BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 1

by @maidambu41

BAƘIN ALƘALAMI..... 

{Mai Rubuta Ƙaddara}


Chapter 1 


Warning ⚠️ 


(Ban yarda wani ko wata su juya mini labari ko sakawa a wani kafar sadaukar ba! Idan haka ya faru akwai mummunar mataki da za a ɗauka.)


©️ Ramlat Abdulrahman Manga 

Mai_Dambu

2024/2025


TikTok:Marubuciya Mai_Dambu

Telegram:Rammy 

WhatsApp:Mai_Dambu 

Facebook:Ramlat Abdülrahman Manga

Handle din na social media kenan😻




*Bismillahi rahamanin Rahim


2018


*Shimfida*

Numfashinta ne ya kusan ɗauke wa sakamakon jin sautin muryar Ummu-Sulaim da take sak da sak da muryan Ya Adam. Wani irin abu ta ji a jikinta wanda ya tilasta mata fara rawa zuciyarta tana wani irin bugawa  da ƙarfi take ta ji duk wani tsoro ya kamata. 

Sulalewa ta yi daga cikin jama'an da suka cika gidan domin taya su murnar sauƙar Alqur'ani mai girma da yarinyar su take yi.


   Dusu-dusu take gani a gabanta, da ƙyar ta yi nasarar samun shiga cikin gidan ta ƙofar baya wanda ba mutane sosai, ta wuce can ɓangaren mai gidan ta samu wani wuri ta zauna a hankali. 

Zare medical glass ɗin idanunta ta yi tana me share ƙwallar da take zuba mata. 

  Shekaru goma sha takwas masu muhimmanci!

Shekaru goma sha takwas masu daraja!

Shekaru goma sha takwas na kuka! 

A hankali ta ji wani irin kuka yana zuwa mata, a yau madadin miyagun mafarkai da ta saba yi, yau ta wayi gari da farin ciki. 

Madadin tsoron da ke bijiro mata ta tashi da wani irin yanayi da ta tsinci kanta da shi. A shekarar da ba zata taɓa manta wa da shi ba a rayuwarta.


*Shiru wani yare ne mai girma*

*Shiru tarbiyyar Africa ce*

*Shiru wata duniya ce da ba a son furta kalma*

*Shiru na ɗauke da wa'azi mai zaman kansa*

*Shiru wani al'amari ne da ke nuna cika ta mizanin hankali.*

  *Ki gani, ki ƙi gani.*

*Ki ji, ki ƙi ji*

*Idan yana abu ba ruwanki.*

*Kada ki zama mai tuno sirrin miji.*

    _Ki zauna a ɗakin Mijinki shi ne rufin asirinki_

_Rayuwar mace a cikin nahiyar Afrika. An riga da anyi Manipulation ɗin Mata da cewa Namiji yana da right na yin abin da ya so, an riga da an nuna mana shi namiji duk abinda ya yi ba kome bane face  Ado a gare shi. Namiji zai yi komai amma ba za a gani ba, asali ma cewa za'a yi ai idan aka aurar da shi mace zata sauya shi! Ta ya za ayi mutumin da ya zama wani addiction akan wani abu ace suddenly mace za ta iya sauya halinsa? Taya za ayi a ce wanda bai ji maganar iyayensa ba, kawai sai ace akwai  wata 'yar yarinya za ta sauya shi?

Kun san sharrin zamanin da muke ciki kuwa? Abubuwan da yawa, wai mutuwa ta shiga kasuwa, amma ku biyo Baƙin  Alkalamin, mai rubuta ƙaddara mu ga ƙaddaran su waye ya rubuta mana, idan zuciyarki tana da rauni kada ki ƙaranta labarin nan, ina kira ga masu fama da cutar hawan jini, Anxiety discords da masu depression, masu fama da trauma please avoiding this story domin yana dauke da abubuwan da zuciya da ƙwaƙwalwa ba zasu dauka ba. Sannan ina kira da iyayen Yara maza da mata. Musamman Yaranmu Teenage masu tasowa maza da mata su bibiyi labarin nan akwai wani sako da zai taɓa su. This story contained violence and domestic stuff._

      Ku biyo ni cikin labarin Naanah Asma'u.


