MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 11

by @mrsisham12


23&24 MATUƘAR INA RAYE
(As Long As I Live)

Writer — MRS ISHAM
*** WhatsApp

Page 11

“Mu ci gaba da saka shi a cikin addu’o’inmu, Zanaya. Ina so ki sani babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji. Tun tasowarmu haka nake ganin ɗan’uwana cikin matsanancin ciwo.”

Ya dakata yana jan numfashi sannan ya furzar da iska a hankali, kafin ya ci gaba da cewa,

“Haka ke ma kika taso kika same shi cikin ciwo, ga Nini ita ma yanzu ta fara shiga damuwa saboda rashin lafiyarsa.

Dukkaninmu muna azabtuwa, amma muna roƙon Allah Ya ba shi lafiya. Ki je ki kwanta, dare ya yi. Ni zan kwana tare da shi a nan.”

Kai ta gyada masa tana kallon Bk, hawaye na saukowa a kumatunta, sannan ta fita daga ɗakin.

Ajiyar zuciya Zannor ya sauke sannan ya ƙarasa gaban gadon ya zuba masa idanu. Sai da ya kwashe wasu mintuna yana kallonsa kafin ya hau gadon ya shiga cikin blanket ɗin ya kwanta, yana ɗora kansa a kafadar Bk dake cikin barci.

Duk da ya san barci yake yi, hakan bai hana shi cewa,

“Dan uwa, ka san me?”

Murmushi ya yi lokacin da ya tuna ba zai ba shi amsa ba saboda barcin da yake yi.

“Na san ma ba za ka ji ni ba. Ina son in roƙe ka wata alfarma ce. Dan Allah kar ka karaya. Idan har ka karaya, zukata da yawa za su azabtu.

Wannan ba shi ne asalinka ba, dan uwa. Kar ka daina yaƙi da wannan ciwon. Mu ma muna tayaka da addu’a.

Ka daina nuna mana kamar ka saba da shi, dan Allah. Ba a taɓa sabawa da wahala ba, komai girmanta ko ƙanƙantarta.

Na jima ina tambayar kaina, shin idan wannan ɓangaren ya ci galaba a kanka fa? Shin ya rayuwata za ta kasance?

Kana ganin zan iya ci gaba da rayuwa ne?

Ko da na ci gaba da numfashi, zan kasance ne kawai a matsayin fanko wanda bai da maraba da matacce.

Kai ne farin cikina. Kai ne abokin haihuwata. Duk duniya kai ne mutum na farko da nake tsananin ƙauna.

Dan Allah ka jure. Komai yana da ƙarshe. Babu abin da baya wucewa.

Idan wani abu ya same ka, zan ƙarasa gaba ɗaya rayuwata cikin matsanancin kaɗaici.”

Ya gama maganar yana goge wasu azababbun hawaye masu zafi da suke saukowa a kuncinsa, suna diga a kan kafadar Bk.

Domin a wannan lokacin, shi kansa ya fara karaya. A tsorace yake. Kullum cikin roƙon Allah yake Ya sauƙaƙawa ɗan’uwansa abin da yake ji, ko kuma Ya dawo da ciwon kansa.

Domin ji yake kamar ya haɗiye zuciyarsa ya mutu duk sanda ciwon Bk ya tashi.

Yana takaicin rashin abin da zai iya taimaka masa da shi a matsayinsa na ɗan biyunsa. Tsabar tunanin Bk da ya mamaye ransa har ciwo yake ji a ƙirjinsa.

Saboda Zannor, duk duniya babu wanda ya sanya a ransa irin ɗan’uwansa.

Masifar ƙaunarsa yake yi, kuma baya son wani abu ya taɓa shi.

Ko Mamie da ta tsuguna ta haife su, baya sonta kamar yadda yake son Bk.
Saboda zama a mahaifa daya ba wasa ba ne.

Duk da Bk yana ja da baya da shi a wasu lokutan, hakan bai taɓa damunsa ba, kuma ƙaunarsa ba ta taɓa raguwa a zuciyarsa ba.

Domin ya san cewa Bk yana sonsa. Ja da bayan da yake yi kawai saboda ya saba da raɗaɗin rashin lafiyar da yake fama da ita. Ko da wannan ƙaddararriyar cutar ta yi nasara a kansa, ya san cewa Zannor ne zai fi kowa jikkata.

