DUHU BAYAN MURMUSHI

5

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 5.

Sarac Stars R Pen...✍️

A ɓangaren Inna kuwa ta haɗa kayanta da ta ciro ta mayar a jaka, sauran tsarabar ta miƙe ta kai kitchen har da man shanu a ciki soyayye a gora, ta nimo faranti ta baza daddawar ta fito ta shanya a waje sai ta ɗauki maganin Mujaheed ta kai masa ɗaki ta fito tana cewa. 

Mai gidana haka ka ƙara zama Ƙazami.? gaskiya ya kamata a gyara ɗakin nan naka. 

Shi dai bai ce komai ba har ta ɗauki jakan kayanta ta shiga falon da sallama, ta ajesu a gefe ta samu Cushing ta zauna tana wash saboda riƙewar da bayanta yayi, ta zauna tana lissafin rayuwa dan mama bata fito ba balle suyi hira. 

Bayan sallar magariba Inna data idar da Sallah ta cigaba da zama a dadduma a lokacin ne mama ta aiko Nasir da abincinta a cikin langa mai murfi, ya aje mata da ruwa guda ɗaya ya koma tsakar gida, ita kaɗaice a falon yaran duk suna waje kan tabarma, dan bayan sun dawo makaranta sun cire uniform anan suka yada zango har Sallar ma su Zahra anan suka yi, Inna ta buɗe kwanon taga taliya da wake can ƙasan kwano babu yawa, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta saka hannu ta fara ci badan tana so ba sai dan kawar da yunwa, a rayuwarta tafi sabawa da tuwo kullun dare amma da yake baƙunta tazo ba tada zaɓi, haka ta cinye abincin tana lashe yatsu badan ya isheta ba kuma ba tada damar tace a ƙaro dan ta tabbatar tunda aka zuba mata haka to iyaka rabonta kenan, sai ta kora da ruwa ta miƙe ta fito riƙe da kwanon, Aina'u da sauri ta miƙe daga abincin da suke ci ta karɓeta.

Inna da baki taso ba, da kwala min kira kika yi na fito na kai kwanon kitchen.

Aina'u bari na motsa jikina, idan kin gama ki dafa min ruwan wanka ki sirka zan yi In Sha Allah.

Aiko inna ina dafa zoɓo a gas ɗin sai dai inna sauke, ai mantawa nayi tun ɗazu ban dafa miki ba.

Cewar mama da take zaune cikin yaran tana cin abinci, ta sabar musu a babban plate take saka musu su uku Aina'u da Zahra sai ita, mazan kuma ta haɗa musu Harris da Nasir, Mujaheed kuma nashi daban a kwano. Inna tace mata to shikenan kafin ta koma ciki ta cigaba da zama a dadduma har aka kira sallar Isha'i ta gabatar, abun mamaki kayan ta suna nan a inda ta aje su sannan ma koda mama suka shigo ciki bata bi ta kanta ba ta yiwa su Harris shimfiɗa a nan falo da katifarsu daga gefe, sai ta koma cikin ɗaki dan ta shirya tarban baba. Inna data gaji da zama ga babu zancen ruwan wanka sai ta miƙe ta shiga ɗakinsu Zahra ta samu Aina'u bata ciki taje amsa waya a tsakar gida sai Zahra ce ke kwance a nasu katifar, sai ta ɗauki tabarma da aka jingine acan gefe wajen sif ɗin kayansu, ta ɗauko ta shimfiɗa sai ta duba zanin gado a cikin sif wanda duk zuwan da tayi da shi mama take yi mata shimfiɗa, ta dawo ta shimfiɗa a saman tabarman ta fito ta ɗauko jakar kayanta ta sauya kayan jikinta zuwa wata rigar shimi ta baccinta ta ɗaura zani, sai ta ɗauki filon da Aina'u take amfani da shi ta aje ta yada kafaɗa ta kwanta tana mai salati da jin babu daɗi a cikin ranta, duk da ta saba da irin tarban da take samu a gurin mama amma wannan karan yafi ko wanne, tunda gashi wajen kwanciya ma itace ta samarwa kanta saɓanin baya da mama ce ke yi mata duk da baba yace ta riƙa kwanciya a kafitarsu Aina'u dan zata ishe su, amma mama bata taɓa yi mata wannan tayin ba sai dai ta shimfiɗa mata tabarma da sanin gado a ƙasa, haka tayi nisa a cikin tunani sai taji muryar baba ya dawo amma ta lumshe ido kamar mai bacci tana saurarensu. 

