DUHU BAYAN MURMUSHI

3

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 3.

Sarac Stars R Pen...✍️

Mujaheed yana gama karyawa anan ya bar kayan ya miƙe yayi waje hankalinsa kwance jin cikinsa ya ɗauka, duk da ba ƙoshi yayi ba amma ya toshe wata kafar, yana tafiya sannu a hankali ya zama abin kwallo babu wanda ya tanka masa duba da abunda ya faru ɗazun, haƙiƙa wannan faɗan da yayi da Anas ya samar da shakkarsa a zuƙatan yara da tsoron kar ya nakaɗa musu duka tunda haukansa ya fara saka shi dukan mutane, shi dai lamarin yayi masa daɗi ganin babu wanda ya ambaci sunan sha tara balle ayi masa ihu, kwakwalwarsa bai hasko masa cewar abunda ya faru ɗazun ne ya haddasa haka ba duba da bayi da zurfin tunani, duk abunda ya gifto masa a kwakwalwa shi ne kaɗai yake iya lissafi, kuma da zancen auren Aina'u ya fito daga gida dan haka shi ne yake ta kai komo a cikin ransa. Lokacin da zai wuce ta ƙofar gidan malam Mati sai ya juya da sauri ya isa kwatan ƙofar gidan ya zame wando ya fara fitsari a tsaye yana tsillashi cikin kwatan hankalinsa kwance, dan har lumshe ido yake yi domin yayi mugun matsansa, Sadiya ce ta fito da sauri zata je makaranta sai ta yi mummunar gamo da Mujaheed yana fitsari kuma bai sakaye gabansa ba, da sauri ta juya gida har tana ƙuma kai da ƙofa, mama dake aikin gyara wajen awakinsu tace cikin mamaki.

Ke lafiyar ki kika faɗo gida kamar an biyo ki.?

Wlh mama Mujaheed ne yake yin mitsari a kwata a tsaye kuma ko sakaye kanka bai yi ba.

Wani ɗan iyan ne yake fitsari a ƙofar gidana.

Cewar Mati daya fito daga ɗakinsa cikin sauri, ko kafin Sadiya ta bashi amsa ya fice zuwa waje cikin sauri kuma cikin ikon Allah ya tadda Mujaheed ya na kiciniyar zage zariyar wandonsa da nufin zai tafi, ya daka masa uwar tsawa.

Kai uban waye yace kayi wa mutane fitsari anan.? To ba sha tara kake ba ko sha takwas ne wlh sai na saɓa maka, banda mahaukaci ne kai ka zo ka saki jiki a waje kana fitsari saboda kwakwalwarka bata faɗa maka gaskiya, to zanje har gidan ubanka na faɗa masa cewar karka lalata mana 'ya'ya mata su riƙa yin mummunar gani, ɓace min da gani kafin na sauya maka kamanni.

Ya ƙare maganar a tsawace wanda ya saka Mujaheed ya tsorata sai ya wuce cikin sauri yana riƙe da zariyar wandon yana waigen malam Mati daya cigaba da sababi, sai daya yaga Mujaheed ɗin yayi nisa kafin ya juya zuwa gida yana ta faɗa, Maman Sadiya tace.

Ni wlh wannan yaro dama asibitin mahaukata suka kai shi, to abun nasa naga cigaba yake ƙara yi.

To ba dole ya ƙara gaba ba ubansa ya sakeshi sai yawo a gari, ya zama tunkiya uwar tamɓele, kuma kina ganin irin waɗannan yaran ɓarna ne dasu wanda ba zaki ce zasu aikata ba, banda hauka taya zai saki jiki a waje salon ya ɓata mana 'ya'yanmu mata a banza.

Aiko gashi nan ya tsorata Sadiya tunda tana ganinsa tayo gida a guje, Allah ya kyauta.

Cewar mama da ranta ya gama ɓaci, Malam Mati yayi kwafa.

Ki bari kawai, ai Liman zan faɗawa ayi magana da babansa, idan nashi tarbiyyar a sake yake mu na 'ya'yanmu a kame yake.

