KING & QUEEN

Alhamdulillah

by @maryamusman144

By 

 

Maryam Usman. 

 

 

Bismillahir Rahmanir Rahim. 

 

Page______1️⃣

 

12b Banana island drive, 

Victoria Island Lagos states 

Villa serenita.


9:00am

A hankali take saukowa daga stairs, yayin da hannayenta masu sanye da wasu kalan high fashion rings masu ɗaukan ido, da kuma tsada,suke kan hannayen stairs ɗin, sanye take da doguwar rigar fara tass ta Companyn _Celine_ A shape, da ta ji adon stones sai ƙyalli suke yi, kanta ɗaure da silk scarf na Companyn _Moschino_ hannunta riƙe da ƴar ƙaramar handbag silver color na _Chanel_ ƙafanta sanye da silver color heels shi ma na _Chanel_sanye da agogon _Givenchy_ sai simple jewelries da ta saka, sai ƙamshin _Vuitton oud_ take yi na LV da kuma _crystal Noir_ na _Versace_ doguwace fara tass don kai tsaye zaka iya kiranta da baturiya, saboda yanayin Idonta da suke green, da kuma gashin kanta mai tsawo da ya fito cikin scarf ɗin ta, wani kyau ne da ita sosai ba ma kaɗan, face ɗin ta shi ake kira da model face, saboda yanda take a haɗe tsap.

Kuma ba wai, cikin ɓacin rai take ba no haka face ɗin yake, irin face ɗin ake kira da resting bitch face, ahankali take saukowa yayinda idan ta taka stair ɗaya sai ya kawo haske, a haka har ta sauka cikin seating room, wanda ya haɗu da wasu irin luxuries, da kuma styling, don irin zubin turawa ne da shi, yanda aka ƙawata palorn da wasu kalan crystals, ga wasu rich expensive furnitures.TV dake palorn kaɗai abun kallo ne, komai ya haɗu tsap, sak zubin turawa, ga wani ƙamshi dake tashi a palorn, mai saka natsuwa, sai ƙaran ac kawai kake ji Tv a kunne yake don akwai mutane a palorn hakan ya saka ta ɗage ƙafafunta yanda heels ɗin ta baza su yi ƙara ba sum sum zata fita,ta ji an ce “Mami, la zia Anaya sta uscendo senza fare colazione (Mami ga Anty anaya nan zata fita bata karya ba).”

Wani yaro da yake zaune nan palor ya na kallon cartoon ya faɗa da ƙarfi cikin yaren Italiya, wata mata ce ta fito daga kitchen riƙe da towel ta na share hannunta tare da ba ma yarinyar side eye "Non abbiamo già parlato del fatto che esci affamata? Non ascolti quando ti si parla, Bella? (Ba mun yi magana akan fita da yunwa da kike yi ba Bella? Baki jin magana koh?)" Matar ta ce cikin yaren Italiya ita ma.

Ɗan fari da ido budurwar ta yi ita ma cikin yaren italiya ta ce “Scusa, Mami Non lo farò più, (ki yi haƙuri Mami ba zan sake ba).” girgiza kai Mami ta yi "Lo so che non cambierai (Na san ba za ki canza ba Bella)." Numfashi yarinyar ta sauke "Na sha coffee da safe." Sai kuma ta kalli agogon hannunta zaro ido ta yi.Da sauri ta ƙarasa in da Mami take tsaye ta yi mata kiss a kumatu sannan ta ƙarasa in da ƙaninta yake zaune shi ma ta yi masa kiss a kumatu tare da jan kumatun wanda sai da ya yi ƙara "Gobe ka sake kai ma Mami gulmana." Ta ce da turanci sannan ta yi hanyar fita da gudu, har ta na tuntuɓe.

Direct wajen motarta Porche 911 purple color, ta buɗe ya shiga, sannan ta rufe ƙofar, eyeglass ta saka na D&G wanda ya yi rabin face ɗin ta, sai da ta yi warming motar sannan ya fisgeta ta fice daga gidan. 

Ta ɗan daɗe a hanya saboda akwai trafic kafin ta kawo bakin wani building, horn ta yi aka buɗe mata gate ta shiga ta yi parking motar ta ta fito a hankali ta rufe ƙofar, ɗaga kanta ta yi ta na cire glass ba Idonta, ta na kallon rubutun dake kan building ɗin _BellaVita_ wato beautiful life, murmushi fito, wani wajen na mai faɗi, kowa ya na yi ta aikinsa, masu zane wato designers suna yi ta zane, models ɗin ta su na na suna ta rehearsing saboda akwai photo shot da za'a yi.

