Page 11.
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*ZEEY KUMURYA*
11.
BRIGHT PENS 2026
YOTA ID 003
Bismillahir rahmanir rahim.
Ramlah tana kitchen suna girkin dare ita da Marka wayarta ta yi ƙara, a yatsine ta dubi Marka ta ce. "Ɗauko mini." Duk da wayar ta fi kusa da ita, ko hannu ta miƙa ma za ta iya taɓo ta. Zagaye ta Marka ta yi ta ɗauka ta miƙa mata cikin girmamawa, zuciyarta cike da takaicin halin Ramlah da har yau ta kasa sabawa da shi, tana kiyayewa ne kawai don kar ta rasa hanyar cin abincinta.
Da mamaki Ramlah ta dubi sunan da ke yawo a kan screen ɗin wayar, a fili ta furta. "Abba Adam kuma?" Tare da ajiye wuƙar hannunta ta ɗaga da sauri, don ta san dole wani abun ne ya faru, haka kawai ba zai kira ta ba.
"Me yarinyar mutane ta yi miki kika yi mata wannan dukan?"
Abin da ya sauka a kunnenta kenan, waro ido ta yi tare da zare wayar ta ƙara duba sunan don tabbatarwa shi ɗin ne sannan ta mayar.
"Wacce yarinyar?"
Ta tambaya don ita ba ta kawo akan Ahayan yake magana ba.
A tsawace ya ce. "Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da hakan za ta kuma faruwa, idan kuma ba ki ji ba za ki yi nadamar abin da zai biyo baya a ƙurarren lokaci." Daga haka ya katse kiran. Sororo ta yi ta ma kasa zare wayar daga kunnenta, jikinta ya yi laƙwas ta kasa taɓuka komai.
"Ba dai akan waccan jakar yake magana ba?" Ta faɗa a ruɗe tare da jijjiga kai.
"Abba Adam? Abba Adam dai namu shi ne yake yi mini gargaɗi akan agola? To akan me? Impossible!"
Sai kuma ta yi saurin girgiza kai tare da faɗin. "No, ba ita yake nufi ba gaskiya, ba ta da wannan dajarar da ko dabba za ta shigar mata faɗa bare kuma capacitated Abba Adam, mutumin da wanda suka zama dolensa ma ba shirginsu yake shiga ba." Haka ta yi ta saƙe-saƙe ita kaɗai tare da hucewa akan Marka, da ta ga ta kasa gano bakin zaren sai ta kira Inno don ta ji gaskiyar lamarin.
***** ******
Duk yadda Mama ta tsara wa Saudat haka ta yi, ta shirya cikin atamfa ɗinkin doguwar riga, ta yafa mayafi ta fito tsakar gidan a kunyace. Kallo ɗaya Mama ta yi mata don takaici, yadda ta yi wani irin ɗauri da mayafin da ta dankama sai ta yi mata kama da yaran ƙauye masu kawo tallan daddawa a fanteka, abin da ya sanyaya mata rai da ta gifta ta kusa da ita ta ji tana ƙamshi mai sanyi da daɗi.
Kan Saudat a ƙasa ta ƙarasa parloun, ta yi mintuna biyu a tsaye a ƙofa zuciyarta na bugu na rashin sabo kafin ta daure ta yi sallama ta shiga. Ta ɗan tsaya ko za a amsa amma ta ji shiru, a hankali ta ɗaga kai cikin mamaki, wani matashi baƙi ta gani mai tarin suma a kai, wuyansa saƙale da wata irin sarƙa, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana zugar taba gami da fesarwa ta baki da hanci.
"A'uzubillahi!" Ta faɗa a rikice tare da ƙoƙarin juyawa ta fita.
"Ke!" Ɗin da ya faɗa a gadarance ne ya saka ta dakatawa.
"Dawo ki zauna mu yi magana, don iskanci kin shanya ni ina jiran ki kuma kin zo kike ƙoƙarin sake fita? Who are you? Me kike taƙama da shi? Wannan baƙin ko nanannen hanci mai shape ɗin tukunya."
