Page 03
HALINSA
©SALMA AHMAD ISAH
Page | 03
A kwananta na biyu ya dauketa zuwa gidan kakarsu wanda yake Galadima Cinema, a nan garin Ngurun. Kuma yana sauketra a gidan ya shiga suka gaisa, sannan yace ya tafi kasuwa, idan ya anjima zai dawo ya dauketa sai su koma gida. Haka kuwa aka yi, ya tafi ya barta a wurin kakarta, wadda ta haifi mahaifinta, tsohuwar ta yi farin cikin ganinta sosai, domin sun dan kwan biyu ba su hadu ba. ita ma Rahma ta ji dadin ziyarar da suka kaiwa kakar tasu sosai, domin har ga Allah ba ta son zaman gidan nan, ga shi dai daga ita sai shi ne a gidan, a tunaninta kamata ya yi ace ta ji dadin hakan, kamata ya yi ace kwanakin farko na amarcinsu sun kasance mafi dadi abin tunawa a tsawon rayuwar aurensu, tana hasashen ace sun kasance ranakun da suka kasance mafiya kyau suka kuma kafa tarihi a rayuwarsu. Amma sai ta ga sabanin hakan, domin sam gidan ba ya mata dadi, duk da dai ta lura shi ma ba ya fita ko ina, da alama yana hutun auren nasu ne. amma babu wani abu na musamman da ya faru tsakaninta da shi. jiya ta fara girki a gidan, idan ta yi kuma za ta shiga har dakinsa ta sanar da shi ta kammala abinci, idan a dakin zai ci sai yace ta kawo masa dakin, idan kuma a waje zai ci zai ce ta aje masa a falo. Bai taba mata tayin su ci tare ba, ita ma kuma ba ta taba naima ba, kawai sai dai ta zauna a dakinta ita kadai, idan dare kuma ya yi ta koma dakinsa su kwana tare, da asuba ta tashi ta dawo dakinta abinta. Haka kwanakin biyu suka wuce, ba komai, ba wani abu special, kullum gidan shiru, ba kuma wai dan babu kowa a ciki ba, sai dan haka mai gidan ya zabi rayuwar gidan ta kasance. Jin sanyin ruwan da Iya ta dora mata shi a kan hannunta, a bazata ta kalleta tana janye hannun nata.
“Tunanin me kika ne Ramatu?”
Cewar iya da ta kira sunanta ya fi sau uku amma ba ta amsa ba. Miyau ta dan hadiya, ta mika hannunta ta dauki ruwan da Iyan ta aje, ta fasa ledae pure watern, sannan ta kai bakinta ta sha kadan, ta sauke ledar, Iya da ta gama karantar yanayinta tun shigowarsu, ta zauna kusa da jikartata.
“Ramatu!”
Rahama ta kalli Iya kamar za ta yi kuka, irin ta samu wanda zai ji damuwar nan tata.
“Kin san ni na sa a hada aurenki da Umar ko?”
Kanta a kasa ta gyada shi.
“Kuma kin san ina sonku ku dika biyu, ba zan taba yin abin da zan cutar da ku ba ko?”
Nan ma ta gyada mata kai. “Na san ba komai kika sani ba a kan Umar, amma Allah ya jarabci Umar da wata kalar zuciya, ya taso da wasu irin halaye da kaf ahalin nan babu me irinsa, babu wanda ya sani, amma damuwar dabi’un Umar shi ya sanyawa mahaifiyarsa ciwon zuciya har ta kai ga barin duniya!”
Idanuwanta Rahama ta zare cike da tsoro domin da gaske ba kowa ya sani ba, ciki kuwa har da ita, amma sai Iya ta yi saurin girgiza mata kai.
“Ya fi karfin kowa, babu wanda yake fada masa ya ji, ya ki tsayawa ya yi karatun allo ballantana ya yi boko, tun da ya gama aji shida na sakandire bai sake shiga aji ba, yau ga shi nan shekararsa talatin da uku, anyi-anyi da shi ya yi aure ya ki, ni da mahaifinsa kuma muna so ya yi auren, domin a ganinmu watakila idan ya yi auren Allah ya sanyaya zuciyarsa ya shiryu ya dawo kan hanya, daga karshe mahaifinsa ya yanke shawarar a duba yarinya a cikin ahali a aura masa, ni da kaina na zabeki a matsayin wadda za ta dace da shi. saboda na san hankalinki, da iliminki da kuma kyakkyawar tarbiyyar da kika samu, idan Allah ya so sai ya shiru ta sanadiyyarki”
Lebenta na kasa ta saba da na kasa cikin damuwa.
