Chapter 21&22
by @deeyamerh10
💖💖 SOYAYYAR ZUCI 💖 💖
‎ (love and Romantic story)
‎ written
‎ by
‎ Deeyamerh‎
‎07070647236
‎page 21&22
‎Abinda ta lura tsawon lokacin shine kamar da Sabeer da Haseenah suna aikata wani abu da ba dai dai ba,domin tana wan ganin ta shiga part din su ko kuma shi ya shigo kai tsaye ya shige ɗakinta.ita kuwa Mubeenah barta da shaye shaye watarn ma bata kwana a gidan.
‎dukk wanna budirin da ake Abba bayama gidan domin yana can neman Ammey dan duk inda akace masa an gama mahaukaci yakan sa a tsare masa ita har sai yaje yagani ko matarsa ce.
‎sosai Mommy take baza mulki a gidan domin ta mayar da Suhaima kamar jakarta komai ita ke yi,abinda yasa ba hanata zuwa makaranta shima shawara Asabe ta bata gudun kada a zageta akan abinda yake faruwa,sosai duk abinda ake take murna dan wllh jitake kamar ta rabu da kya...
‎duk lokacin da zasu tafi makarantan da damuwa akan fuskarta baya da sake wa da kowa acewarta bata da lokacin hakan,
‎shiyasa ko Fatima da ke soyayya sai abin yata burgeta dan tabbas da ace har yanzu tana kusa da Ammey ba abinda zai hana batai soyayya to dawa ma zatayi?ita dai ba fita take ba sannan ba kwalliya ta ke ba bare ace zatayi saurayi shiyasa su Hassena suke ce mata kifin rijiya.‎
‎tana dakinta a zaune kawai taji anbanko mata kofa,cikin nutsuwar da ta gada ta kalli kafafun wanda ya shigo mata,ba kalli fuskar ba domin tasan waye ne wanna haukan.
‎zama kusa da ita yayi yace"ke suhaima wai me kike takama da shine eh ana binki kina wani kaucewa duk mun san irinku fa masu cewa na Allah sai an shiga ciki a jiki a fafake ki tsaya dan nasan yan Matan Abuja sungama kwa....ai bata bari ya karasa ba ta dauki wata flowers dake kusa ta ita ta rutsewa banza a goshi "maza tashi ka fice mun adaki ko wllh na kashe kuma na kashe banza,an fada maka Ni irin Haseenah ce ko wani kare da doki na kwasa eh? zaka fita ko sai naci......‎
‎jin haniyar ta kuma abinda tun zuwan ta part bata tabayi ba yasa suka shigo dakin nata,gashin Sabeer tsaye kanshi ba fitar da jini yasa Mommy tambayar meyakeyi wa dakin nan?Budar ba kunsa sai cewa yayi daga zuwa tambayarta shine tai masa haka?
‎"dan kutumar uban ki wato Hau kan da uwarki take yi ashe gado ne tunda gashi kin fara kema to kamar yadda kika fitar masa da jini haka kema zan fitar Miki cewar Haseenah".‎
‎wllh wllh duk yarinyar da tayi gigin tabani na rantse da Allah sai na nunawa yarinya cewa da banbanci tsakanin zaman aji a islamiya da rashin idan kuma 'ya tana musawa bisimillah"‎
‎wuri wuri ta fara inda zata ga abinda zata dake su dashi,ai ganin da gaske yake yasa kaff suka fita da gudu.
‎daga murya tayi tace"kai kuma Bunsuru idan na sake ganinka a dakina Wllh Allah sai naci me cin.......kai daga jin yadda take ashar kasan ce ba sabawa tayi ba Amma wani har gagin kana yinsa ne dan a ji tsoro.
‎tsakin Sabeer da Haseenah sai da aka samu sabani sosai akan zuwa dakin Suhaima da yayi,hakuri yayi ta bata yana fada mata kalaman yaudara.dan alkwari tayi ya daina kwanciya da ita.
‎tun daga ranar Sabeer bai kuma gigin shigo mata daki ba sai dai idan sun hadu a waje yasata a gaba da batsa kala kala
________________
‎GARIN JEMETA
‎"SHA'AYAN Ni kuwa yau ka dubu mara lafiyar ka kuwa?wata Dattijuwa tace tana mai kallonsa Matashin saurayin da yake gabanta.
