CHAPTER 17
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA SHA BAKWAI
Ta damƙi cikin, ta fara shafawa.
“Ke, lafiyar ki kuwa? Cikin fa kamar yana ƙoƙarin kwantawa ne.”
Ta kalli Farida kafin ta ci gaba,
“Kai, ban yarda da ke ba. Anya kina shan ruwan rubutun nan kuwa, Faridatu? Yoo, jinnun Sufuyanu ma ai kaɗai sa gagara bar miki ciki ya yi abin arziki.”
Ta ƙarasa maganar tana laluben cikin fridge inda ta aje gorar ruwan rubutun.
Ɗaukowa ta yi tana sallallami da guntun hawayenta.
“Oh ni Innojo! Farida, so kike ki cuce ni, ki cuci kanki, ki cuci jaririyar da ke cikinki? Ko so kike ki haifo mana ’yar ruwa ne a dangi? Karɓi nan, ki kurɓe tas. Kuma yanzu zan koma in sa a ƙara yi miki rubutun nan ki sha mu gani. Indai ciki bai tashi ba, dole a san na yi. Kullum abu ba ci gaba? Aa, ba da ni ba wanga doguwar husumar.”
Ta ƙara zungura wa Farida gorar, tana tsaye a kanta, har sai da ta shanye tas. Kafin ta kalli samirar da ta kawo tana nuna mata.
“Dabgene na kawo miki. Na san bakin mai ciki ba a rasa shi da ƙwaɗayo. Ki zauna ki ci, ki sha roman. Yanzu gidan Malam na nufa ni kam.”
Ta faɗa tana ficewa daga gidan.
Farida dafe kai ta yi tana faɗin,
“Ni dai na shiga tsaka mai wuya wacce ba ta da sauƙin tsallakewa. Ga gaskiya, amma babu damar furtawa. Kuma ko da an samu damar ma, duk ranar da Inno ta fahimci babu cikin nan, nikam na kaɗe”
Inno na fita gidan Hansai ta nufa ta je ta ɗauketa, kan ta rakata gidan Malam.
Tun daga ƙofa ta fara tafka sallama. Kawu Hamza ya amsa yana,
“Ke ce tafe, Inno?”
Inno ta gyada kai tana,
“Nice fa, Hamza. Da maraicen nan na hango wata husuma da ke ƙoƙarin bullowa. Ina Hansai take?”
“Gani tafe, Inno.” Hansai ta faɗa tana ajiye butar da ta fito daga bayi.
Inno ta ce, “Taimaka ki rakani mu je wajen Malam. Na lura aljanun Sufuyanu sun kwantar da cikin Farida.”
Cikin sauri kuwa Hansai ta zura hijabi tana,
“Ai kuwa, dai nima ince bana ganin sauyi irin na masu ciki tattare da ita. Gwanda tun wuri a san ta yi.”
Kawu Hamza ya ce, “To, sai kun dawo. Allah tsare hanya.”
Ficewa suka yi, suna ta zuba zance suna tafiya.
Suna zuwa cikin damuwa, Inno ta rattaba wa Malam jawabin abin da ke faruwa. Take ya sanya aka fara yi mata rubutu, sannan ya ba ta wasu ganyayyaki da itatuwa kan aje a fara dafawa kafin a gama rubutun.
—
Sufyan ya dawo kenan da daddare. Yana parking motarsa ya tarar da Farida zaune a farfajiyar gidan, tana ta binsa da kallo.
Ya tsaya ya kalleta, ya ɗaga mata gira ya ce,
“Yane bogaza? Ki fita a sabgata fa, ki yi rayuwarki, in yi tawa. Sai wani bi na da kallo kike, kodayake kin ga handsome guy ko?”
Ya ƙarasa maganar yana ƙara ɗaga mata gira.
Ko gezau Farida ba ta yi ba, idanuwanta ma a ƙafe suke suna binsa da kallo kawai.
Sufyan ya yi gajeran tsaki.
“Wai wannan kallon naki? Ni fa bana so. Kar ki cinye ni ɗanye, please.”
Har a lokacin ba ta motsa ba, bare ta kula shi.
