56
💫MARYAMA💫
by
Ummu Fadeela.
56
Ihun da na kwala ya yi daidai da fitowar Qaseem da Sameera tana makale da shi kamar zata sanya shi cikin cikinta, "Subhanallah,mai ya samu yarinyar nan?" ya fada a rikice, duk yadda Sameera ta so dannewa kasawa ta yi dan wani daci ta ji a ranta sakamakon kulawar da ya nuna amma sai ta danne tunawa da shawarar Anty Falmata da ta yi.
"Honey! Ko dai bata da hankali ne dama, i mean ko tana da aljanu ne kai baka sani ba?"
Yana kallonta da kyau ya ce, "ah'ah bishiyar kukan bulukiya ne a kanta". Hmmmm daga tambaya kuma sai cibi ya zama kari, yanzu dai muje ka karya dan kar kayi latti zuwa office"...."
No Sameera,muje muga mai ya sameta tukunna bai kamata ba kinsan ko dabba ka ajiye ya kamata ka ringa lura da shi balle kuma dan mutum".
Wani wawan kallo ta jefa masa babu shiri ya yi tsit da wucewa dining area,serving na shi ta yi lafiyayyen breakfast da ta hada fried chips with ketchup sai farfesun naman kai da tayi warming gami da hot tea da ya sha kayan kamshi da zuma dan Qaseem bai shan madara da sugar, ta tura gabansa. Yana ci tana masa hira mai cike da kwarkwasa.
Amma ko kadan hankalinshi baya kanta,ihun da yarinyar ta yi sau daya bai kuma kara jin motsinta ba shi ya daga mishi hankali.
Wani gwauron numfashi na janyo sakamakon wani abu mai sanyi da na ji ya taba fuskata, a take kwakwalwata ya amshi sakon kana ya rabawa illahirin gangar jikina.
A kan ceiling fan na sauke idanu na, gudu fankar yake fiye da kima tamkar zai balle ceiling din su sauko tare, gashi kuma babu wutar nepa a dakin babu alamarta,, da azabar karfi na rumtse idanuna dan na tabbata yaukam tawa ta kare, wayyo innarmu kizo ki taimakeni.
Fiiit na ji an sure ni an yi sama dani banji alamar bude kofa ba sai karar faduwata da na ji a tsakar palon gidan. Take goshi na ya bugu har ya fara tsiyayar da jini, a zabure Qaseem da Sameera suka taso daga dining area suka nufo ni
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, honey na fada maka yarinyar nan kwankwamai gare ta amma baka yarda ba. Gashi dai ka gane ma idonka yanzu, atake kawai yarinya zata firgita mana gida, akan wane dalili? lallai kayi gaggawar neman mafita, dan bazan yadda ba ina zaman lafiya a daga min hankal..."
Shiru Sameera ta yi bata karasa abun da take da niyyan fada ba sakamakon ganin da tayi Maryama ta mike tana zuwa baya baya jikinta sai kakkarwa yake kamar ana kada mata gangi, a bangaren Maryama kuwa tana kwance a inda a ka sake ta tsananin azabar da nake ji na buguwar da na yi a kasa ya hana ni ko kwakkwaran motsi, cikin kiftawar ido naga bangon palon ya tsage wani katoton buzun damisa ne ya bayyano daga cikin ginin, samanshi wani irin katoton kumurcin maciji ne bakikkirin ya fasa kai, a saman iska wannan buzu mai dauke da maciji yake tafiya yana tunkaro ni,hakan yasa na mike cikin azama na manta ma da azabar da nake ciki baya baya nake tafiya yayinda wannan buzu ke cigaba da bina a slowly, saura bai fi kamar kamu biyu ba a tsakaninmu wannan maciji ya zare tsayinsa gaba daya ya kawo min wani irin mahaukacin sara, rumtse idanu na yi da karfin gaske na ce, "Kalu Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,"daga haka ban kara sanin inda kaina yake ba....
Cike da zafin nama ganin tana kokarin kaiwa kasa Qaseem dake tsaye gefen Sameera suna ganinta da mamakin mai take yi haka, ya yi azamar cafkotabta fada kirjinsa, cije lebe Sameera ta yi da karfi gaske kamar zata huda su ganin Maryama a jikin mijinta..."Maryamaaaaa" Qaseem ya ambata da karfi ganin gaba daya jikinta ya saki wasu hawaye suka biyo kuncinta.