Fuska a haɗe ta juyo ta ce. "Babu buƙatar zama tare da wanda za ka nema masa aminci ya ƙi amsawa bare ya nema maka kai ma, ban da gurin zama a inda ake busa hayaƙi, ban da lokacin magana da mutane irinka." Ta ƙarashe maganar gabanta na faɗuwa, yau ne karo na farko da ta taɓa mayar da magana mai zafi idan aka yi mata, ba ƙaramin dauriya ta yi wajen haɗo kalmomin ba, har gumi ta haɗa saboda tsoron abin da zai biyo baya.
Tafi ya yi tare da jinjina mata ya ce. "Wow! Kucaka irinki kike da bakin faɗa mini magana haka? Duk da na yi miki uzuri na rashin sanin wane ne Nasir, amma ki sani kin yi iya na kuɗinki, next time ko da kuɗi aka haɗa ki ba za ki ƙara kuskuren faɗa mini magana makamanciyar wannan ba." Ba ta kuma cewa uffan ba ta juya ta fita tana share gumin goshinta. Ya bi ta da wani irin mayen kallo mai cike da ma'anoni daban-daban. Wayarsa ya zaro daga Aljihu ya latsa ya kara a kunne.
"Ita ce, har ta zo mun yi magana."
Daga cikin wayar aka ce. "Nas! Ba za ka rabu da zancen yarinyar nan ba ko? Ni fa na ɗauka wasa kake yi, don na ga ba irin type ɗinka ba ce." Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Ba za ka gane ba, ni kaɗai na san me na gani." Numfashi wanda suke maganar ya sauke cikin damuwa ya ce. "Please kar ki sanadiyyar wargaza rayuwar innocent girl ɗin nan, ka haƙura kawai ko dan zumuncin family kar ya lalace."
"Kai ka san zumuncin da har ka damu da gyaruwarsa ko lalacewarsa, kaina kawai na sani da buƙatar zuciyata."
Daga haka ya katse wayar yana tuno murna da rawar jikin da Mama ta yi da ya faɗa mata abin da ya kawo shi. Murmushi ya yi mai sauti tare da faɗin. "Tunda gyatumarki ta nuna alamar amincewa naki mai sauƙi ne."
Saudat tana tafe tana waiwaye ba ta san da mutum ba sai karo ta ji sun yi.
"Saudat! Lafiya kuwa?"
Cousin ɗin Mama Aunty Hindu ta faɗa tana riƙe ta, daidaita nutsuwarta ta yi ta ce. "Babu komai Aunty." Kallon tsaf ta yi mata ta ce. "Da ma ina neman ki, saboda muna tare Nasir ɗin Baba Gali ya zo suka yi magana da Mamanku, ina son na faɗa miki wani batu da zai amfane ki." Tattara nutsuwarta ta yi gare ta cikin fargaba.
"Ke yarinya ce mai nutsuwa da son addini ma'abociyar son karatun Alƙur'ani, ga ki da hankali da kyawawan halaye, kina cikin mutanen da rayuwarsu take ba ni sha'awa wallahi, babu abin da ya dame ki da ruɗin duniya."
Murmushi Saudat ta yi cikin jin daɗin yabon ta da aka yi, abu ne da ɗaiɗaikun mutane ne suke yi mata, hakan ya sa ba ta ɓata mantawa da su.
"Na gode Aunty Hindu da kyakkyawar shaida." Ta faɗa ƙwalla na cika mata ido.
"Yabon gwani ya zama dole ai Saudatu, abin da nake son sanar miki kar ki kuskure ki yarda jinkirin aure ya sa ki amince da wanda bai dace da ke ba, ki ci gaba da addu'a da neman zaɓin Allah, auren ƙanne abar yaya ba kanki farau ba, bawa ba ya taɓa kaucewa ƙaddararsa, amma akwai wadda dole sai ka yi iya yin ka wajen ganin ka guje mata, na ga murna da farinciki a tattare da mahaifiyarki saboda batun da Nasir ya zo da shi, ragowar mutanen ɗakin na ƙara zuga ta." Ta yi shiru tana kalle-kalle sannan ta yi ƙasa da murya ta ce. "Nasir ba mijin aure ba ne, bai ma dace da kamilar mace irinki ba, aurensa biyar da kike ganin shi, ba shi da aiki kuma sai dukan mace musamman idan ya sha kayan maye suka faɗa masa ba daidai ba, bai san darajar mace ba ko kaɗan, ba shi da tarbiyya bare addini, ba ya bin mata, amma aure-aurensa da yadda bai ɗauki saki a bakin komai ba ya sa ana hasashen auren ɗanɗano yake yi." Dafe ƙirji Saudat ta yi ta ce. "Innalillahi! Kuma duk Mama ta san da wannan kuwa?"