Aina'u ce ta shigo falon da ledar da baban ya dawo da ita, ta aje a center table ta wuce ɗakinsu, mama ta fito daga ɗaki tana gyara zaman ɗaurin ɗan kwalinta, baba ya na kallon ta cikin washe baki. 

Iye kaga uwargida kuma amaryar Musa, gaskiya wannan wanka na siye shi. 

Ka dai faɗa a hankali dan yau bamu kaɗai bane a gidan, inna ta zo. 

Mama ta faɗa tana ɗan murmushi a fuskarta, baba ya waro ido waje farin cikinsa yana ƙara ninkuwa akan fuskarsa. 

Kai dan Allah Innata ta zo.? Da yaushe.? Kuma shi ne bata faɗa min ba dan ko ɗazu nayi waya da ita a kasuwa da safe. 

To aiko bazata ta yi maka, dan tana ɗakinsu Aina'u. 

Ta faɗa tana zama tare da jawo center table tana buɗe ledar da baba ya shigo da ita, tsire ne a ciki mai ɗan yawa gashi da ɗumi sai ƙamshi ke tashi, mama ta saki murmushi farin ciki, ta tabbatar baba ya samu wasu kuɗi ne da har yayi wannan tsarabar, shi kuma baba ɗakinsu Aina'u ya shiga ya hango mamanshi kwance a tabarma yace. 

Gaggona sannu da zuwa, Aina'u ko tayi bacci ne.?

Eh ina ga tayi bacci dan yanzu nima na shigo ɗakin.

Aina'u ta faɗa tana gyara kwanciya, sai baba ya juyo zuwa falo. 

Uwale meyasa Inna bata kwanta a katifarsu su Zahra ba.? Ai zata ishe su, bana son kwanciyar ƙasan nan da take yi saboda sanyi kar ya shiga jikinta. 

To kaima banda abunka baban Nasir kasan fa inna tafi son kwanciyar ƙasa, dan ko nace mata ga katifa cewa take yi ciwon jiki yake sakata, shiyasa nake yi mata shimfiɗa anan kamar kullun. 

To ina ganin zan nimo katifa mai tauri na siya mata dan bana son kwanciyar ƙasan nan. Yanzu kawo min abinci naci kafin nayi wanka dan yunwa nake ji sosai. 

Baba ya faɗa yana zama kusa da mama, sai ta miƙe tana cewa. 

To idan ka siyo katifar a ina za a saka.? ka san ɗakin yaran nan matsewa zai yi, sai dai ko a gyara mata ɗakin hatsi ko daga gefe ne asa. 

A'a ba zata zauna ɗakin hatsi ba ta riƙa fama da cizon kwari, nan ɗakin nasu dai zata zauna in safiya tayi a ɗaga katifar, ba shikanen ba. 

To hakane kuma, Allah ya ƙara rufa asiri da sutura. 

Cewar mama dan ƙara samun gurbi a zuciyar baba, wanda kuma har cikin ranta tana addu'ar kar Allah ya bashi damar siyar wannan katifar dan kar inna ta samu wajen zama ta miƙe ƙafa, dole ma zata yi duk abunda ya dace dan ta koma akan kari. Haka ta gama saƙe saƙenta ta dawo riƙe da tiren abincinsa da kula akai da ruwa da kunun zaƙi data yi musu ɗazun, wanda ƙiri-ƙiri ta kasa bawa inna saboda son zuciya, ba ƙaramin kyashin zuwanta take yi ba saboda a ganinta tana takura musu, shiyasa kwata-kwata ita bata zuwa Katsina sai in babban dalili ko baba ya matsa shi ne take zuwa. Ta aje masa a center table ya buɗe kular ya fara ci ita kuma ta zauna ta fara cirewa yara tsiren a gefe tana cewa zata basu da safe. 

To kuwa ki ware wa inna nata itama ta karya da shi da safe. 

Baba ya faɗa yana taunar abincin daya saka a baki, to tace masa dan baya karya wuya amma har cikin ranta ta ayyana ba zata aje mata ba tunda bada ita ya siyo ba sai dawowa yayi ya samu tazo, ta gama rabo ta ƙulle sauran a ledar ta sakawa baba nashi ta soma cin nata data saka amurfin kula, suka cigaba da hira sama-sama wanda duk zancen auren Aina'u ne mama take yi masa. Baba yace cikin farin ciki. 