"Na fada maka akwai motsi akan yarinyar nan daga kallonta, kai baka ga yadda take bane zubin aljan..."
"Stop talking this rubbish and get me water Sameera, ke baki ga halin da ta ke a ciki bane? Amma kin tsaya kina shirme kamar dai ba ki da imani".
Juyawa tayi a ranta tana fadin "Honey ke nan, idan ba dan nasan abun da na taka ba kai ka isa ka fada min irin haka akan wata? watar ma dake kwance bisa kirjinka sannan ni sameera ina ganinka? hmmm, you are mistaken".
Murmushi ta yi tana bude fridge gami da dauko bottle wata mai masifar sanyi dan har ya fara kankara ta dawo inda suke kwantar da ita Qaseem ya yi akan center carpet dake palon yana karewa kyakkyawar fuskarta kallo yadda fuskar ta rame cikin lokaci kadan, sannan tashin hankali na kwance karara bisa fuskar, hannu ya daura kan cikakkun girarta da saura kadan su hade da juna ya fara shafawa har zuwa kan dogon hancinta yana mai lumshe idanun shi.
Da hanzari ya dauke hannunshi jin takun Sameera tana isowa wajen. Bata jira ya amshi ruwan ba ta balle marfin bottle din ta saita fuskar Maryama ta fara tsiyaya mata ruwan bisa fuskar tata ba tare da ta damu da yadda yake gangarawa cikin hancinta ba da kuma irin sanyin da ruwan ke dauke dashi ba.
"Shafawa ake sameera, baki ga yana shigar mata hanci ba?, Zaki illatata fa" Qaseem ya fada yana kama bottle dake hannun Sameera da ta gama zazzage shi tas a jikin Maryama. "Honey daga taimako kuma, ina ce kai kace in kawo ruwan?"
"Amma bance ki kawo masu sanyi haka ba ai, kuma bance ki bulbula mata cikin hanci ba," daga haka bai kara cewa komai ba ya ciccibi Maryama da har lokacin ke kwance magashiyyan babu alamar tana da sauran numfashi, bisa kafada ya daura ta gami da nufar kofa gadan gadan yana fadin, "Sameera dauko mayafi ki zo da car keys mu wuce hospital da hanzari".
Wani irin harara ta aunawa bayansu, kirjinta na mata zafi na ganin yadda yarinyar ke samun kusanci da mijin nata a maimakon ya tsaneta ya kuma koreta kamar yadda Anty Falmata ta fada zai faru, car keys din ta dauka da hanzari ta bi bayansu ta samu har Qaseem ya shimfide Maryama bayan motar.
"Ina mayafin naki?" ya tambaya ganin babu mayafi a jikinta.
"No honey, kuje kawai ina da abubuwan da zan karasa,".
Bai ce komai ba ya amshi keys din hadi da tada motar a ranshi yana jinjina lamarin Sameera, shi kwata kwata bai dauka zata nutsu haka ba lokacin da ta ji labarin nan sanin halinta da yai, shiyasa bazai daina godewa Anty Falmata a ranshi ba na irin yadda ta saita mishi Sameerarshi.
Sai da Sameera ta tabbatar da sun bar gidan sannan ta koma ciki da dan gudu gudu ta fada saman kujera tana jin wani irin farin ciki a ranta.
wayarta ta dauko ta lalubo layin Falmata bugu daya kuwa ta dauka, wani irin dariya Sameera ta fashe dashi Falmata na taya ta,zuwa can ta tsagaita da dariya kana ya ce, "Allah ya bar minke anty na maganin kukana, komai ya kankama yadda kika fada ko ince fiyema da yadda kika fada, komai ya rikice mata ina ganin nan da kwana biyu kam a bola za'a tsince ta, dariya falmata ta kara kecewa da shi ta ce, "shegiya gobe idan taga mijin wata da gudu zata barshi,a tare suka kara kecewa da dariya sannan suka tsagaita anty falmata ta ce.......