"Ta sani, babu wanda bai sani ba a family sai ku yara, ki kwantar da hankalinki, ki je ki yi ta addu'a, idan an tambaye ki ya yi miki ki ce a'a, in sha Allah Ubangiji zai kawo miki salihin nagartaccen miji."
"Amma kina ganin Mama za ta ƙyale idan na ce a'a?"
"Gaskiya a yadda ta ruɗe da murna daga gani ba za ta haƙura ta daɗin rai ba, amma ki dage da addu'a domin babu abin da ya fi ƙarfin Allah."
"In sha Allah, na gode sosai Aunty Hindu."
Murmushi ta yi mata ta ba ta hanya ta wuce cikin tsananin tausayin ta.
Sosai jikin Saudat ya mutu murus, kanta ya kulle ta rasa tunanin ma da za ta yi. Ita ko Aunty Hindu ba ta yi mata wannan bayanin ba da ma ba za ta amince da auren wannan mutumin ba, don bai yi kalar mutanen arziƙi ba.
A ɗaki ta samu Mama ta faɗa mata sun gama ya tafi, da fara'a Mama ta ce. "Har ya tafi? Kodayake ya daɗe yana jiran ki ai, yaro ne mai zamani, yana murza nera sosai kamar bai san zafinta ba, ga shi wayayye zai wayar da ke ya fito da ke fes kamar tauraruwa, idan kika aure shi ko a dangi sai an dinga ba ki girma na musamman, to ya yi gadon arziƙi, ga shi kuma a kaf family da babansa muke taƙama, shi yake ƙara mana martaba, saboda babu mai dukiya da ya yi fice kamar shi." Kallon ta kawai Saudat ta yi zuciyarta na yi mata ƙuna. Mama ta gyara da zama ta ci gaba da faɗin. "Ni da ma duk abubuwan da nake yi miki ba ƙiyayya ce ta saka ba, don ba uwar da ba ta son ƴarta, kawai yadda kike yi ne yake ba ni haushi, tun kina yarinya idan na saka musu kayan gayu sai kin cire, ko kin ɓata, saɓanin ƴan'uwanki, duk inda muka je sai an ce mini yanzu ke ƴata ce? Ni kuma kin san bana son duk wani abu da za a ga gazawata ko wani naƙasu nawa, yadda nake son da na shiga cikin taro ido ya dawo kaina saboda kyau da shiga ta alfarma haka nake burin a ga ƴaƴana ma, dalilin da ya sa nake barin ki a gida bana fita da ke kenan, da kika fara girma kuma sai taɓarɓarewar abin ta fi yawa, na yi na yi ki dawo kan saiti amma kika ƙi, kika zaɓi rayuwar saka hijabi, duk tsaruwar taro da haɗuwarsa a haka za ki je, ga kaya kwata-kwata ba sa karɓar ki, duk tsadar su sai dai su yi gefe ki yi gefe, wannan dalilin ya sa na fara kyarar ki ko za ki gyara amma kika ƙi, shi ya sa muka yi ta tafiya a haka har kawo yau, amma yanzu tunda Nasir ya shigo cikin rayuwarki komai ya wuce in sha Allah, fatana kawai kar ki bula mini ƙasa a ido, ki amince ki aure shi ki samu rayuwar hutu da kowa yake buri, ni kuma na yi miki alƙawarin nuna miki soyayya da gata fiye da wadda nake yi wa su Mardiyya, za mu koma rayuwa irin wadda kika daɗe kina fata." Daga haka Mama ta miƙe ta fita don amsa kiran wayar da ake ta doka mata, ta bar Saudat durƙushe cikin rashin sanin makama, jujjuya maganganun Mama da na Aunty Hindu ta shiga yi a kwanyarta, ta amince da batun auren ta samu kyakkyawar mu'amala tsakanin ta da ahalinta ko kuma ta ƙi ta ci gaba da rayuwa da mikin da yake cikin ranta? Ta san Mama akan kuɗi da son yin suna a duniya, da burin ganin ta fi kowa babu abin da ba za ta yi ba, amma makomar rayuwarta fa? Aure fa ba abin wasa ba ne, kar fa ta yi gudun gara ta tarar da zago!