Heart to heart 

To you....💋

_________________________________________

Fatan alkhairi

Azizah my darling sister 

And

Seemahwriter my Baby sister 



Arewacin Nijar 

Agadaz 


Jihar Agadaz tana ɗaya daga cikin garuruwa takwas na ƙasar Nijar mai girma da faɗin kadada 33,620 (kimanin kilomita murabba'in 336.2) wannan ya haɗa da birnin da yankunan da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Agadaz. 

Mutanen yankin sun haura dubu ɗari da dama. Kimanin kilomita murabba'in 667,799. Wato kusan kaɗaɗa miliyan 66.8. faɗi da girman gari.

      Wannan ya sa Agadaz take da Region da ta zama mafi girman yanki a Nijar, yana mamaye da Babban ɓangare na hamadar Sahara. 

Tana ɗaya daga cikin yankunan ƙasar Nijar wanda ta haɗa yaruka mabanbanta.

     Ta haɗa Hausa, buzaye,zarmawa, Larabawa, Fulani da kanuri.

Har yau Agadaz ita ce mafi girman Cibiyar Kasuwanci na kasar Nijar, ba iya kasuwanci ba yanki ne na raya al'adun da yawon bude ido, Jaha ce ta take samun kudin shiga daga masu zuwa yawon shakatawa a yankin. Sannan akwai tsohuwar gari da yake dauke da gine-ginen zamanin da na tarihin rayuwar baya da mazauna yankin suka yi.


------


Lumshe idanunta ta yi tare da buɗe shi akan hasumiyar Agadaz wanda kullum yake nan kamar yau aka yi shi,  murmushi ne ya zauna a kyakyawar fuskarta.

  Duk yadda take son Niamey a duk lokacin da ta zo hutu gani take kamar akwai wani abu me muhimmanci da ta yi missing ɗin shi a garin nasu. Jirgin kasan ne ya tsaya a daidai tashar, ta miƙe tare da rufe laptop ɗinta ta saka shi cikin jakarta sannan ta shiga ƙoƙarin ciro kayanta a akwati wanda shi daya ne, sai wani jaka da yake shaƙe da kayan tsaraba. 

A hankali take jan akwatin har ta fito zuwa waje.

  "Didih!" Wata zazzaƙar murya ta kirata tana tahowa da ɗan gudu.  Zare fararen idanunta ta yi wanda suka ƙara mata kyau, tana jin yadda 'yar uwarta ta rungumeta gam. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana faɗaɗa murmushin farin ciki a fuskarta, ɗaga kai ta yi tana kallon wanda yake biye da ƙanwarta da sauri ta yi ƙasa da idanunta tana wani irin dariya me cike da jin kunyar shi. "Ai sai ki sake ta ko." 

           A hankali yarinyar ta janye daga jikin Yayarta tana faɗin. "Kai Ya Moud ka cika saka ido." Ta faɗa tana amsar jakar kayan, wanda shi ta miƙawa, ya amsa yana neman idanun Didih ɗin, amma taƙi yarda fir saboda laifin da ta yi masa.

"Mu je!" Ya furta a saman lips ɗinsa.

Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka take bin su tana ɗauke da jakar laptop ɗinta a kafaɗarta.


  "Didih, shi ne baki ɗauki kiran Ya Moud ba jiya ko?" Ƙanwar ta juyo tana kallon ita didin wacce ta diririce.


  "Hmm hmmm na ɗauka!"  

"Ta ɗauka ƙin magana ta yi!" Ya faɗa kai tsaye dai-dai suna fita daga cikin tashar. 

"Da gaske Ya Moud?" 

