Page | 04
HALINSA
©SALMA AHMAD ISAH
Page | 04
A kalla yau suna da cikakken wata biyu da aurensu ita da Umar, a cikin wata biyun, idan aka tambayeta me ta cimma a cikin mission dinta na sauya shi? Za ta amsa da babu, domin kuwa sai a cikin wadannan wata biyun da ta yi tare da shi takenkara gane asalin halinsa da ba ta san da su ba, duk inda take tunani Umar ya wuce nan, ko da yauhe da sabon halin da zai tsirar mata, kuma ba wai yanayi ne ba dalili ba, a'a a hankali ubangiji yake nuna mata shi a asalin kalarsa, a wannan zaman nata fa shi ta fahimci rashin ilimin nasa ya wuce yanda take zato, domin bayan sallah da azumi da za ta ce ba ta taba ganin ya yi ba ballantana ta yi alkalancin azumin nasa, a cikin ibadun ubangiji babu wadda Umar yake yinta yanda ya kamata, kuma yanda aka koyar da mu. Sannan ta zo ta gane cewar shi bai ma san mene ne aure ba, bai san me ake nufi da matarka ta auren sunna ba. Domin ko, ko sau daya bai taba zama ya yi hira da ita ba, bai taba zama ya ji damuwarta ba, ballantana har ya fada mata wani abu a kansa. Domin banda halayensa da Allah yake sawa take discovering a hankali, a hankali, babu abin da ta sani a kansa a matsayinsa na mutum, ko da yaushe dark side dinsa ta fi sani fiye da kyakkyawan.
Yanzu haka, da wuka za ka dora a wuyanta, ba ta san me ya fi so a duniyar nan ba, ba ta san kalar da ya fo so ba, ba ta san abincin da ya fi so ba, ba ta san miye ba ya so ba, ba ta san miye rauninsa ba, abokansa, burikansa na rayuwa, damuwara da kuma farin cikinsa, ba ta san komai a kansa ba face sunansa da dabi'unsa marasa kyau. Shi ma kuma ta tabbatar bai san nata ba, bai san komai a kanta ba sai sunanta da kasancewar wacece ita. Kuma shi ne bai bada damar hakan ba, Allah yana gani ta yi bakin kokarinta domin ganin kusancinsu yawuce na haduwa a shimfida kawai. Amma ta lura shi ba ya gane ko wani yare bayan wannan, saboda garin Allah yana wayewa zai naimi abin karin kumallo, kuma yana cika cikinsa dai-dai karfe takwas zai fice ya bar gidan, ba lalla ta sake ganinsa ba sai da rana, shi ma sai idan Allah yasa shi ne yake da rabon zuwa karban abincin shago, idan kuma wani akaturo daga shagon to ta rasa wannan damar ta ganinsa. Ba za ta saka shi idonta ba sai dare ya yi, daren ma irin karfe tara ko goman nan. Tun a lokacin da ta fahimci ya maida hakan dabi'a a watansu na farko ta yi masa magana a kai, kalar walakancin da ta fuskanta a lokacin ba karami ba ne, dan kuwa ba ta manta ba, ya ma za ayi ta manta? Ce mata fa ya yi "Na zauna na miki uw*r me a gidan? Ke a tunaninki idan na zauna wani sh*gen ne zai ciyar da ke? Bana son iyayi da kinida Wallahi, idan kika sake zuwa mini da maganar banza irin wannan sai na kwasheki da mari!"