“Na san yanzu za ki ga kamar da wahala, amma na san za ki iya Ramatu, dan haka ki dage kin ji, na tabbatar miki da idan ya sauya sai kin fi kowa jin dadin zama da shi!”
Ta sauke kanta kasa cikin tunani, tana hada maganar Iya da da ta Hajeer, tun da haka ne ko z ata kara dagewa, dama da niyyar da ta shigo gidan ke nan, dan haka za ta kara zage damtse, ai wannan kamar jahadi ne za ta yi, kuma ko ba aure shi dan uwanta ne, dan haka za ta yi domin Allah, da kuma son da take masa, kuma domin kwanciyar hankalinta, ta tabbata idan har ba hakan ta yi ba zamanta da Umar ba abu ne mai iyuwa ba. sai daf da marib sannan ya dawo gidan ya dauketa, bayan ya yi wa iyan da wasu daga cikin kawunnansu da suka cikin gidan Iyan alkairi, ta kula duk rashin halinsa yana da kyauta, abin hannunsa bai tsole masa ido ba, sauran ma idan Allah ya yarda za ta sauya masa su.
A rabar gidan nasu ya yi parking, ta fito rike da laidar kayan da Iya ta bata, su Kuka ne, da kanwa da sauran tarkace. Bai ce mata komai ba ya shi ma ya fita, ya yi alwala a famfon bayin bishiyoyi, sannan ya fita zuwa masallaci. Bayan An idar da Sallah a hanyarsa ta dawowa ya tsaya a wani shago ya siyi ruwa sbd ya ga babu a gidan, ya riko ledar ruwan a hannunsa ya nufo gidan da ita, tris ya yi lokacin da ya karaso kofar gidan ganin abokinsa Mustapha. Ya ja tsaki a kasan numfashinsa, ya dauke kai ya yi kamar bai gan shi ba, kawai ya nufi kofar gidan zai shiga.
“Umar!”
Mustapha ya kira sunansa lokacin da ya gifta shi zai wuce, ai ko kamar mai jiran ya kira sunan nasa, yana kora ya juyo a fusace yace.
“Bana fada maka kar ka sake naimana ba?”
Mustapha ya yi murmushin takaici, yana iya tuna hakan garai a cikin kansa, haduwarsu ta karshe sun samu sabani a kan ya fada masa gaskiya kamar yanda suka saba, shi Mustapha ya yi ilimi sosai, daga na bokon har na arabi, sabanin shi Umar, kasuwa ce ta hadasu har suka zama abokai sosai duk da bambancin halaye da suke da shi. kusancin da suke da shi yasa shi Mustapha a duk sanda Umar zai yi ba dai-dai ba ba ya kyashin ya gyara masa, sannan ya fada masa gaskiya, kuma duk sanda hakan za ta faru sai sun samu sabani, kuma kar ku ce Umar din ne yake naiman sulhu, a’a Mustpha da kansa yake naiman sulhu, da farko shi ma idan sun yi fadan watsar da Umar din yake yi, amma daga baya da ya fuskanci cewar Umar fa bai san inda yake masa ciwo ba, sai kawai ya share shi a duk sanda suka samu sabani, shi da kansa zai naimeshi su shirya, kawai saboda nan gaba idan ya yi ba dai-dai ba ya ankarar da shi. amma wannan sabanin da suka samu na karshe ya munana, dan shi kansa Mustaphan sai da ya yi fushi ya share Umar din na wasu kwanaki, ganin yana tifka ta baya tana warwarewa, domin duk abin da yake yi wa Umar din har yau ya kasa gyara halayensa, a godewa Allah ma ya gyara wasu kadan, irinsu zuwa masallaci a kan lokaci, da shi kansa karatun sallah, da yawan ashar da abin da ba a rasa ba. shi yasa ko da yaushe yake samun yakinin cewa wata rana hakarsa za ta cimma ruwa. Jin batun cewa Umar din ya yi aure yasa shi zuwa ya naime shi domin su sulhunta, ganin fadan nasu ya dauki kwanaki.
“Ka san ai bani da zuiya!”
Mustapha ya amsa masa.
“Idan abin da ya kawoka ke nan za ka iya barin kofar gidan nan, bani da lokacinka!”
“Ni ina da naka, yau nake samun labarin ka yi aure, yanzu duk yanda nake da kai sai a kasuwa zan ji batun aurenka?”
Umar ya ja tsaki ya juya zai shige gidan ta karamar kofar gate din gidan.
“Ka tsaya kaikuwa!”
Mustapha da ya riko rigarsa ta baya ya fada, Umar ya juyo ya fisge rigarsa yana galla masa harara, kamar zai kai masa duka.
