11-12
"hajiya hanne kamarfa sunan alhaji naji ana faɗi a waccan sanarwar ɗaurin auran da,akeyi wanda zaayi gobe"cewar hajiya lami lkacin suna zaune a falo,me aykinsu na jin wani shiri aradion wayarta sukaji ana bada sanarwar ɗaurin auran.
"kai habade ya zaayi alhaji yay aure bamu saniba,kuma n anda abunki shi yanzu alhaji ko kyauta aka bashi mace ya zeyi da ita inde ba BUDURWAR ZUCIYA ba"cewar hajiya hanne.
Hajiya lami zatai magana kenan me sanarwar ta sake rangaɗa guɗa ta sake maimaita sunan angon da amaryar,wanda ba wani tararrabi suka gane alhajinsune zeyi auren.
Salati suke suna sallallami wanda faruwar hakan yay daidai da shigowar alhajin se ƙyallin amarci yake,yaje an masa gyaran fuska da aski sosai yayi kyau abunsa.
"Alhaji da gaske aure zakayi amma baka sanar damuba?"cewar hajiya hanne hankalinta atashe.
"eh aure zanyi me ya faru?"ya basu amsa ba tare da damuwar komaiba.
"kai ko alhaji wacce taɓewace ta sameka tayin aure yanzu awannan shekarun naka,sittin fa kake nema alhaji,mu matanka me muka rageka dashi zaka zaɓi wulaƙantamu irin haka aure sede muji a radiocewar hajiya hanne.
"raayin yin auren gareni,kuma koda shekaruna 80 ne in naso yin aure yin kayana zanyi,dan haka naji daɗi da kuka jiyo batun auran da kunnuwanku, dan an hutashsheni tsayawa yimuku bayanin zanyi auren"cewar Alhajin gamida sa kai yay ficewarsa.
Tagumi kowaccensu tayi ta koma ta zauna sna juyayin maganar aransu.
Hajiya lamice ta nisa tace"wallahi yaya nasan wataƙila irin tsofaffin matan nan zeje ya kwaso mana wanda suka gou da zaman aure,kinga ko zuwa tayi ba wani wayau da zamu gwada mata,bare muyi nasarar korarta"cewar lamin cikin damuwa.
"hmmmm ke naki tunanin kenan lami wanda me sauƙine in iya ita tazo bata shigo da agolaba,kinsani sarai alhaji ve iya son abuba akan agolan da zata zo dashi wallahi ze ia dukan namu ƴaƴan da suke ƴaƴanshi"cewar hajiya hanne.
"amma duk wanda yaba alhaji shawarar ƙara aurannan wallahi ya bashi gurguwar shawara"cewar hajiya lami kamar zatayi kuka.
Haka suka yini zugum zugum abun duniya ya ishesu sun rasa yadda zasuyi da ransu,gashi ƙawatensu se kirans suke ana musu Allah kyauta dan duk anji sanarwar a gidajen radio.
washegari da wuri kamin atafi ɗaurin auran yaje gidan maman nura,bayan sun gaisa taɗan masa barkwanci na angon zee,yana dariya,sannan ya dubeta yace"nifa maman nura tsakani da Allah biki nakeson yi irin na zamani,inaso ɗan hadarin masoyan nan da ake shiga nima duk asakani da zee,duk mawaƙannan de inaso agayyatominsu suzo su waƙeni nida amaryata na shirya kashe ko nawane akan hakan,so nake nima arayuwata in mori wannan lokacin tunda banyi aauran fariba"cewar alhaji mahadi yana murmushi.
"to in banda abunka alhaji ay da wuri yadace ka faɗi se a tsara atsanake,amma yanzu yaune fa ɗaurin auran ay lokacin ya ƙure"cewar maman nura.
"in aka saki kuɗi maman nura duk abinda na lssafa ze yiwu koda a awa guda nace ina so,dan haka zan tua miki miliyan ɗari uku ayi duk abinda ta dace,so nake in kafa tari a aurena da zainab"cewar alhaji.
Ayko de kamar wasa segashi maman nura tabazama neman events planner da sauri,wanda take yanke tai musu bayanin abindacsue so inda suka buƙaci miliyan ɗari da hansin dan gudanar da aykin.
Take yanke ta basu,inda sukaimata alƙawarin kamin magriba zasu kammala komai.
Mawaƙanma haka ta nemosu da ike da kuɗn kamin azahar komai yayi ready.
Tuni taje gidan su zee ta shaida musu batun dinner dan su sani,ay zee ji tayi kamar ta suma dan daɗi dan tana masifar sin dama ace anmata dinner ɗin ashe tana da rabon zaa yi matan.
Itako maryam ranta sosuwa yayi da jin batun dinner,domin tabbacine na cewa alhaji mahadi nason zee tunda gashi ya shirya nunawa duniya ita.
Da azahar dubban mutane suka shaida auran alhaji mahadi da amaryarsa zainab bisa sadakinta naira miliyan guda,wanda aka biya lakadan ba ajalan ba.
Nanfa cikin gida abokan wasa aka shiga tsokanar zee ana ce mata ta zama matar tsoho.
Wata ƙanwarmamantace tace ta hanyar shigarwa zee ɗin"tsoho dakuɗi ay jariri yake komawa,dan haka zee kar ki sake ma cewa mijin naki alhaji ki dunga kiranshi da ɗanshila,tsabar ƙuruciyarsa ke da kike gani,dan Allah ne ya baki dan haka riƙe kayanki miliyan ɗaya sadaki zee ba duk mace ba"cewar anty hauwa tana rungume zee ɗin.
Ayko shewa da dariya gidan ya ɗauka kowa na tofa albarkacin bakinsa,itako zee da shawarar anty hauwan tai amfani shiyasa suka kma gefe ita da ƙawayenta ta kirashi awaya,ƙawayenta na ɗaukarta a waya,yana ɗagawa tace a shagwaɓe"ɗan shilana an ɗaura?"tayi tambayar tana murmushi.
Daga can ɓangaren alhaji dariyace ta kamashi jin sabon sunan da zee ta raɗa masa wai ɗan shila,wani nishaɗine ke ratsa shi ya bata amsa da "eh an ɗaura baby"ayko ƙawayen nata ihu sukasa ana ta rungumeta..
Haka akaita gudanar da taron bikin har zuwa bayan ishai inda aka turo motoci na alfarma suzo su ɗauki amarya da muanenta zuwa gurin dinner.
Amarya zee tayi kyau har ta gaji da yin kyan,sabida dama ita me kyance shiyasa ana gama shiryata kyan nata ya ƙara tsatsowa.
Haka suka ɗunguma inda zaayi dinner wanda tuni angwaye sun halarci gurin taron amaren kawai suke jira.
Haka aka gudanar a wannan dinner wacce tun kan atasi gurin taron taron ya fara trending a social media,sabida alhaji mahadi sanannan mutum ne a faɗin ƙasa shiyasa ko ina yayi boosting.