**** ***** ****
Gogaggun mata ne guda biyar zaune a wani keɓantaccen wuri da aka ƙawata da shuke-shuke masu ɗaukar ido da burgewa, sassanyar iska na kaɗawa a hankali, an ƙawata gurin da kujeru rukuni-rukuni masu ɗauke da table a tsakiya. Kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe da na sha ne burjik a gabansu. Kowacce ta yi shiga ta kece raini, ga wayoyi ƴan yayi a hannunsu.
A yangance ɗaya daga cikinsu ta dubi wadda ta yi tagumi cikin damuwa ta ce. "Wai don Allah da gaske kike mijinki zai yo miki kishiya? Imagine!" Ta ƙarashe maganar tare da keɓe baki. Murmushi Ramlah ta yi ta dube ta, ta ce. "Kina mamaki ne Farha?"
"Sosai ma, don ni wallahi mantawa ma nake da wani abu miji ya ƙara aure, saboda abu ne da ba zai taɓa faruwa da ni ba."
Sauke tagumin wadda ta yi ta ce. "Ki daina cika baki Farha, don ku shaida ne babu irin wanda ban yi ba a baya amma yau ga inda na ƙare."
"Rabu da ita, har yanzu ba ta san maza ba ne shi ya sa, kuma ni ban ga abin tashin hankali a abin da Allah ya halatta ba." Fatima ta faɗa da iya gaskiyarta.
Murmushin ƙasaita Farha ta yi ta ce. "To ni na faɗa na kuma mijina bai isa ya yi mini kishiya ba, ba ma zai soma ba don duk wata hanya da zai haɗu da mata na toshe ta, ko da kuwa a social media ne, don wallahi ba a halicci macen da zan yi kishi da ita ba, ni kaɗai aka halittowa mijina, ni kaɗai idanunsa suke gani, ku ma kun san haka ba sai na ɓata baki gurin dogon bayani ba." Hannu Ramlah ta ba ta suka tafa ta ce. "Ai macen da ba ta kai ba ita ake yi wa kishiya, kuma wayayyun maza ma irin namu ba su cika ƙara aure ba sai gidadawa." Wani kallo Fatima ta yi musu amma ba ta tanka ba, Lubna kuma ta ja tsaki tare da faɗin. "Ƙaryar banza, ni ma duk na yi ta a baya kuma yanzu ya zo ya nuna mini halin nasu, kun kuma san mazajen naku ba wata wayewa da suka fi shi." Kallon banza Farha ta yi mata ta ce. "Kamar kin manta ni surukar Govenor ce ko?" Kafaɗa Lubna ta ɗaga ta ce. "Kamar yadda nake ta former deputy governor ba?"
"Ko ma dai yaya ne ni Farha na ce ba za a taɓa yi mini kishiya ba, ku rubuta ku ajiye."
Da mamaki Laila da take bin su da ido ta ce. "Ke kuwa da me kike taƙama har haka? Don Allah ki ba ni sirrin don bana ƙaunar ko sunan kishiya na ji an ambata." Sai da Farha ta ja lokaci kafin cikin taƙama ta ce. "Duk wata hanya da zai ga wata mace ne ma ba shi da ita, bare har ya ji yana son ta, tun daga kan ma'aikatan gidana har staffs ɗin office ɗinsu duk maza ne, ba ya sabgar social media kwata-kwata don kar ya ci karo da hoton wata mace ta burge shi, na hana shi kuma ya hanu, gida idan da mata ko a familynsu ne ba ya zuwa su ma kuma ba sa zuwar mana, Ni fa har siblings ɗina ba kodayaushe nake bari ya gan su ba, a hanya ne kaɗai zai iya cin karo da mata, nan ɗin ma kuma na ɗauki matakin da ya dace." Dariyar shaƙiyanci Fatima ta saka ta ce. "Wow! Interesting! Gaskiya kin yi namijin ƙoƙari, I salute you."
"Ni shaida ce akan duk abubuwan da kika faɗa, don mijina ba shi da amini sama da mijinki, kuma yana faɗar duk wannan abubuwan a kansa." Cewar Ramlah cikin isa.
"Ku taimaka ku ba ni sirrin, kun san ina da azababben kishin da ba zan iya jurar ganin mijina da wata ba."