Bayan shi kuma Mamie.

Wannan dalilin ne ya sa yake nuna halin ko-in-kula a gabansa, yana ƙoƙarin ɓoye girman damuwar da yake ciki.

Ya lumshe idanunsa tare da rungume ɗan’uwansa sosai, sannan cikin wata murya mai cike da rauni ya furta,

“Ya Allah, idan har shi ba zai iya yaƙar wannan rayuwar shi kaɗai ba, Allah Ka turo masa wanda zai tayar masa da wannan faɗa…”

Bk da ya gama sauraronsa ne ya ɗan yi ɓ murmushi sannan ya amsa da,

“Ameen…”

Ɗago fuska Zannor ya yi da mamaki ya ce,

“Yaushe ka farka?”

Murmushin Bk ya ƙara faɗaɗa kaɗan.

“Tun lokacin da ka ɗaura min ƙaton kanka a kafaɗata.”

Dariya Zannor ya fashe da ita yana ƙara rungumosa.

“Alhamdulillah ba da bangon ɗakin nan muka zanta  ba.”

“Yeah. Ku ci gaba da min addu’a. In kuma nasara ba ta biyo hanyata ba, ka kula min da Mamie da kuma Uncle Mai Martaba.”

Dunkule hannunsa Zannor ya yi tare da nufo fuskar Bk da shi.

“Ka san in ba ka daina min irin waɗannan maganganun kamar mai barin wasiyya ba, zan kai maka naushi?”

Murmushin gefen baki Bk ya yi tare da cewa,

“Ba za ka iya ba ai, rago kawai.”

Dariya Zannor ya sake yi, yana jin wani irin daɗi na mamaye zuciyarsa.

“Nothing will happen to you, In Sha Allah. Sai ka cika duk burinka. Professional player a PSG, sannan ka yi aure ka haifo wa Mamie kyawawan jikoki.”

Shiru Bk ya yi yana kallon sama, yana sauraron Zannor da yake ta lissafa abubuwan da suka kasance manyan mafarkansa.

Daga bisani ya sauke ajiyar zuciya ya ce,

“Dan uwana, ina fatan haka. Amma ka san hakan abu ne mai wahala. Kawai Allah Ya sa mu dace.”

Da sauri Zannor ya amsa da,

“Ameen.”

Mikewa Bk ya yi saboda yana son ya watsa ruwa. Tun da ciwon ya lafa kaɗan, yana jin buƙatar yin wanka da ruwan ɗumi.

Da zarar ya tashi daga kan pillow ɗin, idanun Zannor suka sauka kan robar alawar madarar da Bk ya ɓoye a wajen.

Ya ɗauki robar yana jujjuya ta a hannu sannan ya ce,

“Mutumina, yaushe ka fara rowa?”

Ɗan tsaki Bk ya ja yana tuna lokacin da ta yasar da ita ta arce a casa’in, sannan ya furta,

“Ba tawa ba ce, ta wata ce.”

Da ƙarfi Zannor ya ce,

“Wata ɗin? Wace haka? Ban santa ba.”

Ba ƙaramin mamaki ya ji ba.
Domin jin Bk ya ce wata ce ta ba shi alawar madara abu ne mai wahalar gaske a yarda da shi. Shi da sam baya kula mata ko da kuwa wacece, balle har ya karɓi wani abu a hannunta ya ci.

A karo na biyu Bk ya sake jan wani siririn tsaki.

“Ba abin da kake tunani ba ne, Algaita Sarkin Fassara. Wata yarinya ce mara jin magana da Allah Ya haɗa ni da ita. Sa’ar Nini ce.”

Ya ƙarasa maganar yana ɗaukar towel ɗinsa tare da nufar bathroom.

Da sauri Zannor ya ce,

“Duk rashin jin nata ya kai na Nini ne?”

Girgiza kai Bk ya yi.

Domin ya san Zannor ba zai taɓa fahimtar abin da yake nufi ba sai ya haɗu da Waheeda da kansa.

Dan tun daga ranar da Waheeda ta take masa ƙafa, ta goge masa hadda, har ma ta danganta kyakkyawar fuskarsa da kosai.

Ta kasance tana sa shi cikin mamaki a duk lokacin da ya tuna ta.