Ya ci gaba da faɗin,
“Kya ji da shi dai. Kawai kina ta kallon mutum mai girar ’yan gayu, ga kai fal gashi.”
Ya ƙarasa maganar yana kyalkyale da dariya, sannan ya shige ciki.
Da rawarsa da waka ya shiga. Ganin Farida zaune a kan kujera, da laptop a gabanta, ne ya firgitasa.
Murza idanuwansa ya yi don ya tantance shin Farida ce ko ba ita ba. Da ya ga dai tabbacin ita ce, da gudu ya koma waje. Ya ƙara tarar da waccar ma zaune har a lokacin, idonta na kansa.
Ya ƙara komawa cikin ɗakin, nan ma ya ga Farida aikinta take yi, hankali kwance.
Cikinsa ne ya fara ƙugi, zufa ta fara keto masa. Kan kace me, gudawa ta fara kwarara. Jin hakan yasa Farida ta ɗaga kai ta kalle shi.
Ganin yadda ya tsure yasa ta fara wata irin dariya. Ta rufe laptop ɗin ta ɗauka, tana ƙoƙarin shigewa ɗaki. Tana nufo inda yake, ya ja ƙafarsa, gudawa na kwarara, ya yi ɗakinsa da gudu, yana shiga ya kulle ƙofar.
Tsaki Farida ta yi tana binsa da kallo.
“Ji wata sabuwar ƙazanta,Da alama yau ma ya sha wani abu.”
Ta wuce ɗakinta tana toshe hanci.
Toilet ya nufa a daɗaddafe, ya hau. Gudawa ta dunga kwarara kamar ruwa, ga wata irin ƙarar tsoro da cikin ke yi.
Sai da ya ɗauki wajen minti biyar a bayi, duk ƙarfinsa ya kau kafin ya samu ya fito.
Yana fitowa ya haye kan gado. Ban da Faridar da ya gani a farfajiyar gida ta kura masa idanu, babu abin da yake gani. Ya kankame filo yana rufe ido.
Can wata irin iska ya ji tana kaɗawa a ɗakin. A hankali ya buɗe idanunsa, yana buɗewa ya ci karo da Farida a gabansa, ba ɗankwali, daga ita sai kwallon gashinta da shafilen fuskarta. Ta kura masa ido.
Bai san lokacin da ya saki wata ƙara ba, yana rungumar bango da filo. Ga hawaye, ga kuma gudawa ta ci gaba da kwarara. Majina da hawaye sun yi caɓe-caɓe a fuskarsa.
Ita kuwa ta ƙafesa da ido tana sakin wata dariya da hoƙara, ne kawai, waje ba a jiyo sauti.
Jin hakan yasa Farida ta fito da sauri tana buga ƙofar.
“Kai, ya dai? Lafiya? Za ka ishi mutane da ihu?”
Cikin muryar kuka Farida ta jiyo Sufyan na faɗin,
“A zo, a zo don Allah! Farida, Farida ce!”
Farida ta ce, “Ni ce, kamar ya?”
Bai amsa mata ba, illa jiyo sautin kukan sa da ta dunga ji.
Baba Shuaibu ne yana ta faman ƙoƙarin fahimtar abin da Sufyan ke faɗa, ya gagara. Hakan yasa hankalinsa ya tashi, ya tashi ya je gidan Inno, ya tarar da Baba Haruna, ya shaida masa cewa gidan Sufyan fa ba lafiya.
Dukansu suka runtuma suka nufi gidan.
Farida na tsaye a bakin ƙofar ɗakin, sai jiyo sallamar Baba Haruna da Abba Shuaibu ta ji.
“Me ke faruwa ne?”
Kafin Farida ta amsa, caraf Sufyan ya ce,
“Abba, a taimaka! Gata nan, a buɗe a ciro ni, don Allah!”
Fara murɗa ƙofar suka yi, ta ƙi buɗuwa.
Inno ta ce, “Oh ni! Wanga, wacce irin husuma ce tafe?”
Ta faɗa jiki na ɓari.
Baba Haruna ya kalli Farida ya ce,
“Ina makullin naki ɗakin? Ba mu, mu gwada.”
Da sauri Farida ta zaro ta miƙa masa.
