1
*_BAYA TA HAIHU_*
(True life story)
Na
*RABI'ATU BASHIR ABDULLAHI*
_Ummu Maher(Mrs green) Matar SHU'AIBU_
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*📚
Na sadaukar da wannan littafin ga uwayen É—akina.
Maza
1_Yaya Shamsudden
2_Dadyn dota_
3_Ayuba Muhammad ÆŠan zaki_
Mata
1_Nabiha Aminu_
2_Nabila Dikko_
3_Hassana ÆŠan Larabawa
4_Anty Hauwa shugabar ƙungiyar Arewa WRITER'S
5_Anty Ruƙayya Lawal_
*Doka*
Ban yarda a canza min littafina ta kowacce ba, idan mutum ya yi hakan Allah ya isar min.
*Sharhi*
Wannan littafin ban taɓa kawo muku labari me ban tausayi da ban al'ajabi ba kamar shi, sannan wannan labarin zai faɗakar daku zai kuma nishaɗantar daku musamman darasin da yake cikin labarin ya sha banban da labaran da kuka saba ji, ku dai ku karkaɗe idanuwanku domin karatu sannan ku buɗe kunnuwanku domin sauraro. Taku har kullum Ummu Maher.
*Bismillah_Rahmanir_Rahim*
__________________________
*1*
Aiki muke Sosai yau a gidan yarin, saboda yanayin yawan bishiyoyin gidan yarin sanye muke cikin Uniform ɗin mu ɓangaren da aka ware mana har mun gama. Ƙawaye ne mu sosai tun bayan shigowarmu gidan yarin yau wata 9 kenan har mun saba babu abin da muke kullum sai yawan istigfari sai kuma mu zauna muna labarai, musamman abin da ya shafi rayuwarmu.
Rabiatu ta yi shiru, kamar kullum nasan tunani take na zauna kusa da ita sannan na sanya hannuna a kasalance na dafa kafaÉ—arta sannan na ce"Badaweeya".
Ta amsa "Na'am Maryam".
Ta faɗi hakan idanuwanta rau_rau da hawaye, kuka mai yawa ya fara zuba daga idanuwanta cike da takaicin halin da ta sanya kanta da kuma dangin ta yaranta da sauran abokan arziƙi.
Tana kukan ta fara magana "Yarana Maryam, Yarana na shiga uku Maryam sun shafe watanni basu ganni ba ina nan ƙarshe anan zan gama rayuwa"...
Cikin Sauri Maryam ta rufe mata bakinta ita ma tana kuka ta ce"tabbas Maryam yaranki abin jajantawa ne, musamman yadda ya kasance yarane su amma da sauƙi tunda ke kina ma da yaran ni kuwa ba ni da su ko ɓatan wata ban taɓa yi ba mummunar ƙaddara ta faɗa min, Inason ki bani labarin ki nima yanzu zan baki nawa domin Ni a tunanina babu labari mafi abun tausayi irin nawa". Rabiatu ta ce"uhum Maryam kenan a tunani ki ko? Amma idan kika ji labarina sai kin yi Allah wadai da Ni wataƙila ma a ranar kin rabu dani kenan, sai dai duk abin da na aikata silar namiji ne". Sai ta fashe da kuka. Maryam ta ce" Ba zan ce komi ba domin ban ji na ki labarin ba amma Nima nawa labarin duk silar namiji ne wanda nake tunanin a yanzu ya manta da babi na ma, zan baki labarina kema ki bani na ki. Maryam ta fara kallon shuke_shuken dake wajen ta fara bata labarin rayuwarta.
Labarina
______________________
Adamawa
(Yola)
Duk muna zaune a tsakar gida, Ni ina yi wa Abbanmu wanki Anty Hafsah tana yi wa Umma tsifar kanta wanda duk da shekarun Umma amma kanta cike yake da gashi, kasancewarta bafulatana.
