4
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 4.
Sarac Stars R Pen...✍️
Basu samu wata matsala ba wajen samun jirgin ƙasa, wanda ya wuce dasu Kanon dabo tumbin Giwa. Safiyya ta jingina bayanta jikin seat tana mai lumshe ido, siririn hawaye yana gudana a kuncinta, zuciyarta tayi mata nauyi sosai na kewar Jabir da yake nuƙurƙusar zuciyarta, dama ance sabo turken wawa.! ji take kamar har abada ba zata so wani namiji ba bayan Jabir domin da dukkan zuciyarta ta so shi, ta kuma bashi amanar kanta bisa yaƙinin zai riƙeta da hannu bibbiyu ya kula da ita, sai dai shi ne mutumin da ya haifar da tawaya a cikin lafiyarta bisa wani ƙudurinsa, duk da tasan Jabir ya so ta amma kuma sai da tafiya tayi nisa ta gane yafi son kansa da ita, shi yasa itama ta zaɓi gwada masa zata rayu ba sai tare da shi ba. Duk da ba zata mance soyayyarsu mai sanyi da sauƙin so ba musamman na kafin aurensu zuwa amarcinsu.
Mai napep ne ya sauketa a ƙofar gidansu ta dawo daga makaranta wanda a lokacin tana ajin ƙarshe na kammala jami'a, ta sallami mai napep ta juya da nufin shiga gida sai ta hango shi a can nesa da gidansu yana sakar mata murmushi, itama ta samu kanta da mayar masa sai ta ƙarasa ƙofar gidansu ta tsaya shima ya ƙaraso ya tsaya suna kallon juna.
Nayi kewarki sosai Sofyy Kamar bamu haɗu ba jiya, shiyasa na jure zaman jiran ki dawo.
Tun yaushe kake nan.?
Awa ɗaya da mintuna. Na aika aka ce baki dawo ba ni kuma ba zan iya matsawa daga nan ba har sai na jira ki, yau zan koma Abuja shiyasa nazo muyi sallama.
Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka, Safiyya ta lumshe ido ta buɗe jin wani abu ya shaya mata a zuciya na cewar zai koma Abuja.
Zaka koma kuma, to sai yaushe.? amma ba haka muka yi da kai ba jiya.
To ya zanyi Safiyya a wajen aikin aka buƙaci na koma, shiyasa na zo mu tattauna kan batun turo iyayena ayi magana ko zan samu natsuwar ruhi, kullun cikin tashin hankali da fargaba nake duk in zan koma Abuja, saboda gani nake kamar zan rasa ki.
Ka dai na wannan maganar In Sha Allah Safiyya matar Jabir ce, amma ba zan fasa baka haƙuri ba akan ka jira na ƙare karatuna, kasan Baffa baya son shirme shiyasa tunda nace karatu nake so yace to babu soyayya, ko ka manta shekara guda kenan daya fara bani damar kula samari saboda yaga nayi nisa da karatun.
To me ya rage yanzu a karatun.? nan da 'yan watanni zaki ƙare fa, dan Allah ki duba Lamarin nan, kin san fa ke me tsada ce samun ki sai an sha gwagwarmaya, ina tsoron wani daga danginku ya fito ya yi min ƙafa.
Allah ya kyauta aini bani da miji a kaf danginmu dan bana son auren haɗi, yanzu ka bani lokaci kaɗan na shi ga gida asan na dawo sannan na fito mu gana.
Cewar Safiyya cikin yalwar murmushi, Jabir ya gyaɗa mata kai yana mai yin murmushi, Safiyya ta shiga gida ta samu mama ƙarama tana aiki a kitchen tayi mata sannu da gida mama ta amsa tana cewa.
Wai kinga wannan yaro a waje kuwa, ɗazun Salim yake faɗa min yana waje bai tafi ba kuma bayan an sanar da shi baki nan.
Ai ko yana waje yana jirana kuma bai kirani a waya ba.