Kinga kuwa tunda inna tazo sai na faɗa mata na huta da zuwa Katsina, ina ganin ma sai ta zauna har lokacin biki yayi kafin ta koma. 

Banda abunda babansu sai a zaunar da ita haka kurum har na wani lokaci, ai tafi sabawa da zaman can sannan ma ba tana sana'ar ta na siye da siyarwa ba.? Kawai sai a durƙusar mata da kasuwanci ta dalilin wani aure, a'a.! zai fi ta koma in biki yayi gab sai ta dawo dan kar mu takura ta, kasan inna bata cika so ta daɗe ba dan bata wuce sati take komawa. 

Hakane amma ni zan so ta zauna tunda bada nisa za a saka bikin ba. 

To sai ka tuntuɓe ta kaji dan kar ka tauyeta. 

Ta faɗa tana miƙewa dan zuwa sirka masa ruwan wanka. Haka ya kammala cin abinci ya wuce zuwa ɗakinsu. Inna duk tana jin hirarsu bata yi bacci ba kawai dai zuciyar ta ce babu daɗi shi ne yasa taƙi nuna alamar a farke take, idanunta suka kawo kwalla yadda ƙiri-ƙiri Uwale take amfani da kissa wajen sakawa baba magana a baki, ta tabbatar bata ƙaunar zuwan da take yi musu, duk da idan tazo garin tana son ta zauna cikin jikokinta ta kwana biyu amma irin halayyar da mama ke nuna mata yasa bata iya jure zaman take komawa cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ashe auren Aina'u za ayi, shi ne suka ƙi sanar da ita, ta tabbatar Mama ita ce ke juya akalar baba yadda take so cikin wannan hikimar nata da kissa, tunda tasan Musa tsayayyen namiji ne bayi da wasa sai dai kuma ya haɗu da makirar mace mai juya akalarsa da salo cikin ruwan sanyi, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta soma karanta addu'ar bacci ko zata samu ya ɗauke ta, jikinta yayi mata nauyi taso tayi wanka amma ƙiri-ƙiri Uwale taƙi bata damar haka, gashi taso ta yiwa Mujaheed hayaƙi shima bata san yadda zata samu garwashi ba tunda mama taƙi bada fuska, bayan ta kammala addu'a ta gyara kwanciyar ta zuwa dama ta cigaba da karanta wasiƙar jaki har baccin gaske ya ɗauke ta. 

Mujaheed kuwa tun daya dawo bai fita ba yana ɗakinsa yana har haɗa kayan daya tsinto, tare da kwance na kwance wa, kuma cikin hikima ya harhaɗa wasu igiyoyin dake cikin tocilar ɗin nan wanda cikin ikon Allah ya kunna haske ya bayyana, da karambani ya gyara shi, a lokacin ne baba ya dawo amma jin be nime shi ba sai ya cigaba da zama yana murnan hasken tocilar daya gyara, sai sakin murmushi yake shi kaɗai yana cigaba da kunnata yana kashewa cike da tsantsar farin ciki. Yana jin yunwa amma murnar da yake ciki ya danne shi, kuma mama tasan yana gidan amma bata aika masa da abinci ba a cewarta in yaji yunwa zai fito ya nima, kuma Aina'u ma bata san yana nan ba haka sauran ƙannen nasa, shiyasa bata je ta kai masa ba. 

****

Safiyya.

A motar yaya Ali suka dawo gida dama ya barta a parking lot dake nan train station ɗin, yana aje motar a ƙofar gida Safiyya ta riga kowa fita ta shige ciki da mugun gudu, tayi sa'a mama tana tsakar gidan tana gyara ganyen latas da zasu ci abincin dare da shi, Safiyya ta faɗa jikinta ta rushe da kuka.

Mamanmu na dawo amma ina tsoron kar Allah ya jarabce ni akan sakin dana nima a gurin Jabir.

In Sha Allah Allah ba zai jarabceki ba domin kina akan Gaskiya ne, mafita kika nimarwa kanki bisa alkhairi ga rayuwarki.

Cewar mama tana buga bayanta. Su Anty Indo da suka shigo gidan ta taɓe baki.

Wlh Safiyya baki isa ki dawo kina ɗagawa mutane hankali ba in kina son mijinki gwara tun wuri ki koma gidanki, ni sam banga abun kuka ba tunda maslaha kika samarwa kanki.

