanda ya bambanta. Yana a zaune akan kujera, ƙafafunsa biyu ya ƙwantar da ɗaya kan ɗaya babu alamun tsoro ko fargaba. Fuskar mask ɗin da ke kan fuskarsa  ba ta hana a gane salon tsoratarwarsa ba. Hakan ma ya ƙara ba shi wani irin ƙarfin iko, kamar sarkin da ya fito da masarautar sa.



Ɗaya daga cikin ɓarayin ya juya yana duban wanda ke zaune sannan ya fara masa kirari kamar haka. “Black Devil! sarkin duhu, gwarzon da ba ya jin tsoro, kai ne garƙuwar mu, madogaran mu a fagen wuta. Kai ne mai shigo wa kamar iska, wanda ido ba ya hango saƙon zuwansa, Kai ne jarumin da ke cin abokan gaba da tsoro kafin harbi ya yi ƙara, kai ne shugabanmu, jagoranmu, mai ana zuciya karyewa. Black Devil azzalumin da mutuwa ma ke ja masa tsoro!”.




Dakatar da shi Black Devil ya yi da hannunsa sannan cikin lion voice ya ce. "I want absolute silence". Ya faɗa babu dariya ko walwala a tattare da shi.


Ɗaya daga cikin ɓarayin ya matsa kusa da shugaban ya ce. “Boss, aikin nan ya kammala. Jakunkuna sun cika, aljihunmu ya yi nauyi da abin da muka zo nema. Ba mu da sauran abin jira Boss". Ya faɗa yana kallon shugaban na su.



Black Devil ya girgiza kai a hankali, kamar wanda yake jin daɗin tunanin da ke kansa. Idanunsa suka zazzaro ta cikin mask ɗinsa suka sauka kan jama’ar da ke kwance a ƙasa, zuciyoyinsu na rawa, bakunansu a rufe cikin tsoro.  Ya haɗe girar sama, ya ɗan ja numfashi mai nauyi sannan ya ce. “Eh ka yi gaskiya. Amma kai ka sani, ba kuɗi kaɗai na zo nema ba".


 Nan ya maida kallon sa kan jama'ar bankin ya ce. “Ku da ku ke tsoro na a nan, ku san cewa ba kuɗi kaɗai ne abin da ya kawo ni ba. Nafi buƙatar duniya ta san cewa Black Devil ya taka wannan bankin, ya ɗauki dukiyar ku a idon ku, ya bar ku da tsoro a cikin zukatan ku. Kuɗi za su ɓace, amma tsoron da na dasa a cikin zukatan ku zai zauna har abada. Ina so ƴan sanda su iso, su tarar da ni kamar sarki a fadar sa, domin su gane cewa babu wata ƙofa da za ta iya rufe ni, babu wata bindiga da za ta iya tsoratar da ni. Ni ba ɗan fashi ba ne, ni  mutum ne wanda mutane ke ikirarin aljanin da yake shigo wa a mafarkin jama'a saboda tsoro, amma a yau kuwa, wannan aljanin da suke faɗa, ya fito a zahiri". 



Black Devil ya juyo da idanunsa masu firgitarwa, yana kallon jama’ar da suke kwance ƙasa kamar gawa. Nan ya sauke idonsa kan ɗaya daga cikin security na bankin wanda ke kwance ƙasa yana rawar jiki. 

Nan ya ɗan ɗaga hannunsa alamar umarni. Take yaransa suka finciki security ɗin suka ɗaga shi tsaye, kafafunsa suna karkarwa kamar ganyen da iska ke kaɗa wa. 

Kallonsa Black Devil ya yi sannan ya umarce shi da ya kira jami'an ƴan sanda.


Nan wannan kiristan security ɗin ya yi magana cikin pigin English. "Abeg no kill me, I have children's to take care of". Ya faɗa jiki na rawa yayin da hannayensa ke a sama.


Murmushin mugunta Black Devil ya yi ya ce. " I'm going to spare you if you do what I asked you to do". 


Jiki na rawa security ya dubi manager sannan ya gyaɗa masa kai. Nan manager ɗin ya danna panic button. Lokaci guda ƙarar silent alarm ta kai haske zuwa hukumar ƴan sanda.



Ƴan sanda suna zaune a ofishin su, suka ga hasken red light da ke nuna Robbery alert Marina road First bank.


Nan take suka ɗaga radio walkie talkie suka bada umarnin a fito da motoci da bindigu.


Nan da nan suka nufi bankin ba tare da ɓata lokaci ba. A lokaci guda kuma aka aika da saƙon gaggawa zuwa Police Mobile Force (MOPOL), wani sashe na Nigeria Police Force (NPF) da aka horar musamman domin tunkarar manyan laifuka masu haɗari da kuma hare-haren da suka shafi makamai. Da isar saƙon, jami'an MOPOL suka tattara tawagarsu cikin gaggawa, suka ɗauki motocinsu tare da nufar bankin domin dakile lamarin kafin ya ƙara muni.


Cikin bankin kuwa, kallonsa  ɗaya daga cikin ɓarayin ya yi ya ce "Boss lokacin barin wajan nan ya yi. Let's go".


