BABAN KAWATA

Chapter 31

by @smauta

Sai kusan 2 na dare ta kwaci kanta,maida kofan toilet yayi a hankali ya rufo yana kallonta gaban wardrobe ta dukunkune kanta da hijabi duk kunyar sa ce akeji ahaka😹gefenta ya tsaya ya bude dayan gefen wardrobe kayan baccin sa ya jawo baya ta bashi bai kulata ba ya zare towel din jikinshi yashiga kiciniyar saka kayan gadon su ya kalla duk ya cukurkude dakanshi ya gyara gadon ya kwanta yanajin kanshi uwa wani dan autan zakiiiiii...........





Mintina kadan tagama nata shirin pillow da bargo ta dauko duk yana kallonta shimfida tayi a kasan gadon ta kwanta murmushi mai yar kara ya subuce masa yana tuno duk wani abu daya a faru a yanzu,a nata bangaren itama tunanin ne fall a ranta dama haka auren yake wohoho kowa zai gane ma sunyi wani abu ba wanda takejin kunyar shi sama da halim taya zan kalleta gobe ohhni manar da wannan tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita😹..........







Bai farka ba sai asuba da sauri ya tashi Innalillahi inakan gado matana ta kwana a kasa baccin nan bai kyauta man ba,da sauri ya maidota kan gadon bacci takeyi mai nauyin gaske har gari ya soma haske bata farka yasan tagaji bayason kuma ya takura mata a hankali ya fara hura mata iskar bakin shi mai dan karen kamshi my life cikin bacci taji kamr mutum akanta firgigi ta mike rungume ta yayi ganin ta tsorata nine, kin makara sallah sai lokacin ta kalli labulayen dake kadawa a hankali hasken rana ya soma washe garin................






Anan inda tayi sallah ta kwanta cikinta ne ke mata wata irin damƙa a hankali a hankali sai wuraren 10 yashigo gidan jikin sharkaf yayi exercise inda yabar ta ya sameta hankalin shi ya tashi baby girl meke damunki???dakyar ta ciro kanta ta kalle shi da hannu tayi mashi alama da cikinta yunwa ne ko wayar sa ya dauka dake kan bedside drawer cook dinshi ya kira sir already komai nakan dinning..............





Muje kiyi breakfast jiya bakici abinci ba takalmin shi kadai ya cire ya dauko wasu slippers masu balain kyau ya saka yana riƙe da hannunta har suka iso babban parlourn gidan ka sakeni,why?halim na nan fa shine me?bazan rike hannun matana ba saboda diyata oya let's go kujera yaja mata suka zauna fara bude abinciccikan yayi............






Bari naje na kira halim bata jira amsar shi ba ta haura sama wurin kawarta bacci lakadan ta sameta tanayi bugu ta zabga mata a kafa hali na nan ki tashi muyi breakfast 🙄 kaiiii ummi am tired jikina ba dadi wlh meye kika dafa bansani ba fiddo kanta tayi daga cikin bargon tayi ahhh ya baki sani ba?daddy ne yayi?😳😳😳😳ido ta zaro wane daddy rufaman asiri ke cewa tayi da dariya tasan dama za'a rina............





Wannan idon da kika fito dashi waje na minene?bazanyi fa breakfast ba lunch kawai zanci dan Allah ki tafi ni kike kora eh mana toni zaki takuraman ne bakuma tsareki zanyi da tambayar ina kika kwana ba kinata kame kame feel free dan ma kinyi auren da bazan iya tsoma baki ba hahahaha ai da kinsha iya shege da gudu manar ta bar dakin halim na daria tace hmmm bestie kenan Allah ya dawwamar mana da farin ciki a gidan nan..............





Yana nan inda ta barshi tadawo where is she?ummm wai ta koshi,oya come 🫴 hannu ta miko ya kamota a hankali har kan cinyarsa ta samu masauki mai kyau fara zuba loaded chips din yayi sannan yace do you want to take coffee or tea muryar mai sanyi dadi tace tea,dakanshi ya haɗa mata kakkauran tea ya fara bata tana shaaaaa...........







Kusan hour su daya a wurin yana feeding dinta saida ya tabbatar tayi gammmm sannan ya hada coffee dinshi shima yasha mutum ne shi ba maa bocin son abinci ba,gefen kunneta ya shafo a tare sukaji wani yarrrr a hankali ya langwabe mata i want to take shower 🚿 🚿 🚿 zaki tayani?da sauri ta sauka akan cinyarsa tana girgiza mashi abinda ya faru jiya yana dawo mata sabo filll a cikin kanta knocking kofar parlour ya dawo dasu hayyacinsu duka..............






Ma'aikatan gidan ne suka fara shigowa da wata tsaleliyar baturiya, lokaci daya manar ta hade fuska ganin tawagar harda mace daga nan inda yake ya basu izinin zama a parlour har lokacin hannunta na cikin nashi ya mike tsaye parlour ya nufo da ita sarai yaga yadda fuskar ta ta canza sosai,wasu files suka ajiye gabansa ya bude magana sukayi sosai uffan bata ce ba har suka gama tana makale a gefen shi koda suka mashi sallah bayan sun tafi ya kalleta da kyau MANAR........






Sai da gabanta yadan fadi jin ya kira sunanta duk da ba wannan ne karo na farko a gareta ba,wani abu na damunki?cikin tsiwa tace meka gani mezai dameni me akayi da wani abu zaya dameni?jawota yayi ta shigo jikin shi sosai sannan yace wannan duk kishi ne???Bella ce wannan da abokan aikinta itace mace ta farko data fara taimakona bayan nayi karayar arziki yanzu haka Company na lagos yaranta yakeman managing dinshi matsala ce ta taso ta gaggawa acan din yazama dole gobe naje lagos shine tazo fa..........








Marmarmar tayi da ido,shafa bayanta yayi bakyaso in tafi?batasan ma tayi ba a hankali tace ehhhhh,kara shafa bayanta yayi zaki bini muje tare girgiza mashi kai tayi meyasa za'a bar halim bakowa a gidan dan shuru yayi na seconds sannan yace bazan dade ba idan ma matsalar naje naga ba babba bace kwana daya zan dawo highest nayi kwana ukku nima tunda na sameki banajin zan iya nisa dake baby girl you're my life now🤩🤩🤩