A lokacin ma ya yi kamar zai mareta din, ita yanzu ji take ma ba ta da babbar damuwarda ta wuce ya da yake magana, idan ka gan shi a fuska dai kamar mutumin arziki, domin yana da kyau da kamala, ga kuma farar fatar da ta samu asirin kara masa kyau, amma daga zarar ya bude bakinsa ya yi magana, a lokacin za ka gane cewar abin ba haka ba ne. Shi fa rashin iliminsa da wayewarsa tub a maganarsa za ka gane, domin akwai shi da yawan ashar, hatta salon da zai yi maganar bai iya ba. Amma duk rashin kirkin mutum ba zai rasa wani hali na kwarai ba, to shi ma dai Alhamdulillah, domin halinsa biyu da za ta fada na kwarai shi ne ba shi da rowa, ta lura ba ma a kanta ita kadai ba, ga kowa ma ba shi da rowa,ita ma duk abin da tace tana so ba ya kasa a guiwa wurin mallaka mata shi, sannan bai iya karya ba, duk abin da yake zuciyarsa kai tsaye zai fada maka ba tare da wani boye-boye ba. Matsalar da aka samu ita ce, shi bai san ta yanda zai fito ya fadi gaskiyar ba ne, bai san a wata hanya zai fada ta yanda wurin ɗatata ran mai sauraron gaskiyar tasa za a zamu rangwamen ɓacin rai. Amma me? Ita a ganinta, bayan kyaututtuka da faɗar gaskiya tana buƙatar wani abu a wurinsa, wani ƙaramin abu da ya raina, ƙarami sosai, wanda shi ne kulawarsa, lokacinsa, nuna soyayya, tausayi, riritawa, tausasa lafazinsa idan zai mata magana matsawar ba laifi ta yi ba, haƙuri da ita, tun da ita mai rauni ce, ta hanyar yin ƙananan abubuwa, ba tasani ba ko ita kaɗai ce take buƙatar hakan, tun da mata sun kasu kashi-kashi, ba ta sani ba ko akwai wata mace da take son miji mai hali irin na Umar, ita a hakan ma ya mata, amma ita da ba ta taɓa soyayya da kowa a rayuwarta ba sai shi tana buƙatar waɗannan abubuwan, amma ko sau ɗaya a zamansu Umar bai taɓa nata wannan damar ba, har gara hana rantsuwa da ta yi masa waccan maganar ya je ya tambayo ɗin, shi ma sai da ya ga idan ya zo da buƙatarsa tana bijire masa, saboda wahalar da take sha, to fa shi ne kawai abin da ya sauya tun daga farkon zamanau zuwa yanzu, yana kokari ya kamanta ta wannan fannin. Amma bayan nan, ba tace ga sauyin da aka samu a cikin halayensa ba, kullum da kalar abin da yake zuwa da shi, kuma har yanzu ba ta sare da cewa za ta iya sauya shi ba, tana nan a kan bakarta, kafin ta gane cewa, idan mutum ya yi nisa, ba ya jin kira.
Yau ta tashi ba ta jin dadi, haka kawai take jin ciwon kai, kuma ba wai kaɗan ba, wani irin ciwo mai tsanani, hakan yasa ko aikin gidan ba ta iya tashi ta yi ba, tun da ta rarrafa ta masa breakfast ba ta kara amfanuwa ba. Ta kwanta a kan gado tana ta juyi, wayarta dake aje kan side drawer ta tasheta daga dan guntun baccin da ya saceta, ta mika hannunta ta dauka, ganin mahaifiyarta ce yasa ta tashi zaune da kyar, ta daga kiran cike da kewa da kuma farin ciki.
"Antina!"
Ta faɗa da muryar shagwaɓa, irin ta wanda ya ga mai share masa kukansa, daga ɗayan ɓangaren Antin ta amsa, sannan suka gaisa.
"Wai har yau babu wanda ya kawo muku ziyara?"
Anti ta faɗi daga ɗayan ɓangaren, hakan yasa Rahama ta tuna da wani abu da yake damunta kuma, rashin ganin kowa daga ɓangarensa a gidan, domin tun da ta tare a garin, tun daga ƙannensa har dangin mahaifinta babu wanda ya taɓa zuwa gidan, ita ma kuma bayan gidan Iya da ya kaita ko gidansu bai taɓa kaita ba, tun da ta ga sun haura wata ɗaya abin ya fara damunta, da ta ɗauka ko basa son zuwa gidansu saboda suna sabbin ma'aurata ne, amma yanzu ta fara tunanin ba haka abin yake ba.
"Wallahi ba wanda ya zo Anti!"
