SHI SO DABAN YAKE

Babi na goma

by @dijensy

10


    

    Yau ranar  tarewar su  Jidda a sabon gidansu ba wani alfahari da hakan take ba don akwai sauƙin abubuwa da dama da Anty Ruƙayya ke samar mata ta tabbata idan ta tafi wannan alfanan ya tafi kenan musamman ɓangaren girki,fuskarta ba yabo ba fallasa Anty Ruƙayya baki har kunne ba ƙaramin murna take ba da cigaban da suka samu na musamman ta haɗa mata yan abubuwan miya na kitchen yaji ne curry da kayan kamshi ta zuzzuba mata robobin zamani masu kyau sabbi da ta siyo a kasuwa da yan robobi na amfanin gida wanda ta hanyar kananan sana’ointa na kayan gwanjan yara ta samu yan kudin siya matan sanda suka zo gidan kuwa Jidda tayi mamaki  da kujerun parlour da suka tarar  ruwan hadari mai kyau da labilaye ash da carpet sabbi gwanin  shaawa sunyi kyau.Jidda kawai kallo ne nata kamar ba gidan da zata zauna bane haka ta bar Anty Ruƙayya ita kaɗai tana ta aiki a gidan da gyara ta jera mata komai a muhallinsa harda cabinet na kitchen dai dai kitchen ɗin sai da ya dasa mata ɗaki gado bai samu ba katifa ce meduim aka shinfiɗa sabon bedsheet akai da sif sabuwa mai falle biyu brown turarre daga gefe aka shirya akwatunan kayan nasu ba abinda yake tashi a gidan sai ƙamshin turaren wuta da Anty Ruƙayya ta kunna mata,a cylinder gas ta ɗora musu girki jollop rice tayi mai daɗi ita aka ci da rana ta juye sauran a warmer duk wannan kayan kitchen Hassan ya siyo mata har set ɗin cokula da yan kofuna Jidda ido ne nata ba wani yi mata abubuwan sukai ba in banda ƙaddara ma ya zata zauna gida irin wannan?shiyasa ko faɗawa su Umma zasu tashin bata yi ba Anty Ruƙayya da yamma likis ta tattara yaranta suka tafi Hassan har titi ya raka su ya sasu a keke napep bayan da suka gama yin magana akan wani ƙaninta da zai dawo gidan da zama a shago don zaman ita kaɗai ba tsaro sosai daman ya gama sakandare yana neman jamia a kano ta faɗa masa ya samu admission yanzu haka suna magana kan ranar da zai zo ɗin.Dukda ya biya kuɗin napep ɗin sai da ya damkawa Shafiha dubu biyu a hannu ya tafi kar ma tace masa a a ta leƙo tana godiya  Anty Ruƙayyan ta girgiza kai Hassan baya gajiya da hidima kamar zai bada babu.Jidda ya shigo ya samu a parlour tana danna wayarta ta ɗago tana kallonsa ya zauna gefen kujerar da take mai cin mutum biyu ya jingina bayansa yana kallonta ya gaji amma baya so ya nuna “Ina ɗan kunnen faɗuwa yayi?”Ya tambaya a hankali ta taɓa kunnenta da sauri don tana son ɗan kunnen Anty Baby ta yiwa ƙwace tana shafawa taji akwai ta ga yayi murmushi ta hararesa bai taɓa yin murmushi yayi muni ba Hassan duk yadda ta kai ga ƙinsa zuciyarta bata taɓa ƙaryatawa hassan kyakkwa ne dukda ba fari bane.”Ba gashi a kunnena ba “.Jidda ta faɗa tana kauda ido daga kallonsa yayi murmushi.

 “Kace min kuɗin gyaran gidannan ne dakai kawai ina ka samu ka yi kujera sabuwa?”Yaji ta tambaya tana kallon kujerun da har sannan bata ga makusarsu ba ya ɗan juyo sosai “Tabbas a wancen lokacin babu ,kinsan yadda de lamari ke kasancewa Allah shine jagoran komai Jidda ,jiya  kuɗinnan suka zo min watanni kusan biyar baya munyi saukar ɗalibai toh akwai wani babban malami an gayyacesa bai samu zuwa ba yana Saudiyya tohm sai dawowarsa ɗinnan kawai ya zo islamiyyar mu ya gaisa da shugaban makarantar sai sukayi magana dashi ni bansan ya akai ba dai yace masa nine ‘yan aji na sukai sauka to kawai naji yayi kirana ya karɓi account number na ya turan 500k ɗaliban kuma ya bawa shugaban makarantar kuɗi masu yawa ya ce a siya musu kyaututtuka naso na faɗa miki kawai naga yafi dacewa nayi surprising naki fatan ban ɓata miki rai ba Amirahhh”.