Duk bata kula su ba ta wuce direct wajen wani table, in da lead designer ɗin ta take saka pin a wani kaya da ta saka ma mannequins  (ƴar babin nan da teloli ke saka ma kaya don a gwada ɗinki).

 

"Waƴan nan kalolin baza su fito a cikin rana ba." Ta ce ta na duba yadin da lead designer ɗin take saka ma pin, "Ki canza kalolin, go with something bold and vibrant, I want this collection to be the best collection we ever made, Ina so kowa ya tuna da wannan collection ɗin."

Ɗan shuru designer ɗin ta yi kamar mai jin shakka sai kuma ta ce "Amma miss Anaya, abun zai yi...." "Zai yi me?" Ta kasteta "Kada ki damu just adjust it, babu abun da zai faru." Gyada kai designer ɗin ta yi "Ok." "Good."Anaya ta ce ta na ƙarawa gaba ta na duba aikin da sauran ke yi, every movement every command da take badawa screams I own this place. 

Bayan ta ƙare ta wuce office dinga wanda ya tsaru iya tsaruwa ba kaɗan ba, ya yi wani irin kyau yan da aka ƙawata komai cikin wani kalan elegant purple da kuma white, nan ta shiga aiki aka desktop ɗin ta, ta na tsakar aiki ne landline ɗin ta ya yi ƙara.

Ɗagawa ta yi daga can secretary dinta ta ce mata ta yi baƙo "Let him in." Ta ce ta na cigaba da aikin da take yi, for some secs aka shigo office ɗin, wani mutumi, da zai kai 37_38 ya shigo sanye da captan da kuma hula irin ta yarbawa.

Ƙarasawa ya yi ya zauna, ɗago kai ta yi daga desktop ɗin ta ta kallesa "Good morning miss Anaya." Ya ce a hankali "Sunana Abdullateef, Adebayo, I've been reviewing ur works and they are very interesting." 

Bata ce komai ba tsawo lokaci ta na kallonsa kamar mai karantar sa sannan ta ce "Good morning Mr Abdullateef, I hope u see more than just the pictures,, this brand, isn't about impact it's about, impact innovation and vision."

Ɗan murmushi Mr Abdullateef ya yi, ita ta sa ni, yanda mutane suke jin sunanta da kuma sunan Empire ɗin ta, su na ɗauka maybe wata ce babba take running wannan Empire ɗin, ganinta ƙarama mai ƙananan shekaru ta na mua'amala da manya mutane da kuma manyan kuɗi, she may be small but she is, Smart kuma ta san kanta, babu wanda zai gaya mata shit ta ɗauka.

"Ina so na zuba hannun jari." Ya ce "Amma ina so in San ya da kike planning scale ɗin ku especially international markets." Komawa ta yi bayan ya na jinginewa ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya "I  scale by staying true to my designs, quality na kaya na da muhimmanci a wajena da kuma yanda muke sarrafa kayan mu wato style, mu ba ma bin yayi, mu ɗin mune ya yi, sannan idan har ka na so ka zuba hannun jari, dole ƙa'idoji na zaka bi not the other way round."

Murmushi Mr Abdullateef ya yi "U r confident." "Not confident." Ta ce a hankali "Focused, my brand isn't just fashion it's a statement, idan har ka na iya bin haka U are welcome, idan kuma ba zaka iya ba akwai brands da yawa a garin Lagos 

Shuru office ɗin ya ɗauka na wani lokaci kafin Mr Abdullateef ɗin ya ce "I like that,mu tattauna akan abun da international market take buƙata." Murmushi ta yi Nana suka cigaba da tattaunawa, ita ɗin ta na da yanda take tafiyar da abubuwan ta cikin sauƙi babu ɗaga murya and su tafi smooth, ita bata ɗaukar raini daga clients ɗin ta, idan kasan U will come and talk shit a wajenta.

Then she will remove that shit out of ur damn head, coz sometimes, she can behave like shit, she's like fire for fire.

Mr Abdullateef na fita daidai wata budurwa na shigowa, ita ma siririyace, doguwa, ba fara ba ce kuma ba baka ba ce, ta na da wani kalan caramel skin, wanda skin ɗin ta iri ɗaya ne from head to toe saboda tsadaddun mayukan da kuma sabulan kayan gashi, da ake zuba masa.Ta na da wani kalan kyau mai natsuwa da ɗaukan hankali, ita ma sanye take cikin nata masterpiece ɗin wato fashion, riga da wando ne ajininta, pallazo da kuma t shirt, wandon maroon rigar kuma milk color sai silk scarf da ta ɗora a kanta maroon and milk ƙafa ta sanye da maroon heels masu tsawo da kyau, sai simple jewelries da ta saka, babu kwalliyan komai a face ɗin ta amma yanda face ɗin yake wani shining da glowing sai ya makantar da kai. 

