HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

Hs 60

by @legendspen

Assalamu alaikum warrahmatullah! Yan uwa masoya ya kuke, ya hakurin rashin Bhatool? Ina mai baku hakuri akan hakan, nima ba wai nayi da Niya ba ne tsarin labarin ne a haka, kuma dama babu wamda yake dauwamme kowa ɗan haka ne ya zo ya koma, ya zo ya koma, Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa a cikin Littafinsa mai girma
"Kullu nafsin daikatul maut" (Kowannr mai rai ɗanɗanar mutuwa ne).
Haka nan, Manzon Allah (S.A.W) ya koya mana cewa mu kasance a duniya kamar baƙi.... Rasuwar Bhatool a cikin wannan labari, ba wai ƙeta ba ce ga masoyanta, face ishara ce gare mu duka cewa rayuwa baki ɗaya mai ƙarewa ce, kuma duk abin da yake da mafari, tabbas yana da ƙarshe.
Ina godiya da yadda kuka nuna damuwarku, hakan yana nuna yadda Bhatool ta shiga rayuwarku. Amma ina so ku sani, wani lokacin mutuwa ita ce take ba wa labari ma'ana ta har abada.
Ku ci gaba da kasancewa da ni don jin yadda zamu ƙarashe labarin. 

Naku,
Sayyid Legendspen (Amanar Janafty)

Bayan rasuwar Bhatool, rayuwa ta ci gaba cikin wani irin yanayi na jimami. Jaririyar da aka bari, wadda kowa ya shaida kyakkyawar kamanninta da mahaifiyarta, aka sanya mata suna Bhatool. Yaya Karima ce ta ɗauki nauyin shayar da ita da kulawa da ita tamkar ita ta haife ta. Bayan an yaye Little Bhatool, sai ta koma gidan Ahmad da amaryarsa, inda suka riƙe ta cikin tsantsar gata da ƙauna.

A gefe guda, ganin yadda zama ya kasance ga Umma mahaifiyar Bhatool da kuma yadda zumunci ya ƙara ƙarfi, Mom ta dage wa Dad a kan lallai ya aure Umma. Bayan dogon nazari da tattaunawa, aka ɗaura auren Dad da Umma, wanda hakan ya sa dukkan iyalan suka koma gida ɗaya. Little Bhatool ta zama ƴar kowa; tana hutu a gidan su Mom, tana zama wajen Ahmad, amma zuciyarta gaba ɗaya tana wajen mutum ɗaya ne Mahaifinta.

Senate ya canza gaba ɗaya. Tun ranar da aka rufe Bhatool, Senate ya daina dariya, ya daina yawan magana, ya kuma janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta duniya. Furfura ta fara fito masa a suma da gemu, amma bai taɓa tunanin ƙara aure ba; ya ce Bhatool ɗaya ce a rayuwarsa, kuma ya riga ya kai ta makwancinta. Idan ka ga Senate yana hira, ko yana murmushi, to tabbas yana tare da Little Bhatool ne, wadda yake kira da "Little." Soyayyar dake tsakaninsu ta zarce tunanin mai tunani; tana son mahaifinta fiye da komai, shi ma kuma ita ce rayuwarsa.