   

 Jidda ta taɓe baki amma har cikin ranta taji daɗin sunan “Haushin me ?kai da kuɗinka”.Ta furta ya faɗaɗa murmushinsa yana son wannan rikicin nata ya gyara zama “Kuɗinmu  dai daman so nake na samu zama mu yi maganar me za ai da ragowar”.Jidda ta ɗan juya ta kallesa jin maganar kuɗi tana mamakinsa shawarar tata yake nema shi ko wani iri ne sai kace mara wayo ?wani sarautar mulki taji ta hau kanta ta ajje wayarta gefe shikuwa ya shagala da kallonta yana so yaga ta sauraresa.


 “Nawa ya ragu?”Ta tambaya yace mata “Ɗari da hamsin”.


 “Sai ka siyo kayan abinci dasu”.Ta faɗa.


  “Yanzun na siya mana kaɗan watan gobe zan ɗauki dashi a ciki nake son na siya dayawa har da nasu Anty Ruƙayya zan biya wa yara kuɗin term sannan ina son sa mana ko ƙaramar solar ce sai na siyo miki harda fanka da na maki alƙawari.Jidda ta na kallonsa ya gama zayyane mata ba abinda ya rage ko ya ƙara hatta dunƙulen kuɗin da zai ɗauka sai da ya faɗa ta giɗa kai maganar solar ɗinkaɗai  ta bata maana don zata amfana amma kuɗin term akan me zai ɗauki nauyin yaran wani?


 “Shi kuɗin term ɗin duk akanka yake?”Ta tambaya tana ɓata rai ya murmusa “Marayu ne Jidda idan na tallafa musu nima Allah zai min baki ga tun da nake kula dasu nake samun buɗi ba da bai kai haka ba samuna kuma mahaifinsu shi ya ɗau nauyin karatuna har na gama yarannan jini na ne”.


 “Toh tayi aure man”.Ta furta tana turo baki Hassan yayi dariya mara sauti yana tattaro hankalinsa kanta ba ƙaramin jin daɗin hirarsu ɗinnan yake ba “Jidda shekarunki nawa?”Ya tambaya “Sauran watanni na shiga sha takwas”. ya ɗaga gira “Da gaske?”


 “Ehman”.Ta amsa ya kalleta girman jidda ba me cewa batayi ashirin ba ko ma fi amma ya yarda bai ga dalilin da zatayi masa ƙarya ba tunda ta faɗa hakan ne shiyasa bai taɓa jin haushin wani abu da zata masa don ya tabbata yarinyar ce.


  “Watarana zaki gane ,lokaci ne Jidda ko ta samu wanda zasi aure ba lallai ya riƙe mata yaran wani ba kuma ni nauyinsu bai taɓa damuna ba kada ki damu hakan bazai kawo tsaiko ba yanzu mu koma kan maganar mai za mi da 150k”.



  “Sai naji na ka shekarun tukun”.Ta furta har sannan bai daina murmushi ba “Ki ƙara goma akan naki”.Ya faɗa Jidda ta kallesa tana lissafawa sam bai mata kama da ya kai hakan ba bata ce komai akai ba ta shiga fara karanta masa kusan duk kayan alatun gida ne da zata amfana bai musa ba ya ɗauki shawararta har kuɗin data ta tambayesa a hirar da suke ya tura mata nan take tayi sub sai bayan magriba ya ci abincin da Anty Ruƙayya ta girka musu sallah isha a gida ya jasu tare sukai da ita zuciyar hassan fal da farinciki a yayinda jidda farincikinta ɗaya ne don zaman nan da sukai ya bayyana mata kowaye Hassan tunda har ta samu yana jin maganarta toh kuwa haka zata moresa san ranta.Jidda ke wannan tunanin a ranta ta shiga ɗaki ta na ciro kayan ya shigo ya sameta ya ce mata ta huta kawai  shi ya shirya musu duka kayansu ta shiga banɗakin yasha tile fari kusan yafi komai mata kyau a gidan yayi kama da raayinta.Ruwan da ke flask ta juye a bokiti ta buɗe fanfo taji yana zuba wani sanyi taji a rai sai ta tuna da gida a ranta take tunanin zata kira su Umma gobe ta faɗa musu sun tare nan tayi wankanta ta gama ta fito da towel ɗaure a jikinta iyakacinsa rabin cinya Hassan ɗin ya shigo ta basar tana buɗe sif ta ciro kayan baccinta kusan sif ɗin ma duka kayanta ne ,doguwar riga ta saka bata ƙarasa ƙaurin ƙafa ba duk motsinta da zatayi sai bum bum ɗinta ya muskuta ba abinda ya dameta.


