Chapter 2
by @maidambu41
BAƘIN ALƘALAMI.....
{Mai Rubuta Ƙaddara}
Chapter 2
Warning ⚠️
(Ban yarda wani ko wata su juya mini labari ko sakawa a wani kafar sadaukar ba! Idan haka ya faru akwai mummunan mataki da za a ɗauka.)
Tana shiga ɗakin su kayan jikinta ta fara cirewa ta buɗe drower ɗinta ta ɗauki zaninta na zaman gida, ta ɗaura akan unders ɗinta sannan ta cire bra da pant, ta nufi hanyar banɗakinsu da yake cikin ɗakin, kamar yadda ta sani banɗakin yana nan kamar kullum, ko ina a gyare tsaf-tsaf, kasancewar ana zafi ruwan randar roban ta ɗiba a bokitin wankan ta matsar da shi gefe ta cika buta da ruwa ta san zuwa yanzu period ɗinta ya ɗauke.
Shi ya bata damar fahimtar tsarkinta ya tsaya, wanka zata fara ta tuna da kayan sosanta. Motsi ta ji a ɗakin ta ce. "Khamiee!"
"Na'am Didih kina son wani abu ne?" "Eh bude jakar tsarabar Please kayan wankana!"
"To!" Tana buɗewa ta miƙa mata, tana ɗauka ta buɗe wani ƙamshi me daɗi ne ya ziyarci hancinta murmushi ne ya suɓuce mata ta kalli jakar, sit na kayan wanka, irin na ƙasar Austria ne. Buɗewa ta fara tana ajiyewa daga yadda take ɗaukar kome tana duba rubutun da aka yi da wasu arab words, ta kuma sake murmushi tana jin zuciyarta yana wani irin bugawa. Kamar yana gabanta ta rufe fuskarta da shower gel ɗin. Ta jima a tsaye kafin ta fara wanka bayan ta gama ta tufke baƙin gashin kanta mai tsawo ga cika ta fara wankan tsarki. Tana gamawa ta fito daga bayin tana kallon Mairo da take ta harba manyan idanunta tana kunkuni.
Sai yanzu kunnuwanta ya jiyo mata fadar Hajiya Innah, wani sabon tsoro ne ya cikata da sauri ta ɗauki jallabiyar Khamila ta zura sannan ta fito daga ɗakinsu, bakinta yana rawa ta leƙo tsakar gidan Abba Babba ne a tsakar gidan, Mahaifinsu sai Maama da kanta yake sunkuye.
Sai Tente Hasiya, Matar Abbansu da take tsaye tana girgiza. "Yee isasshiya mai farka da sarkin gari ina wuni Naanah Asma'u kin zo lafiya? Haka kike so na gaisshe ki ko? To sannu uwata uwar da ta haife ni, kin saba duk dawowarki za ki shigo ki yi mini barka da gida yau Rakiya ta hanaki ko?
Wai don Allah makaho ya kake son na yi da Rakiya da yaranta? Ni yanzu banni da galihu kenan? Ina garin rashin mutunci waccan 'yar iskar yarinyar Hasiya ta haifi Yaro ba rai? Duk haka bai isa ba! Innalillahi wainnalihir rajoun!" Ai kuwa ta fashe da kuka.
Shi kanbshi tausayin Rakiya da yaranta yake ji, abin da ake mata ya yi yawa ya wuce lissafin mai sauraro. Cikin sanyin murya da hakurin da Allah ya ɗaura masa, wanda bayan shi babu mai iya zama da Hajiya Innah saboda masifarta da fadanta, uwa Uba ƙiyayyar da take nunawa yaran shi mata, shi kansa abin tashin hankali ne.
"Innah ki yi hakuri!"
Fyace majina ta yi ta ce masa "Kamar ni a gidan nan Nanah Asma'u ta dawo makaranta ta yi banza da ni!" Ta nuna kanta, sai ta fashe da kuka tana mai share hawayen da yake zubo mata da haɓar zaninta.
N Ba yabon kai ba, duk cikin Yaran Hajiya su shida ya fi su tattalin Hajiya, kai ko a yanzu da bai da ƙarfi idan Hajiya ta ce yau Umara zata kafin sati biyu ya shiga ya fita ya nema mata ticket din tafiya, yana kyautatawa Hajiya amma ita bata ƙaunar Rakiya. Duk hanyar da zai bi ya kyautata mata yana bakin ƙoƙarinsa wurin neman su.