Anti ta ɗan numfasa.
"Maƙotanki fa? Babu wadda kuke yi da ita?"
Kashedin da ya mata na ba ya son harka da maƙwabtansa ta tuna, domin akwai gidan da yake jikin gidanta, matar gidan babba ce a shekaru, domin za ta iya zama sa'ar Anti, a satinta na uku ta ɗan fita ta shiga gidan suka gaisa da matar a bisa shawarar Anti, domin ta sanar da ita duk rintsi ta tabbatar ta gidan alaƙa mai kyau da maƙwabtanta, domin sun fi kusa da kai fiye da kowa, ciki har da 'yan uwanka, kuma muhimmancinsu ba abin wasa ba ne. Matar mai kirki wadda ta yanke shawarar kiranta da Maman Munif, kasancewar haka ake kiran ɗanta na fari tana da kirki a haka, duk da ba a shaidar mutum ta fuska, amma a yadda ta karɓeta sai ta ga ba ta da wata damuwa, domin a zuwanta na farko kawai sun zauna sun sha hira sosai, kamar sun taɓa haɗuwa, a karo na farko ta ji kaɗaicin da take fama da shi a garin ya ragu a cikin ranta, domin babu abin da za ta bada labari a kan alaƙar aurenta face kaɗaici. Ai ko a ranar shi ma Umar bai yi wata-wata ba wurin dakatar da ita daga zuwa gidan Maman Munif, duk da ita ma ba shawara ta yanke ta yawan zuwa gidan ba, saboda ta san ko Anti ba za ta goya mata bayan yin hakan ba, yawan fita maƙoya ba gaira babu dalili, haka dai once in a while ta yanke za ta riƙa shiga suna gaisawa, ko ta yaƙu kaɗaicin da take fama da shi. To shi ko Oga Umaru cewa ya yi bai yadda ta sake zuwa gidan ba, ba na gidan Maman Munif ba, ba ya so ta yi mu'amala da kowa a unguwar. Haka kawai yace da ita, ba tare da faɗar dalilin hukuncin nasa ba, dan haka ta yi ƙundun bakar ta baya, shi na kuwa, bai yi wata-wata ba wurin maida mata martani mai zafin da har gobe ba ta manta me yace ba, yo ita tana manta maganganunsa ne ma? Ai duk bayani da zai mata a zafafe yake yinsa ta yanda ba za ta taɓa mantawa da shi ba.
"Ya Umar ne yace kada na sake shiga gidan kowa, shi ba ya son mu'amala da su, wai unguwar nan cike take da munafukai"
"Munafukai?"
Anti ta jaddada maganar cikin tambaya.
"Kamar ya munafukai? Wani abin yake ba dai-dai ba da yake tunanin za su iya tona masa asiri io?"
Rahama ta hi shiru, dan ita ma ba ta sani ba.
"To ai ko rayuwa haka ba za ta iyu ba Rahama, zan faɗawa Abbanku, in yaso shi sai masa magana da kansa, yanzu idan ya hanaki yi da maƙotanki ba fara ake ba wani abu mara kyau ya sameki a gidan, kafin ya kawo miki ɗauki su za su fara taimakonki, sannan ko wannan kaɗaicin za ki rage zama da shi!"
Shiru ta yi tana mamakin yanda aka yi Anti ta gane cewa tana cikin kaɗaici, domin ita fa duk wannan tsawon zaman nata a gidan, ko sau ɗaya ba ta taɓa faɗawa wani halin da suke ciki ba, a ganinta yin hakan ya yi wura, kuma za ta iya gyara abinta. Babban kuskuren da mutum zai yi a zamantakewarsa ma shi ne ya sanar da 'yan uwansa wata matsakar spouse ɗinsa, musamman iyaye, domin kai za ka iya mantawa ku shirya, amma fa su za su ci gaba da kallonsa da wannan abu, shi yasa idan dai matsala ba babba ba ce, kuma abu ne mai wucewa, wanda ka san cewa za ka iya magance shi da kanka ba tare da sa hannhn magabatanka ba, gara ka yi hakan da kanka. To matsalar a nan ita ce, Rahama ba ta gane girman Matsakar da take ciki ba, shin ta kai ta sanar a gida? Ko kuma ta riƙe abarta za ta iya maganceta? Ba ta sani ba sam.
