ZALLAR SHA'AWA...

1-2

by @zahrasurbajo

.........Ko ina in ka duba duhun hadarine in banda rugugi da tsawa,da walƙiya ba abinda kake iya ji.
Ga wata iska me ƙarfi haɗe da feshin ruwan sama,dake yawo asararin samaniya tana barazanar rushe gidajen yaku bayi,gefen wani ruɓaɓɓen gida wanda ke gab da zubewa wata matashiyace rakuɓe agurin wace shekarunta bazasu wuce ashirin da biyarba.
Gefenta ilahirin kayan ɗakintane watse aƙofar gidan,tana nan tsugune in banda kuka ba abinda takeyi,sabida me gidan dasuke hayane yazo yasa aka watso musu kayansu ƙofar gidan ya kulle gidansa,ga shi mijinta be riga ya dawo daga gun aykin da yake zuwa samo musu na abinciba.
Tana nan zaune tana kukan mijinta ya ƙaraso gurin da gudunshi an yasamu labarin an watsar musu da kaya matarshi ma nanan zaune aƙofar gidan shine ya rugo da gudu.
Tana ganinshi ta miƙe da ƙyar sakamakon tsohon cikin da ke jikinta tana kuka suka rungume juna.
"yaya jameelu kaga abinda Alhaji ɗanharu yay mana ko"cewar matar cikin kuka.
"na gani Aisha kuma Allah na tare damu insha Allahu bazamu wulaƙantaba,kanshi yayiwa"cewar mijin nata yana ƙara rungumeta ajikinshi.
Suna nan tsaye ruwan ya tsuge kamar da bakinnkwarya akansu abun gwanin ban tausayi yana rungume da ita.
Hasken motane ya haske su,basu damuba dan sun ɗauka masu wucewane,motar na zuwa kusa dasu ta faka,muryar na cikin motar ne ya doki kunnuwansu,da sauri suka waiga,doctor munir ne zaune cikin motar.
Jameelu ne ya iya amsa sallamar doctor monir ɗin,amma ita aisha ƙara shigewa jikin mijinta tayi dan bata san me yazo yimusuba.
"jameel inba damuwa ka kamo aisha ku shigo mota kar zazzaɓi ya kamata kuma kaga tsohn cikine da ita"cewar doctor monir yana kallonsu.
"mungode kaje kawai"cewar aisha tana rawar sanyi.
"kuna buƙatar taimako aisha,shine yasa nazo dan in taimaka ɗin be dace ki maida niyyata me kyauba,pls ki shigo mota ruwan yawa yake ƙarawa"cewar doctor monir cikin sigar tausayawa.
"aisha tabbas doctor monir gaskiya ya faɗi muna buƙatar taimako duba da halin da kike ciki,kuma shine ya kamata ace yaji haushinmu duba da abinda ya faru amma duk da haka ya iya zuwa taimaka mana dan haka mu amince kinji"cewar jameelu cikin sigar rarrashi.
Haka badan ranta yasoba ta yarda ta shiga motar,shima jameelu ya shiga doctor,ya kunna motar zasu bar gurin.
"kayanmufa awaje suke"cewar aisha tana nuna kayan.
"karki damu zaa zo akwashe muku"cewar doctor monir.
Tafiyar minti talatinne ta kawosu unguwar GRA,nda tabkeken gidan doctor moneer yake wanda ya gaji da haɗuwa,megadine ya buɗe musu ƙofar suka shiga,inda yaje yay parking aƙodar shiga boyquater ɗin gidan sannan yay musu umarnin su sauko.
Ba musu suka sauko yay musu jagoranci zuwa cikin part ɗin.
Sosai ɓangaren ya haɗu sosai,me ɗauke da falo da ɗakuna guda biyu,se kitchen da toilet kuma akowanne ɗaki.
Bayan sun shigane doctor ya dubesu yace"zaku iya zama anan har iya ƙarshen rayuwarku in har kunaso banida matsala da hakan"cewar doctor.
"Mungode da taimakon da kayi mana amma bazamu iya zama tare dakai agida ɗayaba"cewar aisha kanta aƙasa.
"aisha kidena kallona a matsayin tsohon Saurayinki,wannan abune da ya faru abaya tunda yanzu kinyi auranki,kuma kina zaune lafiya da mijinki,mezesa bazaki mance da alaƙar bayaba,ni tamkar yaya nake agurinki yanzu"cewar doctor monir yana kallonta.
"doctor ba wai mun raina bane,amma de muna jin nauyin faruwar hakanne duba da cewa an hanaka auranta sabida kai me kuɗine aka bani kuma yanzu ace an kiremu gidan haya kai ka bamu gurin zama ay ba ma muba su kansu iyayenmu in sukaji nasan dole kunya zata kamasu"cewar jameelu shima akunyacen.
Murmushi doctor moneer yayi yace yana dafa jameelun"to ni agurina ba komai dama haka Allah ya tsaro bazata zama matataba,dan haka kuma hakan ya dena damunku"cewar doctor.
A ƙarshe tunda sun san basu da gurin zuwa inma sun bar gidanne yasa sukai masa godiya suka zauna.
Ɓangarenshi yaje ya kawo musu kayan sawa in sunyi wanka su sauya.
Godiya sukai masa sosai da fatan alkhairi,sannan yay musu seda safe ya wuce ɓangarenshi,ya turo me aykinsa ya kawo musu abinci.