Wani yaro ne ya shiga sanye cikin blue ɗin yadi mai kyau riga da wando, sai hannunsa maƙale dana ƙanwarsa alamar cewar aikensu ma aka yi, yaron ya ƙaraso wanda duk muka mai da hankalinmu wajensa, ya fara magana tun kafin ma ya ƙarasa shigowa. "Wai ana kiran Khadijah". Da sauri na ce" Wai inji w..." Tun kafin na ƙarasa magana ta Anty Hafsah ta ce" zai wuce ɗan ana ce jikan Mayu". Maganar ta ta yi min ciwo sosai, na lura shiru_shirun dana ke yi shi ne yasa ake zagin yaya Habibu kullum a gidanmu, saboda haka yau ɗaya dai na cire kunya na ce"gaskiya Anty Khadijah bana son wannan zagin da kike mai, kince mai faƙiri kin ce mai maye kin ce mai ɗan caca haba don Allah duk shi kaɗai". Na faɗi hakan ina turo ɗan ƙaramin bakina".
Jefo min kibiyar hannunta ta yi sannan ta nuna ni da yatsanta " to ai kinsan karya aka masa ba faƙirin bane, sannan kinsan ba mayen bane to idan ma ba shi maye bane ina shi ina ke, mutumin da kullum kwaki ne abincin gidansu sannan a hakan ma wai shi ne yake ɗaukar nauyin gidansu, to idan ma banda ke mahaukaciya ce kice me dashi? Yadda kike wanke hannu ka taɓa".
Sai a lokacin ne Umma ta magantu, ai wallahi babu inda za taje ma tunda fitar da take shi ne yake ganin kamar zai aure ta, kaf unguwar nan babu wanda bai san halin uban shi ba ba shida aiki sai caca, sannan shima a caca aka ciyo mahaifiyarsa kuma da abincin caca na haramun aka ciyar dashi tun daga ƙaraminsa har zuwa yanzu to shi ne kema kike tunanin zaki aure shi, saboda yana da kyau ko? To kyawun banza kyawun wofi ai shi namiji ba da kyau aka san shi ba in har yana da abun hannu shi kenan". Anty Hafsah ta ce "yauwa Umma faɗa mata dai marar hankali".
Wasu zafafan hawaye ne masu zafi suka fara sauka akan kyakkyawar fuskata mai cike da kyau da haiba, ina auna son da nake wa Habibu kullum ƙaruwa yake a cikin zuciyata ba zan iya rabuwa da shi ba. Ina cikin wannan halin ne Yaya Hamza ya shigo gidan ya hango ni na dunkule a bakin inda nake wanki ina kuka. Idan akwai abin da Yaya Hamza ya tsana bai wuce ganin kukana ba. Ya ƙaraso inda nake ya ce" ke kuma me aka yi miki? Ga Habibu can a waje yana jiran ki amma kuma kin zauna kina kuka haba Khadijah".
Cikin kukan na ce" Ba anty bace da Umma suke zagin Yaya Habibu, wai uban shi ɗan caca ne sannan a caca aka ciyo mahaifiyarsa kuma sannan shi faƙiri ne". Ransa ya ɓaci sosai ya kalli Umma wacce take zaune tana kallon mu tana zabga mana harara, sai dai hararar tawa tafi yawa kasancewar ni ce mai laifin sannan yaya Habibu ɗan fari ne wajen Umma basu fiya wani hira ba a wani sa'in ma sai kaga kamar Umma tsoronsa take ji.
"Umma yanzu don Allah meye laifin yaron nan? Idan ma mahaifinsa ɗan caca ne meye a ciki domin Allah? Tun da shi ba ɗan cacan bane kuma a haka ma yana da ƙoƙarin nema wallahi".
Umma ta kasa mai da mi shi da martani, saboda kunyarsa da take ta ɗan fari tana ji tana gani na fice ba tare da hana ni ba, Anty Hafsah ta yi ƙwafa da sauri ya kawo mata duka ta kauce saboda tasan halinsa bai iya duka ba. Ta tafi ɗaki tana guna_guni.