Murmushi yarinyar ta yi "Our one and only Anaya of BellaVita empire." Murmushi mai kyau Anaya ta  saki, "The one and only friend to the Anaya of BellaVita Empire." Daria suka saki gabaɗayan su budurwar wace suke da Reeyah ta ƙaraso ta zauna, "Milky babe ya kike, ban samu na shigo tun da safe ba i was busy sosai.

 Reeya ta ce cikin harshen turanci "Ni ma ban biya ta wajen ki ba i was hella busy with the new collection prep." Sai kuma ta ɗan matso gaba ta na ɗan marairace fuska "Will u be my model na sabon collection da zan fitar." Da sauri Reeyah ta girgiza kai "Nah ba zan yi ba, sauran models ɗin ki fah? ke fah? Kuma kin fini iyawa since u r professional kin manta koya na yi a wajen ki."

 

Ƙara marairaice wa Anaya ta yi "Pls mana Brownie, don Allah, kin ga sabon collection ɗin is inspired by ur skin color, pls ki taimaka ki yi min kin ji." Ɗan hararanta Reeyah ta yi "Okay na ji." "Thank u my Brownie." Anaya ta ce ta na riƙe hannun Reeyah ɗin.

"Kin yi breakfast." Cewar Reeyah "No ban yi ba, i woke up late today." "Should I ordersomething ko zamu fita mu ci." "Kawai mu yi order anan kin san idan muka fita ba mu san ranar dawowa ba, kuma akwai aiki da yawa yau." "Ok ."Anaya ta ce ta na ɗaukan wayarta ta yi musu order daga nan suka cigaba da magana wanda yawanci akan yanda za su fitar da sabon collection ɗin su suka tattaunawa.

 

Around 5:22 suka fito haraban wajen cikin shirin su na zuwa gida, kowaccen su ta nufi motarta, suka ɗauki hanya, anan cikin Victoria Island suka tsaya a bakin ƙofar wani gida Reeyah ta fito dai dai wani security na fitowa daga gidan amsan card key ɗinta ya yi ita kuma ta nufi motar Anaya dake jiranta. 

Shiga ta yi suka ƙarasa gidan su Anaya ɗin, bayan ta yi parking suka fito suka nufi cikin gidan, su na yin sallama ƙaninta Ahyaan yata so da gudu ya ƙaraso wajen Reeyah buɗe hannu ta yi suka rungume juna "Ya ne mutumin? Baka zo gidan mu ba jiya bayan ka ce zaka zo." Ta faɗa cikin yaren turanci.

Shi ma cikin yaren turanci ya ce "I wanted to come amma dare ya yi, shi ya sa ban zo ba, sorry." Ya ƙarshe ya na marairaice fuska, "No problem ai kai mutumi na ne ba ma faɗa." Ta ce ta na ciro chocolate cikin jaka ta basa "Thanks Brownie." Ya ce ya na kissing kumatunta, ita ma kissing kumatunsa ta yi sannan ya koma in da yake zaune.

Ita dai Anaya sama ta haye, Reeyah kuma ta wuce kitchen ta na ƙwala kiran Mami, ta na shiga suka haɗa ido da Mami, girgiza kai Mami ta yi cikin Yaren turanci mai haɗe da accent na Italiya ta ce "Reeyah har kun dawo." "Umm min dawo." Ta ce ta na ƙarasawa ta rungume Mami, rungumeta back Mami ta yi.

Sakinta ta yi, ta nufi in da aka ajiye snacks da aka gama soyawa yanzu ta ɗauki ɗaya sannan ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa "Mami let me go and freshen up." "Ok." Mami ta faɗa ta na cigaba da abun da take yi ita kuma Reeyah ta fice daga kitchen ɗin ta wuce sama, ɗakin Anaya.Ko da ta shiga Anaya bata cikin ɗakin, ta na toilet, ɗan ƙare ma ɗakin kallo Reeyah ta yi wanda ya ji wasu mahaukatan luxuries, komai na ciki purple ne da golden irin dark purple ɗin nan so dark, and ɗakin ya yi kyau sosai so organized.Rage kayan jikinta ta soma yi kafin Anaya ta fito, zama ta yi kan sofa ta na danna waya Anaya ɗin ta buɗo ƙofar toilet ta leƙo, "Amdone, U can use the bathroom." "Ok." Ta ce ta na miƙewa ta shiga bathroom ɗin. 