Ikon Allah to ki yi maza ki fito dan ya sha zaman jira kuwa. Wannan irin so da yaron nan yake yi miki ina ganin duk duniya ba zaki samu kamar sa ba, ya cancanci sadaukarwar so.
Ai nima shi ne zaɓi na.
Cewar Safiyya tana rufe ido cikin jin kunya ta wuce zuwa ɗaki tana murmushi, mama ƙarama dariyarsu ta manya tayi tana cewa.
Au Allah.? kice na isar da saƙonki wajen Baffa kawai kun gama daidaitawa, Allah yayi dai Safiyya ta fidda gwani Alhamdulillahi. Mama babba ki fito 'yata dai ta yi miji.
Ta ƙare maganar tana kiran mama babba. Haka suke kamar ba kishiyoyi ba, mama babba itace uwargida sunanta Hajiya Saudatu, yaranta biyar Anty Aisha da suke kira Indo ita ce babba sai Yaya Ali sannan Safiyya sai Maryam sai Musa. Amarya mama ƙarama kuma sunanta Hajiya Baraka yaranta shida Salim shi ne babba wanda yake tsaran Safiyya dan wata shida ya bata, a lokacin da Baffa ya aurota yaran mama babba biyu ne, to daga Salim sai Abida, Hassana da Husaini, Kausar, Hafsa. Da farko mama ƙarama taso ta rikita zaman lafiyar gidan amma da yake mama babba ta kama girmanta da kawaici, haƙuri da rashin son rigima hakan yasa mama ƙarama ta aje makamanta ta nima zaman lafiya, sai dai ba a rabata da kishi in ya motsa to sai ta bayyana shi, mama babba dai bata kula ta tana yi mata uzuri kuma dama zomu zauna zo mu saɓa mutum bai isa yace kullun yana aikata dai-dai ba dole wataran ya saɓa, dan hatta ita mama babba tana taɓa nata kishin sai dai ta iya allonta ne wanda yasa ba a gane nata, kuma gaskiya baffa tsayayye mutum ne a gidansa shiyasa aka zamu zaman lafiya da haɗuwar kan iyalin, dan kan Yaransu a haɗe yake, ko lokacin aurensu Abida da Maryam mama babba sakarwa mama ƙarama komai tayi ta zama jagora aka yi aka gama.
Safiyya tana shiga ɗaki ta aje jaka ta sanar da mama cewar Jabir yana waje, tace karta bari Magariba tayi mata a waje, tace mata to kafin ta fito ta yi hanyar waje, ta saba bata jin komai dan tayi hira da rana ko yamma domin wannan dokar baffa ne ba a yi masa zance da dare sai dai ido yana ganin ido. Ko da ta fito ta same shi zaune a ƙofar gida saman dakalinsu, ta ƙarasa ta zauna tana gaishe shi ya amsa fuska sake suka cigaba da hirarsu, a lokacin Hamisu abokin yaya Ali ya ƙaraso wajen su bayan ya aje mashin ɗinsa roba roba daga nesa, suka gaisa yace.
Safiyya yayanki yana ciki kuwa.?
Yana Majalisi shi da baffa, kasan duk yamma suna koyar da mutane a harabar masallaci.
OK ki sanar dashi zan dawo anjima In Sha Allah.
Allah ya kaimu.
Safiyya ta ambata, shi kuma ya ƙara bawa Jabir hannu suka gaisa sai ya wuce ya dau mashin ɗinsa. Suka cigaba da hira sai wajen Magariba suka yi sallama kamar ba zasu rabu ba Jabir ya wuce ya ɗauki motarsa, ita kuma ta shiga kamar zata yi kuka saboda har ta fara Kewar kwanakin da zata ɗauka basu ga juna ba.
Da daddare wajen ƙarfe tara ta gama waya da Jabir kenan sai ga Hafsa ta shigo tana cewa Baffa yana kiranta, bata ɓata lokaci ba ta miƙe ta biyo bayan Hafsa sai ta same su a tsakar gida kamar yadda suka saba cin abinci gabaɗaya, ita da yake ana Magrib taci saboda ta dawo daga makaranta da yunwa, ta zauna ta gaishe da baffa ta koma kan yaya Ali shima ta gaishe shi ya amsa fuska sake yana cewa.