Cikin sauri ya zura key ɗin ya buɗe ƙofar. Hango Sufyan suka yi, dare-dare a saman gado, ya kankame bango.
Tsaki Abba Shuaibu ya yi ya ce,
“Wannan shirmen fa?” Sautin Abba Shuaibu ne yasa Sufyan buɗe ido.
Kallon gun da Sufyan zai yi, sai ya ga ta ɓace. Aguje ya tashi, ya yi wani tsalle ya ɗare jikin Baba Haruna ya kankamesa.
Inno ta ce, “Me zan gani? Na shigange ni, Sufuyanu lafiya?”
Sufyan ya nuna Farida yana cewa, “Ita ce a cikin ɗakin, ita ce ta zama biyu.”
Baba Shuaibu ya yi tsaki.
“Shirmen banza kawai. Tana nan, ta ya zata zama biyu? Kai dai an yi shasha wallahi. Ji ka fa, saukar masa a jiki.”
Ya faɗa yana jan Sufyan daga jikin Baba Haruna.
Baba Haruna ya ce, “Tsaya dai. Yanzu zauna ka huta ka yi mana bayani.”
Sufyan ya zauna baje-baje kan kujera yana maida numfashi. Farida na haɗa ido da shi sai ta saci ba mai kallonta, sai kyalkyale da dariya ta bishi da gwalo.
Inno na ta yi masa fifita tana,
“Ana ta batun ciki ya kwanta, to ga miji ma ni Innojo.”
Sai da Sufyan ya fara dawowa hayyacinsa kafin Baba Haruna ya ce ya yi masa bayanin abin da ke faruwa.
Tiryan-tiryan ya faɗa daga dawowarsa har zuwa yanzu.
Baba Haruna ya kalli Farida ya ce,
“Ki faɗi gaskiya, in dai da sa hannunki a hakan.”
Farida ta ce,
“Aa wallahi Baba, ni ban san ma me ke faruwa ba. Ni na fi tunanin ma kila mafarki ya yi ne, duk ya razana. Tunda ni dai ina ɗakina.”
“Aikuwa dai, ragon banza! Mafarkin ne ma. In ba haka ba, ta ya Farida zata zama biyu, kuma tana bibiyarsa? Wannan shirme ne.”
Abba Shuaibu ya faɗa.
Baba Haruna ya ce, “Ai kuwa dai, domin an duba gidan nan kaf ranar, babu wata damuwa. Don haka ka nutsu kawai, ka kwantar da hankalinka. Kai ne kake tsorata kanka da kanka kawai.”
Sufyan ya yi rau da fuska yana, “Allah, ba mafarki ba ne. Ni na san abin da na gani.”
Abba Shuaibu ya tashi yana, “Ka yi shiru da wannan shirmen. Ku tashi mu tafi kawai.”
Tashi Sufyan ya yi yana ƙoƙarin binsu.
“Don Allah, mu tafi tare. Ni ba zan zauna a nan ba.”
Inno ta ce, “Haruna, anya kuwa ɗan nan bai yi gamo ba?”
Caraf Farida ta katseta da, “Ba wani gamo wallahi, Inno. Daman cewa ya yi sai ya bar gidan nan, shi ya bullo da hakan.”
Inno ta ce, “Ka ji husumammen ɗa? ni dama na ga take-takenka. Aiko dai Sufuyanu, ko ka ƙi ko ka so, dole kai zaman auren nan. Yoo, ma ban da mugunta irin ta yaran zamani, ka narkawa baiwar Allah ciki kace zaka gujeta? Ai zama daram, dole ka zauna ka reni cikin nan. Ku muje mu.”
Baba Shuaibu ya ce, “Wallahi, kar ka kuskura ka ce mun ba ka gidan nan.”
Suka fice abunsu.
Farida ta kalleshi tana dariya ta ce, “Zaman aure ne dai, sai an zauna an yi.”
Sufyan, duk da rashin ƙarfin jikinsa, a fusace ya kalli Farida yana,
“To wai an faɗa miki ma ni tsoron ki nake? To, ko aljanun ne ma, wallahi na fi ƙarfinsu. Ni ba tsaransu ba ne. In ba tsoro ba, su ƙara fitowa su ga yadda zan yi da su mana.”
Yana daga kai…