CHAPTER 16
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA SHA SHIDA
Ta ɗauki wajen minti guda tana kallonta, zuciyarta na ta raya mata abubuwa da dama. A zahiri ta ce,
“Koma waye ya turo saƙon nan, gaskiya ce zalla yake faɗa min. Sai yanzu na fahimci cewa da biyu Sufyan ya yi mini hakan. A tunaninsa zan kasa komai in ci gaba da rayuwa cikin baƙin ciki.”
Ta girgiza kai tana cewa, “Aa, yau sai na nuna masa cewa zan iya fuskantar rayuwa a duk yadda ta zo min. Na sanya a zuciya, ko da za a yi mini dariya fiye da wacce ake yi mini a baya, ko da zan zama abar kwatance fiye da yadda ake kwatanta ni a raina, ni zan so kaina.”
Ta ƙarasa maganar tana sakar wa kanta murmushi gaban madubin.
Kafin ta ƙara faɗin, “Zan gwada.”
Ƙara daidaita nikaf ɗin ta yi, ta ɗauki jakarta ta fice.
⸻
Zaune suke a class, kowa sun kafa dabarsu, ana ta hira, domin lokacin shigar Farida ajin har ya wuce wajen minti ashirin.
Sufyan ne yake ta zuba yana dariya.
“Ai ina faɗa maka, da ƙyar zata iya dawowa School ɗin nan. Kai, kaga yadda ta koma ne? Kai, wannan fa ko da a namiji ta fito, zai yi wuya wata mace ta amince da ita.”
Habib ya miƙa masa hannu, suka tafa suna dariya.
“Lallai Sufy, na lura kai ka fi ni mugunta ma fa, I swear, ka san hannunka.”
“An faɗa maka ni wasa ne? Ai kaga, ko ba komai, na raba kaina da alaƙaƙai. Tana zuwa School ɗin nan ta ci gaba da janyo mini raini.”
Ya ƙarasa maganar yana dariya, daga kan da zai daidai lokacin da Farida ta shiga class ɗin.
Sake baki ya yi yana kallonta. Habib ya ce,
“Sufy, gata fa kamar an jefota.”
Sufyan sa hannunsa yana murza idanuwansa, ganin tabbacin Farida ce ya ce,
“Ita ce wallahi. Na ji mamaki ba.”
Gyaran murya Farida ta yi ta ce,
“Exams ya zo, ba time test za mu yi yanzu, don haka I have to re-arrange some of you, musamman masu dumama bencin nan.”
Magiyar ɗaliban suka fara yi mata kan ba su shirya ba, ta bari zuwa next week. Fir Farida ta ƙi amincewa.
Ta je board ta rubuta test, sannan ta juyo ta ƙara yi musu gyaran murya. Sufyan ta fara nunawa da yatsa tana,
“Hee, fito please.”
Kallon Habib ya tsaya yi, sai da ta ƙara yi masa magana tukunna ya tashi ya je ya tsaya gabanta.
Seat ɗin farko ta nuna masa kan cewa ya zauna.
Ya tsaya kallonta yana zare mata ido. Wani gajeren murmushi ta yi daga jikin nikaf ɗinta, wanda sai da sautin ya fito fili, ta ce,
“Ba za ka iya zaman ba ne?”
Tsaki ya yi ya zauna a fusace.
Ta kalle shi ta girgiza kai.
Har a lokacin idanunta na kan Sufyan, domin a iya saninta babu mara gane karatu kuma koma baya kaf danginsu irinsa. Tun yana secondary school, ban da safgar yan mata da ball, babu inda ya fi kwarewa. Don haka ma yasa ba ta yi mamaki ba da ya gagara rubuta komai, amma sai dai abin tuhumar shine, ya aka yi yake iya wuce jarabawa cikin sauri?
Abin da zuciyarta ke ayyana mata kenan. Ta girgiza kai tana duba lokaci. Ganin lokacin da ta ba su ya yi ne yasa ta dakatar da su, ta sa aka fara submitting.
Cikin kwalisa ko gezo haka Sufyan ya yi submitting paper ɗinsa shi ma, ta karɓa ta fice kawai.
