MATAR GIDA PAGE 34
MATAR GIDA 034
SHUUKRAN/022
P34
Ɗalha bai tsaya ɓata lokaci ba cikin hanzari ya nufi ɗakin Unaisa da shigar sa bayi ya wuce inda ya fara dube dube, cak Ɗalha ya tsaya yana son fahimtar warin da yake ji,da wani irin sauri ya waigo ya kalle kofar ɗakin a tunaninsa Unaisa ta biyo bayan sa sai ya ga gaba ɗaya bata ɗakin,cikin sanyin jiki da kuma tsoron abinda zai gani Ɗalha ya ƙaraso daidai inda toilet seat yake a hankali ya kai hannu ya buɗe murfin toilet seat ɗin kamar yadda ya yi tsammani hakan kuwa ya faru bayan gida ne cikin toilet seat ya kumbura ya tashi saman ruwa yana fitar da wani mugun wari da ɗoyi babu shiri Ɗalha ya fita daga bathroom ɗin zuwa nasa yana toshe baki yana kokarin danna amai da ya taso masa duk yadda ya yi ɗan ganin bai yi aman ba ya ƙasa daga shigarsa bathroom ya nufi toilet seat ɗin bathroom ɗinsa ya fara amai babu kakkautawa duk wani abinda ke cikinsa saida ya fitar da shi a wannan lokacin,Unaisa dake tsaye cikin parlour ta ji motsi a bathroom ɗin Ɗalha hakan yasa ta nufi ɗakinsa doguwar riga jikinta na binta,bayan shigarta ɗaki bathroom ɗinsa ta wuce ganinsa ta yi durkushe yana kwara amai cikin toilet seat tsaye ta yi kofar bathroom tana kallon yadda yake kwara amai bayan wasu ƴan mintina aman ya tsaya a hanakli ya tashi ya kuskura baki bayan ya yi flushing aman,ganinta ya yi tsaye tana kallonsa bai ce mata komai ba ya bi gefe ya wuce a hankali ya zauna bakin gado yan mayar da numfashi jiki babu kwari Unaisa ta ja kafa zuwa inda Ɗalha ke zaune ta rusuna gefen sa idonta kansa ya jingina jikinsa a jikin gado idanunsa rufe yana mayar da numfashi murya can ƙasa Unaisa ta ce ''cizon ka macijin ya yi?" shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba har sannan idonta kansa ta ce ''na kira Ammi?" sai a sannan Ɗalha ya buɗe ido ya shiga ƙare mata kallo ya saka ƙwayar idonsa cikin nata ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta ce ''me ke faruwa babe?" a takaice Ɗalha ya ce ''je ki yi flushing abinda ki ka bari cikin seat ɗin bayin ki'' lokaci guda wani irin kunya ya rufe Unaisa sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta shiga sosa kai sai yanzu ta tuna ta yi amfani da bathroom jiya da la'asar ta manta bata yi flushing ba cikin tsantsan kunya ta miƙe tsaye tana wasa da hannu rigar da ke jikinta da ya rufe gaba ɗaya hannuta Ɗalha ya riƙa binta da kallo da alama ko pant bata sa ba haka ma bra daga ita sai wannan rigar nacin,she looks so unkept ta yi cuku cuku kamar ba amarya ba ga sumar kanta rabi a ciki rabi a waje hular kanta a karkace
Tun da yake bai taɓa ganin amarya kamar Unaisa ba harda wannan shine karo na farko a rayuwarsa da ya ƙara aure lokacinsa ya aure Amirah ta dauki sama da watanni huɗu tana gayu da tsafta,lokacin da ta dauki cikin Sudais ne ta rage gayu a uni sai ta yi wanka sau ɗaya amma Amirah bata taɓa cire rana ba tare da ta yi brush ba,da cikin Sudais ya shiga wata shidda Amirah ta cigaba da harkokin ta duka yaran da ta haifa haka take da cikin ya shiga wata shidda shikenan ta gama laulayi,bai taɓa jin wani wari tare da Amirah ba kama daga warin jiki zuwa baki ko yaushe cikin gyara da tsafta take,lokacin da yara sun mata yawa ne ya fara samun matsala da ita yadda in ya dawo daga aiki zai tarar yara sun ɓata gida kwanuka da suka ci abinci a can uniform ɗin su a can toys ɗin su can tun daga wannan lokacin ya fara ganin gazawar Amirah,bayan ya yi mata saki ɗaya ta tafi ta bar masa yara lokacin ya fahimci lallai tana kokari sannan kuma bata da kazanta sam,kawai dai aiyukan gidan ne sun yi mata yawa,Amirah na kokari sosai wajen kula da tsaftar jikinta da na yaranta a kullum sau biyu take wanka haka ma yaranta,sannan Amirah bata taɓa zama da kaya ɗaya tun safe har dare ba kowanne rana kaya saiti biyu take sa haka ma yaranta,sai dai baza ka taɓa ganin Amirah ta sha kwalliya a fuska ta shafa huda da jam baki ba shi kuma Ɗalha yana son yaga mace ta yi kwalliya ta shafa huda da jambaki ta kuma sa cingan a baki tana ƙas ƙas hakan yana masa dadi sosai,Ɗalha ya bi Unaisa da ido har ta fita daga ɗakin,sosai ta ji kunya hakan yasa da shigarta ɗakin bata tsaya ɓata lokaci ba ta wuce bathroom ta yi flushing kamar yadda Ɗalha ya faɗa mata saboda kunyar abinda ta yi har wankin bathroom ɗin ta yi bayan ta gama ta yi wanka ta yi brush ba dan Allah sai dan kunyar da ta ji,tun da aka kawota gidan sai yau ta yi wanka me kyau ta kuma gyara ɗakinta ko ina ya yi tsaf a ɗakin bayan ta fita daga wanka wata riga da wando na Pakistan ta dauko daga kayan lefenta ta sa sosai ya yi mata kyau,yau dai Ɗalha ya yi sa'a har turare Unaisa ta fesa,bayan ta gama shirya kanta ta kalle kanta cikin madubi ta saki murmushi kafin murya can ta ce ''masha Allah yanzu sai wata ta kwace min miji gwara na riƙa wankan dai ko ba kullum ba kaman bayan kwana uku zuwa huɗu haka..yauwa masha Allah'' ta faɗa tana gyara daurin ɗankwali fuskarta dauke da murmushi
