Page 3
by @rukyelmuaz
RIKON KAKA
✍️Written By Rukayyat
(Rukyelmuaz)
***
YOTA
Page 3
Kowa tsoron fitinar ta koma kanshi yake, hakan yasa kowa yaƙi bashi ruwa. Ga Haisu ta kama ƙugu ta rike kam, tana jiran taga wani mai ƙararran kwanan ne zaiyi gangancin shiga wannan rigimar.
Faɗuwa ƙasa ya yi, yana burgima yana a bashi ruwa. Amma sam yaran gurin sunƙi kulashi.
Delu Mai Ɗan wake ce daga nesa taji ihu ga kuma gurin an taru tayi saurin ƙara tahowa inda taji ƙarar.
Delu Mai Ɗan wake jin ƙarar ihu yana kara tashi gurin.
Hakan yasata idasawa da gudu domin ganin me ke faruwa.
Isowarta keda wuya, ta fara salati, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'ilafa ilallahu!” yanda take salatin kanshi abin dariya ne, domin bata iyaba.
Tukur bai daina ihun neman taimaƙon a bashi ruwa ba hakan yasa Delo Mai Ɗan wake rugawa da gudu neman ruwa.
Maƙwafta ta shiga da gudu, saigata da ruwa cikin bokitin wanka kamo Tukur dake kwance yana ihun neman taimako tayi, ta fara wanke mishi ido tana fadin, “waye ya watsama wannan miyar? kayi tuntuɓe ne ka faɗi ne haka??.”
Atika dake gefe, tana tunanin ya zatayi da abinci babu miya, ta ce.
“Wallahi miyar shinkafata ce ƴar Larabawa ta watsa mishi a fuska.”
Cikin ma'maki, Delu Mai Ɗanwake ta kalli Haisu, dako a jikinta batajin tayi kuskure, ta ce,
“kedai wannan jika ta Hasatu, kin zama annoba a kauyen nan.”
Murguda baki Haisu tayi, ta ce, “ai saiki fara tambayar abinda ya faru, bawai ki yanke hukunci ba ko.”
Ta ƙare maganar cikin yanayin rashin kunya da murguɗa baki tana wani buga kafa kamar wacce zata tashi sama saboda masifar.
Dalu Mai Ɗan wake batace komiba, taci gaba da wankema Tukur fuskarshi da har yau ya kasa buɗe ido.
Jikin shi yayi sharkaf da ruwa, dawowa hankalin shi ya yi sannan a hankali ya fara, bude ido kamar bazai buɗe duka ba amma yana iya kar ƙokarin shi ya buɗe idon duka hakan yaƙi yiwuwa.
Kallo ɗaya Haisu tayi mishi ganin yanda yake wani rufe ido da buɗewa kamar wani sabon makaho tayi tsaki, "Mtwwwwwwww".
Ta ɗauke kanta, daga inda yake taja hannu Mairo, da tun farkon da Tukur ya faɗi kasa ta tafi sumar tsaye ta gama ruɗewa don wallahi duk fitinar ta bata rigima irin ta Haisu domin tasan ita Inno tsaf zata aikata doguwar suma in ta ce zatayi abinda Haisu keyi exactly.
Sannan tun farkon rigimar bata ɗauka abin zai kai haka ba har ayi wannan rigimar akan Gyaɗa ba.
Gefen suka koma, Haisu ta samu guri ta zauna tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.
Delu Mai Ɗan wake ta taimakawa tayi ta kamo Tukur ta maido shi gefe ɗaya ya zauna.
, Domin abinda yakeji a idon shi kawai ya hanashi taɓuka komi domin har yau bai ɗago idon shi ya kalli mutanan gurin ba, bare fara tunanin wani matakin zai ɗauka.
Ganin baida niyyar tashi ne yasa Dlu Mai Ɗan wake kamo shi ta miƙar da shi ta ce.