Ashe Hamisu yazo ɗazun.?
Aiko na manta ne yace na faɗa maka zai dawo.
To ai ke kinyi kasuwa, ashe zancen ki yazo min da shi wai yana kama ƙafa da ni, shi ne nace babu ruwana ya zo wajen Baffa.
Ya ƙare maganar yana murmushi, Safiyya kuwa gabanta ne ya faɗi sai ta haɗe rai tana sunne kai bata ce komai ba, sai taji Baffa yana cewa.
To ai mahaifinsa ya same ni ɗazun nan bayan mun fito masallaci, dalilin daya saka kenan na kira ta dan in sanar da ita.
Allah ni bana son sa bai min ba.
Cewar Safiyya kai tsaye babu kunya ko shakkar Ali da yake abokin Hamisu, Ali ya zaburo yana cewa.
Kina da hankali kuwa Baffa kike bawa amsa haka.
A'a fa Ali kayi shuru a wannan maganar in dai Safiyya ce to fa tana da zaɓinta, kowa a gidan nan yasan babu wanda ta bawa dama yake zuwa zance sai Jabiru, kuma dama ɗazun nan nayi magana da ita tace shi ne zaɓinta, na bari Baffa ya shigo ne na faɗa masa.
Cewar mama ƙarama, Baffa yayi guntun murmushi ya gyara daga kishingiɗen da yake yace.
To ai dama nima ba tilasta mata aurensa zanyi ba, zan tambaye ta ne naji ko akwai wanda ta tsayar dan ban amsa maganar Mahaifin Hamisu ba, na ce sai na tambayi yarinya.
To ai magana ta ƙare Baffa sai yayi haƙuri tunda ga wanda take so.
Cewar mama ƙarama, Baffa ya kalli mama babba.
Ke ba zaki ce komai ba.?
Ai mama ƙarama ta gama magana dan haka ni nawa addu'a.
To madalla, kai Ali sai ka sanar da shi yayi haƙuri dan ba zan iya sanar da mahaifinsa cewar Safiyya bata amince ba.
Yanzu Baffa sai a biye mata, Safiyya fa har yanzu yarinya ce bata gama sanin soyayyar Gaskiya ba.
Ka bita da addu'a da fatan alkhairi, kuma zan baka ragamar bincike akan shi Jabiru, duk da nayi a baya kafin ma na bashi damar zuwa zance, amma yanzu ma zaka ƙara bincike sosai akai daga nan in babu wata tawaya a halayyarsa sai nayi magana da shi ya turo.
Cewar Baffa wanda dole Yaya Ali yayi na'am da maganar dan bai isa yayi masa musu ba, wannan shi ne mafari kuma sadanin ƙulluwar igiya uku akan Safiyya na auren Jabir, sun samu yadda suke so, dama ribar soyayya aure ne kuma haƙƙarsu ya cimma ruwa. Taɓa ta da aka yi shi ne sadanin data dawo daga dogun tunanin data shiga, sai ta sauke ajiyar zuciya tana ɗaura idonta akan fuskar anty Indo.
Mun ƙaraso ne.?
Ina zaki san mun iso bayan kin shiga duniyar tunani, wai Safiyya ko dai anyi miki dole ne kika kashe auren, kar fa ki zo nan gaba kina kuka da mutane, ina ce kin samu 'yancin kai ne amma kin takure kanki da damuwa.
Nifa bacci na fara yi ba tunani nake ba.
Ke dai kika sani, Hindu kinga muje ƙila jirgin zai mayar da ita Abuja ne tunda dama saki ɗaya ne yayi zata iya yin zaman idda ya mayar da aurensu.
In Sha Allahu hakan ba zai faru ba.
Cewar Safiyya a fusace wanda ta miƙe ta yi gaba ranta a dagule, Anty Indo ta yi dariyar ƙeta tabi bayanta, Hindu ma tana taya ta.
