MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 33

by @maimunabala209

MATAR GIDA 033




SHUUKRAN/022






P33



Bayan Unaisa ta idar da sallah ta ji gaba ɗaya suturar jikinta ya takura ta, taji baza ta iya zama da kayan ba hakan yasa ta miƙe tsaye ta cire su,doguwar rigar da Ɗalha ya karɓa a hannuta ɗazu ta dauko ta zura tana mayar da numfashi,wani irin yunwa ne ya fara ɗawainiya da ita hakan yasa babu shiri ta fita daga ɗakin zuwa parlour,wormer's ɗin safe tare da kwanukan da suka yi breakfast suna nan inda ta baro su,daga gefe kuma wani basket da wormer guda ɗaya a ciki sai jug cike da kunun aya da alama har an kawo masu abincin rana,zama Unaisa ta yi tare da buɗe wormer,shinkafa da wake ce dafa duka wanda yaji kifi bushasshe da kayan lambu yana fitar tururin zafi haɗe da kamshin spacies wani yawu Unaisa ta haɗe kafin ta dauki plate ta sa daidai wanda zai ishita kofi ta dauko ta tsayaye kunun aya da kallo ɗaya zaka masa ka fahimci sanyin da ya yi da kauri,a natse Unaisa ta fara cin abincin tana ƙara yaba daɗin abinci a zuciyarta,sosai kunun ya yi mata daɗi saida ta sha kofi biyu kafin ta sarara,hamdala ta yi tana ƙara godewa Allah, tana shirin barin parlourn ne Ɗalha ya fito daga ɗakinsa,tana daf da shiga ɗakinta Ɗalha dake tsaye cikin parlour ya kira sunanta yana kallon yadda ta bar kwanuka gaje gaje,waigowa ta yi ta kalle sa kamar baza ta amsa ba sai kuma ta juya ta dawo parlour har sannan idonta a kansa kamar yadda shima yana kallonta ta ce ''ga ni''nuna mata plate ya yi da hannu kafin ya jefo mata tambaya ya ce ''me wannan?" shiru ta masa bata tanka sa ba,har sannan idonsa a kanta ya ce ''nan ya dace ki bar plate ɗin da ki ka ce abinci har wanda na yi amfani da su? pls Unaisa ban son yawan surutu ki gyara wajen nan  yanzu kin dai ji na faɗa maki'' wani irin murmushi Unaisa ta yi kafin ta ce ''wannan ba aiki na bane aikin masu aikin da ke gidan ne,kuma fa kar ka manta ni amarya ce sai gobe zan cika sati gaskiya bazan iya aiki ba,ba zai yiwu ina amarya a sani aiki ba'' wani irin murmushi mai sauti Ɗalha ya yi kafin ya mayar da dubansa gareta tare da gyara tsayuwar sa ya ce ''wa ce amarya?" shiru Unaisa ta yi tana kallonsa ganin irin kallon da yake mata,wani gajeriyar dariya Ɗalha ya yi kafin ya ce ''amarya da wannan rigar? amarya fa ki ka ce?" wani dariyar ya kuma yi ran Unaisa ne ya ɓaci ta ji kamar ta shaƙe shi ta huta gyarar murya ya yi kafin ya ce ''malama ki gyara wajen nan na faɗa maki bana son yawan magana'' daga haka ya samu waje ya zauna nan cikin parlour ya kunna tv hannusa riƙe da remote yana canza tasha zuwa kwallo,Unaisa da haushi ya gama cikata ta durkusa ta kwashe kwanukan kamar yadda ya faɗa mata ta kai su kitchen ta wanke plate da suka yi amfani da su bayan ta gama ta yi wucewarta ɗaki bata ko kalle Ɗalha dake zaune cikin parlour ba,shi kuwa ya bita da kallon gefen ido tana tafe rigarta na biye da ita bayan shigarta ɗaki Ɗalha ya taɓe baki ya mayar da hankalin sa kan football da yake kallo bayan shigar Unaisa ɗaki bathroom ɗinta ta wuce ta biya bukatarta bayan ta gama ta yi tsarki ta fita daga bathroom tsabar ɓacin rai ta manta wani abu wai flushing kawai ta yi ficewarta 
















