MARYAMA

57

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

57


Dariya sukayi mai dan tsayi kafun su dakata anty Falmata ta ce, "Yanzu saura next step,don haka ki maida hankali da kyau kiyi abun da aka fada miki, kina gahimtata ai ko?"

"Yes anty, yanzu ja da bakin zan hada waje daya ko?"sameera ta tambaya.

"Yauwa yar gari dadina dake kenan kanki yana kawo wuta, maza je ki hada ki jijjiga da kyau yadda zasu hade da juna, idan an dace ma ya yadda shegiyar a hanya, ba kince sun fita ba?".

"Sun fita, kinsan suma ta dinga yi tana farfadowa shine ya wuce da ita asibiti"..Dariya anty falmata ta kuma kecewa da shi ta ce, "Ai na fada miki,yadda ta shigo miki gida a firgice,haka zata bar gidan a firgice".

"Wllh Anty tun ba'aje ko ina bama ta gama firgicewa, ai ko nawa na ba mutumin nan na kan tsauni ban biyashi ba ba don shi ba, da yanzu nice a firgice, in ba'ayi sa'a bama tuni zuciyata ta buga na mutu". 

"Subhanallah, ke Sameera me ya sa bakin ki ba shi da dadi ne watarana? wani irin zuciyarki ta buga kuma, a'a gaskiya banason irin maganar nan, idan kin mutu nida Hajja kika bari da shiga uku ai, mutuwa ba hanzu ba, sai munga yayanmu ni da ke tukunna, (hmmm).

"Allah ya sa anty, yanzu dai bari inje in hadesu da wuri". "Yi maza to, ba'a bori da sanyin jiki. ki tabbatar kin jijjigesu gaba daya" cewar Falmata dake hakimce tsakiyar falonta gefe da ita tire ne mai dauke da grapes mai sanyin gaske sai raba yake yi da apples da kuma yankakkun water melon cikin wani dan bowl tana ci tana yiwa kanwartata bayani.

Da sauri Sameera ta shige dakinta. Sai da ta tabbatar da ta rufe kofar da makulli sannan ta karasa gaban gadonta, katifar ta daga ta fitar da wani dan karamin kwarya marar kyan gani duk bayanshi layu ne kanana kanana a mammakale sai wasu kwalabe suma yan kanana kusan guda takwas cikinsu da wasu abu kala kala kama daga baki, ja, purple,blue,da sauran kaloli,bakin kwalbar ta dauka gami da budewa kana ta dau ja ta bude hadi da juyewa cikin bakin ta fara jijjigawa saida ta tabbatar sun hade jikinsu sannan ta mayar ta rufe ta tura kwaryar kasan gado ta tashi tana gyara gaban rigarta babu alamar imani ko kadan a fuskarta ta ce, "Mijina nawa ne ni kadai ni nasha wahala dashi tun bashi da ko sisi nake hakuri har ya zama wani abu yayi kyan gani ya mallaki abun duniya sannan rana tsaka ki ganshi ki ce zaki aure min abu na kar ya kike yarinya,kamar yadda ban haihu da Qaseem ba, haka babu wacce ta isa ta shigo gidan nan da sunan aure balle ta haifar masa magaji in tashi a tutar babu, daga haka tabar dakin tana hura hanci.

Da gaggawa aka amshi Maryama lokacin da suka iso asibitin, bisa wani gado aka daurata hadi da turata da gudu gudu har accident and emergency dake asibitin, likitoti kusan uku ne suka rufu akanta da fara bata taimakaon gaggawa kasancewar asibitin kudi ne basa wasa da patients nasu, cikin sa'a sukayi nasarar janyo numfashinta da kyar tsawon mintuna arba'in suna akanta, Qaseem sai sakatariyarsa ya kira ya bada excuse din ba zai samu zuwa aiki ba iyalinshi babu lafiya suna asibiti.

Lokacin da aka fito da Maryama kwance bisa gadon marasa lafiya aka wuce da ita ward da za'a bata gado, cike da mamaki Qaseem ya bita da kallo kwance take kamar babu rai tattare da ita, ga wani irin rama da tayi ta kara yin haske fayau kamar babu jini a jikinta,ko lokacinda ya dawo da ita daga Dubai ba tayi irin lalacewar da tayi yanzu ba.

Karin ruwa aka mata hadi da dura allurar bacci cikin ruwan dan kwakwalwarta ya huta daga aikin da yake yi fiye da kima, har wajen azahar Maryama tana bacci Qaseem yana zaune gefenta kamar bodyguard. mamakinsa yadda akayi yau ko sau daya Sameera bata kirashi ba har warhaka.

