MARYAMA

Page 55

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

55



Yana shiga kitchen din ita kuma ta na fita,da gudu ta fice fiiiit zuwa palon, a hargitse Qaseem ya biyota zuciyarshi na bugawa da karfi karfi ganin abun da ke boye hannunta,kan Maryama Sameera ta nufa gadan gadan hannunta dauke da wata wuka sabo dal sai sheki take yi idanunta kuma kamar zai yi aman wuta.

"What the heck are you doing sameera?" ya fada a tsawace lokacin da Maryama ta yo kanshi da gudu ganin matar kasheta zatayi da gaske, ta baya ta kankame shi gam tana kiran help,help,help...Bayan Qaseem din sameera ta bita, "shegiya dan ubanki sai na kasheki in ga waye gatanki a nigeria,karya kike baki isa inyi sharing mijina dake ba, sai na kasheki in yaso nima a kasheni"sameera ta fada tana kokarin kaiwa Maryama sara,da wani irin zafin nama ya kama hannunta ya murde da karfin gaske wukar ta sake ta kwala ihun azaba.

Da azama ya tsunkuya ya dauke wukar, wani wawan cafka Sameera ta kaiwa Maryama ta makure wuyarta da karfi ta fara dukanta duk ta inda ta samu, duka take mata kamar Allah ne ya aikota.

Duk yadda Qaseem ya so kwatar Maryama hannun Sameera kasawa ya yi dan rikon da ta mata tamkar da aljanu ne ba ita kadai ba, "me kike aikatawa haka ne zaki yi kisan kai fa.
Saketa, ki sake ta nace" yana magana yana neman kwatar Maryama amma ya kasa mari ya zabga mata a fuska ya kara kwasheta da wani marin da taga taurari suna walkiya babu shiri ta sake ta, Maryama ta fadi gefe tana sauke nannauyan ajiyar zuciya dan tuni ta fara shakar kamshin mutuwa.

"Honey! Ni ka mara? ka mare ni akan wannan bakar kadarar? Ni sameera ka mara akan wannan yarinyar?" Sameera ta fada tana rike da kuncinta sai dai bata yadda hawaye ko digo ya sauka saman fuskarta ba."How dare you zaki shake yar mutane haka? idan ta mutu kinsan hukuncin da zai hau kan ki kuwa?

"Honey?" ni ka mara akan wannan? ta kara fada tana nuna Maryama dake gefe sai shafa wuyarta ta ke yi tana kokarin neman janyo numfashinta da ya yi daukewar wucin gadi. "look Sam.."

"Babu abun da zaka fadamin," Ta katse mishi maganar da ya fara, da gudu ta juya zuwa dakinta, binta yayi da sauri yana kiran sunanta amma ko juyawa batayi ba, car keys ta dauka da gyalenta ko yafawa bata yi ba ta fito a fusace.

"Ina zaki je Sameera? kar ki yadda ki sa kafa ki fita daga gidan nan"

Cakkk ta tsaya daga shirin fita da take kokarin yi ta juyo a fusace tana kare mishi kallo from head to toe sannan ta juya ta cigaba da tafiyarta...."Idan kika kara taku daya a nan zaki hadu da fushi na Sameera" ya kuma fada yana kallonta.

Wannan karon ba ta tsaya ba tana tafiya tace, "Ka dade banga fushin naka ba honey, kayi duk abun da kaga dama kawai," daga haka ta bar palon, da sauri sauri ta karasa parking space ta fada motarta gami da bashi wuta a dari da sittin ta bar gidan saura kadan ta kade mai gadi da ke rawar jikin bude mata kofar,gudu take yi bisa kwalta sosai tamkar ita kadai ce a bisa kwaltar, ga dare ya fara nisa.

Ikon Allah ne kawai ya kawota gidan anty Falmata shima da mugun karfi ta danna horn mai gadin gidan ya bude mata ta shiga ko parking mai kyau bata gama ba ta bude motar a rikice gyallen ta a hannu ta shiga cikin palon gidan. hannu ta daura bisa kanta ta kurma wani irin ihu sannan ta durkushe nan ta fara kukan da tayi ta dannewa a gidanta dan kar wannan yarinya ta rainata.

"Subhanallah Sameera, me ke faruwa ne? waye ya mutu," 

Cewar anty Falmata da ta fito da mugun gudu jin ihun da akayi a falonta da muryar sameera,kuka take yi babu kakkautawa tamkar ana zare mata idanu ta kasa bawa antyn labari abun da ke faruwa,..Dafe kirji Falmata ta yi ta ce, "munshiga uku mun lalace, ba dai hajja ce ta mutu ba kam. Innalillahi wayyo hajjata.

