AMARYAR GADO

CHAPTER 15

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

AISHA SANI ABDULLAHI

Xayyeesherthul-humaerath

©️2026

 

 

SHAFI NA SHA BIYAR

 

Zata yi masa magana sai ta tuna da cewa su Inno suna baya a zaune. Sunkuyar da kai ta yi, zuciyarta na ci gaba da yi mata zafi domin ta san komai za ta faɗa ba lallai a yadda ba mussaman ma da kasance hoton view once ne bata da wata hujja.

 

Gidan Inno aka fara tsaya suka sauka ita da Goggo Hansai.

 

Inno ta fita daga motar tana, “Ni zan dafa magungunan da kaina in kawo, saboda na san ki da garaje, Faridatu. Kar ki je ki yi aika-aika. Haruna ya ce an gama saukar ma, sai ku je ku huta ko?”

 

Da “to” Farida kawai ta amsa wa Inno, suka wuce.

 

Suna shiga gidan, yana parking, Farida ta buɗe ƙofa ta fita.

 

Zama ta yi a falon tana jiran shigar Sufyan. Yana shiga, cikin fushi da zafin rai ta cakumi ƙwalar rigarsa.

 

Wani irin huci take tana ajiyar zuciya. Sufyan kuwa, kallo guda za a yi masa a tabbatar da cewa ya gama tsorata da yanayin da ya ganta da kuma cafkar da ta yi masa.

 

Cikin ɗaguwar murya ta fara faɗin, “Kai wanni irin mugune azzalumi? Kai ba ka da imani ne? A yadda nake ma, zagi ake ana yi mini dariya, bare kuma yadda fuskata ta ƙara komawa yanzu? Anya akwai zuciya a kirjinka kuwa? Ni ma kaina na san ni mummuna ce, mara kyau, to ka bar ni in ji da wannan ɗin ma mana. Ka bar ni in ji da shi, ka bar ni in ci gaba da fuskantar ƙalubalen da nake ciki. Sai ka min haka? Sai ka ƙara mini wani? Iye?”

 

Ta ƙarasa maganar tana ƙara cakumarsa tare da ɗaga ɗayan hannunta.

 

Hawayen da take ta ƙoƙarin ɓoyewa ne suka fara bubulowa a fuskarta. Ta numfasa tare da kawar da kai, “Ka aske mini gashin kaina, ka aske mini na girata ma, shikenan, shikenan.” Ta karasa maganar tana ajiyar zuciya tare da sakar masa da ƙwalar rigarsa da ta rike.

 

Juyawa ta yi ta tafi ɗaki da sauri, ta ja ƙofarta ta kulle da ƙarfi.

 

Mai da numfashi Sufyan ya yi yana, “Na tsallake rijiya da baya.”

 

Ya saki tsaki yana taɓe baki kafin ya ce, “Damuwarki ce, ki ji da shi. Ai wallahi indai za ki mun abu, to ba fashi sai na rama. Bara ma in fice daga gidan ki ƙaraci jarabarki.”

 

Farida na shiga ɗaki ta fara kuka mai tsuma zuciya. Can kuma sai ta ɗauki wayarta ta kira Azima.

 

Azima na jin sautin muryarta, cikin tashin hankali,

 

Ta ce, “Ki yi haƙuri, Farida. Ki nutsu ki faɗa min, mene ne yake faruwa?”

 

Cikin muryar kuka Farida ke magana.

 

“Azima, wallahi in zuciyata ta buga na mutu, Sufyan na ɗaya daga cikin sila. Azima, sai kashe ni da baƙin ciki.”

 

“Subhanallah! Ki daina faɗin haka, Farida. Ki nutsu ki faɗa min me yake faruwa?” Cewar Azima.

 

Farida tana shassheƙar kuka ta ce, “Azima, ke da Ya Ahmad kune kuka sanya ni cewa dole in rayu kamar kowa. Sannan kuka sanya ni yi muku alkawarin cewa ba zan taba shan wani abu ba da nufin canja hallitata domin maganar mutane,Shi da kansa ya nemo min aikin lecturering tun ina jin cewa ba zan iya ba, har na fara iya, duk da cewa ba wai na daina fuskantar ƙalubale bane, tunda har yanzu ana kallona, ana min dariya, ana min zunɗe, amma na ci gaba da daure. To yanzu kam ba zan iya ba, Azima. Sufyan ya yanke min gashin gira da na kai. Azima, ni kaina bana son kallon kaina.”

 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Farida, wai me kuke nufi ne da rayuwarku? Shin ba za ku karɓi ƙaddara ku ɗauki kanku matsayin mata da miji ba? Ubangiji ya riga ya rubuta cewa ke ce matarsa, shi ne mijinki. Ba za ku amshi hakan hannu bibbiyu ba? Na tabbatar da cewa dukkaninku ba barin juna kuka yi ba, domin na san halinki sarai. Don haka ki manta da wani batun mutuwa ko rashin zuwa school. To, waɗanda suka rasa wani sashe na jikinsu fa? Waɗanda suka rasa wani ɓangare na jikinsu, ba mutane suke ba? Rayuwa suke kamar kowa, kuma hakan ba ya sa su ji cewa sun gaza.”