"Su kuma 'yan uwansa ba shiru za ki yi ba, tambayar su Muwaddan za ki yi me yasa ba sa zuwa, ko ma miye yake a ƙasa za ki ji"
Ta gyaɗa kai a hankali.
"Baki da lafiya ne?"
"Eh kaina ke ciwo"
Ba ta yi mamakin ta yadda aka yi Antin ya gane hakan ba, domin ta san Anti ta santa fiye da kowa.
"Ki samu ki sha magani, su Mahmud ne za su zo yau, sun yi ta kaɗar hankali zuna so su zo, Abbanku kuma yace sai an yi hutun makaranta, dan haka yau za su zo!"
"Dan Allah Anti?"
Ta faɗa cike da zumuɗi, domin ta ji daɗin wannan labari, ta yi kewar kowa na gida, musamman 'yan ƙannen nata abokan zamanta, kuma abokan faɗanta, dan ba wata jituwa ake ba.
"Anti Rahama na siya miki alawar madara zan taho miki da ita!"
Daga can nesa ta jiyo muryar autansu na faɗar hakan.
"Allah sarki Auta, na gode, da yaushe za su fito?"
"Sun gama shiryawa fa, Abbanku ne yace a tambayeki ko akwai abin da kike so a taho miki da shi, ba dan haka ba sai dai ki gansh kawai"
Ta yi dariya a fili, irin wadda ta manta yaushe rabonta da ta yi. Ai ko zama ta gyara ta lissafa musu, cikin ikon Allah ma fiye da rabin abjn da tace tana ak ɗin tuni Anti ta tanadar mata shi, wasu daga ciki ne Abbansu ya siya mata, suka kamo hanya. Tuni ta yakice ciwon da kanta yake, ta kira Umar a waya ta sanar da shi, yace Allah ya kawosu lafiya, nan da nan ta faɗa kitchen ta musu girkin da za ta tarbesu da shi, har suka iso ba ta kammala ba. Ta ji daɗin zuwansu, domin ta yi kewar ƙannen nata. Sun sha hira sosai, suka ci abinci tare, hakan ya tuna mata da gida, sai da azahar ta yi, sannan suka ce za au je ziyara, idan sun gama za su tarar da Abbansu a gidan Iya, dan yana ajesu suka gaisa da Rahama sai ya wuce gidan Iyan.
"Ko za ki biyomu mu je tare?"
Kaninta da yake binta wato Mahmud ya tambaya.
"Allah ko?"
"Eh mana, kin ga za mu ƙara samun time tare!"
"Kuma haka be, bari na tambayi Ya Umar!"
Ya bita da wani kallo.
"Wai matar aure, oh!"
Ya faɗa cikin raha, ta kai masa duka a kafaɗa tana dariya, ya kauce yana faɗin ba za ta dake shi ba, duk da shi ne ƙarami ya ninkata tsayi sau biyu, ba tsayi kaɗai ba, har girman jiki, dana kuma duk gidansu ita ce baya a girman jiki, ba tsayi ba ƙiba. Cikin ikon Allah bai hanata zuwa ba, saboda ya san 'yan uwanta ne suka zo, cike da zumuɗi ta shirya, domin har ga Allah tana son ditar, rabonta da ta fita tun ranar da suka je suka gaida Iya, sai yau za su fita tare da 'yan uwanta.
Ai ko sun sha yawo, duk da ba jimawa suke a gidajen da suke zuwa ba, kuma 'yan uwan mahaifin nasu sun tara musu kaya sosai, gidan su Umar shi ne na ƙarshe da suka je. Domin Abba yace yana can, ya bar gidan Iya bayan fitowarsu, sanda suka isa gidan matar baban Umar ɗin ta biyu, mahaifiyar ƙannensa biyu ta tarbesu hannu bibbiyu, dama can akwaita da kirki, tun sanda Rahaman take 'yar uwa ga gidan, ballantana yanzu da ta zama 'ya. Sun sha hira sosai a gidan, dan su Khalid fita suka yi suka barsu, ya rage daga ita sai su Muwadda, dan haka tace bari ta yi amfani da wannan damar wurin jin ta bakinsu.