Tana fita, Habib ya koma inda Sufyan yake yana faɗin,
“Kai Sufy, ni na zata fa wani abu ta shirya ma. Wallahi har na tsorata fa.”
Sufyan ya ce, “Umm, nima na zata akwai abun da zata yi ne, sai kuma naga ba ta yi komai ba. Amma duk da haka fa na san akwai abun da take shiryawa. Don ban yi zaton zata iya fitowa ba,Muje mu je mu dan wataya mana, na gaji da zaman nan.”
Ya faɗa yana tashi.
Duk da cewa ɗalibai nata kallon Farida, wasu ma har nunata suke, a ganta kau da kanta ta yi ta ci gaba da harkokinta kamar ba ta san suna yi ba. Ko da wani abu ya zo ranta, ƙoƙarin dannesa ta dunga yi, ta ci gaba da harkokinta.
Can yamma Sun rabu da Hod kenan, ta kammala tana ƙoƙarin tafiya gida. Ta zo daidai wajen motarta, ta buɗe kenan ta ji an riƙe ƙofar.
Daga kan da za ta yi ta ga Suhail ne da muƙarrabansa.
Wani irin faɗuwar gaba ta ji, zuciyarta na bugawa da sauri. Ya kalleta sama da ƙasa kafin ya ce,
“Ai na zata kin bar makarantar ne, ashe kina nan? Kodayake ma ai har na sa a bincika min inda kike. Kin gane ba wani abu bane, na san cewa ke yar hannu ce, kamar yadda su sauran suke eyy da ke. Ai kin gane ya kamata nima in ɗan gwada ko? Kar ki damu fa, in ma kuɗi ne zan ba ki.”
Rufe idanuwanta ta yi, tsigar jikinta na tashi, a ranta tana faɗin,
“Allah, Ka tsare ni daga sharrin duk wani mai sharri.”
Suhail ya ce,
“Yane wai? Ina zamu haɗu ne?”
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin ɗaga mata nikaf.
Cikin ƙarfin zuciya Farida ta bige hannunsa, sannan ta ce,
“Ni ba irin wacce kake tunani ba ce. Ba abin da zan ba ka, kuma ina jaddada maka da cewa kar ka ƙara kuskura ka sa mini kazamin hannunka a jiki.”
Daidai lokacin da Sufyan da Habib suka fito kenan, idon Habib ne ya fara sauka kan Farida da Suhail ya taɓa Sufyan yana,
“Kai Sufy, ni fa bana ganewa. Suhail ne fa da Farida, ka san dai halinsa, kuma matar ka ce fa. Ya kamata ka dakatar da ita kuma a hukuntata. In suna tare fa, zaka ga yanayinsa, yana ta sakin fuska, mutumin da ko murmushi ma ba yi yake ba.”
Sufyan ya ɗaga kai yana kallonsu kafin ya kalli Habib ya ce,
“Kamar ya a hukuntata? Ni fa da nake tawa sharholiyar?”
Habib ya ce, “Kai namiji ne ai, ita kuma mace ce fa, kuma matar ka.”
“Don ni namiji ne sai Allah ba zai hukuntani ba ko me? Dukkanmu, daga ni har ita, babu wanda Allah zai bari wajen hukunci. Ni fa ba ruwana da zancen cewa namiji ya yi komai ado ne, ban da mace. Wannan duk zance ne. Shi Allah ba ruwansa, musamman tunda dai ni ba shiga sabgarta nake ta wannan fannin ba, to kawai kowa ya more rayuwarsa. Bar mu dai da gumurzon cakwakiyar da muke, amma ni ba ruwana da rayuwarta. Cikin da ke jikinta ne kawai na ce ta zubar, don ba zan karɓi ɗan wani garde ba.”
Habib ya buɗe baki.
“Ciki? Ciki fa Sufy, ka bari har haka?”
Sufyan ya ce, “E, to ina ruwana? Ni fa, indai zan yi rayuwata yadda nake so, to abar kowa ma ya yi kawai dai ba zan bari ta taka ni bane ta min in mata.”