‎wllh Hajjiya naje nidai fatana Allah ya bata lfy domin sosai take bani tausayi wllh,sannan hajjiya abinda yake bani mamaki da ita shine duk da tana cikin rashin hankali hakan baya hanata ta zauna ta kalli gabas kamar wacce take so tayi sallah to Ni hajjiya na rasa ya zan mata gashi bata bari kowa zo gunta sai Ni ko abinci bata so kowa ya bata idai bani ba.
‎Allah sarki Sha'ayan haka Allah yake hada ji da mutum ko da ba dan uwanka ba sai kaji kana jinsa a jinin jikinka addu'a ta a kullum Allah ya bata lfy.
"‎yawwa hajjiya kinsane me nake tunani?sai nake ganin kamar ciwanta fa na Asibity ba ne ma zai hana kiyiwa Malam Tijjani magana ko zamu gwada yi mata na Islamic saboda komai mun duba na brain dinta komai normal.‎
‎tabbas ka kawo shawara me kyau domin nima haka kawai naji hankalina ya kwanta da ita duk da ban sonta ba kuma bantaba ganinta Amma inshallah zamu tai make ta,zanyi masa magana muji duk yadda za'ayi idan ma gidan nan zata dawo sai ta taho tunda baya dole doke ko?
"‎eh hajjiya batayi kam nima zan tadawo nan don hajjiya domin ance idan aiki yayi mun yawa ko banshigo ba sai ta ta kokarin fita,Ni kuma Kinga aikinsa da yawa ga tafiyar nan da zanyi zuwa Dubai shiyasa nake so ta dawo kusa dake kafin na dawo Amma yadda kika ce haka za'ayi.
‎gidanku Sha'ayan temakon Allah ne sai kafadi yadda za'ayi sannan ayi,Karka manta gidan da nake ciki na kane to dan me zan hana kawo wacce kake so eh?kai dai Allah yayi maka albarka yanuna mun naga jikoki kin ka.
"Ameen y hajjiyata".
Jin Ana kiraye kirayan sallar magrib yasa ya Miki yace"hajjiya bari na je masallaci daga zan biya Asibity naga Yaya ansamu cigaban.
To to Allah ya tsare ayi addu'ar dai SBD makiya domin su basa bacci dan guri kadan suke samu da wannan damar suke amfani da ita wajan cutarwa.
Murmushi yayi sannan ya fita,sai yanzu da yafito na kare masa kallo domin kuwa kyakkyawan saurayini ajin farko,matashi ne shi amma Allah yabashi kyau gayu kudi domin kallo daya macce zatayi masa ya tafi da imaninta ga haske me kyau irin na asalin shuwa ga kasumba ta da zagaye fuskarsa.
Masallacin unguwar ya nufa a kafa yana tafiya yana azkar har yashiga masallaci.cikin jam'i yashiga inda liman ya tayar da kabbarar sallah.
Sun kai wajan 10mins suna Allah dan ko da ya idar mekewa yayi ya hauyin shafa'e da wuriti,ko da ya idar sai da ya zuna zaman addu'ain da yasaba duk da yaji vibration na wayar a samun akan Kira Amma bai yi gaggawar dubawa sai da ya gama addu'ar.
A hankali ya mika zararan hanunsa cikin aljihu ya dauko yara ganin su na me kiran yasa ya saki wani lallausar murmsushi wayoo kyau dan Ni kaina sai da na suma.
Fita yayi daga cikin masallaci sannan yasamu guri daya ya tsaya domin wayace mai mahaimmaci wacce take son nutsuwa da bada dukan wani lokaci gare ta.
Bin miss call din yayi,bugu biyu dauka daga daya bangaren akace.
"Hello"ina ji cigaba akai da magana
Har yanzu dai da damuwa a tare da ita dominx duk ba wannan tsiwar gaskiya Sannan kamar ma ta dan samu matsala
Katseahi yayi da cewa"jabeer kana da hankali kuwa partner life din ta wace kake fadamun tana cikin matsala to meye amfanin barinka wajan kula da ita?abinda kaga dama kake kiyi kenan to na baka nan da 1hours duk yadda za'ayi ayi domin naji murmushinta a cikin zuciyata domin SOYAYYAR TA A ZUCI take na fada maka,bai bari ya sake cewa komai ba ya kashe wayar.
Wata number ya lalabu ya tuwa ga gajeran sako.
Gida ya kuma sai yake wani wanka domin tunawa da partner life din sa wllh sai yaji cigar jikinsa ya tashi Allah yasani ya so da kaunar kayansa,gashi yayi kewar rigamarta,shagwabarta, kai komai ma nata yayi kewarsa.