"Help! help!! help!!!" shi ne kawai abun da Maryama ke fada da wani irin karfi, daidai lokacin kuma mafarki take yi wasu zakuna manya manya suna binta a cikin wani kasurgumin jeji gudu take gaba da baya jeji ne bakikkirin, wani mutum ta hango yana tafiya a hankali sanye da wani katon sweater mai hula irin mai gargasa dinnan wanda ya rufe mishi har fuska hakan yasa bata iya hango fuskarshi daga nesa take kiran Help, help, help, wanda ba iya cikin baccin ba har Qaseem dake zaune bisa kujerar dake bakin gadon yana zabura hade da mikewa.

A duniyar mafarki kuwa, juyowa masked man din ya yi ya daga gun dake hannunshi ya harbe wadannan zakuna guda biyu dake bin Maryama, take a wajen suka mutu, murmushinsa mai kyau ya mata yana nuna mata zakunan dake kwance kasa yana murmushi har hakwaranshi na bayyana, zaro ido ta yi tana dafe kirji tace, "Ham....! 

Kafin ta karasa taga ya fara bacewa ganinta a hankali yana daga mata hannu, "No, no plsss don't let go, kar ka barni dan Allah, karka tafi ka barni zasu tashi su cinye ni zasu cinye ni ka taimakan...." Battt ya bacewa ganina yana ta jefo min murmushinsa da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwa, "Hamma jayyyyyyy". Na kwala ihun kiran sunanshi da karfin da ya karade illahirin jejin, a rikice na farka ina tashi zaune da fara rarraba idanu a dakin,,caraf idanu na suka sauka cikin na Qaseem da ya rankwafo dai dai kaina.

"Ka ce mishi ya dawo in bashi hakuri dan Allah, kace ya fada min inda suke da su Innarmu! na fada ina fashewa da kuka mai tsanani.

Qaseem a ranshi zuwa yanzu ya fara yadda da maganar Sameera na cewa kan yarinyar nan akwai motsi, tabbas tana da damuwa basu sani ba,.

Shigowar doctor ne ya katse mishi zancen zucin da yake yi.

"Masha Allah, patient nawa ta farka, hope komai lafiya?" cewar dr yana duban Maryama da har lokacin bata gama dawowa cikin hayyacinta ba na mafarkin da ta yi amma take ganin abun kamar a gaske. 

Qaseem ne ya yi murmushin yake ganin bata da alamar responding yace, "Alhamdulillah, komai normal a zahiri kam bansan dai internally ba.Dube dube likitan yayi mata kana ya ce

"Komai normal za'a iya baku sallama ma idan kuna so,but ku kiyaye da bacin ranta dan jininta yana barazanar hawa, and kamar yadda kake gani tayi kankanta a sameta da hawan jini, so a ringa kiyaye likes and dislikes nata, paper ya ciro ya yi rubuce rubuce ya mikawa Qaseem da fadin 

"Ku nemi wannan a pharmacy, ku biya bill a reception". 

Hannu ya mikawa likitan suka yi musabaha gami da fadin.

 
"Thank you so much dacta, Insha Allah za'a kiyaye da duk abun da kace, yanzu ma akasi aka samu," daga haka ya fita dan siyan magani da kuma biyan kudin asibitin,saida ya gama komai ya dawo dakin rike da fancy leda da aka zuba mishi maganin a ciki,."Ta so mu tafi gida" ya fada ba tare da ya kalleta ba.

"Babu alamar zata motsa daga wajen, sai ma kukan da ta kara saki tana fadin, "Ka kaini wajen Innarmu dan Allah, kace da Hamma Jay ya yi hakuri ya zo ya dauke ni daga nan, idan na koma gidanku kashe ni zasu yi, kashe ni zasuyi tun ban ga Inna baffa da hamma jay ba." 

Sosai yanayin yadda take maganar yake bashi tausayi, bama shi kadai ba, duk wadda yaga Maryama a lokacin dole ta bashi tausayi, amma bai san mai yasa ba, duk sadda ta kira wannan hamma jay din wani irin tukuki yake ji a zuciyarshi har daci yake ji yana biyowa ta makwogoronshi.

Hannu ya daga mata da sauri yana murtuke fuska da kakkausar murya ya ce. 

"Ta shi mu tafi malama ko inyi wucewata"...