 

Farida ta katse ta da, “Ba ki ganni ba ne fa, Azima. Ba ki ganni ba wallahi.”

 

Azima ta numfasa.

 

“Ko ban ganki ba, Farida, kanki ai rufewa kike, ko? Gira ce kawai za a iya ganin alama in kin sanya nikaf ɗin, bare ma kuma sabon gashi zai fito. Ai ba sun tafi kenan ba. Ni yanzu ki daina wannan kukan, ki kwanta ki yi barci, don Allah. Zuwa anjima zan kira ki, zamuyi magana.”

 

Sallama suka yi, Azima ta katse wayar. Farida na kwance a kan gado, ta rasa abin da ke yi mata daɗi sai shafa kan nata da fuska, wajen girar take.

 

A ranta ta gama ƙudurtar cewa ba za ta ƙara fita haka ba. School ma ɗin ma haƙura za ta yi har sai gashin girarta ya dawo, don ba za ta koma ta zama topic of discussion ga students ba. Kan faruwar hakan ma ya ta kare, ina ga yanzu.

 

Sufyan tun da ya fita a gidan ranar bai koma ba, wajen Falila ya je, suka kwana a hotel.

 

Wajen ƙarfe tara na safe Inno ta dira a gidan, ɗauke da tulun ruwan magunguna da ta dafa.

 

Ta titsiye Farida kenan tana tambayarta ina Sufyan, sai ga shi ya shigo.

 

Inno ta ce, “Sufyanu, kai kuma fa daga ina? Ace ranar hutun ƙarshen mako ma mutum ba zai zauna da iyalansa a gida a ji dumin juna ba, sai dai ya ta zarya kamar sai ka ce jaririn mage?”

 

Sufyan ya haɗa ido da Farida. Da sauri ya kautar da nasa, saboda irin kallon da take masa, ya zauna yana cewa,

 

“Inno, wallahi ita ce wai tun da muka dawo jiya take min rashin daraja, husuma take son tadawa. Wai ni na bar aljanun nan suka mata aski.”

 

Inno ta riƙe baki.

 

“Ke Faridatu, ki rufawa kanki asiri fa. Ki raba kanki da husuma. Kin fi kowa sanin Haruna, wallahi in ya ji kina yi wa mijinki rashin daraja, da kansa zai zo ya ɗauki mataki. Ki dai kiyaye, ki raba kanki da fushin Ubangiji da kuma na iyayenki, ahto.”

 

Ko kala Farida ba ta ce musu ba. Inno ta gama soki burutsunta sannan ta ɗauko magungunan ta ba Farida ta sha.

 

Karɓa ta yi, ta sha, ta bata kofin kawai, don ranar ba ta son rigimar Inno.

 

Sufyan ya tashi zai tafi kenan, Inno ta dakatar da shi.

 

“Kai Sufyanu, ina zaka? Ai ga naka nan, kai ma dole ka sha.”

 

Ya mutse fuska ya yi ya ce, “Ni kuma, Inno? Ai lafiyata kalau. Ita ce dai ake so ta sha ko?”

 

“Yoo, in tasha kai ba ka sha, me aka yi kenan? Bayan hatsabiban na tare da kai. Karɓi nan ka kurɓe.”

 

Inno ta faɗa tana miƙa masa kofin.

Karɓa ya yi, yana kaiwa baki ya kurɓa, amai ya tawo masa gadan-gadan. Aguje ya yi toilet. Inno ta kalli Farida ta ce, “Kin gani ko? Sharinsu ne, sune zasu hanasa sha.”

 

Ta ƙarasa maganar tana binsa da sauran maganin a hannu. Tsayawa ta yi bakin ƙofa, sai da ya gama amayarwa ta ce, “Karɓi nan maza, don ba aikin kowa bane illa nasu. Ba su so su bar jikinka ne, munahikan Allah.”

 

Sufyan ya ce, “Please Inno, ba zan iya shan abin nan ba wallahi.” Ya faɗa yana toshe hancinsa.

 

Inno ta ce, “Fil me? Kaniyarka, in ma zagina kake, sai ka sha fa, ko kuma yi maka dure.”

 

“Inno, Allah, in na sha zan yi amai. Ki bari don Allah.”

 

Inno ta ce, “Au Allah? Har wani toshe kunnuwa kake fa? Oh, to shikenan.”

 

Ta faɗa tana komawa falo. Samun Farida ta yi ta ce, “Faridatu, kin ga aljanun Sufyanun nan hatsabibai ne, ba zasu bari ayi masa magani ba. Yanzu tallafa mini zakiyi, tunda kina da dai jikin ƙarfi gareki. Ki riƙe mini shi in masa dure.”

 

Duk da Farida na ji da damuwarta, amma yadda Inno ke maganar bilhaƙƙi da gaskiyarta sai da ta ba ta dariya. Tashi ta yi tana, “To mu je.”

 

Shiga ɗakin suka yi, suka tarar da shi zaune kan gado yana dannan wayarsa.