Sosai ta rikice hakan yasa sameera tsayar da kukan da ta keyi ta mike hadi da rungume ta,cikin wani irin murya ta ce.

"Anty Falmata kwana na ya kare a duniya wayyo na shiga uku na lalace wllh mutuwa zanyi, mutuwa zanyi bazan iya dauka ba, zuciyata zata fashe bazata iya juriyar ganin Qaseem da wata mace a matsayin matar shiba ba zan iya sharing nashi da wata ba ki taimakeni Anty."

Ta kare hade da sakin wani marayan kuka mai bada tausayi...

Dafe kirji Anty Falmata ta yi gami da fadin

"Na shiga uku ni Falmata, Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani da wannan farar daren, ke Sameera hankalin ki daya kuwa? ki nutsu ki min bayanin da zan fahimta mana? me ki ke son cewa ne? Gaba daya ban fahimci inda kika dosa ba,shi Alqaseem din ne ya ce miki zai kara aure?".

Karfin kuka na na kara na ce, "Anty falmata yarinyar da nake baki labari jiya Qaseem ya kawota gida ashe matar shice ni ban sani ba ashe yaudarata ya ke yi dama, wllh matar shi ce anty zuciyata zafi ta ke min ki taimakeni, bazan iya komawa gidan in kalle ta ba bazan iya ba kashe ta zan yi sai dai nima a kashe ni, wai Qaseem ne ya sa hannu ya mare ni akan wancan yarinyar daga kawota gidan? Anty zuciyata zata yi bindiga idan ina ganinta a gidana bazan koma ba.

Cike da al'ajabi Falmata ke kallon kanwar tata kafin tayi gathering courage ta ce, "Aure? shi Qaseem din ya ajiyeki ya ce miki ya yi aure? Kuma har ya mareki bayan yaudara da cin amana da yayi miki na yin aure ba tare da kin sani ba? To lallai ya jawa ko ma yar gidan uban waye ya auro, ya jan yo mata duk abun da zai sameta and sai yayi nadamar daga hannunshi da yayi ya mareki.

Shi bai san in ban da kaddara da kafiya irin naki ba ko hanyar gidanmu ya isa yaje neman aurenki ne? Bai san rufa masa asiri kike ba, to mu ba'a mana kishiya a kaf zuriyarmu kuma baza'a fara a kan ki ba,batun komawa gidanki kuma ya zama dole ki koma dan ki nunawa yar iskar cewa mu kaffff zuriyarmu babu mai kishiya don haka dole mu nuna mata illar auren mijin wata ta yadda gaba ko a nafarki taga mijin wata idan ta farka sai ta yi sadaka, maza share wadannan hawaye naki kar ki kuma bari su ga rauninki yanzu ina suke shida shegiyar yarinyar".

          "Na barsu a gida anty".

"Ohk maza shige muje daki ki kwanta nan da sati daya da kafarta zata bar miki gidanki yadda ta shigo, sai ta fahimci coinsequensess na auren mijin wata a duniya, haba sai ka ce ba muba? kwantar da hankalinki kar ki ji komai,yadda ta zo a firgice haka zata koma inda ta fito a firgice."

Har dakin baccinta dake upstair antyn ta kai ta ta kara tausarta da bata tabbacin nan da sati daya Maryama zata bar gidan da kafarta.Da yake mijinta matafiyi ne yana yawon kasashen duniya kuma itama kamar sameera Allah bai bata haihuwa ba a nan dakin suka kwana dukkansu biyu, wannan dare shine bakar dare a rayuwar sameera, yadda taga rana haka taga wannan daren bacci ko digo babu sai kukan da takebyi kamar ranta zai fita, da zarar ta rufe idanu Qaseem ta ke gani da wannan sadaka yallar...

Dafe goshi Qaseem ya yi gabanshi na faduwa "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un" ya fada yana tattare fatar goshinsa waje daya,saman kujera ya zauna ya rasa tunanin da zai yi, yasan taurin kan Sameera ko ya bita yanzu sai dai ta tara masa mutane a kan hanya, sai dai saukin yasan babu inda zataje sai gidan Anty Falmata.

Dan haka ya dauki wayarshi ya lalubo layin anty Falmata amma cikin rashin sa'a yaji wayar a rufe, layin Layin Sameera ya kira yaji wayar a kusa dashi tana ringing, "Ya salam" ya ambata jin yadda kukan yarinyar nan ke barazanar nakasa mishi dodon kunne.

Idanunshi da suka rine jawur dan tashin hankali ya dago hade dasauke su a kanta, calmly yace, "bana son wannan kukan".

Kamar wadda ya kara tunzurata ta wage baki iya karfinta gami da kara sautin kukannata.