Har cikin ranta da zai wuce ya barta sai ta fi kowa farin ciki akan irin ukubar da ta ke fama dashi a gidansa, ga shi har yanzu bai nemo mata iyayenta ba kamar yadda ya mata alkawari....


(har yanzu Maryama bata san cewa an daura mata aure da Qaseem ba). So duk wani tataburza da ake yi ita bata sani ba.

"Dan Allah k...." will you get up ko sai na babbalaki na watsar a bola," ya katse mata abun da ta fara fada a hasale da sauri ta diro daga gadon jin yana kokarin kashe mata kunne.

Gaba yayi ta fara binshi a baya a hankali kamar mai tambayar kasa ga wani irin juwa dake diban ta tamkar zata kifa da kasa.

A haka har suka kawo bakin motarsa ya bude mata front seat, gami da kwantar da seat din, da ido ya ce mata, 

"shiga ki kwanta" batayi gardama ba, dan yadda take jin kanta kamar zai tarwatse dinnan bata son hayaniya ko kadan,kwanciya ta yi lamo bisa kujerar shikuma ya zaga driver seat ya shiga hadi da bawa motar wuta suka bar hospital din.

Da gudu Sameera ta zo gaban window gami da yaye curtains tana lekensu jin dirin motar Qaseem da karar rufe get.

Dafe kirji tayi gami da zaro idanu waje, "Na shiga uku ni Sameera, Allah ka dube ni da wannan bakar kaddarar, sake dawowa ta yi, kodai maganin baiyi aiki bane?" ta tambayi kanta.

"Have patient mana hajiya, yaushe ma kika hada, ki basu lokaci kadan," zuciyarta ta bata amsa, ina sakin labulen suna shigowa,banda kyarma babu abun da jikin maryama ke yi sai zare idanu take.

Side hug Sameera ta je ta ba Qaseem hadi da kankance murya ta ce, "Welcome back honey, yanzu na ke shirin zuwa in duba ku jin shirun yayi yawa ashe kuna hanya."

"An yi admitting na mu ne shiyasa amma jikin nata da sauki ma ta samu karin drip".

"Ohhh masha Allah, yanzu muje kayi wanka dan gaba daya warin asibiti kake yi, daga haka bata bashi damar fadin komai ba ta ja shi ba tare da ta ga sashen da Maryama ke tsaye ba suka wuce dakinshi, kamar rakumi da akala haka Qaseem ke binta, duk da yaso yiwa Maryama magana ta wuce dakinta ta huta amma sai ya samu kanshi da kasa yiwa Sameera musu.

Da kyar na iya jan sagaggun kafafuna da nake jin suna barazanar gaza daukar nauyi na na karasa tsakiyar palon na rakube gefen kujera ina kankame jikina waje daya kana idanu na suna kallon kasa kamar kace kyat in gudu tsabar yadda na ke tsorace ba bu abin da nake bukata yanzu sama da kwanciya dan wani irin juwa ke daukata daga zaune amma ko da kuskure bazan yi gigin shiga dakin da nake kwana ba, dan ni kadai nasan azabar da nasha a yau din.

Sameera koda suka shiga dakin ma bata barshi ba sai da tayi dabarar dauke mishi hankali har na wani lokaci kafun su shiga wankan a tare,...Tana zaune bisa stool na mirror daure da towel saman kirjinta, shikuwa yana tsaye bayanta rike da handryer yana busar mata gashin kanta, dan muskutawa ta yi gami da yin fari da idanu suna kallon juna ta cikin mirror ta ce, "Honey,zuwa yanzu ya kamata ka hadamu da kanwata ai mu san juna sosai, and ya kamata mu raba girki, ko ya ka gani?"..

"Ba ni son maganar nan sameera. Ke kadaice matata, wannan tsautsayi ne ya shigo da ita rayuwarmu kuma dan lokaci kadan nake jira zan yakiceta daga cikinmu.

Babban damuwata inda zata shiga da tuntuni ta bar gidan nan, na fi son in samo mata danginta koda mutum daya ne".

Wani irin dadi ne ya mamaye zuciyar Sameera ganin tarkonta ya kama tsuntsu,kara muskutawa tayi tace

"To shi ke nan tunda kace haka, dama ni ganina kar a shiga hakkinta ne shisa a matsayinta na matarka itama, amma tunda kace haka dama ina shirin sallamar su Ma'u sai ita ta karbe su a aikace aikacen da suke taimakamin da,ko ya kagani?".