Da dare Ɗalha ne zaune cikin parlour Unaisa na gefensa tana sarving ɗinsa abinci tuwon shinkafa miyar ɗanyar ƙuɓewa yaji namar rago da man shanu tuwon ya yi fari ƙal yana fitar da tururin zafi Unaisa ta sa masa ta zuba masa miya kofi ta dauko ta tsiyaya masa zobo mai sanyi da ya sha haɗi babu laifin ƴan aikin Ammi sun iya girki,bayan ta yi sarving ɗinsa ne ta sa nata ta samu waje ta zauna ta fara ci sosai ta ci abincin shi dai Ɗalha sai satar kallonta yake ganin yau ta yi wanka ta canza kaya ba tare da ya mata magana ba,bayan sun gama cin abinci ne ta kwashe kwanuka ta kai su kitchen ta wanke daga haka ta wuce ɗakinta Ɗalha na nan zaune cikin parlour yana kallon football bayan shigarta ɗaki ta canza kayan jikinta ta dauki favourite zaninta ta daura ba tare da ɓata lokaci ba ta kwanta tare da kunna data nan ta shiga chating misalin karfe goma daidai na dare wani mugun kaikaye Unaisa ta ji daga can ƙasa hannu ta kai ta fara sosa gefe da gefe saboda har sannan tana jin tsoron taɓa wajen,ganin kaikayin bana wasa bane yasa Unaisa tashi ta shiga bathroom ta surka ruwan ɗumi cikin buta ta yi tsarki har ta kai hannu wajen da niyya wanke wajen taga baza ta iya ba kawai ta juye ruwa a jiki daga haka ta fita daga bathroom ɗin,a wannan daren ƙaikaye ya hana Unaisa sukuni da ta yi tsarki zai bari bayan wasu ƴan mintina kaikayin zai dawo misalin karfe uku na dare Unaisa ta dauki wani zani daga saif ta sa a wajen ta fara sosa alamar wani abu taji kamar dusar awara da wannan zanin Unaisa ta yi amfani ta kwashi abin zaro ido tayi ganin abinda ke fita a jikinta wani farin abu ta gani kamar dusan awara babu shiri ta tashi ta wuce ɗakin Ɗalha hannuta riƙe da zanin, bakinta dauke da sallama ta shigo ɗakin Ɗalha ya buɗe ido a hankali kasancewar baya da nauyin bacci bayan shigarta ne ta kunna switch ɗin wutar ɗakin,nan take ɗakin ya yi haske a hankali Ɗalha ya tashi zaune yana ƙarewa Unaisa kallo da ta nufi bed ɗinsa hannuta riƙe da zani lokaci guda tana gyara daurin kirgi,kallo ɗaya ya mata ya fahimci hankalin ta ba a kwance yake ba hakan yasa Ɗalha gyara zama yana jiran jin abinda ke tafe da ita a kiɗime ta miƙo masa zanin tare da nuna masa abinda ta share daga jikinta ɗazu karɓar zanin Ɗalha ya yi yana kallon wannan farin abun lokacin wani irin kaikayi ya dami Unaisa zuwa yanzu bazata iya jurewa ba nan take ta kai hannu ta fara sosa wajen babu kakkautawa ganin irin sosa da Unaisa ke yi yasa Ɗalha jefo mata tambaya inda ya ce ''me ke damun ki?" shiru Unaisa tayi tana cigaba da sosa ganin da gaske take yasa Ɗalha sauka daga gadon tare da ajiye zanin ya zo ya riƙeta ta baya yana ƙara tambayarta abinda ke damunta,raba jikinta da nasa ta yi ta wuce bathroom ɗinsa ta surka ruwa ɗumi ta yi tsarki bayan ta yi tsarki ne ta samu sauƙin kaikayin sai a sannan ta samu damar yiwa Ɗalha bayanin abinda ke damunta tun da ta fara magana Ɗalha ke kallonta cike da mamaki bai yi tsammanin kazantarta ya kai haka ba sai yau,zanin ya dauko ya ƙorewa abin da ke zanin ido can ya ɗago ya mayar da dubansa gareta ya ce ''ki na nufin daga jikin wannan ya fito'' gyaɗa kai Unaisa ta yi kafin ta ce ''eh'' daga haka Ɗalha bai sake cewa komai ba ya tashi ya wuce bathroom ruwan ɗumi ya tara cikin bathtube daga haka ya fita daga ɗakin zuwa kitchen ya dauke gishiri kafin ya dawo bathroom ya zuba gishiri cikin ruwan ɗumi,fita ya yi daga bathroom zuwa ɗakinsa inda ya tarar da Unaisa tsaye tana matse kafafu kallo ɗaya ya mata ya dauke kai kafin ya nuna mata gado ya ce ''kwanta na duba'' babu musu Unaisa ta kwanta Ɗalha ya duba da torch wayarsa ya yi amfani ya haska wajen wani abu ya gani fari kamar dusa ga wani ruwa dake fita a wajen,ba ƙaramin jurewa Ɗalha ya yi ba saboda yadda wajen ke fitar da wani irin wari haɗe da karni kamar danyen kifi
SHUUKRAN