Saboda tsananin biyayya irin na shi baya iya kyautatawa iyalinsa don kada ta gani tace ya watsar da ita. Ko da zai yi wani abu ya gwammace ya kai gidan su Rakiya a kawo mata. Wanda tun kafin abin ya iso yake gaya mata. Har kwanan gobe Rakiya bata taɓa kallon shi a matsayin wanda ya zalunceta ko ya hanata farin ciki, sai dai tasan halinsa ta kuma san waye shi, bata zarginsa amma kuma yana iya hango gazawar shi a cikin idanunta.
"Makaho ba zaka kira 'yarka ta bata haƙuri ba?" Inji Hajiya Innah.
"Maryama!"
"Na'am Abba!" Fitowa ta yi sai da ta gama hura hancinta da harare-hararenta. Kafin ta ce
"Abba Babba gani!"
"Ki bata hakuri na ce!"
Kallon Matarsa tayi ta ce mata. "Ki yi hakuri."
"Hajiya Innah ni kam na haƙura da auren Ya Makaho!" Ai kuwa Mairoh ta buga shewa tana faɗin.
"Sama Mata!" Tana komawa parlourn sai ga Nanah Asma'u ta yi tsuru-tsuru kamar ita ta yi shewar, abin da ya ƙara tabbatar mata gidansu fa ya fara samun sauyi daga uƙubar da suke sha su da Mahaifiyarsu.
"Makaho ka ji abin da ta ce, tun da ita ba zata bata haƙuri ba to Rakiya ta bata haƙurin!"
"Haba Hajiya kin ajiye ni tun dazu ina jiran ki sai surutu kike!" Aka faɗa daga lungu.
"Kai dai baka da haƙuri Uban Kowa, gani nan zuwa!" Ta fada tana miƙewa, leƙowa ya yi ya gaida Abba Babba, da Maamah sannan ya juya abin sa.
"Hajiya shi ma Uban kowa me na yi masa baya gaisshe ni?"
"Ke bana son jidali, ki ji da abim gabanki, shi wannan bai damu da kowa ba sai kan shi kada ki cusa kanki a fitina na gaya miki. Ke Naanah Asma'u waye kika ajiye da zai dafa mini abinci?"
Miƙewa ta yi simi-simi ta bi bayan Hajiya. Har bangarenta. Part ne da aka zuba masa duniya da kayan more rayuwa. Yadda Hajiya take rayuwa a nan gidan bata kaunar matsawa zuwa wurin sauran yaranta. Domin kuwa a nan take sakewa tabyi rashin mutuncin da ranta yake so. Tasan Maama ba ruwanta duk abin da ta faɗa ba zata taɓa ɗago kai ta yi magana ba.
Shekaru ashirin da biyar tana tare da Alhaji Muhammad Mustapha Ladan, bai taɓa nuna mata sauyi ba ballantana kuma rikicin Hajiya ya dame ta.
Tun da suka shiga Hajiya ta samu wuri ta zauna, ita kuwa Nanah Asma'u ta wuce kitchen ɗin Hajiya a saninta da tun fil azal ta yiwa Hajiya mace ce itama mai azabar tsafta, wanda ake mata laƙabi da Hajiya fes-fes, yana daga cikin dalilin da yasa har take zaman Agadaz saboda Maamah ita ma tana da tsafta har ya wuce yadda ake tsammani. Haka ta duba kitchen din bata ga wani alamar datti ba, asalima babu komai a ciki, tasan wanan mugun matuƙar yana gari to baya taɓa barin Hajiya ta yi wani abu da kanta. Shigowa ya yi cikin ƙananan kaya da suka kwanta a jikinsa kamshin turaren shi ya gama isar mata da yana kitchen, can gefe guda ta raɓe kanta a sunkuye. Bakinta ne yake motsi alamar addu'a take. Ko inda take bai kalla ba. Amma a kasan ransa wani ciwo da ɓacin rai yake ji taya za a yi yarinyar nan ta mai da shi kamar dodo.
Mug ɗin da ya kawo ya ajiye da gayya a kitchen din yadda tana taɓa shi zai fado ya fashe ya ji daɗin samun hanyar da zai mata mugunta. Fita ya yi zuwa parlourn ya baza falla-fallan kunnensa yana jiran ya ji ƙarar fashewar mug din sai aka yi rashin dace Hajiya Innah ce ta shigo kitchen din ganin Naanah Asma'u tana buɗe drower ɗin da ake ajiye kayan abinci. "Mene ne babu na gayawa Uban kowa ya kawo mana?" Hajiya ta fada tana matsawa jikin kofin, ai kuwa rashin sani yasa ta taɓa kofin sai gashi ya faɗi ƙasa tas, ya fashe a tiles sosai.