Nan Black Devil ya zuba masa ido ya ce. “Me yasa za mu gudu?, gudu ba na mu ba ne. Ba inda za mu je, mu jira su. Dole ne su iso su gane ba wani talaka ne ya shigo nan ba, Black Devil ne".


Daidai lokacin ƴan sanda tare da Nigeria police force suka ƙaraso wajan.  

Yayin da suka fara tsare bankin gaba ɗaya ta yadda babu wanda zai iya fita ko ya shiga. Bayan sun zagaye bankin. Suka saka kayan bullet proof. Ɗaya daga cikin ƴan sandan ya ɗauki warning megaphone ya kafa a bakinsa sannan ya fara magana kamar haka.


"Ku fito ku miƙa wuya, kuna cikin kewayen jami'an tsaro, idan ku ka yi ƙoƙarin tsere wa zamu buɗe wuta".



Black Devil da ke cikin bankin ya ji abinda ɗan sandan ya ce hakan ya sa shi ɗaukar wayar landline ya kafa a bakinsa ya ce. 


“Ku saurara da kyau! Wannan bankin a  yau tana ƙarƙashin ikon Black Devil ne!, duk wanda ya motsa, ko da numfashi ne mai sauri ya yi, to zan mai da shi gawa a gaban idon jama’a. Ku sani ba bu jami’an tsaro ko gwamnatin da zai iya hana ni abin da nayi niyya. Ni ne mutuwa a nan, yanzu ni ne dokar ku!. Ku ajiye bindigogin ku a ƙasa, ku zubar da jarumtarku, domin kada ku rasa rayukan ku. Kuma daga wannan daƙiƙa, kowa zai yi abin da nake so ne, idan ba haka ba, ku shirya ku ga yadda jinin ku zai dinga zuba kamar ruwan sama!”. 



Jin sunan Black Devil da kuma abinda ya ce hakan ya sa hankulan  ƴan sanda da jama'ar da ke wajen bankin ya tashi.


Nan ɗan sandan da ke riƙe da megaphone ya ce. "Black Devil mene abinda ka ke da buƙata?, muna son ka rabu da mutanen cikin bankin nan ka fito muyi magana cikin lumana".


Murmushi Black Devil ya yi ya ce. "Ka taɓa ganin inda ɓarawo da ɗan sanda suka tsaya waje guda cikin lumana?, Hahaha!, wannan ba zai taɓa faruwa ba. Ku sani, ni ba ƙaramin yaro ba ne da za ku raina wa hankali. Na fi ƙarfin dokarku, na fi ƙarfin tunanin ku. Ku na mafarkin kama ni, amma ni ne nake riƙe da mafarkin na ku. Duk inda ku ke tsammanin kuna da iko, toh ku tuna, Black Devil ya riga ya yi gaba. 
A ƙoƙarin kama inuwa kuna dukan iska a banza".

Ɗan sandan da ke waje ya ja numfashi ya ce. "Me ka ke da buƙata?".


Nan Black Devil ya ja numfashi ba tare da tsoro ba ya ce. "Ku saurara da kyau, rayukan waɗan nan mutanen da ku ke gani a hannun ku take, amma makomarsu a hannuna take. ku sauke bindigogin ku a ƙasa kafin na zubar da jinin su, idan ku ka yi biyayya, zan bar su, su tafi cikin salama. Amma idan kuka yi yunƙurin jarumta wallahi wannan bankin zai zama kabari kafin rana ta faɗi".



Jin hakan ya sa ƴan sanda suka saukar da makaman su.

Nan take ba tare da kowa ya hankara ba, rukunin Black Devil da yaransa suka  chanza shigar su da siffar su izuwa tsofaffi tare da saka farin gemu.


Nan take ƙarar buɗe ƙofar banki ta daki kunnen kowa!, mutanen ciki suka ruga waje suna ihu, kowanne yana neman hanyar tsira, yayin da ƙafafun su ke buga wa a ƙasa tamkar ana dukan ganga. 


A cikin wannan hayaniya, Black Devil da yaransa suka fito sannu a hankali, ba da surar da suka shiga da ita ba, sai dai cikin siffar tsofaffi masu dogayen gemuna farare, tufafin su kamar ta malamai, hannunsu riƙe da jaka kamar masu fita daga tafiya ta hajji. 
Kamar iska mai wuce wa, haka suka wuce ba tare da ƴan sanda sun gane su ba.


Ganin mutane na fitowa hakan ya sa ƴan sandan suka ɗau bindigun su tare da ganin ta ina su Black Devil za su fito. Har mutane suka gama fito wa basu ga ɓarayin ba, hakan ya sa suka shiga cikin bankin suka bincika ko ina amma babu kowa. Nan suka nufi inda CCTV camera yake, cikin mamakin su kuwa suka ga cctv cameran ba ta aiki, domin an daɗe da fasata. Hakan ya sa suka duba dukkanin cctv da ke cikin bankin amma basu ga komai ba da zai zama hujjar kama Black Devil ba.



