MATAR MUSA

Chapter 1: Ranar Da Komai Ya Canja

by @maryamusman144

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ranar Da Komai Ya Canja S

Chapter 1:

Da farko ina godiya ga Allah, mai kaddara, mai kome

Sunana Maryam. 'Yar  gida ce mai daraja a birnin Kano dake unguwar hotoro

Rayuwata ta kasance mai sauki. Makaranta, gida, ibada.

Har sai ranar da kaddara ta rubuta wani abu

daban a gare ni.

Wata safiyar, juma'a Ina kwance a gida saiga kiran babbar yayar mu safiya ta kirani take tambayata kina gida kuma nace mata eh ina gida mai ya faru tace please Kizo gidana Yanxu su yaya fahad ne sukazo shida abokinsa shine nakeso zan turo miki kudi a account dinki ki siyi musu ruwa me sanyi dan Allah nace okay ganin zuwa gidan zan siyo na kawo miki ban jima da gama wayar ba na tashi naje na siyo na tafi unguwar makasa a kofar gidan me napef ya sauke ni na bashi kudinsa na shiga gidan shigowa ta palo na tarar dasu yaya fahad a zaune sunata shira da maman khalil muka gaisa dazu yaya fahad harda abokin sa Dan ringim bayan na fita anan abokin yaya fahad yake cewa maman khalil wannan kanwar taku ta burgeni da ba ayi mata miji ba da Kun bani ita Ina sonta da gaske……

Tofa anan rayuwar Maryam ta fara sauyawa

Ku biyoni kuji yadda labarin matar musa zai kasan ce masoyana?