 

Da mamaki ya kallesu, kafin ya buɗe baki ya yi magana, har Farida ta damƙe shi. Riƙo ta yi masa tamkar yadda ake yi wa jarirai in za a ba su magani, yana ta wutsul-wutsul, suka masa rufdugu.

 

Inno ta kafa masa kofin maganin.

 

“Kin gani ko? Duk sune fa wannan lamari naka. Ai sai na tashi tsaye, Sufuyanu.”

 

Sai da ta tabbatar ya shanye tas kafin ta sake shi.

 

Wani irin azababben ɗaci da wari maganin ke yi. Rasa inda zai sa kansa ya yi, yana ta juyi.

 

Inno ta ce, “Ohoo dai, ko me zakuyi sai dai ku yi, ya sha. Faridatu, sannu da ƙoƙari, mu je ko.”

 

Suka fita, Inno ta ja ƙofar ɗakin ta kulle tana, “Zuwa anjima in ya yi barci ya dawo daidai ai ko? Yanzu ya kike dai? Ana kuwa da cikin nan dai? Abi, komai a hankali fa.”

 

Girgiza wa Inno kai kawai Farida ta yi.

 

Inno ta kalleta tana taɓe baki, “To, ko ke ma maganin ne ya saki haka ne? Je ki kwanta, ni kam sai anjima.”

 

Ta ƙarasa maganar tana tafiya.

 

Sufyan har tashi ya yi ya je ya yi brush a toilet, amma ɗacin maganin bai bar masa makogwaro ba. Ya rasa inda zai sa kansa, sai zarya yake shige da fice zuwa kitchen. Ya sha gishiri, ya sha sugar da madara, duk a banza.

 

Farida kuwa ko a jikinta, tana kallonsa kawai, sai zare-zaren idanu yake.

 

Tana ta Tunani , ta rasa a duniya me za ta yi masa, ta rama abin da ya yi mata, ya ji zafi kamar yadda ita ta ji.

 

Wani murmushin takaici ta yi kawai, ta tashi ta shige ɗaki.

 

Sati guda Farida ba ta ko tunanin zuwa school, kullum tana zaune a gida a cikin ɗakinta a takure, domin ko falo ba ta zama. Da Hod ya ji shirun ya yi yawa, ya kira ta ta shaida masa cewa ba ta da lafiya ne kawai, amma da zarar ta ji sauƙi za ta koma.

 

Har Sufyan ya gama gararambarsa ba ta taɓa fitowa ba. Tana jinsu ma ranar ya ƙara zuwa da Falilah, suka yi abin da suka saba. Ta shiga damuwa sosai, abinci ma ba wani iya ci take ba. Ko Inno ta zo ta ba ta magani ta tambayeta me ke damunta, sai ta ce mata kawai ba ta jin daɗi ne. Ita kuwa Inno ta fi tunanin laulayi ne ya sa ta haka, shi ya sa ba ta nuna wata damuwa ba illa magunguna da take ƙara tula mata.

 

Ta tashi kenan da sassafe, misalin ƙarfe bakwai, wayarta ta yi ƙara alamar shigar saƙo. Ɗauka ta yi ta buɗe, ta fara karantawa.

 

“Ke wai wacce iri ce? Ke ba ki yarda da kanki ba, wai kin tsaya kina jiran mutane su yarda da ke, su yaba miki? Su soki? Kuma su faɗa miki kina da kyau?

 

Babu wannan ranar, ba za ta taɓa zuwa ba. In za ki so kanki da muninki, ki so. Domin a idanun kowa ke mummunace, kuma babu canji a hakan sai ranar da kika ji a ranki cewa ke ma mai kyau ce a taki duniyar.

 

In kin isa, kina jin cewa kin kai, kuma kin yarda da kanki, ki ba wa kanki ƙarfin gwiwa. Ki tashi, ki yi yaƙi da kanki, ki tafi wajen aikinki.

 

Motsaraciya mai tsoron mutane, wacce ba ta son kanta! Duk ranar da kika kashe kanki, babu abin da za a fasa a duniyar nan, sai dai ki yi wa kanki asara tunda kika bari rauninki yake gallaba akanki”

 

Wani takaici ne ya turneƙe mata a ƙirji nan take. Ta ji zafin maganar sosai. Ta ɗaga ido tana ƙoƙarin ganin lambar wayar, sai ta ga lambar ƙasar waje.

 

Ta danna ƙasa tana so ta yi rubutu, kuma nan ma ta ga a rufe yake, ba dama maida amsa.

 

Ɗaukar lambar ta yi ta fara ƙoƙarin kira, ta ji baya shiga. Riƙe wayar ta yi tana kallon saƙon. Sai can kuma, kamar an tsikareta, ta tashi.

 

Wanka ta shiga ta fito, ta sanya kaya. Bayan ta sa hijabi, ta ɗauko nikaf ɗinta ta tsaya gaban madubi.

 

Daidaitawa ta yi ta sa, ta ga alamun girarta ya fito. Jiki a mace ta zauna gefen gado, tana tuna rubutun da aka turo mata.

 

Sai ta ƙara tashi, ta sa nikaf ɗin tsaye take gaban madubin tana kallon kanta,…