“Na san yanzu haka a ranka ka kikkifa mini mari ko?”
Cewar Mustapha yana murmushi, ganin kallon d ayake bisan da shi, domin ya san Halin Umar din tas.
“Har da naushi!” wannan karon a bayyane Mustapha ya yi dariya, ganin dariyar tasa tasa shi ma Umar din ya murmusa, sai ya fasa shuga gidan, suka zauna a nan kofar gidan suna ta hirar kasuwa, da kuma yadda bikin ya gudana, duk da dare ne kofar gidan tar da haske, saboda gidan da solar 24/7 ko da yaushe da haske. Ya kashe kudi sosai wurin gina gidan. Suna zaune a wurin har aka kira isha’I, suka tafi masallacin tare, suka yi sallah sannan suka sake dawowa kofar gidan, Umar din na kokarin bude wani sabon babin hirar Mustapha ya dakatar da shi da fadin.
“Hirar nan ta isa haka, ba ruwana da kwacewa amarya angonta”
Umar ya watsa masa wani kallo.
“Ji banza, to sai me? Malam idan hirar ce ba ka so sai ka fito ka fada mini, ba sai ka yi amfani da maganar wata amarya a matsayin uziri!”
Cike da mamaki Mustapha yace.
“Da gaske nake, as a married couple ya kamata ace yanzu kuna nan tare, duka yaushe ma aka yi auren ne Umar? Yau kwana uku ko hudu?”
“To ko ma da abin da ya fi gaske kake, ni dan na yi aure ba shi zai hanani yin azurin rayuwata yanda na saba shi ba”
Wannan karon Mustapha bai yi mamaki ba, domin ya san halin, sai dai bai dauka cewar ita ma amaryar za a mata hakan ba, ya yi imanin cewa Umar yana son yarinyar tun da har ya yarda ya aureta, ya san indai har ba ya sonta ba zai traba yarda da auren ba ko da sama da kasa ce za ta hade kuwa.
“Kar ka ce mini ita ma amaryar ana gwada mata dan hali”
Cike da kosawa da maganar Umar ya juya idonsa.
“Ka ga idan za ka zauna mu ci gaba da maganar nan ka zauna, idan kuma ba ka yi, hanya a bude take, a kara gaba!”
“a’a ba zan zauna ba wallahi”
“Ai shikenan!”
Ya juya da nufin shiga gida, wayarsa dake cikin aljihu ta soma kara alamun shigowar kira, ya tsaya yana saka hannnunsa cikin aljihun ya daukota lokacin da Mustapha ke masa sai da safe, bai ma amsa ba saboda mamakin ganin cewar Rahama ce ke kira, dagawa ya yi ya kara a kunnensa.
“Ya aka yi?”
Yana iya jin yanda muryarta ta yi dan rawa, kafin tace.
“Na ga har yanzu ba ka dawo ba ne”
“Ni yaro ne da zan je wani wurin na bata?”
Dan yi shiru, kamar ta girgiza kanta, ya latse wayarsa, sannan ya bude kofar gidan ya shiga. Mustapha da bai tafi ba, kasancewar wayar tasa ta dan ja hankalinsa ya tsaya a wurin baki sake cikin mamaki, wato dai ita ma ana mata, a ransa yace wannan wace ‘yar baiwar c ta iya auren Umar da wadannan halayen nasa? Domin a iyaka saninsa Umar din bai taba soyayya ba, ba shi ma da budurwa, ko da ace wata z ata zo tace tana sonsa sai dai dan kudinsa ba wai kuwa dan kyan halinsa ba, domin ba shi da hali sam, shi ya san hakan sarai. A fili yace “Allah ya kyauta!” sannan ya yi gaba, ya nufi inda motarsa take, duk da shi bai aje kowa ba dole ya koma gida da wuri, kasancewar garin nasu akwai curfew idan dare ya yi.
RAHAMA POV.
Tana shiga gida ta yi sallah, da ta idar ta fito ta shiga kitchen ta yi girki a gurguje, ta shirya komai, sannan ta koma daki, ta yi wanka, ta saka riga da wandonta na bacci, ta dora hijabin nan dai da Umar ba ya so ta saka, ta dawo falon ta zauna, tana jiran ganin ta inda bawan Allahr nan zai bullo. Ganin har aka kira isha’I bai dawo ba yasa ta yanke shawarar kiransa, bayan gabanta ya fadi sau ya fi a kirga ta yi jarumtar kiran wayarsa, ba ta ma yi zaton zai daga ba, sai kuma ya daga, ya fada mata abin da ransa yaso, sannan ya kashe wayarsa. Ita ma ta aje wayar tana fadin “Ni na jawa kaina” ba a fi minti daya ba sai ga shi ya fado gidan ba sallama kamar yanda ya saba, hannunsa rike da ledar ruwa, ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa mata ciki-ciki, sannan ya nufi kitchen ya aje ruwan a cikin store, har ya fito tana binsa da kallo, ganin zai shiga daki yasa tace.