A mugun fusace wannan karon ya ce, "Will you shut your mouth quite or sai na sassaba miki kema, wuce ki bani waje stupid girl, duk ba ke kika janyo min halin da na ke ciki ba ina zamana lafiya daga taimako.

Rufe min baki kafun balla bakin kiyi kuka mai dalili.

Toshe bakina nayi da hannu biyu a kokarin ganin kukan bai fito ba sai hawaye da ke shatata saman fuskata, wannan wani irin tashin hankali ne? na yi wa kaina tambayar da babu mai amsa min ita,wayar boys quarters Qassem ya kira ya sanar da Mau ta zo yanzun nan yana son ganinta, ko minti biyar ba'ai ba Mau ta shigo ta zube gaban shi da fadin "gani ranka ya dade".

Dan nisawa ya yi ya ce, "Guest room din can, ya fada yana nuna mata guest room din da hannu, shi na ke so ki tsaftace min yanzun nan ya yi tas ki canza mishi bedsheet". Yanzun nan zan aiwatar ranka ya dade" cewar Ma'u mamaki fal ranta na wacece ne wannan yarinyar menene a tsakaninsu da uban gidan nata.

Cikin lokaci kadan Mau ta tsaftace dakin tas ta gyara curtains ta canza bedsheet gami da bude AC ta fesa freshner take dakin ya dauki walkiya bathroom din ma tsaff ta wanke shi sannan ta fito ta ce komai ya kammala ranka ya dade.Hannu kawai ya daga mata alamar ta fice, kallonshi ya mayar kan Maryama dake tsaye har lokacin ba ta motsa daga inda ta ke ba, agogon dake makale saman tafkeken plasma dake manne bangon dakin ya kalla.


Karfe goma da kwata na dare agogon ya nuna mishi hakan ya sa shi mikewa da sauri yana kallon Maryama, can kasan makoshi ya ce, "mu je,..."

Babu musu ta bi bayanshi har cikin dakin da mai aikin ta fito yanzu, "nan shi ne dakinki har zuwa lokacin da za muga yadda Allah zaiyi"akwai duk abun bukata a bandaki akwai abun rufa cikin wardrobe." 

Daga haka ko kallon inda take bai kara ba ya sa kai ya fice daga dakin, a hankali na taka zuwa bakin gadon na zauna ina sakin wani marayan kuka da fadin "dan Allah Innarmu ki zo wayyo hamma Jay kazo ka ceceni wallahi Allah matar zata kashe ni dan Allah kuzo gareniiii" na fada da sakin sabon kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Tun ina kuka har na bingire da bacci a wajen ban sani ba,shima Qaseem wannan dare dai a birkice ya karasata hakama a bangaren Sameera.

Washe gari misalin karfe tara na safiya a gidan Anty Falmata ya samu Qaseem,ko da mai aiki ta sanar ma ta zuwan Qaseem din ta kwashe a kalla minti talatin sannan ta sauko kasa cike da fara'a ta karbeshi ba tare da ta nuna mishi komai kan fuskarta ba, sai dai deep down ji take kamar ta sjake shi har sai ya daina numfashi,fara'a shimfide saman fuskarta suka gaisa sannan ya fara bata hakuri akan abun da ya faru..


"Karka damu Qaseem, ko da dai kai ma baka kyauta ba kam ai zaman tare yafi gaban wasa,ya kamata ace akwai communication a tsakaninka da matarka amma ta ji abu haka kwatsam ai sai kasa zuciyarta ta buga, to yanzu dai komai ya wuce sai dai a tari gaba kuma, itama sameera tayi aikin yarinta amma na mata fada sosai insha Allah bazata kara ba kai kuma kayi kokarin ganin kayi adalci a tsakaninsu sannan ka ringa tuna irin hallacin da tai maka a rayuwa, ta zauna da kai tun kana saida leda akan wheelbarrow, ta zauna dakai tun ba'a cin abinci sau uku a gidanka a rana not minding cewa irin gidan da ta fito da irin arzikin da iyayenta suka mallaka amma tayi hakuri da kai, to kayi kokarin yin adalci.

Abu na karshe kuma shine bazata dawo yanzu ba sai nan da kwana uku by then ta farfado daga unexpected shock da ka bata. Daga haka ta mike ba tare da ta bashi daman cewa komai ba.

"Amm anty ko zan samu ganinta" cewar Qaseem yana tsungunnar da kai kasa,.."ehhh to yanzu kam ta na bacci amma ko zuwa anjuma zaka iya dawowa,daga haka ta haye sama ta barshi a wajen.

Da kyar ya lallaba ya fita daga palon, a parkin space ma ya dade jikin motar shi kafun ya shiga ya bar gidan.Sai a lokacin sameera dake makale jikin window ta matsa taa sauke numfashi sama sama.