Daga can na hango shi tsaye, ya yi nisa a cikin nazari da tunani kuma na tabbatar da ba tunanin komi yake ba sai tunanin makomar soyayyar sa saboda yasan ba lallai ne a yarda ya aure ni ba, saboda yadda Anty Hafsah ta tsane sa uwa uba Umma wacce take uwa jigo a gare ni. Sam a rayuwata bana son na gan sa a cikin wani yana yi saboda har ga Allah yana sona gami da ƙaunata, na daɗe banga soyayya irin ta mu ba gaskiya ko Layla Majnun sai dai su gan mu su ƙyale, babu irin wulaƙancin da baya sha a wajen ƴan gidanmu amma kullum yana naniƙe dani, tamkar dai cingum.
Murmushi ya fara sakar min a wannan kyakkyawar fuskar ta shi mai cike da kwarjini da haiba sannan ma'abociyar kyau. Nima sakar masa nawa murmushin na yi, na tsaya É—an nesa da shi na tsugunna na fara gaishe shi cikin nutsuwa da tarbiyya.
Ya kasa amsa wa kawai ya tsare ni da lulu eyes ɗinsa masu kyau farare tarr, Nima kallonsa na shiga yi tamkar zamu haɗiye juna kallonsa na ke yi ina zayyano surarsa a zuciyata. Yaya Habibu ya haɗu sosai gaskiya ga shi handsome da shi fari tarr kamar wata, ga dogon hanci da bakinsa ƙarami pink lips ga kwantaccen dogon sajensa mai kyau baƙi siɗik, sannan yana da wadatacciyar gira wacce har so ta yi ta haɗe saboda yawa, dogon namiji ne faffaɗa wanda mata suke kiransa da giant man, kuɗi kawai ba shi da shi amma duk abin da ake nema a wajen namiji na cikar kyau da zati Yaya Habibu ya kai.
Hira muka fara yi cikin begen juna da shauƙi, muna hirar ne ya ce" My habibty gaskiya ina matuƙar son ki, wallahi da ace Ni mai kuɗi ne da ko zuwa uku ba zan yi wajen ki ba za a ɗaura mana aure, amma yanzu kin ga ba ni da komi tunani duk ya tsaya wallahi hankalina yana ta shi sosai shi yasa akwai wani abokina da ya yi min magana ko zan dinga binsa Legos ina jin zan dinga binsa tunda bansan abin da Allah zai yi ba".
Sosai maganarsa ta karya min zuciya, ƙwalla ta sakko min, na share a hankali sannan na ce" haka ne Allah ya taimaka yasa idan kaje ka samu arziƙi me albarka, amma ko na rana ɗaya kasan bana son rashinka". Ɗan murmusawa ya yi irin murmushin nan da ake cewa ya fi kuka ciwo, sannan ya ce" Habibty ki yi haƙuri ya zamar mana dole matuƙar muna son muyi aure cikin salama naje na nemi kuɗi". Ba don ina so ba haka na yi mai fatan alkhairi, muka cigaba da hirar mu cikin nishaɗi da son junanmu. Muna hirar ne kan wata A'isha ta zo wuce sai kuwa ta ce" ba zuciya an yadda kare ya cinye". A fusace na bita zan kamo ta sai ta gudu, haushi da kuma nadamar rashin kamata yasa na tauna harshena ganin na ɗaga hankalina ya ce" wai me yasa kike biyewa A'isha ne? Raina ki fa za ta yi ki ƙyaleta kawai komi ai yana da lokacinsa watarana ba za ta yi ba".
Kafin ya rufe bakinsa wata mota ta faka a ƙofar gidanmu. Baki ɗayanmu kallon motar muke baki sake saboda hamshaƙiyar mota ce wacce ta amsa sunanta, kana ganinta ba sai an faɗa maka ba kasan cewa mota ce wacce ta lashe zunzurutun kuɗaɗe masu numfashi. Kallona Ya Habibu yake yana zaton wani abu a zuciyarsa, in har kuwa zatonsa ya zama gaskiya lallai za a yi ɗan ƙaramin yaƙi bana kaɗan ba. Tun daga buɗe ƙofar motar wani irin ƙamshi mai tafiya da imanin mutum ya fara yi mana sallama tun kafin na ciki ya yi mana, na lumshe ido saboda jin daɗin turaren a zuciyata na ce uhum lallai turaren nan ya birge ni, ashe na yi magana a fili sai Ya Habibu ya watso min wani banzan kallo, sai na yi saurin haɗiye magana ta saboda sam bansan ta fito fili ba. Wanda ya fito daga cikin motar ne yasa na ji numfashina ya tsaya cak ba tare dana san lokacin da hakan ya faru ba. Ina mamakin yadda aka yi sam Ya Hamzah ya canja haka ko kusa ban taɓa tunanin zai canja a lokaci ɗaya ba, tunda ya tafi Legos neman kuɗi ya yi shekara 3 acan ya dawo da mahaukatan kuɗaɗen da kowa yake mamakinsa.
