HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

Hs 54

by @legendspen

(54)

Bayan kusan sa'o'i biyu da sumewar Bhatool, a hankali ta fara buɗe idanunta waɗanda suka yi jawur saboda tashin hankali. Tana ganin kanta a kan gadon asibiti, sai dukkan abubuwan da suka faru a dakin ICU suka dawo mata daki-daki. Tunawa da kalaman Senate na cewa ya mayar da ita matarsa ya sanya ta yi wani irin kukan kura ta miƙe.
"Wallahi ba zan zauna da shi ba! Na tsane ka Usman! Na tsane ka!" Bhatool ta fara ihu tana ƙoƙarin fizge ƙarin ruwan dake hannunta. Ta haukata asibitin gaba ɗaya, nurses sun kasa riƙe ta, sai kuka take yi tana surutai tamkar wadda ta zauce. "Saki na zai yi! Gara in mutu da in sake zama matar Senate! Umma don Allah ki ce ya sake ni!"
Umma dake tsaye a gefe, hawaye ya wanke mata fuska, ganin yadda ɗiyarta take neman fita daga hayyacinta. "Alhaji, don Allah a sanya ta a mota a kai ta gida kawai. Wannan tashin hankalin zai iya shafar abin da yake jikinta," Umma ta faɗa cikin muryar roƙo ga Dad.
Daidai lokacin da aka fito da Bhatool daga ɗakin, tana kuka tana fizge-fizge, sai ga Abdul da Ahmad sun shigo asibitin a guje, sakamakon kiran da aka yi musu. Abdul ya nufi ƙanwarsa da sauri. 

"Lafiya me yake faruwa, ihun me take?." Yaya Karima ce ta kwashe dukkan abin da ya faru aka gaya masa.
Bhatool tana ganin Abdul, ta faɗa jikinsa ta rungume shi, tana kuka mai ban tausayi wanda ya sanya kowa a wurin zubar da hawaye. " Abdul, ka ji abin da ya yi mini ko? Ya ce ya mayar da ni bayan ya wulakanta ni. Don Allah ka ce ya sake ni, ba na son sa!"
Abdul ya ƙanƙame ƙanwarsa, idanunsa suka cika da ƙwalla. "Yi haƙuri Bhatool. Komai zai wuce, kiyi haƙuri ko don abin da yake jikinki."

A gefe ɗaya kuma, Ahmad yana tsaye tamkar wanda aka shuka. Kalaman Senate na cewa ya mayar da Bhatool matarsa sun dake shi fiye da saukar aradu. Ya kalli Bhatool yadda take kuka a jikin Abdul, ya kalli yadda dangi suka taru suna jajanta wa juna.
Wani irin raɗadi Ahmad ya ji a zuciyarsa, amma sai ya tuna da kaddara. Ya tuna cewa duk yadda ya so Bhatool, idan Allah bai nufa ba, ba za ta taɓa zama tasa ba. Ya juya a hankali, hawaye guda ɗaya mai zafi ya zubo masa a kumatu. Ya fice daga asibitin gaba ɗaya, bai jira kowa ba.
Yana shiga motarsa, ya dafe sitiyari. "Bhatool ba rabona ba ce," ya faɗa a cikin ransa cikin murya mai cike da sadaukarwa. "Idan har mayar da aurenta shi ne zai ba ta natsuwa kuma ya ceci rayuwar Senate, to na haƙura. Allah Ya ba su zaman lafiya, Allah Ya sanya hakan shi ne mafi alheri a gare ta."
Ahmad ya tada motarsa ya bar asibitin, ya bar zuciyarsa a can, ya tafi da wani babban nauyi aransa, shin nadama ce ko kishine shi dai yakasa  cewa komai, yasan dai ya yi jarumta ta ƙarshe.

A cikin motar Dad kuwa, Bhatool tana kuka a jikin Umma har suka isa gida. tana isa gida, ta fada kan gado tana wani irin kuka mai cin zuciya. Kowane sassa na jikinta rawa yake yi saboda fushi da radadin kalaman Senate. Abdul ya shigo dakin, ya zauna a gefen gadon yana kallon kanwarsa cikin tsananin tausayi. Ya sa hannu ya dafa kafadar ta, muryarsa a sanyaye ya ce.

"Bhatool, kiyi shiru haka nan. Na san abin da kike ji, kuma na san yadda zuciyarki take tafasa. Amma ina so ki kwantar da hankalinki, na miki alkawari, muddin wannan auren zai zama silar damuwarki, zan tsaya miki da kaina wajen neman saki a wurin Senate. Ba zan bar ki a inda ba kya so ba, kiyi hakuri ko don abin da yake jikinki."
Jin kalaman Abdul ya sanya Bhatool jin wani dan sanyi, ta dan rage kukan amma har yanzu hawaye ba su daina zuba ba.