Girgiza kai shugaban rukunin na su ya yi ya ce. "Black Devil kana da wayo, wannan karon ma ka ƙara tsere wa. Tabbas wata rana sai an kama ka, domin rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, kuma duk nisan jifa ƙasa zai dawo".

Nan suka haɗa kayansu tare da ƙoƙarin ganin ko za su iya tracking ɗin su, amma samm babu wani hanyar sadarwa da zai iya kai su inda location na Black Devil yake. Babu yadda suka iya haka suka tattara ina so suka bar wajan. Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya bazama cikin gari cewar Black Devil ya yi sata a banki inda labarin Black Devil karaɗe garin Lagos.  Yayin da ƴan jarida suka shiga yin maganarsa a tashar su.




_____
Black Devil da yaransa kuwa daji suka nufa inda wani ƙaton gida yake tamkar Mansion sannan suka fara shiga ciki da motocin su. 

Fito wa suka yi daga cikin motocin kana suka tsaya a gaban Black Devil tare da ɗaga bindigogi sama suka ce. 


"Tsakanin dare da duhu, mune sarakuna, nasara tamu tsoro nasu". Suka faɗa tare da harba bindiga sama.


Girgiza kai Black Devil ya yi ya ce. "Mazaje na kenan. Yanzu our mission in Lagos is completed. Next target ɗin mu shi ne Abuja state. dan haka ku shirya gobe zamu bar nan. Sannan waɗan nan kuɗaɗen ku ɗauki 50% na ciki ragowar ku je ku rabawa mabarata".


Nan suka saki ihuu suna mai yi masa kirari.



    *ABUJA STATE*
         *ASOKORO*


A tsakiyar birnin Abuja, Asokoro tana nan cikin kamewa da kwanciyar hankali. Wata unguwa ce da ke cike da manyan gidaje, tituna masu faɗi, da bishiyoyi masu yalwa da ke shimfiɗe.


Unguwar tana ba da yanayin shiru da kwanciyar hankali, inda masu kuɗi da masu mulki ke shakatawa cikin kwanciyar rai.



Kai tsaye lokacin da na iso bakin kofar babban gidan Barrister ƙasa, numfashina ya ɗauke na ɗan wani lokaci. Gaban kallo na, wani katafaren gida ne mai kyau kamar aljannar duniya, an gina shi da kyan fasaha da salo na zamani.



A harabar gidan, akwai filin ajiye motoci mai girma, inda motocin alfarma suke jera kamar taurarin dare. Gefe guda  akwai katafaren swimming pool.



Da na taka ƙafata cikin falon gidan, na ji sanyi mai daɗi daga air conditioner da ke ratsa dukkan lungunan gidan. Parlour ɗin yana da girma sosai, yana da royal sofas masu launin ruwan toka da diamond, tare da center table mai ƙyalli da ke tsakiyar parlour. A bangon gaban parlour ɗin, akwai babban TV screen  da home theatre system mai ƙarfafan sauti. Gefe guda kuwa, akwai photo frames na kyaututtukan barrister ƙasa, gami da hotunan sa tare da manyan shuwagabanni.




Na tsaya ina kallon wannan katafaren gida mai cike da ƙayatarwa, ba tare da shakku ba, wannan wuri gidan gata ne cike da walwala, aminci, da jin daɗin rayuwa.

Gaba ɗaya babu abin da ka ke gani a gidan sai mata wanda suke sanye da uniform riga white wando kuma blue gaba ɗaya ba abinda suke faman yi sai kai kawo a gidan. Na shiga mamaki sosai ganin yadda naga mata cike a gidan inda kowa da aikin da yake yi, daga mai wanke mota share gida jiran gate da kuma abinda ba za'a rasa ba kai tsaye dai su ɗin ma'aikata ne. 



Wata kyakkyawar budurwa mai takama da Izza na hango tana takowa cikin nutsuwa kamar sarauniya a cikin fadar da aka gina don ita kaɗai. tana tattare da iko  kamar gimbiya da aka haifa domin a girmama ta. Duk inda ta taka, ana jin ƙamshin turarenta yana bayyana, yana shiga zuciya yana bada wani ƙamshi na ban mamaki.

Fuskarta tamkar hoton da aka zana da mafi tsadar tawada a duniya. Fatarta tana da launin ruwan madara da zuma, tana sheƙi kamar zinariya mai haske. Idanuwanta manya ne masu launin ruwan ƙasa mai duhu. Kallo ɗaya daga gare ta zai iya sanya mutum manta da inda yake, domin yana firgitarwa  kuma yana nutsar da zuciya cikin shauƙi.

Lokaci ɗaya ta saki murmushi, take laɓɓanta masu kyau da launin ja suka buɗe cikin lumana, suna bayyana haƙoranta farare kamar sabon kwanon azurfa.  Hancinta madaidaici ne, yana ƙara mata kamala da kyau.

Gashinta dogo ne mai launin baƙi mai ƙyalli, Ya lullube bayanta, yana nuna adon sarƙar gold mai ƙyalli da ke kwance a wuyanta.