Bansan ya ƙara so inda muke ba, sai dana ji yana mana sallama, na yi saurin amsa masa sallamar amma Ya Habibu ko kallo bai ishe shi ba. Raina ya sosu sosai ko ba komi ai ɗan uwana ne ai ya kamata dai su gaisa. Jikin Ya Hamzah ya yi sanyi amma ko kusa bai wani damu ba ya basar ya yi hanyar shiga gidanmu. Binsa na yi da kallo saboda yadda baki ɗaya ya canza dama shi ba mummuna bane yana da kyawun sa dai-dai gwargwado don shi irin mutanen nanne dogaye sosai ga kuma faɗi domin ba zaka ce mishi siriri ba, kuma shi ba fari bane baƙi ne shi amma sai ya yi kama da Sudanese.
Ya Habibu ya daka min tsawar da ta sanya na koma cikin hayyacina. Cike da fushi ya fara min magana " Wai ke Hayaty wani irin abu ne haka? Tun kafin motarsa ta tsaya kike kallonsa har yazo ya wuce ya shiga gidanku to meye kuma na kallonsa haba?.
Da sauri na ce" Haba Habibty tsakani da Allah ɗan uwana ne fa, nufa yadda ya canza ne fa yake bani mamaki amma ba domin kallonsa da wata manufa ba, tunda ai kasan babu abin da yake a tsakaninmu mamakina ɗaya ne yaushe har ya zama haka? Shekara uku fa baya kafin ya tafi Legos ko kuɗin abincin da zai ci fa ba shi dashi sai dai yazo wajen Baffanmu kullum ya bashi kuɗi har gori yake mai, amma tsakani da Allah ace ya yi wannan mahauka tan kuɗaɗen shi yasa nake ta kallonsa da mamaki, bana mantawa da Amminsa ba tada lafiya nan ya zo wajen Baffah da kukansa aka kaita asibiti saboda ba shi da kuɗi a cikin ƴan uwa kowa gudunsu yake saboda talauci amma ace ya yi kuɗi a cikin shekara uku ai dole na kalle shi". Na ja numfashi ina kallon Ya Habibu wanda ya yi kasaƙe yana kallona, kuma har yanzu zuciyarsa bata aminta da abin da na faɗa ba.
" To idan ma don haka ne, sai kiyi ta kallonsa kamar za ki cinye sa ? Ai dole na ji haushi".
Ƴar dariya ce ta ƙwace min sannan na ce" yi haƙuri mai da wuƙar, dama na san kishi kake wallahi ni ko kusa bana son Ya Hamzah, kai sam ma baya daga cikin tsarina ni wallahi kai nake so kuma kai nake ƙauna". Jin haka yasa ya sake jikinsa muka yi ta hirar mu cikin so da ƙauna.
A can cikin gidanmu Addah Hafsah na hango ta rasa inda zata sanya kanta ganin Hammah Hamzah, saboda dama can tana matuƙar sonsa tun ma kafin ya yi tafiya har kuma yanzu da ya dawo. Haushi da nadamar shigowata gidan yasa na dinga zabgawa Adda harara saboda ni na tsani abin da take yi wai ace kai inba me kuɗi ba baza ka yi aure ba har sai lokacin da ka samu miji me kuɗi sannan za ka yi aure. Shi yasa ganin Hammah yasa duk ta ruɗe.