   Murmushin gefen baki ya yi ya isa inda motarsu take ya danna mata key ta yi ƙarar alamar ta buɗe kanta sannan ya nufi boot ya saka kayan. 


         A lokacin ita da bata da gaskiya ta zauna a baya taƙi yarda ta shiga gaban motar. "Ke koma baya ita ta dawo nan!" 

Tura baki ta yi tana faɗin "Wallahi Ya Moud baka kyauta mini! Sai ki fito ai Didih" 

kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki don kunya bata san yadda zata iya kare kanta ba. Tabbas jiya ya kirata kafin ta taso, sai dai a lokacin da suke wayar, Nadrah ta kawo mata waya Ya Almu yana ta kiranta ya ji tana waya shi ne ta kashe kiran Ya Moud ɗin, kamar munafuka haka ta shiga gaban motar ta zauna.

  "Ki saka sit belt!" Ba musu ta saka, suka ɗauki hanyar unguwarsu. 

     Kanta a sunkuye zaman very boring, kanwar ta ce musu. "Ya Moud saka min waƙar Hamisu breaker tun da shiru za ku yi!"


  "Haba Mairo bakya gajiya da magana ne?" 

Wani irin kallo tayi masa, tare da komawa da baya tana murguda baki ta ce masa "Allah ya tsaga mini baki ace na yi shiru? Haba ba zata saɓu ba bindiga a ruwa. Ku dai da kuka gaji ɗabi'ar kurame Allah ya baku sa'a! Ina ai kai ma ba haka kake ba, zama da maɗaukin kanwa ne ya kawo ma farin kai."

  Ya santa sarai da mita, duka-duka bata wuce shekaru goma sha shida ba, amma ba ruwanta da munafunci ko ɓoye-ɓoye bata iya ba, Mairoh kenan duk da bata son sunan amma fa ita ce asalin Meroh 'yar kunama. 


   "Didih!"

"Hmmm" ta amsa mata, kanta a sunkuya tana wasa da zaren mayafinta. 

"Tente Hasiya ta haihu fa!" A yadda ta yi maganar jikinta ya ɗauki wani irin rawa ta juya tana kallon Mairoh.

" Da gaske?" Ta tambaye ta cikin wata irin murya mai sanyi ƙalau, irin muryan da dole ka susuce idan aka maka magana da shi, domin ba da Ya Moud take magana ba amma sai da motar ta kusan kwace masa. ya dafe kirjinsa yana jin yadda yake wani irin bugawa. 

A hankali ya kalleta ya ce mata " Naanah Asma'u idan ba zaki iya zama ba ki koma baya don Allah!" Ya faɗa yana kallon titin da ya kusan buge wani yaro da yake kiwon raƙuma. 


       Haɗiye yawun bakinta ta yi tana kallon titin har raƙuman suka wuce, sannan ya ci gaba da tuƙi. 

"Wallahi ta haifi namiji, shi ma dai kamar sauran ya koma!" 

Wani shiru ya ratsa motar, dariyar da Mairoh ta sake tana me rike bakinta ta ce. 

"Allah na tuba ka yafe min ba ita nakewa dariya ba Hajiya Innah nake wa dariya, yadda take bala'in ji da Babangida tana murna da Uwarsa zata ƙara haifar wani yaron mai laifi."


  "Matsalata da ke baki da hankali!" Ya Moud ya faɗa, ai kuwa ta shiga mita, dai-dai isowarsu kofar gidan da yake cike da mutane, ana zaman makoki. A hankali Mairoh ta fito daga motar ta shiga fitar da jakunan Naanah Asma'u. A cikin motar kuwa kallonta yake, yana mamakin yadda take iya mantawa da shi ta saurari Mustapha. 

     "Me kike so na yi?" 

Girgiza kai ta yi tana wasa da wani zare a hannunta. 