"Amma Uban kowa bai kyauta ba, akan me zai ajiye kofi a nan ga shi ya fashe fisabiilillahi ayi mutum da halin Yara!"
Jin kalaman Hajiya Innah yasa shi barin parlourn yasan ita ta fasa.
"Ina magana kin yi mini shiru? Haba takwara me yasa kike haka ne?" Tun da ta ji Hajiya na lallabata, so take tayi magana da Ya Almu. A sanyayye ta juyo tana kallon ƙasa ta ce mata. "Ban ji bane." Batun gaskiya wannan halin na Nanah Asma'u yasa Hajiya take sonta, amma ƙiyayyar da take yi wa Maamah yasa take ƙin yarinyar a jikinta.
Murmushi ne ya ƙwacewa Hajiya ta ce mata. "Da Alhaji Ladan yana raye tabbas da nace shi ne a gabana." Tana jin irin wannan kalaman wasu lokuta idan Hajiya ta bushi iska.
"Ku uku Allah ya baku ikon ɗauko Alhaji Ladan, Almu, Uban kowa, sai ke. Ke ba za ki san shi ba, domin shekararki ɗaya da rabi Allah ya masa rasuwa. Shi yasa nake son Mustapha domin shi ya ɗauko halinsa, yanzu dai bar abincin nan zo ki kira mini shi."
Ai dama tasan ba wani abu zata yi ba, matuƙar wancan ɗan wahalar yana nan ba zai bar Hajiya haka ba." Duba cikin firji akwai kayan kwaɗayi ɗauka ki zo muje ki kira mini shi. Wata hudu rabona da shi ko 'yar wayar nan baya kira." Hajiya fa Allah mata arziƙi domin duk mazan da suke zagaye da ita babu wanda baya kyautata mata. Sai dai Abbansu Nanah Asma'u ya wuce yadda ake tsammani.
Bata buɗe firjin ba, don baya gabanta abin da Hajiya tace ta ɗauka. Parlourn suka dawo ta miƙa mata wayarta. "Kira mini shi." Kallon agogon wayar tayi karfe uku saura. Tasan yanzu yana filin wasa, "Takwara ba dai mugun hali kika koya ba?" Girgiza kai tayi tana kallon wayar, number ta duba ta gani a hankali ta rubuta mishi sakon.
*_'Uhmm idan ka ga sakon nan Hajiya ke son magana da kai'_* tana turawa ta mika mata tare da mikewa ta ce mata. "Zai kira ki!" Sake baki Hajiya tayi tana kallon Naanah Asma'u. "Ban gane ba an yi gabar da kare, shi yasa zai kira ni?" Diriricewa ta yi domin ita a rayuwarta tsawa ko sababi yanzu take juya mata kai.
"Zai kira na tura mishi sako ne!"
Ta faɗa muryanta na rawa.
"Ai wo!" Fita a parlourn Nanah Asma'u ta yi tana ajiyar zuciya, nufar ɓangarensu ta yi ta wannan lungun babu kowa a wurin. Tana isa ta samu Khamilah tana aiki.
A gurguje ta shiga ta yi sallah azhar da ya kwace mata, tana idarwa bata motsa ba aka kira asr, miƙewa ta yi ta ɗaura akan azhar, tana idarwa kamar wayarta tasan da haka ta fara ƙarar niman agaji.
Tasan a wannan lokacin shi zai kirata shi yasa daga number room mate ɗinta, sai number Ya Moud, sai na Maamah da Abba Babba. Shi ne number wayarta, ita kanta wayar tecno ce mai torch, tafi shekara biyu zuwa uku a hannunta. Gata ta sha azaba da jin jiki amma haka take manejin kayanta, bata da dogon buri ko son abubuwan da 'yan matan yanzu suke yi yarinyar ta saka ranta ita kaza take so, Nanah Asma'u bata da wannan halin ko don ta taso inda kome za a musu a ɓoye ɓoye kamar marasa gaskiya yasa bata saka idanun akan kome na rayuwar wasu ba.
"Hmm!" Aka faɗa mata a wayar, lumshe idanunta tayi ta buɗe ta ce mishi. "Uhmm!" Sautin murmushinsa yasa ta ɓoye kanta a saman gadonsu.