Haba Anty Indo meyasa ba zaki yi min uzuri ba, saki fa ba ƙaramin abu bane kuma dole zan damu tunda ba zaman ƙiyayya nayi da Jabir ba ƙaddara ce ta raba mu. Mama ki faɗa mata ta daina yi min zancen komawa.

Ta ƙare maganar tana tashi daga jikin mama ta wuce fuuu kamar guguwa zuwa ɗaki, Anty Indo ta yunƙura zata yi magana mama ta daga mata hannu.

Idan kina yi mata haka zaki zubar da girmanki ne, ki rarrasheta idan ba zaki iya ba zai fi kiyi shuru. Mama ƙarama sannunku da ƙoƙari Allah ya saka da alkhairi, Hindatu sannu da hanya kun sha fama.

Mama ta ƙare maganar ga su mama ƙarama. Nan dai suka gaggaisa suka shiga mayar da magana, yaya Ali da shigowarsa kenan ya gaisa da mama ya ɗaura da cewa.

Baffanmu fa.?

Ya fita zuwa cikin gari.

To mu zamu wuce gida sai zuwa safiya In Allah ya kamu, dan wlh a gajiye nake.

To batun kayan fa in mota ta ƙaraso.?

Gidana zasu wuce da shi su zuba a wannan ɗakin da yake tsakar gida, kun ga komai yana buƙatar sirri.

Cewar Ali, mama tace.

Hakane amma ai yau da gobe ƙaryata boka dole za a fahimci aure ya mutu tunda ba zama zata yi ba, tana gama Idda da miji ya fito zata yi aurenta.

A'a mama babba a barta ta samu natsuwa zuciyarta ta huta. Hindatu mu huta gajiya lafiya bari naje na watsa ruwa.

Daga haka mama ƙarama ta wuce, su Hindatu ma suka yi musu sallama suka tafi, Anty Indo ma ta wuce sashin mama, Hafsa ta fito daga ɗakinsu ta karɓi yankar latas ɗin sai mama ta wuce ɗaki tabi bayan Indo. Safiyya tana kwance a gadon mama tayi ɗai-ɗai tana mayar da numfashi.

Wannan kwanciyar ba naki bane ki tashi ki je kiyi wanka ki samu ƙarfi a jikinki.

Ai mama abinci ya dace ta fara ci dan zan ce rabon ta da abinci ƙila tun jiya, ɗazun munyi iya yinmu amma taƙi cin abincin da muka dafa a gidanta.

Anty nafa sha tea da safe.

Cewar Safiyya cikin sanyin murya, mama ta zauna gefen gadon.

To tea abinci ne.? Me kike so a dafa miki sai na saka Hafsa ta shiga kitchen, in kuma zaki ci shinkafa da mai da yaji to sai a zibo miki.

Zanci amma bari nayi wanka.

To gwara dai ki saki ranki kiyi addu'a akan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi. Mutuwar aure ba akan ki ne farko ba kuma ba zai zama ƙarshe akan ki ba, sannan ke naki da dalili a yau idan Jabiru ya dawo yace ya sauya muma zamu mara miki baya ki koma.

Mamanmu Jabir ba zai taɓa sauya wa ba dan yayi nisa da wannan tunanin nashi na ya hudanci, da zai sauya da ƙila ma baku san halin da muke ciki ba.

To Allah ya kyauta. Mama nima zan wuce sai an kwana biyu zan zo In Sha Allah

Cewar Indo, mama ta miƙe.

Na ɗauka kwana za ki yi ai, to bari a zubo miki abinci ki ci kafin ki wuce.

To mamanmu gani nayi tunda mun dawo babu amfanin kwanan duk da yaran suna gidan maman Hashimu amma ɗazun munyi waya yasan mun dawo ma.

To gwara ki tafi din Allah ya huce gajiya, bari na zuba miki abinci a kula ki tafi dashi kya huta girki.

Wlh mama kin ko taimaka mini.

Cewar Indo tana murmushi, sai suka fice tare da Mama, Safiyya kuma ta miƙe ta shiga bayin ɗakin mama ta haɗa ruwan wanka ta watsa ruwan kafin daga bisani ta ɗauro alwala ta fito ta wuce ɗakinsu dake nan falon mama ta ɗauko kaya daga jakarta, ta saka sai ta gabatar da sallar la'asar daya samesu a hanya.

***

Jabir

Rahma ce