A can asibiti kuwa, bayan ficewar su Bhatool, Senate ya fara farkawa a hankali. Na'urorin dake jikinsa sun nuna cewa bugun zuciyarsa ya fara daidaita. Ya bude idanunsa, wannan karon babu dishi-dishi. Ya kalli Mom dake gefensa, ya yi wani dan gajeren murmushi na rauni. "Mom... ina Bhatool?" Ya tambaya murya can kasa.
Likitoci sun tabbatar da cewa kumburin zuciyarsa ya fara raguwa sakamakon ganin Bhatool da ya yi, wanda hakan ya ba shi karsashin rayuwa. Jikinsa ya fara sauki sosai, har aka fara cire masa wasu daga cikin na'urorin dake maƙale da shi.

Bhatool tana kwance a gida, hannunta rike da waya. Ta kira Ahmad kusan sau goma amma bai daga ba. Zuciyarta tana wani irin bugawa, tana tsoron kar Ahmad ya fahimcita ba dai dai ba. Ta sake tura masa sako fuskarta ɗauke da ƙwalla.

"Yaya Ahmad, don Allah karka guje ni. Karka yarda da kalaman Senate, kai nake so..."

Ahmad, wanda yake zaune a cikin motarsa a gefen titi, yana kallon wayar tana haske. Hawaye ne ke zuba a idanunsa, amma ya daure ya kudurce wa kansa cewa sadaukarwa ita ce kololuwar soyayya. Ya dauki wayar, ya rubuta mata sako mai ratsa zuciya kamar haka.

"Zuciyata, Bhatool.
Na karbi sakonki, kuma na ji dukkan kukan dake cikin muryarki. Bhatool, soyayya ba wai mallakar masoyi ba ne kawai, soyayya ita ce ganin farin cikin masoyi a inda ya fi dacewa da shi. Senate ya mayar da ke dakinki a daidai lokacin da yake tsakanin mutuwa da rayuwa, hakan ya nuna cewa ke ce numfashinsa. 
Ni kuma, zan zama silar da zan janye domin ki sami natsuwa da danginki da kuma mahaifin abin da yake cikinki. Ba zan iya gina farin cikina a kan rugujewar rayuwar wani ba, musamman mutumin da yake neman yafiyarki a mawuyacin hali. Na yafe miki dukkan alkawarin dake tsakaninmu. Kiyi biyayya ga mijinki, ki raini danki a cikin soyayya. Zan kasance mai taya ki murna daga nesa. Allah Ya bar ku tare, Allah Ya sanya alheri a rayuwarki ta gaba. Salam."
Bhatool tana karanta wannan sako, ta saki wani uban kuka mai taɓa zuciya. Ta kankame wayar a kirjinta, tana jin yadda Ahmad ya nuna mata tsantsar karamci da sadaukarwa.

Sakon Ahmad ya sauka a zuciyar Bhatool tamkar ruwan kankara, duk da radadin dake tattare da shi, amma ya sanyaya mata jiki sosai. Ta fahimci cewa Ahmad mutum ne mai daraja wanda ba zai taba zama silar rugujewar gidanta ba. Cikin kuka ta kira Jannah, ta kwashe dukkan abin da ya faru da kuma sakon Ahmad ta fada mata.
Ba a jima ba sai ga Jannah ta bayyana a gidan Umma. Ta zauna kusa da Bhatool, ta fara mata nasiha mai ratsa jiki. "Bhatool, kaddara ta riga ta gifta har wani abu ya faru tskanin ku da  Senate, amma Ahmad ya nuna miki girmansa, mutunci da karamci, kuma ya sauke miki nauyin dake kanki. Yanzu abin da ya rage miki shine kiyi hakuri ki koma ga mijinki, musamman yadda ya nuna nadama a lokacin da yake tsakanin rai da mutuwa."

Bhatool ta ja numfashi, ta goge hawayenta. "Jannah, na hakura. Zan zauna da Senate tunda haka kaddarar take. Amma ina so in nuna masa cewa na yafe masa ne don Allah."

Jannah ta yi murmushi, "To idan har hakan ne, tashi ki shiga kicin ki yi masa girki na musamman, ki kai masa asibiti. Wannan zai nuna masa cewa baki rike shi a zuciya ba, kuma zai kara masa karsashin tashi daga rashin lafiyar."

Legendspen
***