Shigarta ba kawai ado ba ne, tana bayyana matsayinta. Ta saka doguwar riga mai launin gold da fari, wacce ke manne da jikinta
 Mayafinta ya rufe kafaɗunta cikin wani salo na kwanciyar hankali, yana ba ta sabon izza da kamala.

Lokacin da take tafiya, sai a ji takalmanta masu tsini suna yin ƙarar da ke jan hankali, duk wanda yake kusa ya san cewa tana nan, ba tare da ta yi magana ba. Tafiyarta ba da sauri ba, ba da jinkiri ba, amma kowanne mataki yana da ma’ana. Duk inda ta taka, sai ka ji kamar ƙasa ta san cewa wata ta musamman ta taka ta.


Wannan ba kawai kyakkyawar budurwa ba ce ita misalin mace ce mai cikar kamala, izza, da ƙwarjini wacce da zarar ka ganta, za ka san cewa ba wacce za a iya wulakantawa ba ce. 


Sauko wa ta yi downstairs. Lokaci ɗaya gaba ɗaya ma'aikatan matan da ke cikin gidan suka sha jinin jikinsu sannan suka fara gaisar da ita.


Tsaya wa ta yi ba tare da murmushi ko walwala kan fuskarta ba. Cikin izza ta nufi kujera kana ta zauna tana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. 


Ganin hakan ya sa ma'aikatan suka tabbatar da cewa tabbas akwai matsala.


Dubansu ta yi cikin sweet voice ɗinta ta ce. "Wace ce a cikin ku ta shigo da namiji gidan nan?".


Nan take gaban kowa ya yanke ya faɗi!. Shiru gaba ɗaya ma'aikatan suka yi ba tare da sun ba ta amsa ba".


Girgiza kai ta yi cikin haɗe rai ta ce. "Kun san dai idan nayi magana bana maimaita wa ko?".



Nan take gaba ɗaya suka fara haɗa zufa. Ɗaya daga cikin ƴan aikin ce ta matso gaba, jiki na rawa ta ce. "Madam kiyi haƙuri ki yafe min, shi ɗin saurayi na ne, kuma zuwa ya yi domin ya ga inda nake aiki, amma dan Allah kiyi haƙuri ba zai sake zuwa ba". Ta faɗa tana mai haɗa hannayenta.


Furzar da iska mai zafi ta yi ta ce. "Saurayi?, a gidan nawa?. Karki damu, ba ma zai samu wata damar ƙara zuwa kawo miki ziyara ba, dan haka kije na sallame ki".



Fashe wa da kuka ma'aikaciyar ta yi ta ce. "Na shiga uku! Madam Bhatool na roƙe ki kada ki kore ni wallahi da wannan kuɗin nake taimaka wa Mamata". Ta faɗa tana mai faɗa wa kan gwiwowin ta.



Miƙe wa tsaye Bhatool ta yi tare da saka no respect sannan ta dubi sauran ma'aikatan ta ce. "Idan har ku ka sake na dawo daga makaranta baku sa ta bar gidan ba, toh kuma za ku rasa aikin ku". Ta faɗa tare da fita daga cikin gidan.


Zuwa wajan wacce Madam ɗin ta so ta sallama sauran ma'aikatan suka yi suna mai ba ta haƙuri cikin tausaya wa.




Fita ta yi cikin harabar gidan. Ganin ta ya sa Driver ɗin ta mace ta iso wajan sannan ta buɗe mata mota. Shiga cikin motar ta yi. Kana ita ma direbar ta shiga cikin motar tare da tada wa sannan suka bar gidan.


Basu nufi ko ina ba sai makarantar Nile University wacce take wajan Jabi airport  bypass.


Kasancewar babu cunkoson ababen hawa, hakan ya sa shikin mintuna Talatin suka isa makarantar.

Masha Allah na ce domin duk wanda ya san Nile University ya san ba ƙaramar makaranta bace.


A bakin gate kuwa securities suka yi gamo da shi yayin da saida haka yi checking sannan suka ga ID pass ɗin izinin shiga a jikin glass ɗin motar. Hakan ya sa suka basu umarnin shiga ciki.


Kai tsaye wajan parking space direbar ta nufa tare da parking.


Bayan direbar ta yi parking ta dubi Madam ɗin ta su, a tsora ce ta ce. "Madam mun iso".


Kallonta Bhatool ta yi ta ce. "Na ce miki ban san cewar mun iso ba ne?". Ta faɗa tare da jan tsaki.



Daidai lokacin naga wasu classic ƴan mata suna nufo wa wajan, kallo ɗaya za ka musu ka san aje butters ne. 



Ɗaya daga cikin su biyun ce ta fara magana kamar haka. "Wai ni kam yaushe Bhatool za ta ƙaraso ne, an fa ku san fara lecture".


Nan ɗayar ta ce. "Rahma kema kin san Bhatool ba lallai ta shiga lecture ɗin nan ba".

Kallonta Rahman ta ce. "Hafsah me zai ana ta shiga lecture kuma ana zaune lafiya".


Murmushi Hafsah ta yi ta ce. "Rahma kenen, wai ko kin manta cewar Bhatool duk inda maza suke ba ta zuwa?, karki yi mamakin cewa yanzu haka tana cikin makarantar nan amma ba za ta shiga class ba".


