Introduction
A DAREN AURENA
بسم الله الرحمن الرحيم.
Ranar juma'a da misalin ƙarfe hudu na yamma, wani matsaikaicin gida ne wanda akaiwa sabon fenti da sai kyalli gidan ke yi da daukar ido, yayinda yara ƙanana da matasa keta faman danna kawunan su cikin gidan su na shigewa, ganin nima zasu barni a tsaye yasaka na bi bayan ayarin wasu yan mata da suka nufi ƙofar gidan za su shiga, nima bin bayansu na yi muka shige atare.
Madaidaicin tsakar gidan cike ya ke da mutane, yayinda hayaniya ke tashi kamar ana fada, a gefe guda kuma wa ta matashiyar budurwace sai cika ta ke ta na batsewa tare da hura ɗan karamin kyakkyawan hancinta ta na tunzuru baki gaba.
Muryar wa ta mata na ji ta na fadin.
"Na rantse da izo sittin tsarkakakke idan na yarda ZULAIKA tabar gidannan da nufin aure ba tare da ambiya ni kuɗina ba shegiya uwata Talatu ta haifeni, na fadi na kuma wallahi ko an daura aure nan ne rakazo daukar amarya sai na riketa babu inda za ta je sai ambiyani kudina."
Ta na aje zancenta wa ta farar dattijuwa ta cafe ta fara rantafo nata jawabin itama.
"Yau ni Salamatu ɗiyar Sule jikar Salmai na ga abin da ya ishe ni, wannan wace irin dibar albarka ce da kowace mace zata kwaso kafafuwa rabai-rabai ta zo da wani zancen banza, dan abu da kazar uban mutum mi yasa da can baya babu wanda ya zo yai magana sai yanzu a daren aurenta sannan zaku zo da wani zancen banza da wofi, na rantse da sittin ta Ubangiji duk ƙatuwar matar da ta sake zuwa da wani zance nata na iska sai na saka Maradiyya ta zaune min ita, abin ya ishe ni hakanan."
Tsohuwar na dire maganarta wannan matar ta cakumo wuyan wannan budurwar me zumɓure-zumɓuren baki suka kacame da kokowa.
Aifa kankace mi gidan ya hautsine da dambe dan wanda mafi yawan mutanen da ake fadan dasune suka taru suka rufe wannan matashiyar da duka.
Uban ihu wannan farar tsohuwar ta rafka tare da neman agaji ganin yanda manyan mata kusan biyar suka taru akan jikarta ita kadai.
Taɓar-taɓar wa ta mace me ƙiba ta nufo wajen da hanzarinta, ta na isowa batai wata-wata ba ta juya bayanta me yalwar mazaunai tika-tika tai kyakkyawan tsalle bata dire ako ina ba sai saman wadanan matan masu dambe, cikin sa'a ta murkushe mace biyu tai zaman yan bori akansu.
Ihun da matan suka saki yai daidai da ihun da masu kallon fadan suma suka saki gami da shewa su na fadin.
"GIWAH! GIWA!! GIWA!!!"
Fuskokinsu fal nishadin yanda fadan ke bata citta, matan da Maradiyya wacce ake kira da giwa ta taushene suka saki kukan azaba, domin kuwa iya wuya sun tausu dan ko lumfashin kirki basu iya fitarwa.
Da kyar Maradiyya tai wani juyi akansu tare sa mulmulawa ta sauka kasa sannan ta kuma yunkurawa ta nufi wajen sauran da suka murkushe yarinya su na ma ta dukan sakwara, sa isrta batai wata-wata ba ta daga lafiyayyen hannunta me kama da cinyar Sah ta dakawa matar da ke ta aikin aunawa yarinyar duka kamar ta samu jaka, gantsare baya matar tai tare da zubewa kasa kamar yarinya ta shiga billayi akasa ta na susar tsakiyar bayanta da Maradiyya ta sauke ma ta duka.
Dagewa Maradiyya tai kamar ta samu jakai tahau nadawa matan duka iya karfinta, idan tai nasarar kai mace kasa sa tabi ta ta taushe da mazaunar ahaka ta galabaitar da matan sai haki ta ke kamar wa ta bijimar Saniya.
Yan kallo kuwa sai ihu suke da alama sun nishadantu da yanda Maradiyya ta suburbudi wadannan matan.
Farar tsohuwarnance ta kamo hannun matashiyar yarinyar da wadannan matan suka rufarmawa ta taimaka ma ta ta shi ta na dingishi, kafin suyi wani yunkuri suka jiyo karar jiniyar yan sanda wacce ta karade unguwar, kafin kace mi yan sanda mata sun shigo cikin gidan kansu tsayu, bayansu kuma wani yamusashen mutum ne sanye cikin riga da wando daban-daban wanda duk sun jeme sun fita hayyacinsu, kafin kowa yace wani abu Malam Auwalu ya nunawa yan sandar wannan matashiyar ya ce.
"Ranki ya dade ofishiya kinga barauniyar can, sannan ki hada sa wadannan matan da ke kwance a kasa dan harda su aka haura gidan nawa ta katanga duk a daure yan banza."
Wa ta irin karar tashin hankali hadi da kuka wannan matashiyar ta fashe da shi tare da fadin. "Na shiga uku ni Zulai wannan nace irin lukutar masifa ce ta same ni A DAREN AURENA, sai kace se Zainabu tace min jeki kya gani, da kwarankwatsi dubu bazanje ofishin yan sanda ba A DAREN AURENA."
