Hs 49
by @legendspen
"Kana da tabbacin akan mazan da take kulawa."
"Ina da shi Mom."
"Tun da kana da shi ai shikenan, amma ka tabbatar kana da sahihinaci akan shaidar."
"Mom, mene sahihanci?." Kallonshi ta yi sannan ta ce. "Tabbatciyar shaida." Shiru ya yi gaba daya abun ya canja masa, ji yake kamar ba Senate dake Abuja ba, wanda ya manta da Bhatool da rayuwarta ba, dan tun da ya dawo nan ba shi da wani aiki sai faman tunanin Bhatool, tun da ya sa ƙaffarsa a garin.
"Mom ni dai kawai gani nai an turu min hotonta." Daidai lokacin motarsu ta shiga gidan. "Ka bincika wa ya turu, ka tabbatar ita ce, ba hadin Ai ba, kasan yanzu muna cikin wani zamanu na fasaha, a yanzu fasaha ta yawaita kuma zata iya abinda hankali ba zai tunani ba." Shiru ya yi gaba daya jikinsa ya mutu, yana fitowa daga mota ya yi dakinsa ya kwanta, sai dai tunanin Bhatool da tausayinta ya cika masa rai, ya hana shi sakat gaba daya.
****
Washe gari Bhatool da aiki ta tashi, ta yi alƙwarin bawa Ahamad mamaki, dan girki za ta yi masa yaga ƙoƙarinta da yake cewa bata iya komai. Umma ce ta shigo cikin kicin din. "Bhatool lafiyanki dai?." Murmushi ta yi sannan ta ce. "Lafiya Umma, daman Yaya Ahamd ne zai zo."
"Wai Bhatool wani abu dai na soyayya bai ta ɓa shiga tsakaninku ba ko, kinsan dai yanzu kin haramta ga kowanne namiji har sai kin fita daga iddarki ko?." Shiru Bhatool ta yi, a ranta ta ce. "Nasani Umma, amma dai tabbas wani abu na soyayya ya shiga tsakaninmu, dan a yanzu ina jin Ahmad a zuciyata fiye da Senate."
"Ki yi hakuri, lokaci ƙalilan ya rage miki." Umna ta faɗa, tana fucewa daga Kicin din. Ci gaba da aikinta ta yi a ranta ta dauki aniyar yau idan Ahmad yazo za ta sanar dashi cewar su yi nisa da juna, su kuma janye al amarin soyayya zuwa lokacin da Allah zai sauketa, ko ranar ne ma sai a ɗaura musu aure.
Wajen karfe uku da rabi Ahmad ya shigo gidan, lokacin Umma ta zagaya maƙwaftansu Barka anyi haihuwa. Bayan ya zauna a falo Bhatool ta shiga fito masa da filasai na abinci, da mamaki sosai yake kallonta. "Kar dai ki ce ke kika yi girkin nan?." Ya tambya. "Ba daman kaine kake cewa wai bana iya girki ba, gashinan kuwa yamzu ka gani."
"Gaskiyya dai kam nagani, naga girki iya girki." Ya faɗa yana tashi ya fara zuba abincin. "Aikuwa kasan dai ba iya zubawa zanyi ba, dan nagaji."
Dariya ya yi sannan ya ce. "Ai na hutarshe ki." Bayan ya zuba abincin yana ci ne ta ce. "Cikina ya shiga wata bakwai." Kallon ta ya yi sannan ya ce. "Ina lissafe fa."
"Har yanzu akwai iddar tsohon mijina akaina." Ta faɗa kanta a ƙasa. "Nasani Bhatool, lafiya dai ko?."
"Lafiya kalau, wata alfarma kawai nake nema a wajenka."
"Faɗi Bhatool ina saurarenki."
"Ina so Ranar da na fita daga idda, ma'ana na haihu indai na haihu lafiya ina son a ɗaura mana aure a ranar."
******
Senate haka ya raba dare yana faman tunanin Bhatool, gaba daya kalaman Mom sun cika masa kai, sun tsaya masa a cikin zuciya sun ƙi gaba sunƙi baya. Sai tsakar dare ya samu bacci ɓarawo ya yi gaba dashi, amma kuma da safe yana tashi da wani tunanin Bhatool ɗin, gaba ɗaya mamakin kansa yake lokacin da yake Abuja fa mantawa ya yi an hallic wata Bhatool, har ma ya yi rayuwa da ita, amma tun da ya sa ƙafarsa anam ta dawo.
Sai wajen 1 ya fito ya yi breakfast, Mom tana kwance kan doguwar kujera tana kallonsa, har ya gama sanan ta kirashi ya zo. "Me ya hanaka fitowa da wuri?."
"Mom bana jindadin jikina."
"Meke damunka?."
"Headche."
"Zaka iya tuna ranar da ka fara samun saɓani da Bhatool?." Mom ta tambayeshi, ya yi shiru na 'yan mintuna sannan ya ce. "A'a gsky."
"A cikin saɓanin da kuka samu, kafin azo na saki wanni yafi tsaya maka a rai?."
"Wanda ta fito waje ta tsaya ita da wancan ɗan iskan."
"Wa ya sanar da kai?."
"Hoto aka tura min."
"Waya tura ma hoton? Kasa wani ya dinga bibiyar ma ita ne?."
"A'a bansa kowa ba."