Ta karisa tana daga mishi gira sama.

"Duk yadda kika yi daidai ne madam" ya samu kanshi da fada ba tare da ya shiryawa hakan ba.

Kayataccen murmushi ta saki tana mikewa da rungumar shi.

"Thank you haney" ta fada da bashi wani kyakkayawar sumba a kan lip nashi ta ce ka kwanta ka huta honey, nasan yau ka wahala da yawa let me dressed up sai in sanar da amarya ta hada maka lunch, ya kamata ta fara koyan aiki tun yanzu" 

"Kin san bana iya cin abincin kowa idan ba naki ba sameera, so ke ki girka min kawai ko da abu mai dan sauki ne,nan da karfe hudu zan dan fita ya kamata in leka office dinnan akwai abu mai muhimmanci daya kamata inyi a can "cewar Qaseem har cikin ranshi yana tausayin yarinyar yasan sameera kuwa farar sani yanzu idan ta sanyata gaba Allah ne kawai zai kwace ta.

Sameera bata ce komai ba ta sa kai ta fice daga dakin, sai da ta kimtsa ciki wasu kayan a dakinta sannan ta dawo palo tana ta baza kamshi da nufin shiga dakin Maryama.

Turus ta yi ganin ta kwance a tsakar dakin gyangyadi yana daukarta, kafarta ta sanya gami da ture kan Maryama da karfin gaske tana fadin "ke tashi,".

A zabure na mike jikina yana kyarma na fara ja baya baya,strictly sameera ta ce, "Tsaya daga nan kuma ki nutsu da kyau kiji abun da zan sanar dake, tunda har kika samu zarafin aure min miji to ya zama dole ki fara aiki irin na borar matar gida. Yess ke bora ce kuma dole ki zama baiwa ta.

Daga yau za sallami masu aikina, ke kuma zaki maye gurbinsu,dan haka ki nutsu da kyau kiji aiyukanki a gidan even by mistake kika tsallake ke guda ranar sai kin gwammaci ba'a haifeki ba.

Girki sau uku, sharar gaba daya dakunan dake gidan nan.
mopping, wanke wanke sharar compound da bawa flowers ruwa, wankin motocin honey da tawa, sannan wankin kayan sawarmu kuma da hannu zaki wanke bada washing machine ba and daga yau zaki fara kuma kullum ne zaki gabatar dasu ba tare da tsallake ko wani aiki ba. tana kallon agogon dake daure tsintsiyar hannunta tace, "lokacin ki ya shiga daga yanzu zaki fara, mijinki yana bukatar abinci marar nauyi, ga can kitchen make sure kin min aiki mai kyau inba haka ba jiki magayi" daga haka ta finciki hannuna ta fara jana zuwa kitchen din.

Tabbas in ba don ta jani ba ko dan yatsa na bazan iya ja daga wajen da nake ba babu shakka suma nayi a tsaye sakamakon dukan kirjina da maganarta ya yi.

Wai na aure mata miji, da kuma mijina yana bukatar abinci, is this for real, Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, maganar wannan tsohon ce ta dawo min a raina ranar da zamu dawo daga yola, 

"Maryama kin amince da zabin da nai miki? kinsan bazan zaba miki abun da zai cutar dake ba? to ki mishi biyayya har Allah ya sa iyayenki su bayyana Allah yayiwa rayuwar ku Albarka".

Wani irin kuka ne ya kufce min babu shiri na saki kukan har da gunsheka,a fusace Sameera ta juyo tana zare min idanu hadi da daura dan yatsarta bisa lebenta "Shhhhttt" ta fada tana zare idanun sosai.

Babu shiri na gumtse baki na ganin idanunta sun koma min wani kala rawar da jikina ke yi ne ya tsananta abubuwan bukata ta fitar kamar su irish nama kwai dafaffiya da kayan miya sai spices, "Just for today zan taimake ki in girka a gabanki dan kar kimin shirme nasan a gida ba'a saba girki akan gas ba,"na tsinkayi muryarta.

Cikin minti talatin ta gama hada jollof na irish potatoes da yasha kwai da nama sai kamshi yake yi,duka ta daura bisa babban tray da plate and spoon sai serving spoon da cup bottle water da juice duka ta bani in kai dining area, da sauri na kamar dan dama tsaye nake kamar statue a wurin, numfashi ne kawai ya bambanta ni da gawa, ina fita sameera ta kwashe da wani irin dariya har da rike ciki kafun ta daidaita nutsuwarta ta fita itama.