SHEKARU GOMA SHA BIYU BAYAN HAKAN

"My mother died to give me life, and my father lived to give me love," Kyakyawar yarinya 'yar shekara goma sha hudu dake zaune a kan babban stage a babban ɗakin taro na alfarma dake ƙasar Amurka (USA), hasken lantarki ya mamaye ko'ina. Taron na musamman ne inda aka gayyato yara daga sassa daban-daban na duniya don su ba da labarai masu taɓa zuciya (Inspirational Stories) yarinyar sanye take da doguwar riga ta alfarma, kamarta ɗaya da marigayiya Bhatool, idanunsu, hancinsu, har zuwa murmushinsu, babu abin da ya bambanta.
Cikin natsuwa da harshen Turanci mai sauƙi da daɗin saurare take magana.Hannunta riƙe da babban littafi mai suna "The Journey of Bhatool Senate." Wanda mahaifinta ya ɗauki tsahon shekaru yana rubutawa.
A cikin taron, a sahun gaba, ga Mom da Dad suna kuka. Umma da Yaya Karima suna share hawaye. Abdul yana zaune da matarsa da yaransu biyu (namiji ɗaya da mace ɗaya mai suna Bhatool). Ahmad ma yana nan da matarsa da ƴarsa mai suna Bhatool. Hatta Jannah da mijinta sun kasa riƙe hawayen su.
A tsakiyar su, ga Senate zaune. Ya tsufa kaɗan, furfura ta bayyana sosai a fuskar sa, amma kwarjininsa na nan. Yana kallon ƴarsa a kan stage, hawaye na zuba a fuskarsa. Yana jin tamkar Bhatool ɗinsa ce take tsaye a wurin take yi masa magana.
Lokacin da Little Bhatool ta kammala labarin ta hanyar cewa, "My mother died to give me life, and my father lived to give me love," dukkan mutanen dakin taron suka miƙe tsaye suna tafi, yayin da kuka ya sarƙe kowa.
Senate ya miƙe ya nufi kan stage ɗin. Yarinyar ta rugo ta faɗa jikinsa, ya rungume ta tsam yana kuka. A daidai wannan lokacin, ya ɗaga kansa sama ya kalli silin ɗin ɗakin, yana jin tamkar yana hango murmushin Bhatool.
"Mun gode Allah, Bhatool. Ga amanarki nan ta zama tauraruwa," ya faɗa a cikin ransa.

"Ni wallahi Allah sai an siya mini." Ta faɗa tana burgima a ƙasa. Tare da fara kuka. "Mama kin mutu kin barni, kin bawa ɗan uwanki amana ta amma yakasa cikawa." Little Bhatool ta faɗa tana kuka, shi kam Abdul da ido yake kallonta, yana tuna yadda Bhatool take kuka tana kiran Mahaifinsu da ya rasu. "Oh Allah! Bhatool ga abinda kika barmin nan." Ya faɗa yana murmushi. 

ALHAMDULILLAH!

Tsokaci. 

Daidai da lokaci ɗaya Little ba ta bar komai na halin mahaifiyarta ba, duk ta kwashe su tana kuma yinsu, haka Abdul da Yaya Karima zasu sa ta a gaba su yi ta kallonta suna jjn dadin abinda take yi. 

Senate ya rasa Bhatool, amma tabbas ba ta tafi duka ba, domin ta bar masa little da take masa dukkam soyayyar da Bhatool take masa, girki, ruwan wanka, taje masa kai, fesa masa turare, har da zaɓar masa kayan da zai sa, indai Little na nan ita ce zata yi masa. Yana jin kamar bai rasa Bhatool ba. 

Mom da Umma zama suke cikin so da mutunta juna, Dad yana ƙoƙari wajen yin adalci a zamansu, amma soyayyar da yake yi wa Umma ta ninka wacca ya yi mata a baya. 

Amrah da Jannah da Suhaima suna rayuwa da rashin Bhatool, amma suna jin Little a ransu kamar su ne suka haife ta, ita ma tana ganinsu kamar sune suka haifeta. 

Haka gidan Ahmad Little ta dauke shi kamae gidansu, idan tana jin rigimarta har nan take zuwa tai ta bori.

Yaya Karima ce Uwar little, nan ta taso ta girma ta yi yawo, baka gane banbanci tsakaninta da 'ya'yan Yaya Karima sai ma babban ɗan Yaya Karima da ya ke son ta, ita ma take son sa, amma Senate yaƙeƙashe ƙasa ya ce, Little Bhatool ɗinshi yarinya ce ba yanzu za ta yi aure ba.
Daidai da rana ɗaya Senate bai taɓa jin sake son wata mace ba, haka babu wanda ya takura masa akan hakan. 

ALHAMDULILLAH!

Wanan shine ƙarshen a labarin Bhatool da Senate, kuskuren da cike ubangiji ya yafe mana, alherin dake ciki ubangiji ya bamu lada baki ɗaya. 

Na gode da bibiyar ku tun daga farko.