Closet ɗin ta Jad ta nufa ta na sanye da dark purple bathrobe, sai da ta fara tsane ruwan jikinta sannan, ta shafe jikinta da tsadaddun creams da lotions, underwears ta saka tare da jawo wasu silk riga da wando dark purple na _Salvatore Ferragamo_ ta saka tare da ɗaure gashin kanta cikin silk purple ribbon sannan ta hula light purple tare da socks, sannan ta feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi

Closet ɗin irin closet ɗin nan ne da ake kira dream closet, like ya tara duk wani abu da ake buƙata, wani kalan large luxury closet ne da ita , komai nata is arranged and organized, abun ka da fashionista, gefen turaruka da ban, gefen accessories ɗin ta ɗan agogo sarƙa ɗan kunne wace tsiya dabam.Gefen dogayen riguna dabam, kayan bacci riga da wanda, jackets takalmi, veils, kai hatta da in da take ajiye purple kayanta daban don ita ta na mugun son purple it's her favorite color, sannan kayanta ta na jerasu ne according to shades ɗin su, kai komai na ta is well arranged and organized. 

Fitowa ta yi daga closet ɗin bayan ta yi arranging duk abun da ta ɓata, akwai masu aiki a gidan su, sai dai ita ta fison kome ta taɓa ta gyara sa bata jira masu aiki, ataƙaice she is obsessed with arranging things. 

Zama ta yi kan sofa ta na duba email ɗin ta ta waya, bata daɗe da zama ba, Reeyah ta fito ita ma ta na sanye da silk riga da wando purple color sai dai ita bata light purple ne da yake kayan Anaya ɗin ta saka.Zama ta yi kan gado ta na lankwasa ƙafafunta ta yi zaman cin tuwo, ita ma wayarta ta shiga dannawa, su na haka aka kira sallah, tashi suka yi kowa ta saka hijab suka nufi wani kebantaccen waje da yake can gefen ɗakin, da yake dukan su sun yi alwala bayan sun yi wanka.

Sallah suka yi bayan sun ƙare suka ɗan yi karatu, har aka yi Isha suka yi Isha sannan suka fito palor don cin dinner, ko da suka fito komai ya zama ready zama suka yi, suka shiga fira kafin iyayensu su ta ƙaraso, su na nan zaune Mami tare da wani dattijo suka sauko, da sauri Ayhan ya miƙe ya nufi wajen a guje ya yi tsalle ya haye jikin dattijon riƙe sa da kyau dattijon ya yi ya na sakin murmushi.

Ayhan ya ce "Good evening Papa." Girgiza kai Papa ya yi "Ni ban iya wannan yaren ba." Ɗan tura baki Ayhaan ya yi cikin Hausar shi da bata fita a hankali ya ce "Ina ....yi...ni Dad." Ya faɗa a rarrabe "Yawwa lafiya qlu, ya kake?" "Lafiya ƙalau nake." "Masha Allah, let's go and eat food." Papa ya ce ya na sauke shi ƙasa.suka yi dinning ɗin in da sa anaya na ganinsa suka shiga gaida shi, da hausa suka gaida shi, in da, Reeyah is very fluent ta iya hausa sosai,Anaya ne bata iya ba, Reeyah ce ta yi musu serving abinci, suka soma ci sai fira suka yi da turanci, da kuma yaren Italiya, don ita ma Reeyah ɗin ta iya yaren sai dai ba sosai ba.

Kallon su kawai Papa ke yi kafin ya ɗan bubbuga table ɗin, "Rule no 1." Ya ce ya na kallonsu sannan ya kalli Anaya ya ce "What's rule number 1." Ɗan tura baki ta yi kafin ta ce "No speaking English and Italia in the house." Jinjina kai ya yi "Only what." "Hausa." Cewar Reeyah ta na yi ma anaya gwalo, kallon Dad Anaya ta yi "Papa ka ga Reeyah koh?" "Ni ban ga komai ba." ya ce ya na ɗauke kansa.

Don sun fi kusa in dai su ne ba'a shiga fadan su koh mutun ya ji kunya, nan dai suka cigaba da cin abinci, bayan sun kammala suka gyara wajen sannan suka koma ɗaki. 

Aiki suka shiga yi na office su na ɗan tattauna yanda abubuwan su zasu kasance, game da sabon collection da za su fitar, sun daɗe su na yi kafin, su canza zuwa kayan bacci bayan sun yi skin care routine ɗinsu suka kwanta.


Maryam Usman pen ✍

Reading chapter "Chapter 1” from "Anaya Hameed"