Bayan kujera na koma na kuma rakubewa dan wani irin sarawa kaina ke yi ga yunwa dake dawainiya dani ga tsamin jiki amma bazan iya shiga dakina ba ko da wasa.

Ina zaune a wajen Qaseem ya fito tsabar yadda zuciyata ta bada wani sauti saida hawaye ya zuba min a idanuna, aure min miji, mijinki na bukatar abinci,zabin da nai miki.wadannan maganganun ne ke yawo a kwanyata, "iam sorry hamma jayyy iam sorry, sorry plssss bazan sake ba". 

Na fada wani marayan kuka yana kwace min, Qaseem da bai kula da ita ba direct dining area ya wuce yana gyara wuyar rigarshi car keys ya ajiye da wayrshi a gefe guda sannan ya janyo plate da serving spoon ya daga cup gami da tsiyaya ruwa mai sanyi sannan ya bude food warmer din, a haukace ya mike saura kadan ya fadi amma yayi nasarar rike bayan kujera wurgi yayi da marfin dake hannunshi yayinda ruwan da ya zuba a glass cup ya watse a wajen cup din ta tarwatse "SAMEERRRAAA!" ya fada da kardin gaske kamar wuyarshi zai balle.

A zabure na mike daga bayan kujerar sai dai na rasa inda zanbi dan in gudu,sameera dake makale a balcony tana jiran tarwatsewan bomb din ta fito a rikice, "what happen honey,gaba daya ka tsoratani". "yana nuna mata saman dining yace "me wannan? me wannan nace?"

Rumtse idanu tayi itama bayan ta leka da sauri ta dawo baya subhanallah honey me wannan din haka?" 

"Baki da hankali ne ina tambayarki kina tambayata?" 

"To ai bansani bane dan amarya ce ta yi girkin".

"Maryamaaaaa" 

Ya juya akalan kiran zuwa kaina gaba daya ya rikice, cikin rawar jiki na karaso wajen.

"Me wannan kika girka min?" ban ji mai yake fada ba tun bayan kiran da ya min, ina dai ganin bakinshi yana motsi amma bana jin komai, da ido kawai nake binshi kamar ma son karantar wani abu daga bakin nashi...."are you daft? Ina magana kina kallona kamar mayya?" .

Tabbas banji abun da yake fada ba naga dai ya tunkaro ni kamar zaki banyi aune ba naji saukar lafiyayyen mari saman fuskata kan in dawo hayyacina ya kuma kifa min wata yaja hannuna har gaban tebur din,..

"Zauna ki cinye abun da kika dafa" still banji abun da ya fada ba amma tuni cikina ya hautsine sakamakon manya manya tsutsotsi da nayi arba dasu suna ta yarindo cikin kwanon maimakon lafiyayyen abinci da samera ta kwashe a ciki.

Da gudu na wuce kan sink dake dining area din na fara kwarara amai tamkar zan amayar da yan hanjina tun ina aman ruwa yana fita har ya zama babu abunda ke fita sai kakari kawai.

Lokacin da na juyo baya wajen sai samera dake tsaye ta rike kugu tana min kallon sama da kasa,hannu ta tafa tace tana nuna ni da yatsa, wannan shine illar auren mijin wata,ga mamakina tsaff na ji abun da ta fada ba kamar lokavin da shi yake magana ba.Daga haka itama ta bar wajen, da kyar na yunkura zan mike sai dai abun da na gani karkashin dining table din ya sani kwalla kara da karfin gaske, wani katon muzuru ne bakakkirin idanunshi kuma jajawur kamar wuta yayinda bakinshi ke tsiyayar da jini, ihun da na kwallah yasa wannan muzurun huro wani abu daga idanunshi take wajen ya fara kamawa da wuta.

Da wani irin mugun karfi na mike wanda bansan ina dashi ba na fara gudu, kamar an bude min kofar palo na ga kofar ya wangale kanshi fitttt na fice daga palon ina ci gaba da zuba gudu irin na famfalaki, cikin sa'a na samu get ma a bude kamar ni ake jira dama dan haka na sa kai na cigaba da gudu, dariya sosai Sameera ke yi ta ce, Allah raka taki gona, sai abi wani sarkin kuma.

Gudu na ke yi sosai akan hanyar ba tare da nasan inda kaina yake ba,horn yake ta dannawa amma ina yanayin yadda take gudun yasa bata jiyoshi gashi tana tsakar hanya a kokarin da ya ke na kauce mata mistakenly ya.....