" Wannan ba dan gurin Iya Mai Ƙosai bane??
Kamar mutanan gurin jira suke tayi tambayar caraf suka haɗa baki suka bata amsa
" Shine Tukur Mai Caji ne.
Shi ko gogan naku iya kai kawai ya iya dagawa ganin hakan ne yasa Delu ce wa.
" To zonan tunda hanyar ku nayi in raka,ka ka wuce gida.
Ƙin motsawa Tukur yayi saima ce wa da ya yi
"Wallahi sai na ci uwar yarinyar sannan zan bar gurin nan.
Furucin da yayi ne yaba Haisu damar sake waigo wa ta kalleshi ta ce.
"Uwata na ƙabari kaje ka ƙwa'ƙulo gawarta inka isa sai ka cinyeta tunda maye ne kai.
Jin daga inda sautin ya fito ne yasa Tukur cikin kasalar jiki da yanayin da yakeji a fuskar shi ya juya a fusace zaije inda take ya bugeta.
Da hanzari Delu Mai Ɗan wake ta rike shi tana jan hannun shi akan yazo su wuce amma fizgewa yake sakeyi ganin yanda yake tubu rewa yaba yaran gurin dariya da ita kanta Haisu ɗin magana ta fara tana ce wa...
"Ai da kin sake shi wallahi yanzu ruwan barkono zan jiƙa in watsa mishi.
Cikin tsokana ta fara dariya irin mai ƙarfin nan
"haha'haha ƙyal ƙyal ƙyal.katon kauye yaji kunya wayyo Allah cikina ta ƙarasa dariyar tana riƙe cikinta.
Raɗaɗin dariyar da take mishi ne yasa Tukur ƙara yun ƙurin kwacewa amma Delu Mai Ɗan wake ta riƙeshi ƙamm har zaninta na ko'korin kwancewa.
Tsawa ta daka mishi kai Tukur banison iya shege karkasa inyi tsirara gaban jiko'kina mana.
Yara suka ƙara fashewa da dariya ciki kuwa harda Haisu da dariyar ta tafi ta kowa, Domin ita abun daɗi yake mata sosai ganin tayi nasara akan wani ƙaton ƙauye.
Duk abinda ake yi Atika da Mairo jikin su yayi sanyi dukan su biyun akwai abinda zuciyar su ke saƙawa.
Mairo tunani ta ɗaya in wannan fitinar bata mutu ba ya zatayi da tarin gyadar dake cikin farantinta?
Inda a bangaren Atika kuwa tunanin ta taya zata saida abinci babu miya take tambayar kanta?
Da kyar Delu tabar gurin da Tukur ba don yaso ba sai dai yasa a ranshi dole akwai ɗaukar fansa.
Ajiyar zuciya mairo ta sauke ganin Tukur yabar gurin yanzu duk da tasan wannan fitinar bawai ta mutu ba ne.
Atika ce tazo inda Haisu ke zaune ta ce....
"Yar larabawa yanzu ya zanyi da abinci babu miya wa zan saida mawa Haisu ɗagowa tayi ta kalle Atika ta ce.....
"Ki samo mai da barkono mana yau kiyi fara da mai ai itama za'a saya.
Atika dake cikin halin rayuwa ko mutuwa akan wannan miyar domin tasan yau in duk garin Batsari gatanta ne wallahi ta koma da gayar shinkafa sai inna ta daketa magana tayi cikin muryan tausayi.
"Yar larabawa zuwa na kenan gurin nan ko ciniki banyi ba.
Miƙewa Haisu tayi tana haɗa kayanta dake a ƙasa ta ce.
" Zan kawo miki man gyaɗa da barkono amma kar ki biyo ni don wallahi in kika zo gidan mu na fasa"
Tana kaiwa nan ta ɗauki kullin gyaɗar da aka zubowa Mairo ta kawo ma ta tana ɗauka taga wasu yara tsaye sunyi gungu suna kallon ta.
