SHI SO DABAN YAKE

Babi na takwas

by @dijensy



8



     Saurin turesa ta yi a dirice ta cakumo towel ɗinta tana rufe ƙirjinta tuni hankalinta ya dawo jikinta hakan ya karkato da hankalin Hassan da ya lula tunda yake bai taɓa jin irin abinda yaji yau ba ga wata ɗiya mace hasali ko riƙe hannu wata bai taɓa yi ba “Kada ka sake kusantowa kusa dani irin haka”Jiddan ta faɗa tana juya masa baya sai ya ji ba daɗi lokaci guda ya shiga dayasanin abinda ya yi sam ba ya so ya mata tilas lokaci mai yawa ya ware musu domin su fara fahimtar junansu ya fi so duk wani abu da zai shiga tsakaninsu sai da izininta sai a sanda ta shiryawa hakan baya son mata gaggawa.


  “Ki gafarceni ki yi haƙuri Jidda i am very sorry”Ta turo baki tana tuna alkawarin da tawa kanta bazata taɓa amincewa ya kusanceta ba har zuwa sanda zai gaji dan kansa ya sauwake mata ita ba ma tasan yadda akai bata fargaba ba har ta kai ga ya yaye mata towel wani ɗan banzan haushinsa yana mamayeta,Hassan ya tashi daga kan gadon Jidda ta ɗauke kayan sawarta na bacci tana shiga banɗaki ta saka kafin ta fito ya ja bargon shinfiɗarsa ya shinfiɗa a ƙasa ta ɗare kan gado tana yafa blanket rabi a ɗari ɗari tayi bacci don gani take kamar zai hawo kan gadon ya sake taɓa mata jiki.Jidda har washegari fuskarta a tamke Hassan duk abin ya damesa fitar sassafe yake baya so ya tafi bai ji daga bakinta ba ko da kalma ɗaya ce yana son yaji ta furta bayan da ta idar ko azkar bata yi ba ta ɗare kan gadon ta ja blanket ya shiga banɗaki ya yi wanka yana sa kayansa ya fito cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala shirinsa ba karyawa yake ba daman sai dai idan ya je can ya nemi abu ya ci wani lokaci ma sai rana.Dede gefen gadon ya zauna daga ƙasa yana ɗora gwiwoyinsa ya sa hannu yana dafa kan gadon yana jin kamar ya taɓo ta amma bazai ma fara ba cikin tattausan lafazi yake maganar “Jiddana na tuba kiyi haƙuri bazai sake faruwa ba kinji ,nasan ban kyauta ba nayi garaje ina neman gafararki ki agaza ki yafemin kar na fita da fushina a ranki Jiddana”.


   Jidda tana jiyo sa tayi luf ya yi kusan minti biyar kafin daga baya ya tashi yana ɗakko biro da takarda ya rubuta mata note na bada haƙuri ya ajje mata gefen gadon kafin ya fita ta gyara kwanciyarta tana lulawa baccinta sai goma da rabi ta buɗe ido da takardarshi ta fara cin karo tana karantawa ta ja tsaki ta cukwikwiye ta jefar.



  Yau ma kamar koyaushe wuni guda tana ɗakin Hassan kuwa ya ƙosa lokacin tashi yayi ,koda ya tashi daga aiki supermarket ya je ya mata shoping  na su chocolate biscuit da chewing gum kwarya kwarya dai dai halinsa ya siya mata tsire a bakin titi mai nama yana tsokanarsa yaji labarin ance yayi aure ba ko gayyata shidai Hassan murmushi kawai yake har ya baro wajen ya dawo gida da tsarabar da yayo mata ƙullin da yayiwa su Amal ya kira Usman ya bashi suna godiya suka tafi ɗaki da ganinsa ta canja fuska yayi sallama taƙi amsawa ya ajje mata ledar kan tebur.Yanzun ma sake bata haƙuri yake amma Jidda zaka rantse batasan da mutum a ɗakin ba wani waje daban take kalla Hassan ya rasa da wani siga zai bata haƙuri ta sauraresa.Yayi shiru ya nisa kafin ya ce “Gobe ina off ki shirya zan kaiki gida ki gaisheda Baba”.Sai a sannan ta ɗago ta kallesa yayi murmushi.”Da yaushe kike son mu je?da safe ko da rana?”Ya tambaya ta jefeshi da kallo rai a haɗe kamar bata so  “Da safe”Ta amsa a ciki ya jinjina kai yana jin daɗi ta yi magana,yau ya je makarantar magriba sai wajen tara ya shigo gida bayan fitarsa da maghriba Jidda ta ɗare kan gado tuni ta ƙosa gobe tayi ta ganta gidansu da wannan tunanun tayi barci.


    

     Anty baby na tsakar gidan ta ji sallamar Jidda cak ta tsaya tana kallonta da mamaki Jidda ta falfalo da gudu tana rungumeta cikeda kewarta ta ɗago da kai bakinta ko rufuwa baya yi “Wayyo nayi missing ɗinki Antyna ina Umma tana ɗaki?”Ta jero mata tambayar ta jinjina mata kai suka shiga parlour tana faɗawa jikin Umman tana zaune kan sallaya ta idar da walha “Zaki danneta haka sai kin ji mata rauni Jidda kina nan da halinnan tohm jiya ta gama karɓar allura”.