 “Ban ga kin ci abinci ba da daddare lafiya?”.Taji muryarsa yana tambaya  “Na ƙoshi da rana ita naci”.


“Me kike son ci sai a siyo”.Ya tambaya daman tana ɗan jin yunwa tace masa nama balangu Hassan nan take ya fita ba jimawa ya dawo da kullin nama me yawa ta zage ta ci ta koshi ta kora da ruwa ta karkace kan katifar tana danna waya hassan kuwa littattafan islamiyya  ya dakko batasan komai yake ba don hankalinta baya wajen shikuwa lokaci lokaci yake satar kallonta sha ɗaya saura ta kifa wayar bacci ya ɗauketa bata sani ba ya taso ya ajje mata wayar gefe a hankula ya gyara mata kwanciya ya sa mata pillow ƙasan kanta yana ƙara kalle fuskarta da zanen leɓenta mai ɗaukan hankalinsa  idan tana bacci kamar ba ita ba a hankula ya kai yatsansa yana shafawa saman leɓenta kafin ya saurin janyewa ya tashi agogo ya duba ya ga lokaci ya tattara littafansa ya mayar a gefen katifarta ya yi shinfiɗa daga gefe ya kwanta shima bayan da ya tofa mata adduar bacci don ba yi take ba.




                             ********


Jidda washegari ta kira su Umma ta faɗa musu aikuwa sai da ta mata faɗa da bata sanar musu da wuri  ba sai a washegari ta turo mata su Yaseer shi da Abdallah suka ga gida Baba ma ya kira ya masa Allah sanya alkairi ya faɗa mishi zai zo idan ya samu lokaci.Jidda tun da suka tare bata taɓa ɗaga tsintsiya tayi shara ba ba abinda takeyi bai taɓa jira ba ko ya sa ta yana tashi bayan sallah subh da ya gama azkar da karatun Al qurani  abinda yake fara yi kenan aikin gida sannan ya yi wanka ya shirya yaje aiki ko da dare kafin su kwanta sai yayi wankewanke yan kwanuka da ta ɓata don shi da ya ci abu yake wankewa Jidda ba abinda ya dameta ta saki jiki ci kawai take ta danna waya ba abinda ya canja ba abinda ya shiga tsakani ko tunanin hakan ma batayi kamar sharing ɗaki kawai suke ,Hassan yana bin ta yadda take so duk abinda take so shi yake mata duk sanda shaawarta ta taso mashi sai dai ya yi kokari ya danne ko ya tsiri aiki shiyasa koyaushe yana tafe da ya dawo gida daga aiki sai ya tafi makarantar dare idan yana off ya je tahfuz ya dawo idan baya gida sai dai tayi ta kame kamen girki cikakke sai yana gida zai yi haka zai dawo ba abinda zata dafa wani lokacin kawai sai dai ya siyo a waje ya zo dashi.



    Yau tana zaune da safe bayan fitarsa Anty baby ta kirata tace zata zo yau nan jidda ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin lace ruwan inibi tayi kwalliya kar tace tana ƙazanta ,Jidda da ƙyar ta ja jiki ta dafa taliya fara da miya itanma ta duddunqule ta saka a warmer.Anty Baby ita kaɗai tazo ta taho mata da kayayyaki wanda Umma ta sa ta kawo mata tana buɗe mata ƙofar gate ɗin ta rungumeta kafin ta shigo ta rufe ƙofar suna shiga ciki tana kallon gida.


 “Allah ya sanya alkairi ko ina yayi kyau ma sha Allah”.Anty baby ta furta Jidda bata ce komai ba .


  “Ya fita kenan?”Ta tambaya.


“Ya fita tun safe”.Ta amsa Anty baby ta kalleta ta ga Jiddan ta ƙara jiki  “Umma na gaisheki”.Ta faɗa.


Murmushi tayi ta amsa “Ina amsawa yaushe zata zo dan Allah?”


