Hs 55
by @legendspen
Ahmad fa ya ɓata min rai, na so ka zauna da ita ka rabata da wancan Senate din, amma ka nuna kai ba haka ba, canka yanka. 😒😒
Bhatool ta amince, ta shiga kicin ta hada wani daddadan girki wanda kowa ya gani yasan ta yi bajinta akansa. Lokacin da ta kai asibiti, kowa ya yi mamaki da murnar ganin Bhatool da abinci a hannunta. Wannan karimcin ya burge Mom, Dad, da dukkan dangin Senate.
Washe gari, garin Yobe ya dauki dumi da shagalin bikin Jannah. Dangi da abokan arziki duk sun hallara.
A daren Ladies Night da ake yi a gidan Yayar Jannah, falon biki ya cika da mutane yan uwa da kawaye. Bhatool tana zaune a cikin wasu kawayenta, sai ga Amrah ta shigo.
Tana ganin Bhatool, Amrah ta kasa karasawa cikin taron. Ta tsaya daga nesa, idanunta suka cika da kwalla. Bhatool ta lura da ita, ta mike ta karasa wajenta. Amrah ta fashe da kuka, ta kama hannun Bhatool tana neman gafara.
"Bhatool, kiyi hakuri. Na san abin da na yi miki ya wuce misali, amma don Allah ki yafe mini. Zuciyata ba ta ƙara samun natsuwa ba tun ranar da kika bar gidan mijinki."
Bhatool ta tausaya mata, ta kamo hannun Amrah ta ce, "Amrah, komai ya wuce. Na yafe miki duniya da lahira. Allah Ya yafe mana baki daya."
Amrah ta ji wani irin dadi, ta gaya wa Bhatool cewa itama bikin ta ya rage saura sati biyu kacal. Suka gaisa cikin mutunci, abin da ya ba kowa mamaki ganin yadda suka yafe wa juna.
A can gidan Mom kuwa, Senate ya wartsake sosai. Kumburin zuciyarsa ya ragu, kuma likitoci sun ba shi damar komawa gida domin ya ci gaba da hutawa. Yana shiga gidan, ya iske ko'ina an gyara masa.
Zama ya yi a falon kasa, yana kallon hoton Bhatool dake manne a bango. Ya ji wani irin dadi a ransa jin cewa Bhatool ta duba shi har ta yi masa girki, kuma ya ji labarin yadda ta hakura da zama da shi.
"Zan nuna miki soyayya fiye da wadda na nuna miki a baya, Bhatool," Senate ya fada wa kansa, yayin da yake jin karsashin lafiyarsa na dawowa gaba daya.
Bikin Jannah ya ci gaba da ƙawata gari Bayan taron Ladies Night da aka yi wanda ya zama silar sasanci tsakanin Bhatool da Amrah, washe gari aka gudanar da gagarumar Walima. Malaman addini mata sun gabatar da wa'azi mai ratsa jiki, inda suka yi bayani a kan haƙuri da zaman takewar aure. Bhatool tana zaune cikin sauran ƙawaye, tana sauraren kowane kalma, tana jin tamkar kanta ake yi wa wa'azin. An tashi taro lafiya, kowa ya fito fuska cike da annuri.
Rana ba ta ƙarya. Ranar Juma'a aka ɗaura auren Jannah da abokin Senate a babban masallacin Juma'a. Taron ya cika da manyan mutane, kuma an yi komai cikin tsari da albarka. Senate, duk da cewa bai daɗe da fitowa daga asibiti ba, ya halarci ɗaurin auren, koda yake bai zauna ya sha wahala ba. An gama biki lafiya, amarya ta tare a gidanta na Abuja cikin so da ƙauna.
Bayan kwanaki biyu da kammala bikin Jannah, Senate ya fara fitowa waje don ƙara samun natsuwa. Yanzu hankalinsa gaba ɗaya ya karkata ga neman gafarar Bhatool ta hanyar nuna mata tsantsar soyayya.
A karon farko, Senate ya nufi gidan Umma da yamma. Ya tsaya a ƙofar gida, ya kira wayar Bhatool. Muryarsa a sanyaye ya ce, "Bhatool, ina kofar gida. Don Allah ki ba ni dama ko da na mintuna biyar ne in ganki."