"Amma kin san raina ya ɓaci jiya ko?" Gyaɗa kai ta yi domin ta yi ƙoƙarin kiransa yaƙi ɗaukar wayarta.

"To me yasa kike ɓata mini rai? Bayan kin san ba ni da uwar da zata tausaya mini!" Hawayen da ya ga tana sharewa yasa shi miƙa mata hanky, ya ci gaba da cewa. "Shi kenan tunda ba zaki iya bani haƙuri ba, ni na baki haƙuri share hawayenki kin ji ba zan ƙara fushi da ke ba." Ya furta yana kallonta. 

   Jiya har dare yana ganin sakonta a jejjere. A hankali ta juya zata fita ya ce mata. "Naanah!" 

Juyowa ta yi tana kallon shi. "Ki huta lafiya!"  Gyaɗa masa kai ta yi tana me fita a motar ta rufe, sannan ta ɗan tsaya sai da ya bar kofar gidan, kafin ta nufi inda mutane suke zaune ana zaman makoki. Har ƙasa ta durƙusa tana gaishe su. Sun amsa cikin fara'a da sakin fuska. Sannan ta shiga cikin gidan. Bata isa ta nufi bangarensu ba dole ta fara kai gaisuwa ga tsohuwa mai ran fitina inji Mairoh. 

       Yar lungu ce da zata sadaka da cikin ɓangaren Hajiya babu wanda yake bin wannan hanyar sai ita da Ya Almu da kuma ɗan jaraba. Domin akwai asalin hanyar da sai kabi ta cikin gidansu Babba karami. Warin hayakin taba da ta shaka wanda ya yi daidai da cusa kanta cikin lungun yana tsaye sanye da kananan kaya, ya riƙe ƙatuwar sigarin yana zukarta. Wani irin tsoron shi ne ya kamata ta yi kamar zata juya, amma sanin bai da mutunci yanzu zai iya shiga har cikin gidansu ya kamota ya kuma falla mata mari yasa ta yi kasadar tafiya kamar wata mage jikinta wani irin rawa yake tana takawa a hankali. Har ta iso gaban shi ƙafar shi yasa ta tokare hanyar da zata wuce. 

  Ɗago kai ta yi tana kallon ƙafar. Tsoronsa take ji kamar zata mutu. Idan fa zaka taɓa ta a wurin to zata iya yankar jiki ta suma. Juyawa zata yi ya sauke wannan kafar ya saka ɗayan yadda ba zata taɓa juyawa ba. A hankali ta juya tana kallon yadda yake zukar sigarin. Ya fesa mata hayakin a fuska, da sauri ta yi ƙasa da kai.

   "Don gidanku ni sa'an ki ne da zaki kalli idanuna?" Ya daka mata tsawan da sai da ta zabura, shi lallai so yake ta yi magana amma ya lura duk cikin yaran zuri'ar Baba Ladan babu miskila irinta musamman da waɗanncan yan iskan suke wani ji da ita. "Ina magana kin yi banza da ni!" Ya fada tare da ɗaga hannu zai mare ta.

  Ta yi ƙasa da kai tana faɗin. "Ka yi haƙuri!" Can ƙasa-ƙasa muryanta na rawa alamar zata yi kuka, irin yaran nan ne da basu da auki kome nata karami ne hatta muryanta me sanyi 'yar ƙarama ce. 


  Tsaki ya yi tare da dasa mata guntin sugarin a wuyarta kamar yadda ya saba idan suka haɗu ta gan shi yana shan sigari,  kallon yadda ta rintsa idanunta haɗi da kunshe kukanta ya ƙara  bashi haushi, yarinyar tun tana yar mitsisiya bata taɓa ihu idan yana azabtar da ita ba shi ya tsaneta tun daga lokacin da ya lura Yarinyar kalar munafukai ne da ita, durkushewa ta yi a  wurin jikinta yana rawa, takaici ya sa shi saka ƙafa ya yi shuri da ita ta tafi can tana me buga kanta da bango, ya tsuguna a gabanta ya fesa mata hayakin tabar da bata so, sannan ya wuce abinsa ɓangaren kakar su.