Aifa sai gida ya sake kacamewa da hargowa gami da hayaniyar babu wanda ya isa yakai Zulai station a daren aurenta, da dai yan sandan suka gaji sai daya daga cikin wadanda ke waje ya daga murya ya ce "Idan basu fito da wadanda ake zargi ba ku basu wuta kawai ku subulbulesu da alburushi."
Nanfa hantar cikin kowa tahau kadawa jin ance a halbesu da alburushi sannan gashi maccen ta saita bindiga da alama harbawa zatai, ai Zulai da sauran wadanda Auwalu ya nuna tuni suka kai kansu wajen yar sandar jikunnansu na rawa, haka aka tisa keyarsu zuwa waje ko hijabai babu a jikunansu aka loda su cikin mota sauran yan sandan da Auwalu suka hau a tsaitsaye.
Kukane me karfi ya kuma kubcewa Zulai yayinda zuciyarta ke tsalle tare da zullumi akan yanda za'ayi taje asibiti yau cikin darenan dan ta sake dubo ajiyarta, tabbas ba zata bari su isa station ba dolene ta na bukatar zuwa asibiti a yau kuma yanzu nan.
Cak ta tsaida kukanta yayinda ta ayyana wani abu a zuciyarta wanda ya kwantar ma ta da hankali.
Juyawa tai ta kalli makotansu da sukai fada, gani tai kowace a cikinsu hankalinta atashe ya ke sannan kuma ga tsoro nan ta na gani muraran a idanuwansu, a hankali ta dukar da kanta kasa ba tare da ta dago ba kusan minti biyu.
Wa ta irin razananniyar kara ta saki wacce ta ratsa ilahirin hanyar gaba dayanta musamman da hanyar ta kasance tsakiyar gonaki, wani irin taka burki drivern motar yai tare da fara waige-waige kafin ya yi wani abu ta kuma kurma wa ta tsawar wacce ta doke ta farko wajen sauti, cike da tsananin tsoro yan sanda da Auwalu suka dire daga motar jikunansu na rawar mazari, matan kuma saboda tsoro sai curewa sukai waje daya suka kankame junansu cikin tashin hankali.
Cikin zafin nama Zukai ta mike tsaye tare daka wani uban tsalle sai kace yar buri ta dirko kasa ji kake "Timmmm" har kura sai da ta tashi, kafin Auwalu da sauran yan sandan sui wani abu tini Zulai tai nasarar yin girgizar da tai fatali da kallabin kanta yalwataccen bakin gashinta ya safko tare da rufe ma ta fuska, lankwashe yatsun hannuwanta tai tare da yin yar girgiza ta watsa gashin kanta ya koma baya, aifa nan Auwalu ya zufe kasa ya na rawar banjo tare da sakin wasu irin tusoshi masu doyin gaske, sauran yan sandan ma jikinsu bari yahau yi ganin yanda idanuwan Zulai suka markwade bakin ya bace bat sai farin kawai ake gani.
Cikin karairaya da tangadi gami da lauye harshe Zulai ta fara takowa ta na tunkarar Auwalu sa Yan sanda ta na fadin.
"Ku bil adama yan isaka marasa mutunci da sanin darajar mata, ku sa ni cewa yau ajalinku ya zo domin kuwa dole ne mu kashe ku mu shanye jinin jikinku sannan mu rataye namominku a bishiyar gidan me gari, dolene yau ku karbi hukuncin kama godiyarmu da kukai ba tare da ta muku laifin komai ba saboda kawai wancen me kama da sauron ya baku cin hancin naira dari biyar."
Tai maganar ta na lauya kanta zuwa inda Auwalu ya ke a kwance hannuwansa a sama alamar yayi saranda sai faman sakin tusa ya ke yi tare da shan majina kamar karamin yaro.
"Kai Auwalu dan gidan Malam Barau jikan Hassula diyar Auduwa ka sa ni yau dole ne muyi gutsi-gutsi da kashin jikinka tunda dan sam babu tsoka a jikinka sai kashi lullube da fata kamar wani kwarangwal."
"Assalamu alaikum ranku ya dade mutanen boye masu abin mamaki ku dubi girman ubangiji ku yi man rai, wallahi na bi Allah sa Manzonsa kuma na biku, na amince zan zama baya ga godiyarku kuyi hakuri ku barni d raina tunda dai kunga bani da wani nama a jikina sai kasusuwa, suma kasusuwan wallahi tauri ne dasu kamar karfe Kakan kakan kakana na gado wajen rama da bushewa haka ya ke shima kamar tsinke sai katon kai kamar tulu." Auwalu ya fada ya na fashewa sa matsanancin kuka dan harga Allah a mugun tsorace ya ke ga shi zawayi ya kubce mai irin me fitowarnan da tsananin kara ji ka ke "Furutsutsutautsu, futsts, fettttt baratatatata." Karar fitar zawo mai tsananin karni.
Saurin kawar da kai Zulai tai zuwa gefe dan wani irin bala'in doyi ne ya dumame wajen wanda ya saka saura kadan asirinta ya tonu dan da kyar ta hana kanta toshe hanci sa zubar da yawu, kallon yan sandan nan tai wadanda sukai tsamo-tsamo tumbinsu sai rawa suke su kowa matan sai kara kankame juna su ke tare da zazzare udanuwa dan kukanma yaki futowa saboda tsabar tsoro, gani suke kamar Zulai Aljanna ce ba mutumba ganin yanda suffarta ta juye lokaci guda.
A DAREN AURENA littafin kudi ne akan naira 300 kacal
KU BIYONI DAN JIN WANDA ZATA KAYA ACIKIN WANNAN LABARI MAI TAKEN A DAREN AURENA.
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR⭐⭐⭐
(YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪)
***