Ya ƙare maganar yana shiga ɗakinsa, Mama ta duba Sadiya tace ta wuce makaranta kar tayi latti, jiki a sanyaye ta juya ta fita duk zuciyarta babu daɗi akan zantukan iyayenta ga Mujaheed, menene laifinsa.? tunda ba hankali gareshi ba ai abun a tausaya sama ne ba a riƙa faɗar muyagun magana akansa ba, ita data san abunda zai faru kenan da bata shigo gidan ba ta tsaya a zaure ya gama fitsarinsa ya wuce ba tare da ta jawo wannan maganganun ba, haka ta tafi tana ƙara jin tausayinsa a zuciyarta, mutum har mutum amma ba cikakken lafiyar da zai amfani rayuwarsa, tasan yayan ƙawarta ne Aina'u tana zuwa gidan sosai wanda tana da masaniyar abubuwan da suka shafe shi, kuma duk a bakin Aina'u take ji, haka ta ƙarasa Islamiyya jiki a sanyaye.

Mujaheed kuwa ya mayar da hankalinsa zuwa titi yana sauri kamar zai tashi sama, bai zame ko ina ba sai jikin wani shagon masu gyaran TV, kuma yayi sa'a basu koreshi ba sai ya tattara duka tunaninsa a guri guda yana kallon yadda wani yaron mai shagon yake buɗe wata decoder zai gyara. Anan Mujaheed ya ɓata yinin ranar ba tare da ya yi yunƙurin barin gurin ba duk da yunwar da yake damunsa, ya kasa ya tsare duk abunda suka jefar a matsayin shara to ɗauka yake yi yana tara shi a rigarsa daya ɗago gaban ya riƙe wanda ya zame masa wajen ajiya, kiran Sallar La'asar shi ne ya dawo da tunaninsa jikinsa sai dai kuma tunawa da koran da ake yi masa in zaiyi sallah a masallaci sai ya kashe masa duk wani karsashin son yin sallar, sai ya turo baki yana jin babu daɗi a cikin ransa, dan haka ya miƙe ya kama hanyar gida yana yi yana kallon ƙasa ko zai ga abun da yake buƙata, a haka ya isa gida yana tsince-tsince, daya shiga ɗaki ya juye kayan anan tsakar ɗankin ya fito tsakar gida ya tadda mama ta fito daga bayi tana alwala.

A yawo sai yanzu ka tuna da gida tun safe, wai kai Mujaheed kana ganin wannan rayuwar naka zata ɓulle maka da kyau kuwa.? baka tsayawa ka yiwa kanka tunanin arziki sai shirme ka saka a gaba, to abunda kake yi kana ƙara mayar da kanka mahaukaci ne da gaske, kuma ni nasan da gangan kake wasu abun dan akwai sauran hankali a tare da kai, to ni dai nayi iya yina akanka, Allah ya gani na fita sauran ya rage naka.

Tana gama faɗar haka ta cigaba da alwalar data fara, Mujaheed daya gama jin maganarta ya kaɗa kai kamar ƙadamgare ya nufi kitchen.

Karka kuskura ka shiga min kitchen da wannan Ƙazamin jikin naka da sai wari kake yi kana hamami, to abincin rana ban aje maka ba dan nasan ba lallai ka dawo akan kari ba, ka jira yanzu na ɗaura na dare kafin magariba In Sha Allah na kammala sai ka ci. Nayi mamakin dawowarka a wannan lokacin, dan wani sa'ilin in ka nausa baka dawowa sai dare can.

Mujaheed ya ja burki yana saurauren maganar mamansu, sai bai shiga ba ya juyo ya tsaya a ƙofar ɗakinsa ya dafe bango da hannu ɗaya kansa a ƙasa kamar mai nazari, mama data gama alwala ta zo giftashi ta tsaya tana taɓe baki.

Shekarunka Sha takwas Amma tunaninka kamar na ɗan shekara shida, Allah ya baka lafiya.

Ta ƙare maganar cikin tsananin damuwa a fuskarta tana girgiza kai sai ta wuce, Mujaheed bai ɗago ya kalleta ba harta wuce ya cigaba da tsayuwarsa har sai da ya tabbatar ta fara Sallah kafin ya shiga kitchen ɗin ya fara buɗe-buɗe, cikin sa'a ya tsinci wata roba mai murfi an saka sauran abinci a ciki, bai jira komai ba ya ɗauko dafadukan shinkafa na manja ya zauna a kitchen ɗin ya cinye tas, kafin ya ɗauki pure water ya sha sai ya saki gyatsa mai sauti wanda a dai-dai lokacin mama ta fito dan ta duba sanwar waken data ɗaura a gas, nan tayi kiciɓus da shi yana shirin fitowa.