  Tafi minti goma tana kuka tare da shafa inda ya konata, saboda yadda ya wurin yake mata zafi da ciwo, haɗi da shure ta da  ya yi yasa ta  ji ciwo a hannunta. 


Da tasan yana gidan da bata zo ba, ai kuwa shiga bangaren Hajiya Innah da bata yi ba kenan ta dawo ɓangarensu tana share hawayen da yake idanunta. Ɗakin Matar Babansu ta shiga ta samu da mutane.

"Assalamu alaikum!" Babu wanda ya amsa mata. 

  Ɗago fararen idanunta da suka yi ja  ta yi tana faɗin. "Allah ya masa rahama, yasa mai ceto ne Tente!"

  Tsaki wata dattijuwar mata tayi a ɗakin tana faɗin "Hasiya ni wannan yarinyar 'yar gidan nan ne?"

  Gyaɗa kai ta yi tana faɗin. "Eh, ita ce babbar 'Yarta, tana can Niamey wai tana karatu." 


  "Karatu ko karuwanci? Mene ne 'yan matan yanzu basu yi? 'Yar gidan Feyde ina cewa daga zuwa Niamey karatu ta haɗu da wata shaidaniyar yarinya suka jone!"

   Ita dai idon Naanah Asma'u a sunkuye bata ce musu ƙala ba, suka gama zaginta kafin suka ɗaura da cewa "Shegiya ta haifi baka kamarta. Gashi ta 3auko Alhaji Mustapha sak har tsawon. Fita ki bamu wuri munafuka!"

  Wannan tsawon da Naanah Asma'u take da shi ba karamin ciwo yake yiwa sauran mutanen familyn ba domin dayawansu basu da wannan tsawon da rashin jikin. Sannan uwa uba ita ɗaya ce ta  jikoki maza biyun gidan ta dauki wannan tsawon idan tana gefen Ya Almu a bata kai kafadarshi ba. Haka wancan masifaffen shima kamar ya Almu yake domin kusan tsawonsu daya. Duk sauran jikokin tafisu tsawo. 

     A hankali ta fito tsakar gidan, ta kalli bangaren Mamansu. Murmushin kewa ta yi ta shiga takawa kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki, wannan yanayin nata shi ma yana ƙara sakawa ana mata kallon kamar bata da ƙoshin lafiya. Wata 'yar matashiyar budurwa ta fito cikin wani irin farin ciki ta ce mata. "Didih!" Ta isa gare ta tana me rungume ta. 

"Faɗime!" Ta furta yadda ita Faɗimen ce kawai zata ji muryanta. 

"Didih! Kin sayo mini turaren?"


   Ware ido ta yi tana murmushi. Suka shiga ɓangarensu. "Assalamualaikum Maama ga Didih!" Wacce suka kira da Maama tana karatun Alkur'ani, sai da ta kai aya sannan ta ɗago kai tana kallon 'Yarta wacce rabonta da ta sakata a idanunta yau wata hudu kenan, kodayake ai ba yau aka fara ba ballantana ta ce yau ta saba jin kewar 'Yarta. Ajiye Alqur'anin ta yi tana murmushi. "Uwah!" Sunan da take kiranta kenan saboda sunan surukarta ce. Gaban Maama ta je ta zauna a ƙasa tana murmushi me cike da farin ciki. "Maah!" Shafa kanta ta yi tana fadin. "Uwata kin sha hanya!" Fitowa Mairoh ta yi daga dakinsu na 'ƴan mata ta dafa kafadarta. "Washhhhh!" Ta furta a hankali, tana cire hannun Mairoh. Kallonta suka yi ganin yadda take rintsa idanunta, tare da cizon bakinta. 