******
Mujaheed.
Wajen ƙarfe biyar saura sai ga sallamar Inna ta shigo gidan ɗauke da kaya akanta, Mama dake aiki a kitchen ta leƙo da sauri dan tabbatar da muryar wacce ta ji, zuciyarta ne tayi mata baƙi dan har ga Allah bata ƙaunar zuwan Inna gidan dan tana rage mata walwalarta, sannan a yanzu bata son abunda zai kawo cikas ga auren Aina'u, shiyasa ma tun farko ta bawa baba shawarar kar ya sanar da Inna sai komai ya kankama, ta haɗiye miyau kafin ta amsa sallamar Inna tana cewa.
Maraba da baƙin Daura, Inna kune tafe da yamman nan.?
Uwale kuna nan ashe ina ta sallama, sannunku da gida, na same ku lafiya.?
Inna ki shiga ɗaki mana sai mu gaisa, ina zuwa bari na ƙarasa sanwa.
Mama ta faɗa tana komawa kitchen, Inna kuma ta wuce ciki ta ɗauki kujerar tsakar gida ta zauna akai bata shiga ɗaki ba dan tana buƙatar iska saboda zafi take ji, sai ta soma kwance jakar kayanta dan ta ciro daddawar da take cikin kaya saboda bata gama bushewa ba, mama kuwa ta cigaba da sanwar taliya da wake dafaduka, waken dama tuni ya dahu bata fasa girkin da ta niyya duk da tana da masaniyar Inna tafi son tuwo da daddare, to dan me ma zata sauya bayan abunda mijinta yace kenan ta dafa, adadin taliyar ta ƙara tunda ga Inna tazo dan ya ishesu, tana sane da inna amma ta share ko ruwa bata iya kawo mata ba balle tazo su gaisa, ta ayyana sai ta kammala komai kafin za ta fito gabaɗaya, kuma har cikin ranta tana cewa ba zata yarda Inna ta ɗauki lokaci a gidan ba dole zata koma inda ta fito dan bata son takura. Bayan ta gama komai ta fito riƙe da ruwa pure water guda ɗaya a hannu, sai dai warin daddawar daya daki hancinta yasa ta yatsine fuska.
Warin menene haka Inna.?
Ta faɗa tana ƙarasawa wajen ta miƙa mata ruwan, inna kuma ta amsa ta buɗe ta fara sha dan sosai take buƙatar ruwar saboda ƙishin data kwaso, sai da ta shanye tas kafin ta duba mama.
Uwale inda ruwan daɗo mini wlh na kwaso ƙishi sosai.
Hmmm mama ta faɗa ta koma kitchen ta ɗauko ruwan guda ɗaya ta dawo ta bata, inna ta kuma shan rabi kafin ta riƙe sauran a hannu tana cewa cikin murmushi.
Kin ga ɗauko faranti ki baza wannan daddawar ta sha iska, shekaran jiya nayita, amma bata gama bushewa ba yanzu kuma saboda na saka a leda ta ƙume, shiyasa take ta wannan warin.
Aiko inna da baki wahalar da kanki ba, wannan irin wari ai da wuya na sakata a cikin miya, dan wacce muke amfani da ita daga Magami ake aiko min da ita daddawar kalwa ce mai kyau, zaki ji bata wari sam.
Ta ƙare maganar cikin yatsine hanci, inna kuwa sai taji guiwarta ta sare ganin ƙoƙarinta na son kyautata musu, amma sai ta kuma murmushi cikin rashin nuna ko in kula ta ce.
To ai data bushe ba zata yi warin ba, wlh ta kalwa ce mai kyau zata yi daɗi a miya, ɗauko farantin ki baza, gashi ma harda kuka da kuɓewa busasshe nayi muku tsaraba, dan nasan Babangida yana so sosai.
Inna ina yini bamu gaisa ba.?