  Fuska ta ɓata tana saurin sauka daga jikinta “Wai haka Ummanmu? Baki da lafiya daman?”Ta tambaya Umma ta murmusa “Ai na samu sauki ma duk kuna lafiya?”Umma ta ƙare da tambaya Jidda ta amsa da lafiya “Ina Abdallah?”


 “Basu dawo daga tahfiz ba”.Umma ta amsa Jidda tuni ta sauke mayafinta tana cilli dashi kan kujera ta zauna gefen Umma “Kamar na shekara haka nake gani ,Umma ba wanda ya zo min”.Ta ƙarasa maganar tana rage muryarta bata sani ba ko Baba yana nan.


 “Jidda zarya kike so muyi tayi? Hassan ɗin duk suna lafiya?”


 Kai ta giɗa Jidda ta dubi Anty baby ta tashi tana sake rungumota tana dariya “Naga kinyi ƙiba Anty”.


 “Daman ke kike ramar dani ai ba kya nan bakina alaikum”.Anty ta faɗa da zolaya Jidda tayi kamar zatayi kuka Anty baby tayi dariya “Kema kinyi kumatu”.


  Sallamar Baba suka ji ya shigo gidan yana tsayawa ƙofar parlourn Ta saurin rissinawa tana gaisheshi kanta sunkuye tana wasa da yatsunta zaka rantse wata nitsattsa ce Baba ya amsa fuska ba yabo ba fallasa “Ba a kai masa carpet ko kujera ya zauna ba  kun barshi a tsaye?”Cewar Baba Umma ta kallota “Laa tare kuke daman Jidda?”


Bata amsa ba su Yaseer suka yi sallama Baba ya sa su buɗe ɗakin su ya ibrahim da ya zama sitting room na baƙi ya sa Hassan ɗin ya shigo kafinnan sai da ya gaishe da Umma cikin girmamawa sannan Anty baby ya koma sitting room duk kunya ta cikasa abin sha da snacks da aka kawo masa ma yaƙi sha ya tashi zai tafi Anty baby ta korata ta je gurinsa don ta shagala tana zaune kan gadon nata.”Don kinga ba tare zaku tafi ba kar kisa mu ce masa ya jiraki ku koma tare”.Jidda ɓata fuska  tayi tana tashi ta fita a sitting room ɗin ta samesa ko zama batayi ba “Zuwa yaushe ne zan zo mu tafi?”Ya tambaya ta ɗan kallesa “Sai can yamma”.Ta amsa shima don tasan Baba zai iya mata faɗa idan ta kai dare Hassan  ya ce ya amince jidda ba sallamar arziƙin da ta masa ta yi komawarta ɗakin Anty Baby bayan tafiyarsa.


  “Anty baki ga wasiƙata ba wai?”Ta tambaya tana ta buɗe mata drawer kamar ta mata ajiya.


“Sai akai yaya?”Cewar Anty Baby Jidda ta shagwaɓe fuska “Ni kaɗai fa yake bari idan ya fita ba waya hannuna don Allah ki roƙamin Umma ta bani wayata na tafi da ita”.


  “Sai kin ƙara yin hankali idan kina son waya damu ki ari wayar mijin naki har zuwa lokacin da zaki sake riƙe taki”.Jidda ta shiga roƙarta da magiya da kyar anty baby ta amince ta ce zata faɗawa Umman.Jidda wuni guda tayi a gidan da yamma kamar yadda ta faɗa masa ya dawo su tafi Anty baby ta tana bata wayarta lokacin da take shirya mata kayan da zata tafi dashi wasu daga cikin kayanta na sakawa ta ɗauka Anty baby ta mata packaging snacks chin chin da cupcake ta ce ta kaiwa Hassan da Anty Ruƙayya dayawa ta ɗiba ta haɗa mata wasu kayan sawan ma sai da ta rage Umma tace su Abdallah zasu kawo mata ragowar ba ƙaramin daɗi taji ba Anty baby ta kirata ɗaki tana tsareta da ido “Kinyi amfani da magungunan da na haɗo miki a akwatinki ?”


  “Nayi”Tayi ƙarya Anty ta kalleta “Ki kula da tsaftarki sannan ki cigaba da haƙuri komai zai dai daito kuma kinyi sa a Hassan bai kamada mai matsala ba na lura ki dinga jin magana pls ,zan sake yo miki wani aiken kuma ki rage lalaci yanzu ba kamar da bane kada ki naɗe ƙafa matar brother shi ta dinga komai dagani tana da kirki bazata baki matsala ba”.Ta faɗa Anty Baby Jidda kai kawai ta jinjina tana mai kallon Anty baby tana harhaɗo mata turaren wuta da humrah da take dasu ba yawa kaf ta haɗo mata ta bata  ta karɓa Abdallah ne ya riƙe mata kayan tana mai musu sallama ta rungume Umma kamar bazata tafi ba Baba ya fita tun ɗazu shikaɗai ne bata wa sallama ba ta fita ƙofar gidan tana iskeshi ya ɗakko mata keke napep shata Abdallah yasa mata kayan a baya ta shiga ciki shima hakan tana ɗauke kallonta daga kansa Abdallah takewa bye bye har mai keken ya ja suna barin unguwar.




On Arewapen

Comment and like