Tun dana zauna Hammah yake kallona, haushinsa ma duk yabi ya cika ni sai murguɗa mai baki nake shi kuwa sai wani smiling yake me cike da annuri, Amminmu sai murna take domin ita ma masoyiyar kuɗi ce ko da zai tafi ma kuɗi ya ƙirgo sosai ya miƙa mata, ta yi caraf ta karɓe babu a a ka barshi ba karar Fulani ta amshe. Haushi ya ishe ni na shige ɗakinmu ina turo baki ina jin sa yana musu sallama ya yin da aka fara shigowa da buhun hunan shinkafa da sauran kayan masarufi.
Ammi har da kukan murna saboda aduniyarta tana don jin daɗi, a zuciyarta tana ayyana wa dama ace ya auri ɗaya daga cikin yaranta da taji daɗi saboda tasan in har ta zama surukarsa ai dole ma taji daɗi. A lokacin da na shiga ɗakin na ga A'ishah ai kuwa na ce dawa Allah ya aiko ni na janyo ta muka fara dukan juna tana ta ihu tana neman taimako ni kuwa naƙi sakinta, saboda so nake ta banbance aya da tsakuwa ta dena raina min Hayatyna saboda yadda nake ji zan iya faɗa da kowa akan shi.
Ammi ta juyo kukan A'isha ai kuwa ta fara banbami tana tambayar me ya haɗani da ita? A maimakon na bada amsa, ai sai na cigaba da dukanta. Ammi ta fusata ta kawo min duka na zame dama tasan halina da muguwar zuciya ko an cuce ni bana daina faɗa, A'isha da bakinta yaƙi mutuwa ta ce" wallahi ko gobe na gansa a ƙofar gidanmu sai na fadi abin da raina yake so me za ayi da matsiya"...
Buge mata bakinta na ƙara yi ya fara zubar da jini nan da nan. Ammi ta sanya salati ta rufe Ni da duka tana ce wa" Ai Wallahi idan baki yi da wasa ba wannan zafin zuciyar ta ki zai haifar miki da BAYA TA HAIHU, sannan indai akan Habibu ne ki ke wannan abin har kike nema ki zubarwa da ƙanwarki haƙora wallahi ba za ki aure shi ba, idan kuma kika aure shi ba ni ba ke, sakarya wacce bata san abin da yake mata zafi ba". Sai da ta yi min li_lis sannan ta wurgar da ni gefe ta fita, wani irin kuka ne ya kufce min. A zuciyata ina tuna adadin son da nake wa Hamma Habibu sam ba zan iya auren wani in ba shi ba, amma Ammi ta yi min wannan furucin sai nake ganin kamar ba ta yi min adalci ba, tun da a wannan zamanin yaro shi yake zaɓawa kan shi abokin rayuwa ko yayarmu Anty Sailuba ita da kanta ta zaɓawa kanta miji wanda ma ba nagartacce ba kuma aka aura mata shi, sai ni za a hana wanda nasan Hammah Habibu baya shaye_shaye baya aikata duk wani alfasha sannan a hanani auren shi, ina ji a raina duk abin da ma zai faru sai dai ya faru amma sai na aure shi.
Ina kukan ina wannan tunanin Anty Hafsah ta shigo. Na wurga mata wani kallo saboda duk ita Ummul aba'isin komi, sam ta tsani talaka shi yasa ma ta tsani Hammah Habibu.
Durƙusawa ta yi dai_dai fuskata da yake a zaune nake, ta dafa kafaɗata cike da tausayin ƙanwarta gami da son ta domin ita ce take bin ta a haihu ma'ana sakuwarta ce, ta fara magana" Haba Maryam, wai me yasa ba za ki nutsu ki fuskanci me muke nufi ba wallahi ko kusa bana ƙin abin da kike so wahalar da za ki sha nake jiye mi"...
Saurin ɗauke hannunta na yi da ga kafaɗata sannan na fara magana cikin zafin zuciya " ke ɗin ce kike son abin da nake so? Ke ɗin me son zuciya da son kanta da raina arziƙin wasu shi ne za ki zo min da labarin ƙanzon kurege, to wallahi ina daga da fara yi miki mummunar tsana idan ba ki dena yi wa Yaya Habibu abin da kike yi mai ba, sannan ki goya min baya na aure sa shi ne zai nuna min kina son abin da nake so da gaske".