"To wanda ya tura ma kasan shi?."
"A'a."
"Kasan lambar?."
"A'a."
"To me ya sa ya tura ma?."
"Mom! Nima bansani ba."
"Ita lambar ita ta sake tura ma hoton da kake magana na ƙarshe?."
"Eyh ita ce."
"Sannu Shashasha, an tura ma hoton matarka da wani, sai baka bibiyi wanda ya tura ma ba, amma kazo ka saki matarka, kai ko hakan bazai sa ka yi tunanin cewar akwao wata maƙarƙashiya a ƙasa ba?."
"Mom, wallahi sai yanzu na yi tunanin nan, waye yake son raba ni da matata haka?."
"Wa ya rabaka da matarka dai Senate, ai ka riga da ka saketa, saki mafi hulaƙanci shine ta waya. Shin ta waya ka karɓi aurenta? Da zaka sake ta ta waya?."
"Innullahi wainna illahir raji'un! Astagfirullah Lallai dole na yi bincike akan hakan."
"Babu wani bincike da zaka yi domin gasky ta gama bayyana kanta, kai kuma ka zama miji mara adalaci, mara tausayi."
"Mom waye da wannan aikin, ko waye wallahi sai na dau mataki akansa."
"Hhm, kawai kabar maganar wayanda suka yi sun bayyana kansu. Wata ce ta yi amfani da ƙawarta, sai daga baya ƙawarta ta ta faɗa."
"Amrah ko?." Ya tambaya a fusace. "A'a." Mom tabashi amsa. "Jannah take ko jannat."
"Ita ma ba ita ba, wata ƙawa can daga gefe."
"To wace ta yi amfani da ita?."
"Senate ba za ta fadu ba, amma tabbas ba kai ta cutar ba ni ta cutar, dan har kwanciya na yi asibiti kuma har yanzu jikina babu daɗi."
"Mom wace dan Allah?."
"Har abada ba zakaji wace ba Senate."
*****
Suna zaune a falo Ahamd Yana cin girkin Bhatool yana ta murmushi abunsa, ya kai lomar abincin karshe bakinsa, sannan ya ajiye cokalin yana hamdala. Ya kalli Bhatool wadda take zaune a kasa gefen kujerar da yake kai.
"Bhatool, gaskiya na gamsu da wannan girkin. Amma maganar da kika fada din nan, ita ce ta fi kowane dadi dadi," Ahmad ya fada yana murmushi, idanunsa suna kallonta cikin so da kauna.
Bhatool ta sunkuyar da kanta kasa, tana wasa da yatsun hannunta. "Yaya Ahmad, na yi wannan maganar ne saboda ina son in biya ka dukkan kulawar da kake nuna mini. Kuma ina son in nuna maka cewa na yarda da kai fiye da kowa."
Ahmad ya sauko daga kan kujerar ya dawo kasa kusa da ita, ya rage muryarsa yadda ita kadai za ta ji shi. "Bhatool, alkawarin da kika ba ni, ya zama tamkar igiyar da za ta jawo ni zuwa ga rayuwar farin ciki. Zan jira ranar da za a sauke ki, zan kuma jira ranar da za a kulla igiyar aure a tsakaninmu. Ina son na zama uba ga danka, kuma zan zama miji gare ki wanda ba zai taba yarda da jita-jita ko sharrin makiya ba."
Hira ta balle a tsakaninsu, hira mai cike da natsuwa da bayyana sirrikan zuciya. Ahmad ya dinga gaya mata yadda zai gyara mata daki a gidansa, da kuma yadda yake son su gina rayuwa mai sauki amma cike da aminci. Bhatool ta saki ranta sosai, tana jin wani irin dadi yana ratsa ta, har ta manta da cewa tana cikin idda.
A can gidan Mom kuwa, Senate ya gaza zama. Kalaman Mom na cewa an yi amfani da fasahar AI wajen yaudararsa sun riga sun rikita masa kwakwalwa. Ya tashi ya dauki mukullin motarsa, ba tare da ya sanar da kowa ba, ya nufi hanyar gidan Umma. Wani irin nauyi yake ji a kirjinsa, yana son ya tabbatar da abin da zuciyarsa take gaya masa.
Yana isa kofar gidan, ya yi fakin a gefe. Ya dade a cikin motar yana saƙawa da warwarewa. Daga karshe ya fito, ya taka zuwa cikin gidan. Bai sami kowa a tsakar gidan ba, bayan ya yi sallama babu amsa kai tsaye ya turo kofar falon, idanunsa suka sauka a kan abin da bai taba zato ba.
Ahmad ne zaune kusa da Bhatool, suna hira cikin wani irin yanayi na shauki. Bhatool tana dariya irin wadda Senate ya dade bai gani ba a fuskarta. Fuskarta cike da so da ƙauna, duk da ramar da take da ita, tana kallon Ahmad cikin wata irin kulawa.
Senate ya tsaya cak a bakin kofa, numfashinsa ya fara fita sama-sama. Wani irin kishi ne ya turnuke shi, kishin da ya fi na farkon zafi. Ya kasa magana, sai dai kallon da yake jifa da shi zuwa gare su.
Ahmad ne ya fara lura da mutum a bakin kofa. Ya kai idonsa ga bakim ƙofar, fuskarsa cike da zallam mamaki yake kallom Senate a tsaye.
Legendspen
***