Tsaya wa Rahma ta yi ta ce. "Ki kalli chan ki gani, motar ta ce fa".


Da sauri suka ƙarasa wajan parking space sannan suka nufi inda motar ta take.


Suna ƙarasa wa suka fara ƙwanƙwasa ƙofar glass ɗin.


Saukar da glass ɗin motar Bhatool ta yi sannan ta dube su ta ce. "Lafiya?".


Kallon juna suka yi kana suka maida kallonsu kanta suka haɗa wajan faɗin. "Kamar ya lafiya?".


Ajiyan zuciya Bhatool ta yi ta ce. "Kunga  yanzu bana cikin mood mai daɗi please".


Kallonta Rahma ta yi ta ce. "Bhatool yanzu fa muna da lecture fa".


Kallon ta Bhatool ta yi ta ce. "And so what?". 


Girgiza kai Hafsah ta yi ta ce. "Bhatool bai kamata ki cigaba da dodging din class ɗin lecturer maza ba, yanzu fa muna 300 level ne kuma kinsan science laboratory technology ba sauƙi gare shi ba".


Haɗe ranta Bhatool ta yi yayin da ranta ya soma ɓaci. Cikin ɓacin rai ta dube su gaba ɗaya ta ce.  “I have told you guys countless times to stop telling me to attend classes with male lecturers. Ina ruwan ku da rayuwata ne?, this is my life, so I have the right to do whatever I want okay".


Ta faɗa tare da fito wa daga cikin motar sannan tare da ƙoƙarin wuce wa ta gefen su.


Da sauri suka sha gabanta sannan Rahma ta ce. "Bhatool ki chanza hali wallahi, ke komai kin tsani maza, da zarar an ambaci sunan namiji shi ke nen ranki ya ɓaci. Mazan department ɗin mu har su sun fara gulmar cewa ƴar barrister tana da aljanu shi ya sa ba son zuwa wajan maza. Kuma ke ga ki kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa, babu ɗa namijin da zai ganki bai ji kin shiga ransa, please kiyi ƙoƙari ki chanza".



Murmushi Bhatool ta yi ta ce. "“I don’t mind what people say about me. Ku sani cewa, ko shi mahaifi na bana kula shi balle kuma wasu banza chan wanda ba dangi uwa ba, ba na uba ba".


Daidai lokacin ta ji wayarta yana ringing. Duban wayar tayi, yayin da fuskar screen ɗin ke rubuce da. "First Enemy". Ƙatse kiran ta yi.


Mamaki ne ya kama ƙawayen nata ganin sunan da ke rubuce kan fuskar wayar.


Sai da aka kira har sau biyar ba ta ɗaga ba. A na shidan ne ta ɗauka ta ce. "Me ya faru?".


Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Ki same ni a part ɗina idan kin dawo". Ya faɗa tare da ƙatse wayar.



Zaro idanuwa waje su Rahma suka yi jin muryar mahaifin Bhatool.


Girgiza kai Hafsah ta yi yayin da al'amarin Bhatool ya soma ba ta tsoro. "Bhatool kina lafiya kuwa?, number mahaifin ki za ki yi saving da irin wannan sunan?".



Kallonta Bhatool ta yi rai a haɗe ta ce. "Ƙwarai kuwa shi ne First Enemy na, domin shi ya saya rayuwata ta kasance a haka". Ta faɗa tare da wuce wa hanyar cafeteria.



A chan cafeteria kuwa maza ne  su biyu suna zaune  suna ta dariya da shewa.


Ɗaya daga cikin su ne ya ce. "Wai Prince ka san wannan ƙasurgumin ɓarawon nan mai suna Black Devil ya sake yin sata a Lagos, kuma a bankin First bank".



Nan wanda haka cewa Prince ya ɗago ya kalle shi ya ce. "Eh wallahi ɗa zu na gani a news, shi dai wannan Black Devil ɗin gaba ɗaya ya tada hankalin gwamnati da ƴan kasuwa, kowa ɓoye dukiyarsa yake yanzu, gudun kar Black Devil ya zo ya kwashe su. Kuma abin mamakin shi ne babu wanda ya san ya fuskarsa take, kuma ko cctv cameran inda yaje ya yi sata ba ta da bayanan fuskarsa domin fasa wa yake yi, kuma idan ya yi satan ba zai bar gurin ba har sai ya san waɗan da ya yi wa satan su kira ƴan sanda. Kuma wani abun mamakin shi ne, idan ya yi satan sai ya je ya rabawa mabuƙata da mabarata kuɗin. Shi ya sanya yanzu ƴan kasuwa suka shiga taitayinsu kowa ɓoye dukiyarsa yake".


Nan ɗayan ya ce. "Ai dole su ɓoye, ku san fa state ashirin na Nigeria ya yi sata a ciki. Allah ne ya san yanzu wane state ne next target ɗin sa".

Nan Prince ɗin ya ce. "Mu dai Allah ya sa kada ya shigo Abuja dan babana ɗan kasuwa ne kada ya kwashe dukiyoyin mu. Allah ya sa ma wata rana a kama shi kowa ma ya wuta".