Washe gari monday Amirah ce tsaye cikin parlour tare da yara yadda tana sa masu uniform Aina'u na can kitchen tana zubawa yaran abinci cikin flask zuwanta gidan kenan taga Amirah na fama da yara hakan yasa ta cire hijab ta linke tare da ajiye kan kujerar parlour, kafin ta tambaye Amirah ko akwai abinda zata taimaka mata da shi bayan sun gaisa Amirah ta ce ''ta gama komai abinci kawai zata zuba wa yara cikin flask hakan yasa Aina'u wuce kitchen dan zubawa yaran abinci karfe bakwai da mintina arba'in tuni Amirah ta gama ma yaran shiri ɗakinta koma ta dauki doguwar hijab ta zura ta dauki kuɗin mota kafin ta fita,bayan fitar ta daga ɗaki ne ta cewa Aina'u ta fara yin wanke wanke da mopping kafin ta dawo daga kai yara makaranta,cike da girmama Aina'u ta masa daga haka Amirah ta haɗa kan yara ta fita kai su makaranta,bayan dawowar Amirah ta tarar tuni Aina'u ta gama share gidan da mopping wanke kwanuka take yanzu,Amirah ta ce ta bari su yi breakfast kafin ta ƙarasa babu musu Aina'u ta bar mopping ɗin,tare suka yi breakfast ita da Amirah,bayan sun gama ne suka cigaba da aiki yadda Amirah ta wuce ɗakinta ta fara gyarawa ita kuma Aina'u ta zuba kayan wanki cikin injin wanki,karfe biyar daidai Amirah ta bar gida zuwa makaranta su Sudais domin daukar su daga makaranta tare suka fito da Aina'u bayan ta gama aikinta na ranar,sosai Amirah ta ji dadi ganin yadda gidanta ya yi tas ko ina tsaf babu datti gashi bata gaji ba saboda kusan duka aikin Aina'u ce ta yi,bayan ta dawo daga daukar yara ta sa sun cire uniform ta yi masu wanka ta zuba masu abinci,bayan sallar magrib Amirah na zaune da yara cikin parlour ta ji ana buga gate haɗe da sallama hijab ɗinda ta yi sallar magrib ta dauko ta zura kafin ta fita kafafunta sanye da black simple shoe bayan ta isa wajen gate ɗin  ta ce ''waye''  muryar wani ta ji ya kuma yin sallama a karo na babu adadi amsa sallamar Amirah ta yi ya ce ''suna na Abdullahi mai gidan ne ya turo ni,malamin da zai riƙa koyar da yara ne'' da sauri Amirah ta ce ''au sannu da zuwa malam'' ta faɗa tare da buɗe kofa bayan ta buɗe kofar ne ta koma can gefe kafin malamin ya shiga cikin gidan ba tare da kallon fuskarsa ba suka gaisa kamar yadda shima bai kalle fuskarta ba da sauri Amirah ta wuce cikin gida ta haɗa kan yara ta ba Sudais shimfiɗa ta ce ya shimfiɗa su zauna a kai,bayan fitar su duk suka gaishi Malamin ya amsa masu,ba tare da ɓata lokaci ba ya fara koya masu karatu,da karatun kur'ani ya fara inda ya tambaye su surar da suke duk suka faɗa masa,tilawa karatun Alkur'ani ya fara yi masu bayan sun gama ya yi masu ƙari,sosai Mallam Abdullahi ya yi mamakin yadda yaran suke fahimtar karatu da wuri, bayan sun idar da karatun Alkur'ani ya yi masu tarihin annabawa ya kuma daura da nasiha yadda ake zama da iyaye, kafin daga bisani ya ce suje su kawo littattafan su na boko,da kansa ya taimaka masu sun yi homework saida ya tabbar sun fahimci duk abinda ya ƙoya masu kafin ya ja su sallar isha'i sannan ya  sallame su bayan ya yi masu addu'a,a gajiye suka shiga gida kallo ɗaya Amirah ta yi masu ta fahimci gajiya dake tare da su hakan yasa ta umurce su da su je su yi fitsari kafin su kwanta kamar yadda ta faɗa hakan suka yi,addu'ar da Ɗalha ya bata ya ce ta riƙa karanta cikin ruwa ta tofa ta basu su sha, takardar Amirah ta dauko ta samu waje cikin ɗakinta bayan ta diba ruwa cikin kofuna uku ɗaya Sudais me mantuwa ɗaya Ummu Abiha da ke zama ita kaɗai ta yi surutu ɗaya kuma na Rayyan mai yawan faɗa da kowa,Amirah ta karantawa kowanne addu'arsa kafin ta je ta ɗaga su ta basu ruwan addu'ar suka sha 


