"Muwadda!"
"Na'am Anti Rahama"
"Ni ko na ce me yasa ba ku taɓa zuwa ba? Na yi jajen, na yi har na gaji!"
Nan da nan murmushin da yake kan fuskar Muwaddan ya ɓace ɓat, suka haɗa ido da Husana, cikin zargi Rahama ta kallesu, dan ta tabbata akwai wata a ƙasa.
"Me yasa dan Allah?"
Ta sake tambaya.
"Ai Yaya ne yake kada mu kuskura mu je gidansa!"
Wani irin ƙaran fargaba ta ji a cikinta, wanda ba ta san na miye ba, musamman da ta ɗaga kanta, ta saka idonta cikin na Mahmud da ya ɗaga labulen falon, idonta cikin nasa, domin ta tabbatar da ya ji abin da aka faɗa.
*
UMAR POV.
Yau da wuri ya dawo gidan, musamman da ya san cewa Rahama ba ta nan, sansa ya shigo ana kiran sallahr Magrib, maimkon ya ɗaura alwala ya nufi masallaci, sai kawai ya nufi ɗakinsa domin yin abin da ya kawo shi. Kai tsaye banɗaki ya shiga, ya tura ƙofar, bai damu da ya rufe ba, sabosa ya san Rahama ba ta nan. A kan toilet sit ya zauna, sannan ya sa hannu a aljihubsa ya fito da wani baƙin abu a cikin takarda ya fara muza shi yana jan tsaki.
"Ni da gidana ina abu kanar ɓarawo!"
Ya kai aya yana tuna shawarar abokinsa Mamman.
"Ka san Allah, kar ka bari a farkon aurenka ta san kana harkar nan, idan ta sani daga baya shikenan, amma a farkon aurenka idan ta san kana harkar nan tsaf za ta tona maka asiri, kuma ba za ta sake sa kai ba!"
Ya sake jan tsaki, shi d aina ruwanda wata sakewarta, ko ta sake, ko karbta sake duk ita ya yi wa zafi, shi a ganinsa duk wanni hakki nata yaa sauƙewa, tun da zai bata ci, zai bata sha, zai mata sutura sannan ya sauƙe nauyinta dake kansa, to me ake a auren bayan wannan? Haka nasa ilimin ya nuna masa, domin bai san cewa auren! Da yake jin kalmar haka a bakin mutane, ta ƙunshi abubuwa da dama, wanda ba kowa ke son furtasu ba. Kuma shi dai wannan Mamman ɗin shi ne ƙara ziga zigegen zuciyarsa kan kada ya kuskura yana bata fuska, za ta raina shi, mata akwai raini, dan haka ko da wasa, jada ya kuskura yana wasa da ita. Yayin da ya yi nisa a hutar da kuma samarwa da ƙwaƙwalwarsa abin da take so, hankalinsa na kwanciya kaɗan da kaɗan, bai zata ba, bai yi tsammani ba, kawai ya ji an turo ƙofar bayin, hayaƙin da ya cika banɗakin yasa sam da farko bai ma gane waye ya fito ba, tarin da ta yi cikin muryarta yasa ya gane ita ce. Maimakon hankalinsa ya tashi, tsaki ya yi cikin ƙosawa, dan shi ko a jikinsa dan ta gane cewa yana shaye-shaye. Rahama da ke ta tari sakamakon shaƙar hayaƙin, ta toshe hancinta tana amfani da ɗayan hannunta wurin kaɗe hayaƙin da ya cika bayin, wai ko za ta ga mahaluƙin dake ciki, dan ko kusa ba ta bari zuciyarta ta ce Umar ba ne.