Daidai lokacin su Bhatool suka ƙaraso wajan.


Da sauri Prince da abokin nasa suka dubi su Bhatool da ke tawo wa wajan.


Ganin maza a wajan hakan ya sa Bhatool ta ja burki yayin da zuciyarta ya soma buga wa da sauri-sauri!.


Riƙe hannunta Rahma da Hafsah suka yi sannan suka ce. "Kada ki damu babu abinda zai faru, kinga babu ruwan da su kinji tawo mu je".


Ba tare da ya so ba ta bi su yayin da suka samu guri suka zauna. Yayin da kujerar su da ta su Prince yake kallon juna.

Nan Rahman ta tashi ya je domin siyan snacks.



Abokin Prince ya dubi.prince ya ce. "Prince ka tuna wannan yarinyar da na faɗa maka, ita ce wani ɗan department ɗin mu ya ce yana so kwanaki, kaga rashin mutuncin da ta yi masa kuwa?, chabb da kana gurin saika sha mamaki. 80 percent mazan makarantar nan crushing suke a kanta, saboda kyawunta fa ake mata lakabi da Beauty queen of  Nile University. Amma abin aushin shi ne wai ta tsani maza, ko fa lecturer namiji ne zai shiga aji ba ta shiga, abin dariyar ma a nan shi ne direbanta ma mace ce, ko me ya sa oho, komai tace ta tsani maza sai kace ba ta hanyar namiji haka haife ta ba".


Murmushi Prince ya yi ya ce. "Nima naji labarin ta sai dai ban taɓa ganin ta ba sai yau, ba laifi kyakkyawa ce, nima kuma ka san ba haka kawai na samun wannan sunan Prince ɗin da ƴan makaranta ke kira na ba, sun san da cewa babu yarinyar da zan ce ina so ba ta amince ba, shi ya sa suka samun wannan sunan, dan haka ina ganin wannan ma ba za ta yi min wahalar shawo wa ba da zarar na ce ina sonta za ta amince domin nima ba'a baya ba wajan kyau".


Murmushi abokin na sa ya ce. "Chabb aikuwa lallai ka kama gaibu, domin wannan ta bambanta da sauran matan da ka ke cewa kana so, wannan fa ba ta da zuciyar soyayya kwata-kwata".


Tashi tsaye Prince ɗin ya yi sannan ya ce. "Toh Aminu ka zuba ido ka gani, za ka sha mamaki".


Prince ya faɗa. Kafin Aminu ya dakatar da shi Prince ya nufi inda su Bhatool suke.


Ganin Prince na nufo inda suke hakan ya sa Hafsah ta kalli Rahma wacce ta ajiye musu snacks da coffee me zaf, sannan ta ce. "Me ya sa kuma Prince yake tawo wa nan wajan?".


Nan Rahma ta ce. "Nima ban sani ba".


Ganin suna kallon wani wajan da ban hakan ya sa Bhatool ta kai duban ta inda suke kallo. Nan take bugun zuciyarta ya soma tsananta.


Kawar da kanta ta yi gefe tana mai cije leɓenta, yayin da zuciyarta ya soma tafarfasa.


Ƙarasawa wajan Prince ya yi sallama riƙe a bakin sa. Duk sun amsa amma banda Bhatool.


Kallonta ya yi tare da sakin murmushi ya ce. "In ba Hello akwai hi dai ko Madam Bhatool?".


Jiki na rawa Bhatool ta dubi su Hafsah ya ce. "Ku ce ya bar wajan nan".


Maida kallonsu su Hafsah suka yi kan Prince sannan suka ce. "Prince kayi haƙuri, Bhatool ba ta san mu'amala da maza, ka tafi dan Allah".



Murmushi Prince ya yi ya ce. "Kada ku damu kanku kunya ta take ji, a kan me zai sa na tafi. Ni fa na zo ne domin shan shayi ba wani abu ba kuma....

Bai inda ƙarasa maganar ba ya ji saukar shayi mai zafi a jikinsa.


Nan take ya saki ihuu wanda ya janyo hankulan ɗaliban makarantar sannan suka fara ɗaukar video.


Bhatool na huci ta dube da kofin shayin da ke hannunta ta ce. "Wannan ya ishe ka, ko kana da buƙatar ƙari?".



Zaro idanuwa waje su Rahma suka yi, da sauri Aminu abokin Prince ya karasa wajan tare da fara karkaɗe masa jikin sa.


Ɗago idanuwansa Prince ya yi wanda suka kaɗa suka yi ja ya ce. "Har ke wace ce da har za ki ɗauki shayi ki watsa min?, kin ɗauka ke wata sarauniya ce da za ki abinda ki ka gadama kuma a ƙyale ki?, wallahi saikin biya farashin abinda ki ka yi min".


Ajiye kofin shayin Bhatool ta yi tare da duban sauran ɗaliban da ke kallonsu ta ce. "Muddin wani ya ce zai ƙara shiga rayuwata a makarantar nan, toh abinda zan yi masa sai ya fi na wanda nayi wa wannan shashashan". Ta faɗa tare da ɗauka jakarta kana ta nufi hanyar fita daga makarantar.