Ya sake girgiza kai sannan ya ce,

“Ai rashin jin Nini nafila ne idan aka kwatanta da waccan yarinyar. Dan yadda ka san ‘yar dangin aljanu, haka take.”

Sosai Zannor ya shiga dariya saboda yadda Bk ya faɗi maganar.

Shi kuma Bk, ba tare da ya ƙara cewa komai ba, ya shige bathroom ya barsa yana ta dariya shi kaɗai.

“Yaya Salma…”

“Naam, Waheeda.”

Ta mirgino kusa da Salma wacce ta ba ta baya, sannan ta soma tabarta.

“Yaya Salma, don Allah ki bani rigarki.”

Salma, wacce bacci ya gama cin idonta, ta ɗago ta dubeta idanunta a lumlumshe.

“Waheeda, don Allah ki bar ni in yi bacci. Kin san ƙarfe nawa ne kuwa?”

Ta turo baki tana cewa,

“Dama na san ba so na kike yi ba.”

Cikin gajiyawa da al’amarinta, Salma ta ce,

“Yi haƙuri, autar. Faɗa min to, wace riga zan baki?”

“Braziyar ki za ki bani. Waccan baƙar kin tuna sa?”

“Kin ga ai ita ce yar ƙarama, kuma za ta yi mini cif-cif.”

Duk baccin da ke addabar idanun Salma lokaci guda ya ɓace. Ta mike zaune cike da al’ajabi, tana karewa Waheeda kallo kamar yau ta fara tozali da ita.

Waheeda ta kwaɓe fuska ta ɗan harare ta.

“To wannan kallon na meye?”

Salma ta ce,

“Tsakani da Allah, ba dole in kalle ki ba? Yaushe kika fara nono? Maza mu gani. Nuna min nonon da za a sawa braziya.”

Ta faɗa tana ɗage rigar Waheeda sama. Shamulallen cikinta ya bayyana, sannan ta kai dubanta zuwa ƙirjinta da ya soma fito da ƙananan ƙirgen dangi kamar kuraje.

Tafa hannaye ta yi ta hau dariya tana bugun kafaɗar Waheeda.

“Ahhh, lallai kanwata ta soma girma. Yanzu wannan kurjin da ko lemon tsami bai kai ba za ki sanya masa braziya?”

Wani mugun kallo Waheeda ta watsa mata, sannan ta kwanta tana juya mata baya. Nan take kuma ta fashe da kuka.

A firgice Salma ta hau bata haƙuri don kar kukanta ya farkar da Ummah.

“Ki yi wa Allah ki yi shuru. Karfe ɗaya saura fa yanzu. Na miki alƙawari zan baki, kuma zan siya miki fari mai bala’in kyau, amma ba yanzu ba.”

Ta ɗan tsaya sannan ta ce,

“Saurin me kike yi? Tunda kika zo a mace ai sanya braziya ya  zamo miki wajibi.”

Waheeda ta juyo da fuska duk hawaye.

“To sai yaushe zan fara sawa?”

Salma ta danne dariyar da ta zo mata, sannan ta ce,

“Nan ba da jimawa ba. A cikin ’yan kwanakin nan za su fara girma. Daga nan sai balaga, shikenan kin zama yanmata . Sai aure, mu ci uwar sabada .”

Sai a lokacin Waheeda ta ji sanyi a ranta. Murmushi kaɗan ta yi, sannan ta matsa kusa da Salma ta rungume ta.

Washe gari suka tashi suka gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba. Ana cikin zuba kayan da za a fita talla da su a cikin roba, sai suka ji sallamar Baba Karami. Ya shigo tare da wani farin dattijo mai cike da kima, sanye cikin manyan kaya, kansa ɗaure da rawani.

Da gudu su Waheeda suka nufe shi suna rungume shi tare da fadin,

“Ga Mallumjo! Oyoyo Mallumjo!”

Murmushi ya yi yana shafa kawunansu.

“Sannunku, ’yan matan Mallum.”

Da sauri Ummah ta dauko tabarma ta shimfiɗa masa tana yi masa bismillah. Bayan ya zauna ne suka tsugunna har ƙasa suna gaishe shi cikin ladabi.