Mama ta faɗa cikin kawar da zancenta dan ita ko kaɗan tsarabar nata bai yi mata ba musamman busasshe kuɓewa, tasan in dai baba yaji tazo dashi tofa basu da wata miya sai shi har sai ya ƙare, inna ta amsa gaisuwar mama data cigaba da tambayar mutanen ƙauyen, inna tana bata amsa da duk kowa lafiya lau, sai ta cigaba da cewa.
Ina mutane na naji gidan shuru.?
Suna makaranta anjima kaɗan zaki jisu.
To Mujaheed fa ya jikin nashi, Allah yasa an samu cigaba dan gane da lafiyarsa.?
Inna ta tambaya cike da jimami a fuskarta, mama ta taɓe baki.
Ai lamarinsa sai abunda yayi gaba inna, jiya ma satar burodi yayi sai da ya saka nayi asarar ɗari biyar, gashi baya magana kwata-kwata.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kai wannan ɗa yana ganin rayuwa, to amma anya kuna bashi abinci sosai yana ci.? dan in ya ƙoshi ba zai yi sha'awar sata ba.
Ka ji inna da wata magana, taya ba zamu bashi abinci ba meye ribata in na hana shi, karma ki kawo wannan maganar kawai dai juyewar kwakwalwarsa ne ke faɗa masa rashin lissafi, sai taurin kai da rashin jin magana, wlh ni na fara sarewa da lamarinsa ma.
Inna ta jinjina kai tana mamakin yadda surukarta bata tauna maganar da zata yi mata, ita dai tasan tana kama girmanta balle raini ya shiga tsakaninsu, tana iya ƙoƙarinta wajen kyautata alaƙarsu amma kamar hakan bai yiwa Uwale ba kamar ma bata son zuwanta a duk lokaci data kawo musu ziyara.
To Allah ya bashi lafiya, akwai hayaƙi da rubutu dana amso masa a gurin malam Babba dake nan Daura, maganinsa sadidan ne shiyasa na amso.
Ta faɗa tana cigaba da ciro kayan dake Jakanta dan ta ɗauko maganin, mama ta miƙe tana cewa.
Inna kina sawa kanki wahala kawai, a nan wani irin magani ne bamu yi masa ba, ai lamarin Mujaheed sai addu'a kawai.
Ta ƙare maganar tana shiga kitchen, a lokacin kuma Mujaheed ɗin ya fito daga ɗakinsa ya ƙaraso inda inna ke zaune ya zauna fuskarsa a sake sai dai bai ce komai ba, Inna ta saki murmushi.
Maigidana ashe kana nan, to na sameku lafiya.?
Ta faɗa tana shafa kansa, Mujaheed murmushi kawai yayi bai ce komai ba, nan ta aje maganin data ciro daga Jakanta a gabansa.
Wannan guzurinka ne yau In Sha Allah zaka fara amfani dasu, Uwale bani kofi na bashi wannan Rubutun yanzu ya sha.
Ta ƙare maganar cikin buɗe murya ga mama, sai ta amsa da to kafin ta fito ta kawo kofin inna ta amsa ta saka masa Rubutun ta bashi yasha ta miƙawa mama kofin.
A'a ki barshi a gurinki ya riƙa amfani dashi wajen shan maganin.
To hakan ma yayi kyau, zan samu ruwan wanka na watsa jikina duk tsami yake min saboda zaman mota.
Inna ruwan nan da sauƙi, sai dai in na kammala girki tukuna, ki shiga ɗaki sai ki miƙe a kujera.
Ta ƙare maganar tana yin gaba zuwa ɗakin da lissafin inda inna zata kwana, ɗaki ciki biyu ne a falon, ɗaya nata da baba sai ɗaya nasu Aina'u da Zara, a falo kuma su Nasir suke kwana, sai ɗakin Mujaheed dake nan tsakargida sai kuma wani extra ɗaki da suka zuba kayan hatsi wanda baba yayi nomansu, sai kuma kitchen. Mama ta wuce uwar ɗaka ta zauna gefen gado tana tunanin abunda zata yi dan ganin inna ta koma cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da ta daɗe ba.
Rahma ce.