Kallon Laila da ta yi maganar suka yi a tare, Farha ta taune leɓenta gami da jijjiga kai ta ce. "Ba ki kai ni kishi ba na sani, amma kar ki damu zan zo har gida gobe mu ƙara tattaunawa." Da sauri Laila ta ce. "Zan zo da kaina ma ba sai na wahalar da ke ba Hajjaju." Murmushi Farha ta yi ta ce. "Yanzu fa na gama faɗa miki ko sisters ɗina ban fiya son su zo mun gida ba don kar mijina ya gan su bare kuma ke ƙawa, saboda haka kar ki damu, zan zo ɗin kawai."
Godiya Laila ta yi mata, daga nan suka ci gaba da tattaunawa Fatima na ƙoƙarin fahimtar da su ba a cin alwashi akan namiji, su kuma suna ƙara nanata mata su sun ci, musamman Ramlah da Farha da ta fi kowa zaƙewa.
***** *****
Juraij yana zaune a office ɗinsa ya yi tsam yana tattara wasu bayanai da ya samu akan binciken da yake, hankalinsa da nutsuwarsa gabaɗaya yana kan abin da yake yi, wayarsa ce ta fara vibrate, bai kula ta ba har ta katse wani kiran ya sake shigowa. Ɗauka ya yi da niyyar mayar da ita silent, ganin mai kiran ya saka ya ɗaga tare da sallama.
Daga ɗaya bangaren aka amsa gami da faɗin. "Masu ƙasar." Murmushi Juraij ya yi ya ce. "Masu tsaro dai, ƙasa ai taku ce."
"Ya jikin Daddy?" Tahir ya faɗa cikin maganarsa kamar ba ya so.
"Alhamdulillah!"
Sai da ya ja sakanni sannan ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, ya haƙurin rashin Sheikh Adnan?"
"Sai yau za ka yi mini gaisuwa."
"I'm so sorry Juraij, ka san bana gari sai jiya muka dawo da daddare, yau kuma tun safe muka fita da Father, yanzu muka dawo, sallah kawai na yi na kira ka."
"Uhm." Kawai Juraij ya ce.
Tahir ya yi wa Sheikh addu'ar dacewa a gidansa na gaskiya sannan ya ɗora da faɗin. "Za mu zo yau da daddare in sha Allah idan Farha ta dawo, sun fita da friends ɗinta ne ma da mun zo anjima da yamma." Juraij ya ce. "Allah ya kai mu bitazaizai." Murmushi mai sauti Tahir ya yi ya ce. "Ya muke da kai? Kai ma ai ba ka da dama akan Ramlah."
Guntun murmushi kawai Juraij ya yi ya katse wayar, bai ci gaba da abin da yake yi ba sai da ya lalubo wani hoto a wayarsa ya ƙura masa ido, zuciyarsa cike da tarin tulin tambayoyi akan mamallakin hoton.
**** *****
Ramlah ta riga kowa baro inda suka yi taron, saboda Juraij bai san ta fita ba, tana son haɗuwa da ƙawayen nata ta san kuma idan ta sanar masa ba zai bar ta zuwa ba saboda jinyar Daddy, sai da ta gan ta a ɗakinta sannan hankalinta ya kwanta, ta san da ma lokacin dawowar Juraij bai yi ba.
Farha kuwa ganin yadda Laila ta damu ya saka suka wuce gidanta tare don ɗora ta akan layin da zai katange ta daga kishiya har abada, text kawai ta yi wa Tahir ta sanar masa.
**** **** *****
Amma tana ta kai wa da komowar aiki a tsakar gida da yamma, Hasina kuma tana bakin rariya tana wanke undies ɗinta, tana yi tana mitar wankin da fatan ganin ranar da za ta daina yin shi kwata-kwata a rayuwarta, Amma dai ba ta tanka mata ba ayyukan gabanta kawai take yi. Sallama suka ji an yi daga soro cikin kamilalliyar murya, Amma ta amsa tare da tambayar waye.
"Baƙo ne."
Aka ba ta amsa cikin raha.