“Na kammala abincin dare, a ina kake son ka ci?”
Ya dan dakata ya kalleta na sakkani, “Ki kawo mini daki, kuma dan Allah ki daina wahalar da kanki da hijabin nan, domin ni ban ga wani abin kallo a jikinki ba da kike ta boye shi, ke jiki ba jiki ba amma sai shegen iyayi!”
Da sauri ta sauke kanta a kasa, domin ba ma ta san me yake shirin fita daga idonta ba, wani abu kamar kwalla. Ta gyada masa kai a hankali, shi kuma ko a kwalarsa ya wuce dakinsa abinsa, dama ta san ba nata zai shiga ba, domin tun ranar da ya zo dakin ya sameta bai sake takawa dakin ba. jiki a sanyaye ta zare hijabin daga jikinta, ta ninke shi, sannan ta aje shi a nan falon. Ba ta san ta fara hawaye ba sai d ata nufi kitchen ta ji suna dika a kan hannunta. Sai kuma ta yi sauri ta sharesu, a ranta tana fadin. Ai ba karya ya yi ba, ta san dama ita ba jiki gareta ba, ba ta da wata kiba kamar Anti, wani lokacin Mahmud kaninta da yake binta har Tsigarallahu yake ce mata, mutane da dama na mata ba’ar rashin jiki, kuma ta san da abin ba ya damunta, ta rasa dalilin da yasa tasa maganar ta mata zafi fiye da kima. Ta kasa hana kanta kuka, ta dan taba kadan, sannan ta share hawayenta, kana ta wanke fuskarta, ta dauki kayan abinciin ta kai masa dakin nasa. Ta aje masa, sannan ta yi serving masa, ta tashi ta soma gyara dakin ganinsa ba a kimtse ba, bai damu da ya tambaya ko ta ci abinci ba, yo ita kamaramr yarinya ce da sai ya tambayeta? Ita kuma da yau da kwarin guiwarta take so ta yi masa ta yin su ci abinci tare, amma wannan abin da ya mata yasa ta ji abincin ma ya fita a ranta, dan haka ta yi fushi ta fasa tambayar tasa, duk da yin fushin nata ba shi da amfani, yo wanda take don shi bai san tana yi ba, dan haka kuwa babu amfani a ciki. Duk abin da take yana binta da kallo, kawai kallon yana dan siririn jikinta yake yawa a cikin riga da wandon da suka mata yawa yake.
“Wai ke dama Rahama haka kike?”
Jin maganar yasa ta juyo ta kalle shi yayin da take kakkade shimfidar gadon.
“Na’am!”
“Ban sani ba da ko kallon tsoro nake miki, kawai sai nake ga kamar kina da jiki da cikar hallita, amma ban taba sanin cewa haka kike kamar tsigicola!”
Ya karashe maganar da ‘yar dariya gajera, ta fahimci maganar da ya fada mata yanzu a wurinsa ba komai ba ce. Amma har ga Allah tana jin zafin maganganun nasa daya bayan daya, murmushin yake ta yi, ta ci gaba da abin da take.
“Na dauka kin kai Muwadda (kanwarsa wadda take binsa) jiki, ashe ko Husna (Kanwarsa da take bin Muwaddan) baki kai ba!”
Ya ci gaba da fada yana cin abincin nasa, ba ta amsa masa ba, to ta amsa amsa tace me.
“To ke kuwa ko abinci ne ba kya ci?”
“Ka taba ganin wanda ya rayu ba tare da abinci cin abinci ba?”
Ta ara ta maida masa martani, amma ta lura sam bai gane hakan ba, sai ma samun kwarin guiwar ci gaba da maganar da ya yi.
“Ko kina ci dai wata kila ba mai kyau ba, amma ba damuwa za ki yi kiba a gidan nan, ko me kike so zan siya miki, saboda ki ci ki yi kiba, bana son rammamiyar mace, musamman irin ramarki, ta yi yawa!”
Cike da ta takaicinsa ta dube shi, kamar za ta ce wani abu kuma sai ta yi shiru, ta danne ta shanye komai, tana gama gyaran gadon ta naimi wuri ta kwanta abinta, ba ruwanta da jiransa. Shi ma bai jima ba ya zo ya kwanta ba tare da ya kashe haske ba, jin ya zauna a bakin gadon yana shirin kwanciya ba tare da ya kashe hasken ba yasa tace.