Dan abu kaza-kazanka ɗan sauran abincin dana ajewa su auta ka cinye, wani irin mara mutunci ne kai, na faɗa maka magana amma baka ji ba saboda ka rai na ni ko, mahaukacin banza da wofi shiyasa wani lokacin bana jin haushin abunda mutane suke yi maka dan kana cika min ciki da takaicinka. Nasan halin auta da rigima shiyasa na aje musu barbaɗen shinkafar data rage amma saboda kai shashasha ne kazo ka cinye, ana magana kana sunne kai kamar munafuki.

Ta ƙare maganar tana kafeshi da ido rai a ɓace, shima nasa idon ya zuba mata da suke farare kamar mangyaɗa kwance a ciki yana jin bacci.

Au kallona kake yi saboda rai ni ko.? zaka ɓace min da gani ko sai na sheme ka da muciya ɗan iska kawai.

Cewarta a harzuƙe kamar zata kai masa duka, sai ya wuce sum-sum ya shiga ɗaki ya zauna a ƙasa jikin bango ya manna bayansa, ya saka kansa a tsakanin guiwansa yana sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci na damuwar faɗar da mama tayi masa musamman da ko da yaushe yake gudun ɓata mata rai. Mama ta cigaba da mita ta ɗibo kayan miya ta fara jajjage. 

****  

SAFIYYA.

Tana zaune a cikin motarta a mazauni driver ƙafafunta a waje, hannun hangunta ta ɗaurashi a sitiyarin mota, tana wani irin kuka mai gunji da tashin hankali, tana yi tana share hawaye da farin hankacif da ta riƙe a hannun damanta, idanunta sunyi tulu-tulu sun kankance saboda kukan da take yi tun jiya, jijiyoyin kanta sun fito sosai sai fyace majina take yi lokaci zuwa lokaci, ba zata ce tana fama da mura ba amma wannan kukan shi ne ya haifar mata da tsinkewar majina. Ta ɗago kai ta kalli gidan da yake mallakinta a dalilin igiyar auren Jabir da yake sarƙafe a wuyanta, amma kuma a yanzu ya tashi a matsayin nata zai koma na wata wacce bata sani ba, ta tabbatar Jabir ba zai taɓa zama babu aure ba dan kawai saboda ya rabu da ita. Mutuwar auren yazo musu a wani bahagon yanayi wanda daga shi har ita babu wanda yayi mafarkin haka zai faru a tsakaninsu duba da zazzafar soyayyar da suka gudanar a shekarun baya, wanda mutane da dama suke ambaton zamansu sai mutuwa ce zata raba, amma kuma ƙaddara ya riga ya rantse cewar akwai wata tazara da zai gudana a tsakaninsu na rabuwar har abada wanda ya zame musu duhu ne a bayan murmushi, ga shi dai saki ɗaya ne ya shiga tsakaninsu amma kuma mai ban haushi ne dan babu kome a cikinsa, daga shi har ita basa fatan rabuwar amma kuma hakan shi ne masalaha a tsakaninsu. Safiyya sai da ta kai kololuwar yin nesa da zuciyarta ta bawa kwakwalwarta dama tare da gangar jikinta wajen sarrafa zuciyarta domin yankewa kanta hukuncin daya zama shi ne dai dai a cikin rayuwarta, tayi fatali da soyayyar Jabir da duk wani kulawarsa a gareta domin makomar gobenta, shiyasa da kanta ta zaɓi sakin wanda hakan sai da ya asssasa ƙaramin yaƙi a tsakaninsu, Jabir ya dage ba zai saketa ba, itama ta dage akan lamarin dan ba zata tsaya ta cutar da kanta akan nasa farin cikin ba, tana buƙatar tayi nesa da Jabir ko hakan zai kawo mata farin cikin data ke buri anan gaba. A lokacin ta kuma rushewa da sabon kuka tana share hawaye da dukkan hannunta, tace a cikin ranta.

Rabuwarmu shi ne alkhairi In Sha Allah, ba zan yarda son kanka ya jefa nawa rayuwar cikin kaico ba. Nayi sadaukarwa na shekara takwas a yanzu kuwa tura ta kai bango ina buƙatar farin ciki, kuma dole na koyi son kai na in ba haka ba a hankali zan gama kashe rayuwa ta a dalilinka.