Habib ya girgiza kai, “Lallai ka ce ita ma jar wuya ce sosai, kuma abin bai dame ka ba ko? Ko a ji ƙinka.”
“Ah, to akan me zan damu? Rayuwarta ce fa, kuma ka sani sarai ni ba so, bare ƙaunarta nake ba.”
Ya ƙarasa maganar suna shigewa mota.
Suhail ya yi wata dariyar mugunta yana cewa, “Ni fa na san irinku, kuma wallahi kin ji, na rantse sai na aikata abin da nayi niyya da ke, ko kina so ko ba kya so. Mu zuba mu gani.”
Shigewa motar Farida ta yi, ta ja murfin. Ɗaya daga cikin yaran Suhail ya yi yunƙurin shiga kenan, Suhail ya dakatar da shi.
“Noo, kar ka damu, barta. Please, zata shigo hannu.” Ya faɗa yana cizon yatsa.
Suna cikin mota, Habib na ta girgiza kai ya ce, “Kuma haka za ka ci gaba da zama da ita, Sufy? Ba ka jin kishi ne wai? To, ka ƙara aure mana kawai.”
Sufyan ya yi murmushi yana driving ya ce, “Ina da kishi mana, amma ba akanta ba. Yanzu fa, inda ace nine kaɗai nake irin wannan rayuwar, aka sani a gida, ko da za a nuna baƙin rai, ƙarshe cewa za ayi ta yi haƙuri ta ci gaba da zama da ni. To, me yasa su mata, in aka same su da kuskure sai ace namiji ya rabu da su kawai?”
Habib ya ce, “Saboda bai dace ba ai, akan me? Wallahi, inda ni ke da Farida, ba ta isa ta dunga irin wannan rayuwar ba ina kallo. Ni daban ai, ita daban.”
Sufyan ya yi tsaki.
“Ni fa duk abuna, ban da wannan bagidajen tunanin irin naku ba. In yanzu nace zan auri wata, ina da tabbaci a kanta ne?”
“Koma ya ne fa, ni ba zan bari ba. Na faɗa ma, ni daban, ita mace daban. Kai dai don dama ba ka ra’ayin auren ne.”
Sufyan ya ce, “Tsaya, wai duk zancen nan akwai inda a Qur’ani aka sanar da cewa iskanci wajen namiji ado ne? In akwai, faɗa min.”
Habib ya yi dariya.
“Kureni za ka yi kenan? To, ni dai ban da wannan amsar.”
Dariya suka yi duka, suka ci gaba da tafiya.
Farida na isa gida ta tarar da Inno tsaye a ƙofar gidan,hannunta dauke da kwanon Samira tana ta zabga mita.
“Yoo, wai ace yarinya na ɗauke da ciki, ba za ta tsugunna waje guda ba sai ta yawo a titi.”
Farida ta fito daga motar tana, “Barka da yamma, Inno.”
Harara Inno ta bita da shi tana, “Na bi yammar da barkar a fusace. Ni ban san wacce irin rayuwa kuka ɗaukar wa kanku ba, yaran zamanin yanzu! Ba za a zauna a ɗaki a reni ciki ba, sai dai a titi. Daga nan tun yaro na ciki, idanuwansa su buɗe kafin ya zo duniya. Ki ga jarirai kamar tsofi.”
Ta ƙarasa maganar tana karewa Farida kallo.
“Ke wai ya haka ne? Kullum jiya iyau, ciki kusan wata huɗu yanzu, amma bana ganin canji? A yadda tumbinki yake tun da fa har yanzu haka yake. Ah, ba zai sabu ba. Shigo mu je, ki buɗe mini in duba.”
Ta ƙarasa maganar tana jan hannun Farida.
Shiga ciki suka yi. Inno ta ajiye kwanon samirar tana,
“Dama ɗan dabge na kawo miki. Matso nan, cire hijab ɗinki, buɗe mini cikin nan, ban gane ba.”
Farida na fara ƙoƙarin cire hijabin, kafin ta ƙarasa Inno ta kai hannunta kan rigarta tana ɗagawa…