BUDURWAR ZUCIYA

9-10

by @zahrasurbajo

Itako zee tunda ta ƙaraso gabanshi take ta wani iyayi ita ala dole ga cikakkiyar budurwa.

Ɗan rusunawa tayi ta gaisheshi ya amsa mata fuskarsaɗauke da murmushi dan azuwan farko yarinyar ta gama yimasa.

"abbanmu ne yace inzo kana kirana"tafaɗi tana wasa da mayafinta.

Gyara zama yayi yace"hakane zainab,inaso dama in tambayi raayinkine game dani,shin zaki iya auran rsoho kamata?"yayi tambayar yana kallonta.

Murmushi tayi tace"inde bazaka dinga ɗaukar gulmaba akaina zan iya mana,sabida su nan ƴangidanmu komai se ace musu nayi su kama su yarda ayta yimin faɗa,ni kuma banason hakan"ta faɗi ashagwaɓe tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

Murmushi yayi yace"ni agidana zaki rayune yadda kikeson ki rayu,ba me takura miki dan haka bame kawo munafuncinki in saurareshi kinji ko zainab"cewar Alhaji yana jin daɗin muryar tata.

Ɓata fuska tayi tace"ba zainab ba zee zaka ce,zainab a makarantane"ta bashi amsa ashagwaɓe.

"to zee zan kiyaye kinji ko"cewar abba yana murmushi.

Haka ya ɓata kusan awa guda yana sauraron zee ɗin tana masa soki burutsunta ita azuwan hira take da saurayinta se iyayi take ta bazawa domin shine taɗinta na farko,dan ko samarin sun zo gunta bata fita.

Daze wuce ne ya bata dubu hamsin yace ta sayi kayan kwalliya,tai masa kwalliya in ze sake dawowa,daga nan ya bata numbarshi,asa awayar hannunta dan tana da waya da aka siya mata sanda zata shiga ss2.

Kiran numbar tayi shima yasamu tata,sunanan tare ya kira numbar maman nura kan ta fito su wuce,ayko maman nura tai sallama da umman zee ɗin maryam ta rakota har motar dan taga waye sirikin nasu.

Ay tunda taga tsohonevtake dariya aciki ciki,haka sukai musu sallama yaja motar suka wuce su sukuma su maryam suka wuce cikin gida,ay tunda suka shiga gida maryam ke mata dariya harda kwanciya aƙasa,

"amaryar tsoho me capacity,hajiya zee,ay dama me iya zama dake ay sede tsofaffin"cewar maryam tana dariya.

"eh naji ɗin kuma wallahi kome zakice sena aureshi,duk da tsufan nashi,ay yafi wasu samarin da yawa tunda kaf samarinki ba,wanda ya taɓa zuwa ya baki koda dubu gomace sede ƙarya,nifa zuwan farko ma dubu hamsin ya bani n sayi kayan kwalliya"cewar zee tana zaro kuɗin tana yin fifita dasu gamida yin wani juyi agaban maryam ɗin.

Bakin maryam mutuwa yayi dan gaskiya zee ɗin ta faɗi dan duk samarinta ba wanda ya taɓa bata koda dubu biyarce.Se gashi ƙanwarta ta anbata.

Ummansuce tasako baki a maganar tasu"au zee sabida rashin hankali shine har ya baki kuɗi kikasa hannu kika karɓa?"cewar umman tasu cikin faɗa.

Turo bai gaba tayi tace ashagwaɓe"to ba mijin dazan aura bane,kuma ay kayan kwalliya yace in siya,in de kuma ba haushi kike taya maryam jiba dan anban"cewar zee tana kauda kanta gefe.

"zakici gidanku zee uban waye ke miki haushin an baki kuɗi,wallahi zan darfashe miki bakin rashin kunyar nan kinde ji na faɗa miki"cewar ummansu tana nunata da yatsa.

"umma ay kibarta kawai ia gidan kushiyoyi zata shiga,wallahi muna nan zasu seta mana ita acan gidan tunda ay in tayi anan an barta acan ubanta zasu ci"cewar maryam tana watsawa zee ɗin harara.

Ficewa tayi afalon ta wuce ɗakinsu ta haye kaifarta ta kunna waƙar gwanja a wayarta me take Allah ke sonmu bada bamba da se sun karmu.Tana bin waƙar abunta hankalinta kwance dan ta gama lissafa ƴan gidansu sontane basa yi.