"To munafukai ana tsara yanda za'a shiga ƙauye a bada labari ne???? Haisu ta faɗa tana kallon su jin furucin da tayi ne yasa Mairo saurin ce wa..
"Yar larabawa don Allah kije ki kawo ma Atika man gyaɗan da kayan haɗin kin ga hadari ne ke yaɗuwa tayi ta saida tabar gurin nan.
Haisu ta turo baki "shikenan bari inje in dawo karki tashi ki jira ni fa yanxu zan dawo"
Tana faɗin haka bata jira amsar Mairo ba ta ruga da gudu.
Atika ce ta kalli Mairo da fuskarta irin ta tausayi ta ce.
"Don Allah kina ganin zata kawomin kinsan halin Haisu??
Amsa Mairo ta bata "ehhhh ai inda bazata kawo miki ba to tun anan zata ce bazata biya ba".
Ajiyar zuciya Atika ta sauke ta reda samun guri ɗaya ta zauna.
Tun isar Kaka gida take kallon hanya taga shigowar Haisu amma shiru kake ji malam ya ci shirwa.
Zaune ta ke a falo kan kujera tana kallon ƙofar waje, don ganin mai shigowa sallama taji.
"Assalamualaikum warahamatullah"
Amsawa tayi " Wa'alaikumussalam".
Ba tare da an ɗauki lokaci ba taga matasa biyu ne da yara ɗauke da kayan abinci ana shigowa dashi basai ta tambaya ba tasan tabbas saboda ƙarshen wata yazo ne.
Anyo musu ai ke daga Abuja miƙewa tayi taje gaban wardrobe ɗnta, da take ajiye, ajiye Naira Dubu ɗaya ta ciro domin ta saba duk sanda aka shigo mata da kaya tana bayar da tukuici takowa ta yi a hankali ta fito tsakar gidan.
" Sannun ku da aiki kunji yaran nan sauƙin garin babu rana yau amma duk da haka akwai nauyi kayan ". Ta faɗa tana kallon masu shigo da kayan cikin gidan.
Matasan suka amsa mata da yauwa Kaka Hasatu suna kaiwa nan a maganar su suka juya waje domin cigaba da shigowa da kayan dake waje.
Tafiya take ranta fasss babu tunani ko damuwa face burin taje ta kawo ma Atika man gyaɗa da barkono abinda ta hanga ne yasata murmusawa da faɗin.
" Aiko yau ba man gyaɗa ba ko sabuwar miya Atika keso saina kawo ma ta kayan haɗi"
Wata yar rausaya ta fara a tsakiyar layin alamar yaufa garin nasu ne. Bakar motar da, ta hanga a kofar gidansu ƙirar Range Rover black anyi packing ne ya bata ya ƙini da tabbacin ba kowa bane fa ce daddy
"Ruwa narke gari" ta faɗa tare da ƙara rike hijabita kammmmmmm tana shirin rugawa.
Jazuli mai kayan gwari dake zaune a runfa ya ce
"Iya gidanku muguwar yarinya kawai in ruwa ya narke gari gidan ku zamu samu kasuwa"
Waigawa tayi ta mishi gwalo domin yanzu cikin farin ciki take da tunanin samun kuɗi ta sake faɗin "narke gari.
Ta zuba da gudu ko waige bata yi ba bare taga me zaice ma ta.
Domin kuwa duk sanda akace daddy ne zai shigo Batsari da kan shi ya kawo musu sakon ƙarshen wata to tabbas tasan tanada sabbin dinki da kuɗin kashewa siyayyar binni kuwa agunta zaka fara ganinta cikin kauyen.
Shi yasa wasu ke kiran ta da "yaro yabar uwar shi ya bi ki.
Don kuwa in ta tara tawaga a gida ana wasa to komin kiran da uwa zata ma yaron ta sai in yana shakkar ta zai zo ƙiran nata.