Mallumjo, wanda farin cikin ganin jikokinsa ya mamaye zuciyarsa, ya amsa cikin fara’a tare da tambayar lafiyarsu.

“Fatan ba wani abu da kuke buƙata ko? Na san yanzu haka ya bar garin nan bai bar muku komai ba.”

Murmushi Ummah ta yi ta ce,

“Ahh, komai Alhamdulillah. Mun gode sosai.”

Ta zaɓi ta ɓoye masa halin da suke ciki ne, saboda ba ta ga dacewar su ɗora masa nasu dawainiyar ba. Shi kansa yanzu yana buƙatar kulawa daga ’ya’yansa da jikokinsa, amma hakan bai samu ba. Daga Baffah har ɗan’uwansa da ke ƙauye, babu mai ƙarfin da zai taimaka masa yadda ya kamata. Maimakon ya samu taimako daga gare su, shi ne ma idan amfanin gona ya yi kyau yake taimaka musu da kayan abinci.

Mallumjo har zuwa wannan tsufan nasa bai naɗe hannu ya zauna yana jiran a ba shi ba. Babban malami ne, kuma manomi ne. Duk da tsufan da ya zo masa, har yanzu yana iya ƙoƙarinsa wajen taimaka wa gidan Baffah duk sanda ya samu dama.

“To masha Allah. Allah Ya muku albarka, Ya ƙara muku zaman lafiya. Sannan ku riƙa haƙuri da juna.”

Daga nan ya shiga yi musu nasiha cikin hikima kan rashin zaman lafiyar da kan taso a tsakaninsu.

Alama Ummah ta yi wa Salma da ta zuba masa alale da ƙosai a kula ta kawo masa.

Sai ya dubi Waheeda da ke zaune a gefensa, cikin harshen Fulfulde ya ce,

“Matso nan kusa da ni, Mamana.”

Waheeda kuwa ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, domin babu abin da ta sani a Fulfulde. Salma ma dai tana gane wasu kalmomin, wasu kuma ba ta ganewa.

Murmushin manya ya yi, sannan ya dubi Ummah ya ga yadda ta zuba musu ido tana jiran abin da zai yi.

Sai Mallumjo ya ce,

“Ban ji daɗi ba sam ace wai jikokina ba su jin yarensu ko kaɗan. Gaskiya ya dace ku fara koyan yaranku, kar ku dogara da na wasu.”

Baba Karami ya yi murmushi yana sosa gemunsa cikin zolaya ya ce,

“Tsohon nan, kai fa rigimarka yawa gare ta. Me kuma koyan yare rana tsaka fisabilillahi?”

Dariya kawai Mallumjo ya yi, sannan ya sake kiran Waheeda, amma wannan karon da Hausa.

Ta matsa kusa da shi cikin fara’a. Allah Ya ɗora mata son tsohon fiye da yadda take son Baffah ma. Yana nuna musu gata fiye da ƙima, duk abin da ya samu sai ya tuna da su.

“Mu ga hannunki.”

Ya faɗa yana buɗe mata tafin hannunsa mai laushi da tsufan shekaru ya tattara fatarsa.

Waheeda ta ɗora hannunta a cikin nasa kamar yadda ya buƙata.

Shiru ya yi yana ƙarewa tafin hannunta kallo.

Nan take Ummah ta ji gabanta ya faɗi da ƙarfi. Da sauri ta janye hannun Waheeda tana rungume shi.

Duk idanu suka koma kanta.

Ba wannan ne karo na farko ba, kuma ba na biyu ba. Duk lokacin da Mallumjo ya yi yunƙurin karanta zanen ƙaddarar Waheeda, sai Ummah ta dakatar da shi.

Murmushi Mallumjo ya yi sannan ya miƙe tsaye ya dubi Ummah.

“Maimunatu, abin da kike son ɓoyewa dole sai ya bayyana. Hanani karanta zanen ƙaddarar Waheedatu ba zai hana abin da kike gudu faruwa ba…”

Sai ya ci gaba cikin harshen Fulfulde

“Da kin bar ni na duba, watakila zan iya ganin wani abu dangane da rayuwarta, a san ta inda za a shawo kan lamarin.”

Ya ɗan dakata kafin ya ƙara da cewa,

“Saboda haka ki yi kuka da kanki idan wani abu ya faru a gaba, wanda ba ma fatan hakan.”