Hijabi ta ɗauko ta saka leƙa, da mamaki take duban mutumin, haɓa ta riƙe cikin murmushi ta ce. "Wa nake gani kamar Aminullahi?" Murmushi ya yi ya ce. "Ni ne Yaya Zahra'u." Da fara'a sosai Amma ta ce. "Maraba lale, Bismillah ka shigo." Bayanta ya biyo yana sake yin sallama, Amma ta shimfiɗa masa darduma ya zauna fuska a washe. Mamaki ne ya kusa kashe Hasina, ta tsayar da wankin tana kallon shi cikin al'ajabin inda Amma ta san shi, a cikin hirarsu ta fahimci second cousin ɗinta ne, tsabar kaɗuwa kusan daskarewa ta yi a zaune, yanzu Amma suna da wannan a dangi amma ta zauna tana wahalar siyar da abinci da wuni a tsaye kamar taɓarya? Tana daga lungu ne shi ya sa shi bai gan ta ba har ta gama ƙare masa kallo, fari ne tas ga jiki lukwi-lukwi sai hasken hutu yake, ƙamshinsa gabaɗaya ya cika gidan, babban abin da ya ƙara ba ta mamaki yadda ya zauna hankali kwance babu ƙyanƙyami babu komai.
Ganin zaman ba zai fishshe ta ba ta fito ta tsugunna har ƙasa ta gaishe shi tana washe baki, ya amsa da fara'a tare da duban Amma ya ce. "Ba dai wannan Babyn taki ce ta girma haka ba?" Amma ta ce. "Hasina ba, ita ce." Ya ce. "Ikon Allah, lokacin bikina da kuka zo riƙe mata hannu fa kike." Dariya Amma ta yi ta ce. "Lokacin ma da girmanta, kawai dai Auta ce shi ya sa."
"Ma sha Allah!" Ya faɗa tare da yi mata tambayoyi akan karatu ta ba shi amsa, ya ɗan jima kafin ya miƙe yana faɗin. "Mun dawo state ɗin nan da zama fa." Amma ta ce. "Yaushe?" Ya ce. "Za mu yi six months, ina ta son na zo ayyuka suna sha mini kai, sai yau Allah ya yi, Lailan ma sun tafi wani taro da ƙawayenta ne amma da tare za mu zo, yara kuma suna makaranta sai yanzu zan biya na ɗauko su."
"Ma sha Allah, abu ya yi kyau, in sha Allah ni ma zan samu lokaci na zo na ga gidan naka, na ji daɗi ni ma na samu ɗan'uwa a kusa, daɗindaɗawa kuma mai son zumunci."
"Ai yanzu ma ba don yamma ta yi ba da mun tafi da Hasina ta gano gidan."
Da sauri Hasina ta ce. "Zan iya zuwa duk da haka, ai dare bai yi ba." Da murna ya ce. "To ki shirya mu tafi, sai ki kwana ma don ku fi sabawa da su Suhail." A hanzarce Amma ta ce. "Ka bari wani lokacin dai ma zo, yanzu matarka ba ta sani ba, ba ta shirya ba kawai sai ta gan ka da baƙuwa? Ba za a yi haka ba gaskiya."
"Ba wani abu ai, tunda ba wata makaranta take zuwa ba mu je kawai, ma samu ladan zumuncin duka."
"Wai kar a takura muku ne."
"Babu takura Yaya Zahra'u, ni haka ma nake so na dinga ganin ƴan'uwana a gidana, ai na ji daɗi sosai, na yi farinciki da hakan ta kasance."
Duk yadda Amma ta so ta hana wannan tafiya don ta san halin Hasina amma ya dage, don mutum ne shi mai tsananin son zumunci, tana ji tana gani Hasina ta kimu kaya cikin rawar jiki suka tafi, ta bar ta da ƙarasa mata wanki.
Ran Hasina fari ƙal kamar takarda tsabar farinciki, daga ganin shi gidansa babba ne kuma a unguwar hamshaƙan masu kuɗi yake, inda za ta kai ƙawayenta ba kunya sai ma tarin alfahari, ta san kuma za ta yi samari a unguwar irin waɗanda ta daɗe tana buri, tunda an ce ƙwarya ta bi ƙwarya ake to idan suka gan ta a gidan Uncle Aminu ai dole su zo su ƙyasa, ko a gidajen maƙota ta san ba za ta rasa mai tayawa ba, tsabar daɗi kamar ta taka rawar murna haka take ji. Ba ta ƙara gigicewa ba sai da ta ga gidan da ya shiga da su bayan ya yi waya da matarsa ta sanar masa ta dawo.
*#Zeey Kumurya*
*#****