Yauma kamar kullum karfe goma na dare Ɗalha ya kirata bayan sun gaisa ne Amirah ta sanar masa Mallam Abdullahi yazo ya yiwa yara karatu daga haka sun sha hirar su ta masoya kafin daga bisani ya kashi waya ita dai Amirah har sannan ta ƙasa sakin jiki da shi kamar ɗa harda tana jin daɗin yadda ya canza lokaci guda yana nuna mata soyayya,washegari karfe shidda da rabi na safe Unaisa ce zaune kan darduma bata daɗe da idar da sallah ba,daren jiya ta samu bacci me kyau dalili kowa Ɗalha yana fushi da ita,rabon da ta sa shi a ido tun jiya da la'asar da ta gama cin abinci ya ce dole ta wanke plate tun sannan bata sake ganinsa ba,da dare ita kaɗai ta ce abincinta,dadi ma ta ji da ta fahimci yana fushi da ita ko babu komai daren jiya ta yi bacci yadda ranta ke so,da hannuta ta yi amfani wajen yin tasbihi ta shafe addu'a maganar azkar kowa babu ita, daman bata saba yi ba kwanciya ta yi bayan ta shafe addu'a ba ita ta farka ba sai karfe takwas da rabi,sauka ta yi daga gadon da wannan rigar dai a jikinta,bathroom ta wuce ta wanke baki,da hannuta ta yi amfani ta goga hakuranta,daga haka ta fita daga bayin,bayan fitarta bata tsaya ko ina ba sai parlour ta tarar har an kawo masu abin kare waje ta samu ta zauna kafin ta buɗe wormer, dan wake ne cike cikin wormer,daga gefe kuma wata karamar farar roba ce da aka cikata da mangyaɗa soyayya ga kuma robar yaji cike da yaji sai wani faranti da aka yanka salak haɗe da dafaffen kwai,wata ƴar madaidaiciyar flask ta gani cikin basket ɗin hakan yasa ta buɗe flask ɗin cike yake da kunu tsamiya,Unaisa bata tsaya ɓata lokaci ta diɓe dan wake daidai yadda zai isheta ta sa a plate,bayan ta gama breakfast plate da kofi da ta yi amfani da su ta kai su kitchen ta wanke kafin daga bisani ta wuce ɗakinta bayan shigarta ɗaki bathroom ɗinta ta wuce wani irin wari ya dake hancinta nan ta shiga tunani ko warin me oho,nan ƙasan bathroom ta rusuna ta yi fitsari ta yi tsarki haka dai ta yi abinda zata yi ta fita daga bathroom ba tare da sanin dalilin warin da bathroom ɗin ke yi,kwanciya ta kuma yi a karo na biyu,unin ranar gaba ɗaya bata sa Ɗalha a ido ba kuma hakan bai dameta ba,haka ta uni kwance daga bacci sai chating karfe biyar daidai ta tashi ta shiga bathroom ta dauro alwala bayan fitarta ta haɗa sallah azahar da la'asar bayan ta idar ta fita parlour ta ci abinci,karfe goma daidai na dare Unaisa ce tsaye cikin bathroom tana ta tunanin dalilin warin da bathroom ɗin ki yi can dai wata tunani ta faɗo mata babu shiri ta fita daga bathroom ɗin da gudu tana kiran sunan Ɗalha dake zaune cikin parlour yana shan tea ajiye kofin ya yi tare da miƙewa tsaye a guje ta ƙaraso parlour tana nuna masa kofar ɗakinta Ɗalha ya riƙe ta da sauri yana tambayarta me ne ta ƙasa magana sai nuna masa kofar ɗakin take wani tsawa ya yi mata tare da fadin ''ke me haka me kika gani a ɗakin?" da kyar dai ta saita nitsuwarta kafin ta ce ''wallahi ina tunanin maciji ya shigo min bathroom tun safe nake ta jin wari na rasa warin me sai yanzu na tuna maciji ke da irin wannan warin'' Ɗalha ya zaro ido waje ya ce ''what!! maciji a gidan nan?" Unais ta ce ''eh wallahi je ka duba'' ta faɗa tana sosa kai









 


*SHUUKRAN