Bhatool ta ɗan yi shiru, sannan ta sanya mayafinta ta fito. Ta iske shi jingine da motarsa, ya ɗan rame amma kwarjininsa na nan. Ganin Bhatool ya sanya Senate sakin wani murmushi mai sanyi. Bai yi mata maganar baya ba, sai dai ya miƙa mata wata leda mai ƙamshi.
"Na kawo miki abubuwan da kike so ne. Na gode da kika amince kika fito," ya faɗa cikin girmamawa.
Haka Senate ya dinga zuwa kusan kowace rana. Wani lokacin yakan zauna da Abdul su yi hira, wani lokacin kuma ya samu damar zama da Bhatool na ɗan lokaci. Yanzu ya daina nuna isa ko izza, ya koma tamkar wani sabon saurayi dake neman soyayyar budurwa. Wannan sauyin hali na Senate ya fara sanyaya zuciyar Bhatool, duk da cewa har yanzu akwai tabon abin da ya faru a baya.
A haka aka kwashe sati biyu, inda zumunci ya fara dawo wa tsakaninsu. Ahmad ma ya janye gaba ɗaya kamar yadda ya yi alƙawari, wanda hakan ya ba Bhatool damar fuskantar rayuwarta ba tare da rudani ba.
Gari ya sake ɗaukar wani sabon dumin na bikin Amrah. Tunda amincinsu ya dawo, Bhatool ta tsaya tsayin daka wajen taya Amrah shirye-shiryen bikinta. An yi shagalin biki na gani ta fada, kowa yana mamakin yadda Bhatool ta ci gaba da mutinci da Amrah har ta taya ta abubuwan bikim ta , wanda ya nuna a tsakaninsu akwai wani aminci da zumunci mai ƙarfi.
Ranar ɗaurin auren Amrah, gidan ya cika da murna. Amrah tana kuka tana sake neman gafarar Bhatool yayin da take shirin tafiya gidan mijinta. "Bhatool, kaddara ce ta sa na yi miki kishin hauka, amma yau gashi zan tafi nawa gidan. Don Allah karki daina sanya ni a addu'a."
Bhatool ta rungume ta, "Allah Ya sanya alheri a aurenki Amrah. Komai ya wuce."
Bayan an tafi da Amrah, Senate ya zo ya ɗauki Bhatool don mayar da ita gida. Suna cikin mota, ya kalle ta cikin sanyi. "Bhatool, yanzu kowa ya fara samun natsuwa. Saura mu kadai. Ina so ki sani, ina jiran ranar da zaki ce mini kin yafe mini baki ɗaya."
Bhatool ta yi murmushi ta kalli titi. "Zuciyata tana kan hanyar hakan, Senate."
Soyayya tsakanin Senate da Bhatool ta koma sabuwa ful, tamkar yanzu aka fara zancen. Duk da cewa tana gidan Umma, amma Senate ya mayar da gidan tamkar nasa. Kullum yana nan, idan ya zo ba ya tafiya sai dare ya yi, hira suke yi ta natsuwa inda Senate yake ta ba ta haƙuri tare da nuna mata tsantsar nadama.
Sai dai, duk da wannan shauƙi, Mom ta tsaya a kan matsayarta na cewa: "Babu maganar Bhatool ta koma gidan Senate har sai ta haihu lafiya, ta yi jegon ta ta gama." Wannan hukunci ne Mom ta yanke wa Senate a matsayin horo na rashin bincike da gaggawar da ya yi wajen sakin mata ta wayar tarho. Senate ba shi da yadda zai yi, ya amshi wannan hukunci cikin sanyin jiki, yana mai cewa, "Mom, zan jira koda shekara nawa ne, muddin zan sake samun Bhatool a matsayin matata."
kunga ina ta baku post akai akai ko? ina so na sallameku ne, na mai da hankali a kan new book din zamu fara on 10th Sept in sha Allah. masu buƙatar complete su yi min magana ta wannan number din ta ƙasa.
Legendspen
***