************

Tun daga ranar Alhaji seya kwashe awa biyu yana waya da zee ɗinshi,in zeje aɗi kuwa seya mata shopping na kayan kwaɗayi masu yawan gaske,wanda yawan kyautar da yake mata ne yasa zee jin tana sonshi har cikin ranta kuma in yazo taɗi in tana bashi labarin wata katoɓarar da ta aykata goya mata baya yake yi be taɓa nuna mata wai itace bata da gaskia biye mata yake yadda take so.

Itako maryam tunda taga irin kulawar da Alhaji mahadi keba zee tun kan ayi auran hankalinta ya tashi taji ta kamu da son shi,sabida ta gama lissafi ta hangi zee zata huta agidan nashi,wanda ita samarina kaf daga me achaɓa,se masu napep,wanda kusan dukansu ba nasu banema haya sukeyi,shiyasa basa iya tsinana mata komai.

Kullum da wannan damuwar take kwana take tashi aranta ta rasa wa zata faɗawa halin da take ciki.

Ana saura sati guda biki aka kawo lefen zee akwatina guda talatin wanda babuce kawai babu aciki domin harda key ɗin mota da zinari set uku wanda ba na ƙasa da miliyan goma sha biyar,abinda se wanda ya gani.

Wayyo zee ba abinda ya dameta haka taita tsalle tana murnar ganin kayan ance duka natane,rasa inda zata sa kanta tayi dan murna haka ta kira numbar Alhaji mahadi tana ta masa godiya da yimasa adduon samun ci gaba acikin rayuwarshi,wanda abindake burgeshi da ita kenan yawan yi masa addua da takeyi da yimasa godiya akan komai idan ya bata,wanda su matansa na gida ko abu yay musu ba godi bare nagode gani suke kawai dama ay wajibinsane yay musu.

Duk wannan bidirin da akeyi gidan Alhaji mahadi basu da labarin auran da zeyi,dagashi se maman nurane kawai suke faɗi tashinsu,se manyan abokansa.

"Umma dama inason magana dake sede bansan taya zaki ɗauki maganarba"cewar maryam wacce tun bayan kawo lefen zee ta kwanta rashin lafiya dan lefen ya daketa sosai taji ta ƙara mutuwa akan son auran alhaji mahadin.

"ina jinki maryam wacce maganace?"cewar umma tana kallonta.

"dama akan auran zee da Alhajin nanne umma,ina ganin kamar zaa tafka babban kuskure,idan har aka aura masa zee umma"cewar maryam ɗn cikin damuwa.

"wanne kalan kuskurene kike ganin zamu tafka in an bari ya auri zee ɗin?"cewar umma.

"sabida umma kinga de zee ba hankali garetaba kar taje taitamusu hauka agida wanda aƙarshe ta ja akorota,wallahi umma abinda nake ta tunani kenan"cewar maryam.

"maryam ayba munafurtarsu muka yiba mun faɗa musu halayenta,kuma shi aɗan zamanshi da ita ay ya karanci wasu halayen nata dan haka wannan ba wata matsala bace maryam"cewar umman tasu.

Nsawa maryam tayi tace "da de ni aka bashi umma abar zee ta ƙara wayau da girma kamin aymata aure"cewar maryam ɗin.

"zee sukace suna so maryam"cewar umma.

"to umma ay maman nurace ta zaɓa masa ita bashi yace dole se itanba"cewar maryam hawaye na taruwa a idanunta.

"amma ay kinsan yasha zuwa gurun zee ɗin wanda da bata mishiba ay baze yarda ze auretanba har ya kashe irin wannan dukiyar akantaba,dan haka banason wannan maganar in sake jinta abakinki,kowa da ƙaddararsa ki gaggawar korar shaiɗan ɗin dake zuga zuciyarki kan jin haushin niimar data samu ƙanwarki,naga har tsokanarta kikeyi zata auri tsoho,to ina ruwanki da haukar da zataje tayi agidan auran nata"cewar umma cikin faɗa dan ta gane hassadace tasa maryam yin wannan maganar.

Haka tai shuru ranta na mata zafi sabida rashin samun goyon bayan umma da tayi akan ƙudirinta na son yiwa zee ƙwace.