Ganinshi yanzu ya sa ta ji kamar ta je ta rungume shi.bayan fitar Qaseem da kamar minti talatin anty Falamata ta fito shirye tsaff da ita ta samu Sameera dake jiranta nan falo suka rankaya suma, ina suka tafi Allah masani.

Bayan kwana uku da faruwar lamarin kullum Mau ke shigowa ta yi musu abinci breakfast lunch da dinner kuwa shike shigowa dashi daga wajen aiki, Maryama dai sai wanka da Sallah da cin abinci shine aikinta,kullum kayanta kala biyu ne kuma Qaseem na ankare da hakan yadda zai sai mata wasu ne har hanzu bai sani ba.

A daren ranar Anty Falmata ta dawar da Sameera dakinta bayan sunyi kulle kullensu, sosai ta hada su ita da Qaseem da bakinshi ya kasa rufuwa dan dadi ta musu nasiha mai kama da fada fada, bata nemi ganin yarinyar ba, dan tasan ita tafi Sameera zafin kishi tsab zata iya hawan yar mutane da duka,..

Koda anty Falmata ta tafi Sameera bata yi wasa da damarta da shawarwarin da aka bata ba, har kasa ta tsungunna ta ce, "honey! plsss forgive me, na yi ne dan kishinka, kuma sai abun da kake so zakayi kishi dama plsss bazan kara ba Insha Allah."

Kamota yayi ya hade ta da jiknsa yana wasa da hannunshi akan bayanta yace, "Na san ba da gangan kika aikata ba, but the way kika dauko wukar nan nima ba da gangan na mareki ba, na yi ne dan ina sonki, kuma bana fatan rabuwa dake, kinsan duk abun da kika aikata da wuka to kema makancin haka za'a aikata miki nima ki yafemin."

Cike da shagwaba ta ce na yafe maka honey" daga haka labarin ya sauya salo don hade bakinshi yayi da nata ya fara bata waai irin hot kiss.daga karshe daukarta ya yi suka shige bedroom nashi.

Washe gari ma lafiya lau suka tashi sai soyayyar da suke sha kamar ba su ba, tuni Qaseem ya manta da hallitar Maryama a gidan breakfast mai rai da lafiya sameera ta hada musu, sannan ta tafi shirya mijin nata dan zuwa office wannan al'adarta ce, yana cikin abun da yasa take kara samun tagomashi wajen Qaseem.

Maryama na zaune bakin gadon dakin da yake mallakinta a yanzu ba tare da tasan zaman me take ba, gaba daya ranta babu dadi tun da tayi asuba take zaune a wajen bata tashi ba,kamar ance ta daga kai taga labulayen dake daure bisa window sun fara wani irin rangaji kamar ganyen bishiya idan iska sun yi yawa, sosai labulayen ke rawa kuma babu alamar ana iska daga waje hasalima windows na dakin a rufe suke rufff,a zabure na mike ina dafe kirjina da hannu biyu,ban kara rudewa ba sai da naga spider da tunda Innarmu ta haifeni ban taba ganin spider mai girman shi ba koda Film ne kuwa,suffarshi na Spider ne, amma girmanshi ya kai kadangare babba, a tsakiyar dakin naga yana yawo gami da fara zagaye ni shiba a kasa ba kuma shi baikai kan ceiling ba kamar dai yadda tsuntsaye ke shawagi a sararin samaniya haka yake zagaya dakin.  

"Innalillahi" kawai nake ambata, a take na ji jinin jikina yana konewa, kafafuna sun min wani irin nauyi tamkar an sanya kaca an daure su, lokaci daya labulayen suka tsaya cibbb kamar an sanya remote an yi pause na su.Kofar dakin ne ya fara jijjiga cikin sakwan daya ya budu fittt wannan spider din ya fice daga dakin, sai a lokacin na samu damar kwalla wani irin kara mai firgitarwa nima na nufi kofar da wani irin speed.


Ina isowa wajen garaff naji na bugu da kofar da wani irin karfin gaske kamar an tura ni ne, take goshi na fa fara zubar da jini sakamakon kofar da ta kullu gam ba tare da na taba ta ba , wani irin duhu ne ya mamaye illahirin dakin ko tafin hannuna bana iya gani. ikin duhun na fara jin taku tap tap tap sawayen mutane a cikin dakin ban ankara ba naji an fara jan rigata da hannaye masu yawa, bugun da na yiwa kaina a jikin kofa da wannan abu dake faruwa yanzu su suka hadu suka haddasa min karewar jinin jikina duk yadda na so karanto addu'a kasawa na yi,take dakin ya fara wani irin jijjiga kamar zai rufta dani cikin kasa, wani irin ihu na kwala mai karfin gaske na fadi kasa sumammiya........