Da sauri su Hafsah suka dubi Prince tare da bashi haƙuri sannan suka bi bayan Bhatool.


Kallon Prince Aminu ya yi ya ce. "Dama na faɗa maka, ita ba kamar sauran matan makarantar nan take ba, kace zan sha mamaki idan kaje, yanzu ai gashi nan na sha mamakin sosai".


Cikin huci Prince ya ce. "Wallahi ba zan barta ta ci banza ba, saina ta yi nadamar abinda ta aikata min".



Bhatool kuwa, kai tsaye inda motar ta take ta nufa tare da umartar direbar ta da ta tada mota su tafi.



Ta faɗa tana mai shiga cikin motar. Kafin su Hafsah su isa inda take motar ta su ta bar wajan.


Gefe guda kuwa, waɗan da suka ɗauki videon yadda Bhatool ta watsa wa Prince shayi suka yi posting ɗin shi a social media kan kace me labari ya bazu a makaranta.



Kai tsaye gida motar Bhatool ta nufa. Mintuna Talatin suka isa gida. Yayin da mai gadin ta buɗe ƙofar gate ɗin.


Bhatool ba ta jira direbar ta yi parking ba, ta fito daga cikin motan sannan ta nufi part ɗin ta. Ganin ranta a ɓace ya sa kowa ya sha jinin jikinsa.


Kai tsaye upstairs ta nufa tare da shiga ɗakin ta tana mai wurgi da duk wani abu da ta yi harba da shi. Huci ta soma yi tana mai dafe kanta tare da wargatsa gashin kanta, tare da zama  kan gado.


Nan take hawaye suka fara sauka bisa ƙuncinta. Cikin baƙin ciki ta ce. "Wai me ya sa ba za ku fita daga cikin rayuwata ba ne?, a yayin da nake gudun ku, ku kuma kuna ƙara kutsa kai cikin rayuwata, me ya sa ba za ku fahimci irin tsananin tsanar da nayi muku ba?".


Daidai lokacin ta ji ana ƙwanƙwasa mata ƙofa.


Da sauri ta share hawayen ta tare da jan dogon numfashi ta dubi hanyar ƙofar waje ta ce. "Waye?".


Nan ƴar aikin da ke bakin ƙofa ta ce. "Madam ni ce, Oga ne yake neman ki".


Sai a lokacin Bhatool ta tuna cewa ɗa zu ya kira ta a waya.


Nan ta ce. "Ki ce masa bana da lokaci, ba zan je ba".


Jin hakan ya sa ƴar aikin ta girgiza kai cikin ranta ta ce. "Lallai yarinyar nan, mahaifin ki yana kiran ki amma ki ce ba za ki je ba, da a ce irin gidan da ake cin tuwon dawa ne, gidan talakawa irin namu ai da kin sha duka wallahi". Nan ta gyara tsayuwar ta tana mai galla wa ƙofar harara tamkar tana ganin Bhatool ta ce.



"Ya ce magana ce mai mahimmanci kuma dole ki zo". Ta faɗa tare da barin wajan da sauri gudun abinda zai biyo baya.



Jin hakan ya sa Bhatool ta ɗauki hula ta zira kana ta fito daga ɗakin ta nufi ɗayan part ɗin wanda ya kasance shi ne na mahaifinta.


Ko ina a tsaftace, babu abinda ke tashi a part ɗin fa ce ƙamshi mai daɗin ji. Chan na hangi dattijo zauna kan sofa hannunsa riƙe da newspaper yayin da idanunsa ke sanye da medical glass. Kallo ɗaya za ka masa ka gane cewa shi ɗin mahaifinta ne saboda kamar da suke yi harta ɓaci.


Ƙarasawa inda yake ta yi tare da harɗe hannayenta ta kawar da kanta gefe ta ce. "Barrister me ya faru ka ke kira na?".


Ɗago da fuskarsa mahaifinta ya yi tare da ajiye newspaper ɗin hannunsa, sannan ya maida hankalinsa da kallonsa kanta ya ce. "Bhatool me ya sa za ki kori Saude mai shara daga gidan nan?".


Kallonsa ta yi sannan ta saki murmushi ta ce. "Na kore ta ne saboda ta shigo da namiji cikin gidan nan, mene ne abinda ya shafe ka da hakan?".


Girgiza kai Barrister ya yi ya ce. Do you realize who you're talking to?".


Murmushi Bhatool ta yi yayin da zuciyarta ke cike da baƙin cikin ganin sa. Nan ta ce da shi. "Of course na sani Barrister".


Kallon ta Barrister ya yi ya ce. "Me ya sa ki ka kasance a haka ne Fatima?, mahaifiyar ki ba ha...