Daga can ya san abin da take yi ba mamaki ta kifa kanta a gado ko a pillow.
"Asma!" Ya faɗa da hunky voice ɗinsa. Daura hannunta ta yi a ƙeyarta ta ce. "Hmm!"
Shima daga can ya ce mata. "Uhm!" Idan za su shekara suna waya tow wannan ita ce yarensu, idan zai zo kuwa su hadu tow wannan shine hirarsu.
"Naan!" Ya kira sunanta can ƙasan maƙoshinsa.
"Hm!" Ta ce mishi, tana me ƙara ƙanƙame wayar kamar wani zai fisge a hannunta, shiru ya yi kamar wanda ruwa ya cinye shi, tana jin sautin numfashinsa da yake sauƙa akan wayar, kafin ya ƙara da cewa.
"Ba zaki bani suna ba?" Ya tambaya tare da yaƙinin yau za ta bashi sunan da ya dace da shi, after many years yana jiran sunan da zata bashi, muryanshi a sanyayye.
Buɗe idanunta ta yi tana kallon ƙofar ɗakinsu ba kowa amma za a iya shigowa da sauri ta miƙe tare da rufe ƙofar, ta jingina da ƙofar a hankali take zamewa a ƙasa har ta zauna dabas. "Ba ki ji ba ne?" Ya kuma tambayarta.
"Hm!" Ta furta.
"Mmn!" Ya fada. wannan yaren kuramen su biyu suka san shi, murmushi ta yi har yana jin yadda ta ɗan sake sauti shi ma murmushin ya yi yana jin yadda ta sauƙe numfashi da ɗan ƙarfi.
"Asma!" Ya kira sunanta a can ƙasa kasa.
"Hm!" Ta ce mishi, yadda take wannan hmm da hmm, tana masifar driving ɗinsa izuwa wani part na daban, nauyin da yake ji a kirjinsa yana ƙara yawa, duk da baya gabanta yasan yadda take cike da matsanancin kunya domin yasan tana takure wuri guda bazata ta ji muryar shi "Ki gayawa Abba Babba zan fito!"
Buɗe idanunta ta yi cike da mamaki da wani irin abu da ya daki zuciyarta irin abu ya zo maka ba zato ba tsammanin nan kamar yana gabanta da sauri ta kashe wayar, tana dafe ƙirjinta.
Wayarce ta ƙara yin kuka ta kalli wayar kamar wacce ta ga abin tsoro, katse kiran ya yi wani ya kara shigowa dai-dai shigowar Mairo da ta turo ƙofar ɗakin da ƙarfi domin bata san cewa Naanah Asma'u ce a bakin kofar ba. Sai da ta shigo dakin ta ganta a gaban kofar.
"Didih ke ce a ƙofar dakin?"
Wayar ce ta yi ƙara ta kalli wayar da wutsiyar idanunta, sannan ta ɗauke kai kamar bata san da shi ba. Tasan tun da ta takalo shi, dole ne ta amsa amma ita bata iya magana da shi a gaban kowa. Mairoh tasan cewa matuƙar tana ɗakin ba zata taɓa kula wayar ba, don tsokana irin nata ta ce mata.
"Didih kamar kiranki ake?"
Bata amsa mata ba, asalima share wayar tayi tana me nade abin sallah da tayi. "Bari na dauka to naji waye haka ya samu damar saye zuciyar Didih da ta rufe kofar ta hana kowa shigowa!" Ta kai hannu zata taɓa wayar tayi maza ta make hannunta, tana ƙoƙarin haɗe rai amma murmushin da Mairoh take mata ya hanata yin katabus.
"Wash Allah hannuna!" Sake abin sallah ta yi tana cewa "Ya ilahi sannu, mu gani sannu, mu gani kin ji!"
Murmushin tsokana Mairo ta yi mata tare da maƙala mata wayar a kunne tana faɗin. "Ya Almu ne fa!" Ƙurawa Mairoh idanu ta yi tana son ta yi magana amma kalaman Ya Almu ya kashe mata jiki, zubewa ta yi akan gadon tana mai daukar pillow ta rufe fuskarta tana jin wani irin abu yana yawo a jikinta. A duniyar Mairoh tana son soyayya tana son kalar soyayyar Ya Almu da Nanah Asma'u, tana son irin soyayyarsu ta kurame. A hankali ta san magana take amma ba zata taɓa yin yadda zaka ji sautin Muryarta ba, jan stool ta yi ta zauna tana kallon su. Wani irin tausayinsu take ji, domin tasan su waye Familynsu. Bai zama dole a raya soyayyarsu ba, shafa kanta ta yi idan ta tuna bangaren Maamah ita ma tana ganin Didih ta amshi soyayyar Ya Moud shi ne babban arzikin Didih yadda babu me mata gori, babu me wulaƙantata. Babu me cin zarafinta. Za su sota sama da dangin Mahaifinsu.