Da guduta, ta ƙarasa gurin motar ganin glass ɗin an sauke shi kasa zagawa tayi tare da faɗin...
"Dadyn Abuja Oyo"...... sauran maganar ce ta maƙale domin ta kasa ƙarasa maganar.
Ganin waye a motar zaune abinda tunani ta ko hankalin ta bai taba kawo,wa ba ne.
To taya za'a yi haka kuma???? Ina Dady yake ko dai yana cikin gida shi da Kaka ne ita kaɗai ke tambayar kanta kuma taba kanta amsa.
Wanda kuwa tun lokacin da take tsaye agun mutumin dake cikin motar tunda yaji muryan ta tana Oyoyo kallo ɗaya ya juyo ya yi ma ta ya maida kanshi ya sake kishin giɗa jikin kujerar motar da ya kwantar yake ɗan hutawa.
Kallo ɗaya zakama fuskan shi kaga tsantsar kamar dake tsakanin shi da ita. Sai,dai ya fita manyan idanu da fari dogo ne wanda duk da yana kwance a motarm bai hana bayya na tsayin da yake da shi ba matsa kaicin jiki da faɗin fuska haɗe da tsayin fuska gare shi ga bakin sajen da ya fara taruwa ya kwanta a fuskan shi wanda ya kara fitowa da hasken fuskan shi sosai da dogon hancinshi.
Turo baki tayi a hankali tayi magana batareda sanin zataje mishi ba.
,"Kai innalillahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan bala'i yazo mana yanzu zai fara kiran mutum duk bayan daƙiƙa ɗaya kamar kuturu ko makaho Allah yasa yau zaka koma garinku.
Ta juya zata tafi cikin muryar irin ta gajiya ya ce.. "Ke daga gidan ubanwa kike????????? ". "Sannan baki iya gaisuwa ba?"
Turo ƙaramin bakinta ta yi ta nuna kanta da yatsan Hannunta ta ce.
" Niiiiii?????????? Daga inda yake bai motsa ba ya ce "A'a da kaina kike".
Dawow gurin glass din window ɗin motar tayi sannan ta yi magana irin yanda kasan wata ƙaura ta ce..
"Ina kwana yaya zuraibib"
Yanayin da tayi maganar ne ya bashi dariya amma yaƙi yin ta a fili a zuciyar shi ya ce.
"Yarinya kamar ƴar dambe kalli yanda take magana yanda kasan ta haɗu da abokin dambe
zasu gwafza .
Inda a fili kuma ya ce "kinason bakin,ki yayi jini ne? Tun yaushe nike gyara miki Julaibib ake ce wa ba zuraibib ba??"
Turo baki ta sakeyi a karo na babu adadin tun tsayuwarta take turo baki kamar zata ciza motar. ta ce
"Ni gida zanje Kaka ke nema na kuma yunwa nikeji"
Tana kaiwa nan bata jira amsar shi ba ta faɗa gidan da gudu.
"Kaka! kaka! kaka!" Kiran kaka kawai takeyi da saurinta tazo kusada inda ta hangi Kakar zaune ta ce
"Kaka me ya kawo wancan basamuden gidannan"
Cikin rashin fahimta Kaka take kallonta,
"Wani basamude kike magana ke Hafsatu???? Kaka ta tambaya domin ita dai mutum ɗaya tasan Haisu na kira da wannan sunan kuma baizo gidan ba.
To basamude nawa kika sani don Allah kice in an sauke kayan ya tafi basai ya tsaya mana a gida ba.
Kakan miƙewa tayi tsaye ta nufi ƙofar gida tayi banza da Haisu ta wuce domin tabbatar ma da idon ta da gaske ne domin ita yaran da ta sallama yanzu da suka gama shigowa da kaya basu ce ma ta da wani ba.
Ta zaci Sani Me Acaɓa ne da akeba saƙon su yana kawowa duk ƙarshen wata .
Rukyelmuaz
***
RIKON KAKA