“Sai kin haihu”.Ta amsa  cikeda zolaya jidda tayi dariya tana saurin share zancen ta tashi ta je kitchen ta ɗakko mata warmers ɗin abincin da plate ta kawo ta je ta ɗakko mata ruwan roba ta ajje Anty baby na kallonta ta dawo ta zauna ta nuna mata ledar kayan da Umman ta aiko mata ta tashi tana fara dubawa abubuwa iriri yawanci na kitchen ne taji daɗi Anty baby ta ce ta kira Umman a lokacin ta mata godiya don baba bai sani ba daga kasuwa ta yo nan karma ya gani don rannan kayan kulle kulle na miya ma faɗa yayi tayi yace sun raina samun hassan ne ko me ? yasa yanzun ta yi a boye.Anty baby kuma snack ta yo mata ta kawo da turaren wuta da humra da yan kayakun da ta saba kawo mata.Jidda ta ɗauki waya ta kira Umman suka gaisa ta mata godiya sukai sallama.


“Ina kayan da na kawo miki sun ƙare?”Jidda ta gida kai Anty baby ta ɗakko mata turaruka masu kamshi da misk ta miƙa mata  a cikin leda “Ki adana wlh kayanta akwai kyau sai shegiyar tsada 120k duka wannan da turaren wutar har da na jiki”.Jidda ta waro ido “Kuma Anty da kuɗink kika siya?”


 “Da da nawa zan siya?”


 “Kina sana a yasa nide ki barsu haka sun isa”.Jiddan ta faɗa tana juya misk ɗin “Da wanne kike using nasan wancen ya ƙare”.Anty baby tayi mata tambayar tana kafeta da ido.


  Baki ta taɓe “Ni fa Anty baby kuna asarar kudi wannan ɗin ma Allah sa…..”Sai tayi shiru bata ƙarasa ba kar ta saki layi don jidda bata iya boye abu sai ka ganota.


  “Cikin yasa ba kya amfani dashi ko me?”Anty baby ta tambaya Jidda ta karkatar da kai “Nifa ba wani ciki banda komai kar ma ki faɗa a gida Allah zasu yi jiran hotiho wai Anty Baby ke kin ga gidan haihuwa anan tsakani da Allah fa haba kema ki duba mana Jiddanki fa matar manya ce ke kanki kina faɗa”Ta faɗa Jidda tana ƙin yarda su haɗa ido Anty baby ta saki baki “Matar manya ? Ke baki san wasa ba a da ɗin ma ai ba wai gaske bane wasa ne?Jidda wace ke yaushe kika girma ma da zaki ɗauki burin rayuwa ?ki bi duniya a sannu duk uban faɗan da aka maki Jidda tunanin ki yana nan na ɗauka komai ya wuce aurenku wata nawa dan ubanki wata na huɗu fa?”Anty Baby ta ƙarasa faɗa tana ƙanƙance ido alamar gano wani abu “Ke kalleni don ubanki ko har yanzu baki haɗa shinfiɗa dashi ba?”Ta tambaya Jidda ta turo baki “Da wannan bagidajen ni bazan iya ba bana son shi Allah shima yasani kawai sai na yarda ya kwanta dani”.Furucinta yasa Anty baby rike baki bata san sanda ta tashi ta kai mata dundu ba tana lafta mata duka a baya sau biyu Jidda ta riƙe bayanta tana yar ƙara ta tashi da sauri tana zagayawa bayan kujera ta haɗe rai……..


  “Kaji fitinanna me ne kike yi a gidan to gadin gidan kike masa hala? Ki hana bawan Allah ….tabdijan amma ke baki da hankali kamar ba mata suka rainek ba,Duk faɗan da ake miki duk waazin da ake miki karshe ma malamin kika aura karatun  islamiyya yaji sa zalla kina neman zamar masa shedaniya toh kisani kamar Baba ya ji don bazan rifa maki asiri  ba uban wa kike ajjewa budurcin naki? Ki gode Allah kina kankanuwarki  kinsamu miji shekarata talatin da huɗu jidda har yanzu zaman jira nake a zamanin nan kowa hakuri take kuma mijinki da iliminsa boko da arabi  da aikinsa me kike so?kyale kyalen duniya ko ubanki sanda suka rikeni hakuri Umma take ,ni jikina ya bani wannan nutsuwar da luff da aka ji kinyi kwana biyu karanki kike ci ba babbaka shiyasa kike hawa kamar farashi sai dai kici kisha ki cika masa masai?toh karyanki ya sha karya mu ba mutanen banza bane wlh kin hadu da yaro me hankali bazai iya kawo mana kararki ba shine zaki zalincesa sabida ba a miki abinda kike so ba”.Anty baby take faɗa kamar zata ari baki garin haka ta taɓa warmer taliya da ƙafarta murfun ya buɗe ta kalli kalar taliyar da ke ciki  tana ɗaukan warmer ta na motsa taliyar ko gezau dunqule dunqule duk ta haɗe jikinta ta kalli Jidda da ta gwalalo mata ido a tsaye bayan kujerar……