            "Didih!" Mairoh ta kira sunanta a hankali tana kai hannunta saman rigar da wutar sigari ya huta. Jan zip ɗin rigar ta yi ƙasa tare da zame hannun rigar, "Ya Allah"  Khamilah ta furta wacce take bin Naanah Asma'u a baya ta ce mata. "Yau ma kin tsaya ya sake ƙona ki?"

  Tsaki Mairoh ta yi wacce take bin Khamilah ɗin tana fadin. "Sai ta zauna ya kashe ta ai, ni yanzu Didih na fi jin haushinki sama da shi ma, wallahi sai na gayawa Ya Almu tun da na fahimci shine kaɗai yake iya taka masa birki, ɗan iska kawai."


  "Kul na ƙara jin wani ya ƙara zagin wani bayan kun san cewa ya girme ku, wai ku ina ruwanku ne da wannan lamarin? Kun ga halin da muke ciki ko? Azumi zamu fara jibi don Allah ku rufa mini asiri ayi azumin nan lafiya a gama lafiya bana son tashin hankali, idan kuma na ji wani abu Mairoh kece domin kece baki da hankali da haƙuri!" Fuuuuuuuu ta wuce ɗakinsu. Tare da buga kofar ɗakinsu garam. 


  "Maamah na same ku lafiya?" Ta fada tana jan zip din rigarta Khamilah ta ja mata tana faɗin.

  "Didih ki yi hakuri!" Kusan Khamilah da ita Naanah Asma'u halinsu ɗaya amma ita Naanah Asma'u ta fita daban a cikinsu, wani ƙaton magen turawa ne ya zo da gudu ta rungume shi tana faɗin " Habibi! " Tana dariya,   ɗaga shi ta yi tana cewa"Maama su waye suka ci zalin Habibi naga ya rame?" 

Murmushin farin ciki da baya ɓuya a fuskar Hajiya Rukayyah da baya taɓ barin fuskarta ta ce mata. "Uwa waye zai iya da halin Habibi ai sai ke?" Faɗime ta ce mata.

"Didih shi fa Habibi bai da mutunci, abinci sai ya zaɓa. Ko wancan satin da ya ki cin abinci sai da aka sayo mishi kifin gwangwani ya ci gaskiya Habibi yana cinye tattalin arzikin Maamah!"


   Kallon shi take tana shafa bayansa ta kalli Khamilah. "Sis ya jarabawar dai?" 

Juya kai ta yi tana cewa "Ba sauƙi, mun gama ai!" Mairoh ce ta fito har ta sauko, haka take yanzu zata yi fushi ta yi zuciya, amma minti sha biyar albarka ta sauko.

  "Didih a kawo miki abinci ko sai kin yi wanka?" Ta tambaye ta.

  "Ban gama jin dumin Maamah ba!" Ta matsa gefenta sosai, sannan ta kwantar da kai a cinyarta. "Maamah ashe Tente Hasiya ta haihu? Allah yasa mai ceto ne!" 

Shafa kanta tayi tana cewa "Eh, ta sauƙa jiya da safe yaron ya koma dadaren jiya!" 

" Allah ya ƙara musu hakuri!"

  "Amin Ya Allah!" 


      Shiru ne ya ratsa parlourn, can Hajiya Rukayyah ta ce mata. "Ya kika baro Hajiya Rufaida? Da shi Alhajin tsakiya?" 

"Alhamdulillahi suna lafiya!"

 Shafa kanta ta yi suma sauran Yaran suka lulluɓeta suna masu kwantar da kansu a jikinta. 

"Ya kuma Yayanki?" 

Ɓoye fuskarta ta yi tana faɗin. "Yana Austria, an samu wani babban Club ya saye shi na shekara biyar." 

      "Didih idan kuka yi aure tare zamu tafi can ko?" Inji Faɗime.

  Janye jikinta ta yi ta barsu nan ai sun san ba zata bawa Faɗime amsar ba...