Tana zaune a ɗakin har Faɗime ta shigo ta same ta da ci. "Maamah ta ce me kike yi da baki fito ba?"
"Shine za ki tsaya a gabana ƙerere kamar wata bishiya dalla ware gani nan zuwa." Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Cire wayar Naanah Asma'u tayi a kunnenta.
"Didih wai in ji Maamah azumi kike?"
Shi ne saƙon da ya kawo ta amma ta ƙare a kallon soyayya.
Miƙewa tayi da sauri tana cewa "Sai an jima!" Ta kashe wayar tana me kallon Mairoh cikin 'yar ƙaramar faɗa ta ce mata. "Dama shi ne baki gaya mini ba?"
Taɓe baki ta yi irin na lallai ma "Didih soyayya na samu kina yi da Ya Almu!"
Riƙo kunnenta ta yi "Bakya ji!"
"Sakar min kunne kada ki tsinka, dama Abba Babba yace mini ni ce akuya ba kunne!" Ta faɗa tana murmushi.
Parlourn suka fito an zuba abincin a tire Khamilah da Maamah sun fara ci sai Faɗime da take jiran su. "Afwa Maamah na samu tana sallah ne."
"Kai Addah Mairoh tana waya ne fa!" Kallonsu Maamah ta yi ta ga Naanah Asma'u ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta.
"Ku ci!"
Ba musu suka fara ci a hankali, hankalin Maamah yana kan Nanah Asma'u wacce take juya cokali a cikin abincin maganar Ya Almu na yana son ya turo ke ta kai kawo a zuciyarta.
"Uwata ya dai?"
Ɗago kai ta yi tana murmushi ta ce mata. "Babu komai!" Ta fara cin abincin tana cire ɗanyen albasar da aka yanka a cikin abincin.
Har yanzu da girmanta bata daina wannan tsince-tsince ba, kodayake a jinin yaran gidan yake tun Almustapha yana yaro shi da Adam idan suka zo cin abinci kusan haka suke suna ta cire abin da ransu baya so, ta ɗauka tsirfa ce irin ta yara maza, amma bayan ta haifi Naanah Asma'u ita ma ta biyo bayan 'yan uwanta, komai na mazan Nanah Asma'u ita ma ta ɗauka.
Duk abin da Almu zai yi Adam zai yi haka ita ma zata yi. Ɗaago kai ta yi suka haɗa ido da Maamah. Murmushin nutsuwa ya ƙwacewa Maamah din saboda ganin Naanah Asma'u s cikinsu kamar wata rahama ce. A duk lokacin da ta kalli Yarinyar bata iya ɓoye ranar da ta aka mata albirshi din cikinta ba. Bata manta ranar da Naanah Asma'u ta fara motsi a cikinta ba. Akan ce iyaye suna ɓoye soyayyar yaransu amma Maamah bata ɓoye soyayyar Nanah Asma'u a gaban kowa. Ko don irin rayuwar da suka yi a baya. Murmushin ita ma Nanah Asma'u ta yi tana mai cin abincin sosai domin ta lura Maamah ita ma ba wani abincin take ci ba matuƙar bata ci sosai ba, kusan a tare suka cire hannu a cikin abincin
.
"Alhamdulillahi!" Maamah ta faɗa tana miƙewa, ita ma Naanah Asma'u ta miƙe tana bin bayan Maamah. Kitchen ɗin da yake parlourn Maamh ta shiga ita ma ta biyo bayanta, tsayuwa ta yi a hankali ta ce "Maamah baki ci abincin ba fa?"
"Ai cikina da naku yanzu ba ɗaya ba ne, sannan ko don lafiyata dole na kula da abin da nake ci!"
Gyaɗa kai ta yi tana kallon yadda take wanke hannunta amsar kofin ta yi tana zuba mata ruwan.
"Saura wata nawa ki gama makarantar?"
Da mamaki take kalli Maamah."Saura wata shekara uku." Yadda ta yi maganar a ɗan takaice.
"Allah ya rufa asiri. Kun daidaita da Mahmoud.....