Kankame hannun Waheeda Ummah ta yi a ƙirjinta, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi. Wani irin tsoro ne ya mamaye ruhinta gaba ɗaya. Kalaman Mallumjo sun sake tayar mata da tsohon fargabar da ta shafe shekaru tana ƙoƙarin binnewa a zuciyarta.

“Ni zan wuce. Ku kula da kanku, Allah Ya muku albarka.”

Ummah, da kanta ke kallon ƙasa, ta ce,

“Mun gode, Mallum. A huta lafiya.”

“Ameen, Maimuna.”

Su Mama Sadiya ma suka masa addu’ar Allah Ya tsare hanya.

Baba Karami kuwa, Salma ta miƙa masa kular Mallumjo, sannan suka fita domin mayar da shi gida.

Bayan fitarsu ne Salma ta ce,

“Ummah, ni kam na fece, kar lokaci ya kure mana in yi kwantai.”

Ummah ta gyada kai.

“To shikenan. A dawo lafiya. Waheeda ta ce a ƙofar gida za ta yi tallarta.”

Tare Zuwaira da Salma suka fice. Zuwaira kuwa sai faman aikawa Waheeda saƙonnin harara take yi. Ita kuma, ko kaɗan hakan bai dame ta ba. Ai farin ciki ne ya cika zuciyarta. A yau ta samu ’yancin yin tallarta ita kaɗai, sai yadda ta ga dama.

Saboda haka, hararar Salma da ta Zuwaira ba su shafi kwalarta ba balle su dame ta.

Ƙaramar kujerar tsugunno ta fito ta ajiye a bakin ƙofar gidansu, sannan ta kawo bokitin da aka cika da manyan ƙosai masu zafi, waɗanda suka sha suya suka yi jajir. Ko daga nesa kana hango su, za ka ji bakinka ya cika da ruwa.

Kamar wasa, mutane suka fara zuwa suna siya.

Cikin annashuwa da farin ciki take yi wa kwastomomi hidima. A zuciyarta kuwa sai faɗi take,

“Ko naira ɗaya Ummanmu ba zai yi ciwon kai ba. Sai na fi Yaya Salma yin ciniki. Tunda ita uwar tausayi ce rabawa mutane kaya take yi, ba ta damu da wahalar da Ummah take sha ba.”

Tana cikin hirarta da zuciyarta, sai ta ga an ajiye mata takardar naira biyar a kan roba.

Sai ta ji wata siririyar murya tana cewa,

“A ba ni ƙosan naira biyar.”

Da sauri ta ɗago, tana son ganin  wani isasshen mara mutunci ne da bai san tsadar wake da man gyada ba zai ce a ba shi ƙosan naira biyar.

Amma da idanunta suka sauka a kansa…

Wata irin dariya ta fashe da ita, tana rufe fuskarta da hijabinta.

“Kai, Ya Ado! Allah, ban yi zaton kai ne ba. Na ɗauka wani ne, har na shirya in masa tijara, in ce bai san tsadar kwanon wake ba.”

Dariya ya yi, sannan ya ja kumatunta cikin kulawa.

“Inyeee… Da gaske fa, Yar Autar Ummah an girma. Ummah ta yi dabara da ta kintsa ki a nan.”

Da rashin fahimtar inda maganarsa ta dosa, ta ce,

“Eh mana. Ai su Yaya Salma ne suke min walakanci, shi ya sa na ce wa Ummah ta rabani da ita.”

Ya sake sakin dariya.

“Ah, da gaskiyarki. Kin ga a nan ma za ki fi yin ciniki.”

Ta washe baki cikin jin daɗi.

“Bari in ba ka ƙosan ko ta Murtala ce.”

Ya girgiza kai yana murmushi.

“Kar ki damu, Hajiya Waheeda. Na san an ajiye min nawa. Bari in shiga ciki kawai.”

Yana faɗin haka ya nufi cikin gidan yana dariya.

A ransa kuwa ya ji daɗi matuƙa. Ya lura wannan talla ta taimaka wajen karkatar da hankalin Waheeda daga abubuwa da dama. Rashin jinta  da son tsokana sun ragu ƙwarai. Yanzu duk hankalinta yana kan ciniki, abin da ya sa kunnuwan gida da bakunansu suka samu hutu kenan.