"Waye a cikin bayin nan?"
Ta tambaya sanda ta kutsa kai ciki, a sanda idonta ya yi arangama da abin da ke gabanta, ba ta jin akwai wani abu da ya ƙara motsi a jikinta bayan zuciyarta da ke aikin watsa jini zuwa sassan jikinta, saboda tsabar mamaki, bakinta ya faɗo har ƙasa. Ta kasa gane shin abin da take ganj da gaske ne ko ko dai gamo ta yk a cikin bayin. Bayanta ta zuya gabanta na tsananta wurin faɗuwa ta mitsika idonta har sau biyu, sannan ta juya ta sake kallonsa, fuskar Umar ce tare da aljanin har yanzu, sai dai saɓanin ɗazu da yake zaune, yanzu a tsaye yake yana ci gaba da busa hayaƙinsa. Da ma kar ku tambayeta hawaye, tuni sun fara mata zuba, bakinta na rawa, cikin ƙololuwar mamaki tace.
"Ya Umar!"
Bai amsa ba sai kallonta da yake shi ma, kuma bai fasa abin da yake ba, babu alamar nadamar ganjnsa da ta yi ko ɗaya a idonsa. Wasu hujjoji ta fara tarawa, wanda za ta yi amfani da su wurin kama shi, dama tana yawan jin ƙauri ko warin abu a bayin da kuma kayansa idan tana haɗa kayan wanki, ashe abin da yake yi ke nan. Jikinta na rawa, bakinta na rawa sannan idonta na zubar da hawaye, ta sani cewar ikon Allah ne kaɗai yake riƙe da ita a kan ƙafafunta, amma da tuni ta faɗi. Ba ta daina kallonsa ba har ya ƙare shan abarsa, ya jefar da ita a ƙasa, sannan ya kama hanya zai bar bayin, ta san cewa falo ya nufa, dan haka ta riƙe hannunsa.
"Kar ka fita Ya Umar!"
Wani banzan kallo ya wurga mata, sannan ya ƙwace hannunsa daga riƙon da ta masa, ya ci gaba da tafiyarsa, bisan ta yi a baya, sannan ya sake riƙe shi.
"Dab Allah kar ka fita!"
Ta sake faɗa kukanta na ƙara ƙarfi.
"Kin san Allah idan baki sakeni ba sai na wankeki da mari!"
Ƙaimi ta ƙara wurin riƙe shi, dan ta gwammace ko kasheta zai yi sai dai ya yi, amma ba za ta bari ya fita ba. Ƙwacewa ya hi daga riƙon da ta masa, sannan ya haɗa da mata kashedi.
"Wallahi idan kika sake riƙeni sai na mareki!" Faɗa da kakkausar murya, Yana faɗin hakan ya juya, ita ma ba ta fasa ba, ta ƙara riƙe shi, ai ko yana juyowa, zuciya ta kwashe shi, dan ya je ƙarshe wurin fusata, ga abar da ya sha tana nata ƙaryar ƙarfi, ai da ya taƙarƙara ya kwasheta da mari, sai da ta rasa hawaye a idonta, marin da ya mata yasa hatta yatsunsa sai da suka fito a kan farar fatar fuskarta. Ta ƙame a wurin cike da zallar mamaki, dama zai iya marinta? Ta tambayi kanta a lokacin da ba ta san sanda duk ƙarfin da take riƙe da shi ya suɓuce ba, ya zare jikinsa a nata, sannan ya buɗe ƙofar ya fita, sai dai abin da ya faru shi ne, yana fita ya iske Abba, Mahmud, Amir da Ibrahim tsaye a falon.
_______
Fam! Me kuke tunanin zai biyo baya? Sai ku bini sannu a hankali, wannan shi ne last free page, ga duk mai son ci gaba sai ya tura naira 700 dinsa a kan 5487270431
Salma Isah
Monie point, sai a tura shaidar biya a kan ***
Bye!
#SalmaAhmadIsah
#Candy
#Ammerh
#SM
#Halinsa
#Rahama
#Umar
2026