Hawaye ya cigaba da kwaranya sai dai ta gimtse saurin kukanta saboda rarrashin da Mama ƙarama ta ke yi mata cike da tausayinta wacce take tsaye daga jikin motar. Haka suna kallo aka cigaba da fitar da kayan Safiyya ana ɗaurasu a babbar motar kwasan kaya, a jiya aka yi sakin amma kuma a jiya da yamma Baffa ya aiko mota daga Kano zuwa Abuja dan kwashe kayan Safiyya, sai cikin tsakiyar dare suka ƙaraso Abuja. Su mama ƙarama kuwa suna yin sallar asubahi suka tafi Train station ita da Yaya Ali da matarsa Hindatu sai babbar yayarsu Anty Indo. suka samu ticket suka hau sannan suka tawo Abuja, bayan sun ƙaraso suka samu taxi ya kaisu gidan Safiyya, kuma babu ɓata lokaci suka fara haɗa kaya suna fito dasu ana ɗaurawa a mota, hakan ya yi matuƙar ƙara tunzura Jabir wanda yake ganin da laifin iyayan Safiyya a mutuwar aurensu, da basu goyi bayanta ba da zasu cigaba da zama a inuwa daya duk wuya duk runtsi, ya tabbatar akwai zuga acikin lamarinta shiyasa ma ya yi sakin ko zai shaƙi iskar 'yanci dan ya jima a takure bisa ga matsin lambar da Safiyya tayi masa akan lallai sai ya saketa, shiyasa ya bar musu gidan su gama kwasar kayan sai dai yayi wa kansa alƙawarin Safiyya ba zata fita idda ba zai yi wani auren dan ya tabbatar musu ba ita kaɗai bace mace a duniya, yana da rufin asiri yana da kuma surar da dole zai samu me sonsa a duk yadda yake. 

Sai wajen ƙarfe uku suka gama tattara kayanta tas a mota sauran kayanta da yake gidansa na Kano shima za aje a kwashe su dan su rabu da kwallon mangoro su huta da ƙuda, auren Safiyya gabaɗaya ya same musu ƙaya a maƙoshi da ko wanne yake jinsa a wuya, kawai Baffa shi ne yaƙi bada damar da zasu kai maganar kotu tunda yaƙi saki, sai gashi cikin ruwan sanyi yayi kamar an yi ruwa an ɗauko. Mama ƙarama ta isa wajen da Ali yake tsaye da yake bawa driver umarnin su kama hanya. 

Gadanga ya namu tafiyar zai kaya.?

Ai yanzu kuwa zamu je mu samu jirgin ƙarfe huɗu ba ɓata lokaci In Sha Allah. 

To ya zamuyi da motarta.? ko zamu kwana a gidan Alhaji Ladan dake nan Wuse in yaso sai mu tafi goben in Allah ya kaimu. Sai na kira Baffa na faɗa masa. 

Mama ƙarama wlh bana son kwanan garin nan jina nake kamar akan ƙaya. 

Nima dai nafi son mu tafi. 

Cewar anty Indo data ƙaraso wajen fuska babu walwala saboda gajiyar aikin da suka sha, mama ƙarama ta jinjina kai. 

Wai dama motar ta ne nake tunanin yadda zamu tafi da ita tunda Baffa yace kar mu bar komai a gidan. 

Ai anan zamu barta domin yace kar na sake na tafi masa da wani abu daya shafi mallakinsa, ciki har da motar duk da ada ya bani amma yace ya karɓe abunsa. 

Cewar Safiyya data ƙaraso cikin jan ƙafa, ta tsaya tana nishi kamar mai asma, gabaɗaya ta zabge lokaci guda kamar mai jinya, fuskarta ta matse kamar mage sai girman idanu da ƙashin hanci. Yaya Ali ya ja tsaki. 

Kun ga ƙaramin mutum ko, motar banza motar hofi ai wlh bai isa ba dan kinci mota saboda wahalar daya baki na tsawon shekarun nan. 

A'a Gadanga ba za ayi haka ba, ku bar masa tsiyarsa, ke Indo yiwa Hindatu magana ta fito mu kama hanya yanzu kar mu rasa jirgi, ke kuma sai kije ki kwashe duk abunda kika san naki ne a motar ki saka a jaka. 

Cewar mama ƙarama data ƙare maganar ga Safiyya, ita kuma sai ta juya ta kalli motar tana kuma dawo da kallonta gare ta. 

Tun ɗazu na kwashe komai suna jakar anty Indo. 

To magana ta ƙare, Malam Ali sai mu kama hanya. 

Mama ta ƙare maganar tana yin guntun murmushi. Ali ya gyaɗa kai ya wuce wajen mai gadi dan ya bashi saƙo, su kuma suka gyara zaman mayafi Indo taje ta kira Hindatu ta fito suka yi hanyar waje, mama tana riƙe da Hannun Safiyya kamar wata ƙaramar yarinya, da yake jikinta babu kwari tafiya kawai take kamar zata daɗi.

Rahma ce.