Bai kai ga ƙarasa maganar ba ta katse shi da faɗin. "Kada ka kuskura ka sako mahaifiyata cikin zancen ka domin baka cancanci ka kira sunanta ba, sannan kuma maganar cewa me ya sa na kasance a haka, kai ne sila. Dan haka baka da right ɗin da za ka yi min maganar da raina baya so ba. Sannan maganar Saude na riga na sallame ta, kuma babu me dawo da ita cikin wannan gidan, daɗin ta ma ba kuɗin ka nake kashe wa ba, kuma ba kai ka ɗauko ƴan aiki ba, ni na kawo su ina da right a kan duk abin da na gadamar yi da su".



A fusa ce mahaifin nata ya miƙe tsaye sannan ya ce. "Wai me ke damun ki ne Fatima?, komai ke kin tsani maza, aba abin ya fara yawa fa, yanzu ki dubi gaba ki ɗaya ƴan aikin gidan nan duk mata ne, driver kin kawo mace, mai wanki da guga kin kawo mace, a maimakon gateman kin saka gatewoman, duk kin cika mana gida da ma'aikata mata sai ka ce masifa. I can’t stand what you’re doing in this house anymore. Idan har ban iya sauya wannan aƙidar ta ki ba, toh in sha Allah wani zai sauya wannan aƙidar ta ki".


Murmushi Bhatool ta yi ta ce. "Kamar yadda ka sani babu abinda zai taɓa chanzu wa, har abada tsanata a kan maza ba za ta taɓa gushe wa ba, domin kun dasa min tabon da ba zai taɓa gaguwa ba a rayuwata. Babu wanda ya isa chanza min aƙida, kuma kaima idan har baka daina shiga harka ta ba a gidan. Toh za'a yi ɗayan biyu, ko ka bar gidan nan ko kuma ni na bar maka wannan gida".


Ta faɗa tare da barin part ɗin na shi.

Girgiza kai Barrister ya yi yana mai neman Allah ya maida ƴarsa hanya madaidaiciya, sannan Allah ya bayyana wanda zai cire mata wannan tsanar mazan da take yi.







_____________
Yaran Black Devil kuwa shirya komai na su suka yi, yayin da kowanensu ke sanye da fararen kaya suit tare da mask a fuskokin su. Yayin da shi kuwa Black Devil ke sanye da baƙin kaya da farin mask kan fuskarsa.

Gefe guda kuwa, tsakiyar gidan private jet ne a ajiye.

"Boss umarnin ka muke jira, yanzu mu ɗau hanyar Abuja". Cewar ɗaya daga cikin mutanensa.


Shiru Black Devil ya yi musu sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya ya ce. "Zamu tafi, amma saina fara fitar da munafikin da ke kaiwa ƴan sanda rahoto a cikin mu".


Zaro idanuwa waje Gangs ɗin nasa suka yi.


Kallonsu ya yi. Nan ya ga ɗaya daga cikin su ya yi sauri rufe wayarsa. Murmushi ya saki kana ya ce da shi ya zo inda yake.


Jiki na rawa ya ƙaraso wajan sa.


Duban sa Black Devil ya yi ya ce. "Zaki  me ka ke ɓoye wa ne a waya?".


Nan wanda aka kira da zaki ya ce. "Babu komai".


Haɗe rai Black Devil ya yi ba tare da dariya ko walwala ya ce. "Ba wasa nake ba. Common, show me what you're hiding". Ya faɗa cikin bashi umarni.


Da sauri ya fito da wayarsa sannan ya ce. "Boss dama wani abu nake kallo a facebook na wata yarinya da ta watsa wa wani ɗalibi shayi a jiki saboda ya ce zai sha shayi tare da ita".


Shiru Black Devil ya yi sannan ya ce. "Let me see".


Ya faɗa tare da karɓar wayar  hannunsa.  Nan ya ga videon yayin da ya ga yadda Bhatool take ta yi masa rashin mutunci.


Murmushi ya yi na ɗan wani lokaci kafin daga bisani ya haɗe ransa. Bashi wayar ya yi sannan ya ce. "Wannan yarinyar yar gidan wace ce da za ta yi wa namiji irin wannan rashin mutuncin?".


Nan zaki ya ce. "Boss ni kaina ban san ƴar gidan wace ba, amma idan kana so zan nemo maka duk inda yarinyar take".


Kallon banza Black Devil ya watsa matsa sannan ya ce. "Me zan yi da ita idan ka nemo?, bana da buƙatar. Yanzu a bar wannan maganar, ku wuce mu tafi kan mission ɗin mu na gaba".


Nan suka nufi inda private jet ɗin take tsaye. Yayin da matuƙin jirgin ya kasance a cikin tuntuni. Buɗe masa ƙofa yaransa suka yi sannan Black Devil ya shiga ciki, nan gaba ɗaya suka shiga cikin jirgin. Cikin ƙanƙanin lokaci mai tuƙawan ya tayar da jirgin sannan suka nufi hanyar Abuja.






*WANNAN SHI NE FARKO, KO YA WANNAN TAFIYAR ZATA KASANCE MUJE DAI ZUWA🤸‍♀️💃💃*

*WANNAN LITTAFIN PAID BOOK NE A NAIRA #500 KACAL*.

*IDAN KUNA SHARING DA LIKING ZAN BAR MUKU A FREE BOOK*


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA MB💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU.