AMARYAR GADO

CHAPTER 18

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026

SHAFI NA SHA TAKWAS

Ya ga ɗayar Faridar da ke tsorata shi, aguje ya tashi ya yi kan Farida, ita ma tsoro ta ji, ta jura aguje ta riga ta shiga ɗakin, shi ma shiga ya yi ya bi bayanta. Farida ta hankaɗa shi, yana ƙoƙarin shiga, tana ƙoƙarin fitar da shi, sai da ta fitar da shi da ƙarfi kafin da sauri ta kulle ƙofar ta.
Buga mata ƙofar ya dunga yi yana, “Muguwa, ki buɗe, Aljanarki za ta cinye ni.”
Farida na daga ciki tana, “Ba ka ce za ka iya da ita ba? Ai ku je can ku ƙarata.”
Ci gaba da buga ƙofar ya yi yana ihu, Farida kuwa ko a jikinta ta kwanta ta daura filo a kanta.
Ya rasa inda zai nufa, domin ko motsawa ya yi, gani yake za ta shiga jikinsa. Rufe idanunsa ya yi ya dunga karanto Ayatul Kursiyu da ƙarfi.
Sai can a hankali ya buɗe idanunsa, ya ga ba komai. Ya kalli gabas da yamma ya tabbatar, sannan ya afka ɗakinsa aguje ya kulle.
Ya shige cikin bargo ya dukunkune kansa yana kiran sallah, can kuma sai ya ci gaba da Ayatul Kursiya, “Allahu la ilaha illallahu hayyul qayyum, la ta…” Sai kuma anjima kaɗan a koma kiran Sallah, “Allahu-Akbar, Allahu Akbar, la ilaha illallah.” Daga haka har barci ya yi awun gaba da shi.

Ko da ya farka da asuba, kasa fita daga ɗakin ya yi, bare ya je masallaci. Haka ya yi wanka, ya yi alwala, ya yi sallah a ɗakin, yana ta tofe-tofen addu’a.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Habib yana ba shi labari. Habib ya sheƙe da dariya, “Kai, yanzu ka yarda akwai wata aljanar Farida ne? Sufy, wallahi wasa da hankalinka kawai take. In za ka dage ka murza idanu ka nuna mata kai kwaro ne, ka dage haba, sai ka ce ba namiji ba.”
Sufyan ya ce, “Kai fa Habib, ba ka san tashin hankalin da na shiga jiya ba ne.”
“Ni dai na faɗa ma, kar ka kuskura ka bari ta gano lagonka, don ka shiga uku kenan wallahi.”

Wayar da suka yi da Habib ne ya ɗan samu ƙwarin gwiwa. Ya tashi ya shirya, ranar sai dai aka tuna da makaranta, dole ya ɗauki Qur’ani ya dunga karantawa har sai da gari ya yi haske. Sallamar Inno da ya jiyo ne yasa shi fita falo, ita ce tsaye da Hansai da tarin ruwan magani.
Inno ta ce, “Kai, ina Matar taka?” Sufyan ya nuna ɗakin Farida, “Tana ciki.”

Hansai ta ce, “Ban gane, tana ciki ba wai an yi gabas da kare, kana nufin kana kwana anan, ita tana kwana a can?” Ta faɗa tana nuna ɗakunan.
Inno ta riƙe haɓɓa tana, “Ni fa ba taɓa haifa mini husumammun jikoki irinku ba, gashi kune na ƙarshe, gashi ku ke son kashe ni da husuma.”

Ta ƙarasa maganar tana buga ƙofar ɗakin Farida. Cikin yanayin barci Farida ta buɗe ƙofar, Inno da Hansai suka haɗa ido.

Hansai ta ce, “Wato barcinki kike, hankali kwance, shi mijinki na can kin barsa a gantale?”

“Fito nan, duk ku fito ku zauna anan.” Inno ta faɗa tana zama kan kujera, ita da Hansai.

Farida da Sufyan suka zauna a ƙasa.

Inno ta yi rau da ido tana kwakulo hawayen ƙarfin hali da ƙyar har sai da ya fito, kafin ta ce, “Yanzu fisabilillahi, kun kyautawa rayuwata kenan? Kun kyautawa amanar da Alhaji Audu ya bar mini kan cewa kada in bari zuriyarsa su fandare su shiga husumar fushin Ubangiji? Tsakanin da Allah, ba za ku kwana ɗaki guda kuna jin ɗumin juna ba? Wani irin baƙin hali gareku ne wai?”
Hansai ta ce, “Yi shiru Inno, yi shiru, ai nima sai ki sanya ni kukan.” Ta faɗa tana goge ido da gefen zani, kafin daga bisani ta ci gaba da faɗin, “Yoo, ba dole aure ya ta mutu ba a zamanin nan, tunda ba su san darajarsa ba, kuma ba su iya riƙon ba. Yanzu ke Faridatu, da nake tunanin za ki fi Sufuyanu hankali, ashe za mu je ce ta tarda mu je mu?”
Farida da Sufyan kuwa sun yi fiki-fiki da ido, sun rasa abin faɗi. Kawai bin Hansai da Inno da ido suke.
Inno ta face majina da gefen zani tana maida numfashi, “Na rantse da Allah, kuka ƙara kwana ba a ɗaki guda ba, ban yafe muku ba. Kila ma harda hakan yasa cikin jikinki ya ƙi gaba, ya ƙi baya. Ku haɗa kanku, ku kau da husuma, ko in tsine muku, in tsinewa iyayenku. Kai, Hansai ma tashi mu je in sanar da Shuaibu abin da yaransu suke aikatawa.” Ta ƙarasa maganar tana miƙewa.

Atare Farida da Sufyan suka yi magana, “Aa Inno, za mu gyara, ki yi haƙuri.”
Saboda sun san halin Inno sarai yanzu sai ta tara Family meeting akansu.

Inno ta taɓe baki ta ce, “Kun yi alkawari? Kodayake ba laifinku bane, laifi nane da na ɗauki soyayyar duniya na daura maku.” Ta karasa maganar a sanyaye tana goge guntun hawayen da ke fuskarta ka fin ta ci gaba, “Don aradun Allah, duk ranar da kuka yi wasarere da cikin jikin Faridatu ya ɓare, ina ga nima a ranar zan ɓare in bar duniya. Ku yi wa iyayenku da kanku asara.”

Hansai ta ce, “Aa Inno, bar faɗi, ai kawai su lallaɓa cikin nan, a zauna cikin lumana.”
Sufyan ya ce, “Za a gyara Inno, ki yi haƙuri, daga yau ba za a ƙara ba.” Ya faɗa yana gallarawa Farida harara.

Inno ta ce, “Kun yi alkawari?”

Dukansu suka girgiza kai da faɗin eh.

Inno ta ce, “To, kar in ji, kar in gani, zan zo in duba kuma. Yanzu tashi, ki zo a shafa ruwan rubutun nan a cikin, Malam ya ce a shafa. Wa can kuma na sha ne?”
Take a gun Hansai ta ɗaga rigar jikin Farida, Inno ta shafa mata ruwan maganin, sannan ta ɗauki sauran na sha ta ba ta, ta sha.
Inno ta ce, “Yawwa, yanzu nan da mako guda, indai cikin nan bai motsa ba, dole a nemi wata mafitar. Kuma duk abin da na faɗa muku a kiyaye. Hansai, mu je ko?”
Hansai ta ce, “E Inno, Allah dai ya tallafi wannan ciki ya zauna.”

Suna fita, Farida ta bi Sufyan da kallo tana, “Da wa kake nufin za ku kwana waje ɗaya? Kar ka manta fa, har yanzu a ɗan tayi nake kallonka, yaron da na wankewa kashi da fitsari.”

Sufyan ya yi wata gajeriyar dariya yana, “Au haba? Ke fa ki gode wa Allah da ko kaɗan ba kya birgeni, da kin ga aikin ɗan ta yi. Ni kin san miye ma? A yadda nake kallonki, ba ki da maraba da irin tsofaffun ’yan barikin nan. Ga ’yan mata masu jini a jika na bina, a kan me zan biki? In kwashi takaici?” Ya sheƙe da dariya, “Wallahi, ko a kafa aka daura min ke, sai na yanke igiyar na gudu. Ni masu binki ma mamaki suke bani, da har aka samu mai maka miki ciki.”

Farida ta ji zafin maganarsa har cikin ranta, hakan yasa kawai ta girgiza kai, ta tashi ta wuce ɗaki.
Tashi ya yi ya shiga kitchen, ya samu abin da zai ci. Yana gama ci ya ɗauki filajin ya sha, ya koma ɗakinsa ya hau kan gado, domin idanunsa har rufewa suke tsabar barcin da yake ji, kasancewar jiya bai samu isasshe ba.

Farida kuwa da ta koma ɗakin wanka ta yi ta sanya kaya, ita ma ta shiga kitchen ɗin ta dafa Indomie, ta zauna a falo ta ci. Da yake a buɗe ya bar ƙofar, hangosa ta yi ya baje yana ta sharɓan barci.

Ta fita farfajiyar gidan, tana ta kai kawo, ta je nan, ta dawo ta je can. Tana ɗan wasa da shuke-shuken gefen gidan ta ci karo da ƙaramar kunama. Wani murmushin mugunta ta yi ta girgiza kai. Da sauri ta tashi ta je ta ɗauko wani ludayi a kitchen, ta zura kunamar ciki.

Ta ɗauka ta shiga ciki, tana tafiya a hankali, a hankali ta tura ƙofar ɗakinsa ma ta shiga. Ta tsaya a kansa da kunamar a hannu, tana kallonsa yana ta barcinsa cikin kwanciyar hankali.

“Ina kai har jin daɗin faɗa min cewa kana iskanci kake? Yanzu naga da abin da za ka yi iskancin ai, sai a yi jinyar iskanci ai, kuma kai ma ga biyan bashin da ka ci.”

Ta ƙarasa maganar tana ɗaga wandonsa a hankali, da yake gajeren wando ne.

Tana buɗewa ta zura kunamar ciki.

Tana sawa ta ja jiki da sauri ta fice a ɗakin, ta koma ɗakinta aguje.

Ita kuwa kunamar sai da ta daidaici setinsa a cikin wandon, kafin ta buɗe ƙarƙar ɗalinta ta kai wajen.

Jin dallin kunama ya yi tun daga ransa har tsakiyar ƙafafunsa, ya farka yana sakin wata irin ƙara, da shi kansa bai san yadda sautin ke fita ba.
Farida na jinsa, ta kafa earphone a kunnenta kamar ba ta san me ke faruwa.
Cikin ƙarfin hali ya kai hannunsa wandon ya zame da kunamar a ciki.
Lokaci guda gabansa ya sauya ya yi jajur, ga wata irin azaba da ke ƙaruwa masa.
Janyo wayarsa ya yi, da yake number Habib ce a sama, ya kira yana, “Zan mutu… na mutu…”
Habib na tambayarsa me ya faru, ko iya amsa shi bai yi ba, take ya sume akan gadon.