“Ya Umar hasken fa?”
Wannan tsakin da ta riga ta san cewa yana daya daga cikin dabi’unsa yawan yin tsakin ya mata, sannan ya kwanta abinsa yana fadin.
“Ni fa haske a kunne nake kwana abina, ke ce da kika zo da wani sabon iyayi na kashewa haske kafin bacci, ban kulaki ba ne saboda na ga ba komai kika sani a kaina ba!”
Ajiyar zuciya ta yi, ya kamata ace ta daina mamakin halayen Umar. Sauka ta yi daga kan gadon, ta je ta kashe hasken, sannan ta dawo ta kwanta, gabanta na faduwa, domin ba ta san miye kuma zai biyo bayan kwanciyar tata ba, yau kwana uku bai mata komai ba, shi ma dan ta ce masa ya yi hakuri ya bari ta warke ne, da tun a washe garin daren farkonsu ya so ya sake, sai da ta yi magiya ta hada da kuka sannan yace zai bata kwana biyu, ta tabbatar komai zai iya faruwa a yau din nan, ilai kuwa. Ba a jima ba ta ji ya riko hannunta, har ga Allah cike take da tsoro, har yanzu tana jin tsoron na farko, yanda ya zo mata tun karfinsa, babu salama, babu lallashi babu komai sai gujirin tsaki da ya bar mata.
“Ya Umar!”
Ta kira sanda ya jata jikinsa.
“Miye?”
Ya tambaya murya can kasa.
“Ba ka san foreplay ba?”
Ya dakata, takan iya karanto kokwanto a kan fuskarsa a cikin duhun dakin.
“Miye shi din?”
Dama ta san bai sani ba ai, dan haka tace.
“Wasa dasa da ake kafin saduwa”
“Mts za ki fara ko?”
Ta girgiza kai a fili, domin tun yanzu ya kamata ace ta fara sauya shi, kafin tafiya ta yi nisa ya fi karfinta.
“Ba haka ba ne, yana da kyau ace ka sani ne”
“Ban sani ba, kuma bana bukatar na sani!”
Janye jikinta ta yi a nasa, a hankali tace.
“Dan Allah ka bari na maka bayani idan ma ba za ka iya tambayar wani ba”
Bai amsata ba, za ta fara magana ya daka mata tsawa a cikin duhun dakin.
“Dalla Malama idan ba za ki bani hakkina ba ki rike abinki, bana bukatar wani karatunki da wannan daren, aikin banza kawai!”
Tana kallonsa ya tashi zaune, sannan ya sauka daga kan gadon ya ma fita ya bar mata dakin, ta tashi zaune ta fara abin da ya zame mata sahibi abin yi, wato kuka. Ta yi mai isarta, sannan ta tashi ta fita ita ma, ba ta gan shi a falo ba, dan haka ta soma leka dakuna, nan ma baya nan, dan haka ta fita waje, a entrance ta gan shi tsaye, ya wani makale a gefe, ran nan a hade, tana fitowa ya kalleta, sannan ya sake hade rai tare da yin kwafa ya kauda kansa. A hankali ta isa wurin da yake tana ta hawaye, sannan ta karfafi zuciyarta, ta mika hannunta ta rike shi ta baya,kafin ta kwantar da kanta a gadon bayansa, a bazata rungumar ta zo masa, dan haka ya kame cikin mamaki.
“Ka yi hakuri Ya Umar, ba wai na yi hakan saboda bana son baka hakkinka ba ne, Wallahi na sha wahalar na farko, duk da na san dole na farko ya yi azaba rashin wannan wasan ma ya bada gudunmawa, bana so ju ci gaba da tafiya a haka, shi yasa na fada maka, dan Allah ka yi hakuri!”
Duk haushinta da yake ji sai ya ji ya ragu a cikin zuciyarsa, shi fa ba wai ba ya sonta ba ne, kawai halinsa ne a haka, duk son da yake maka in dai ta hadaka da shi sai dai ka yi hakuri kawai.
“Na ji ya isa”
“Ka yafe mini?”
“Eh”
Ta sake shi a hankali, ta koma gefe.
“Na san na yi rashin kunya da na ce zan koya maka, amma za ka iya tambayar wani cikin abokanka”
yay shiru yana kallonta, sannan yace to, zai yi hakan.
````````````
Wannan littafin paid book ne a kan 700 kacal, za ku iya fara making payment tun daga yanzu. Ta
5487270431
Salma Isah
Moniepoint