Jan numfashi ta yi kaɗan, alamar har yanzu ba ta son Hammah Habibu amma sai ta ce" to shi kenan na ji ƴar ƙanwata zan yi yadda kike, kin san inason ki sosai ba zan juri ganin ki cikin yanayin baƙin ciki ba, saboda haka yi haƙuri share hawayen".
Kallon ƙurilla nake mata, saboda sam ban yarda da ita ba ina tunanin ko tana auna rashin wayona. Ganin hakan yasa ta ce" haba ƙanwata ki yarda dani don Allah, wallahi bana son ganin ki a cikin irin wannan yanayin kin san yadda nake jin ki a cikin raina kuwa, banda iyayena bana hada son ki dana kowa ƙanwata ba a son raina nake baƙsnta miki ba, bana son kiyi auren wahala irin yadda Adda Sailuba ta yi shi yasa kike ganin ina takura miki amma Please and please ki yi haƙuri ba zan ƙara takura miki ba, kuma zan bawa Umma ƙwarin gwuiwa akan aurenku".
Ai bansan lokacin da na rungume ta ba saboda tsabar murna, ina ƙara jin son ƴar uwata yana ƙara huda jinin jikina.
Mafarin matsala
_____________________
"Hammah!Hammah!!".
Yarinyar budurwa ta ƙara kiransa a karo na biyu, juyowa ya yi da sauri saboda ya yi nisa a cikin tunaninsa mai cike da daɗi.
Ta zauna, ta fara magana "Haba Hammah tun É—azu Ammi ta ce na kawo ma abinci na zo na ajje amma ko kallonsa ba ka yi ba, saboda ta ga baka fita dining ba ta ce na kawo maka É—akinka".
Murmushi ya yi wanda ya fi kuka ciwo, saboda a yau ne yaga abin da ya damu zuciyarsa wanda tunda ya dawo ya kasa walwala ba ki ɗaya, yarinyar da yake so tun tana zanin goyonta, yarinyar da yake mutuwar so tamkar dai son ta zai zautar da shi, wai yau ita ce ya ganta da wani tana zance tabbas akwai sauran rina a kaba sannan dabara ta ragewa me shiga rijiya, domin garin kallon ruwa to fa kwaɗo zai masa ƙafa. In har bai aure ta ba wallahi komi zai iya faruwa da shi, kunyarsa za ta iya jefa shi cikin matsala ƙarshe kuma ya afkawa karin maganar nan da ake cewa BAYA TA HAIHU, azo yana ji yana gani wani ya ƙwace masa abar son sa.
Ganin Hibbah za ta dame shi da surutu, sai ya kore ta saboda yana buƙatar ya samu enough time (lokaci mai yawa).
A tunanin ne ya samo mafita, saboda haka da saurinsa ya miƙe yana mai ce wa "Yes!Yes!!".
Da ɗan ƙarfi yake faɗar hakan, fuskarsa ɗauke da mallaki yar fara'ar da ta kasance tun daga zuciyarsa har fuskarsa.
Ya fito daga cikin kyakkyawan ɗakinsa zuwa ɗakin mahaifiyarsa domin ya faɗa mata abin da yake cikin zuciyarsa ayi ta taƙare saboda ya fuskanci in har bai furta ba wani zai iya riga shi.
_Uhum Ni kuwa Ummu maher na ce, cab amma fa akwai cakwakiya a cikin wannan littafin domin kuwa an riga shi É—in, sai ku biyo ni domin jin yadda za ta ka ya shin yana auren Maryam? Shin za ta yarda? Shin yaya labarin Maryam zai kasance? Shin wata illa ta yiwa rayuwarta har ta kasance a cikin gidan yarin?. Uhum nasan kuna ta hasashe to ba lallai ne hasashen ku ya faÉ—a muku gaskiya ba har sai kun karanta complete É—in wannan littafin, inda zai zo muku a book 1 har zuwa 3 domin yanzu aka fara taki har kullum Ummu Maher Matar SHU'AIBU)_