Chapter 2
بسم الله الرحمن الرحيم
Dariya ce keson kwacewa Zulai ganin yanda jaruman ƴan sandan da ake ji da su a ƙauyen sun tsure daga tada aljannun ƙarya, da kyar ta yi jarumtar saisaita kanta tare da sake juye idanuwanta suka yi sama ta fara magana cikin murya mai firgitarwa.
"Ku bil Adama!!!!!! ina so ku bani hankullanku nan dan ku ji abin da zan fada muku, ina so ku duka mazan da matan ku tashi ku fara share wannan hanyar da hannuwanku, kuma ban yarda kowa ya zo wucewa ku fadi ma shi abin da ya faru ba, muddin kuka saki wani ya ji wannan magana to babbu shakka sai mun zo mun dauki mutum mun kaishi can bayan duniya ya rinka yi mana gadin dabbobinmu, sannan kuma duk wanda ya sake shiga sabgar godiyarmu koda kuwa bashi ya ke binta babu makawa sai mun ɓatar da mutum mun bat, daga doron ƙasa, yanzu muna sauri ne zamu je can bangon duniya mu dubo sabon jinjirin da aka haifa mana idan muka dawo nan da minti ashirin muka iske baku gama ba zamu tattare ku mu tafi da ku can duniyarmu."
Ta na gama faɗin hakan ta fara tafiya ta na karmaɗe jiki kamar macijiya tare da ɓaɓɓaka wa ta irin mumunar dariya mai saka tsoro a zuciyar mai saurare, da yake Allah ya azurta Zulai da zazzakar murya irin mai tsuwarnan kamar kukan tsumtsaye.
A jiyar zuciya mai ƙarfi Zulai ta saki lokacin da ta sha wata yar kwana, numfarfashi ta shiga saukewa gami da sharce gumin da ya tsatstsafo mata, fararen manyan idanuwanta sai tsiyayar hawaye suke saboda yanda ta dinga juyasu, siririn hannunta ta saka bayanta gami da tattare yalwatacciyar baƙa ƙirin ɗin sumar kanta ta tufke ta a baya, wa ta arniyar dariya ce ta kubce ma ta tuno yanda Auwalu ya tsure har da sakin zawayi a wando bayan tusoshin da ya gama kumbura ma su ciki da su, sai kuma yanda Ta Rasulu ta dinga zare kananan idanuwanta ta na muzurai tare da bude baki kamar zatai magana amma ta kasa sai wani irin tsoro da ya bayyana a fuskarta muraran kamar ba ita ba ce ta gma cika baki har da yin dambe a gidansu saboda ta na binta kudi.
Saurin yana gyalen rigar jikinta ta yi mayafi da shi, cikin hanzari ta ke taka fararen kafafuwanta da suka sha jan lalle ta na tafiya ta na tunanin ajiyar da tai a sibitin da ke garin.
Tafiyar mintuna sha biyar ta kawo ta bakin karamin asibitin wanda jama'a sukai dafdala a wajen su na ta gudanar da harkokin kasuwanci su ga hayaniya da ta cika wajen saboda kai komo, babu wanda ya damu da wajen asibiti ne akwai marasa lafiya waɗanda ba su buƙatar hayaniya.
Cikin sauri ta janyo mayafinta gudun kar wani ya gane ta ta yi hanzarin shigewa asibitin, ba ta tsaya ko ina ba sai dakin da aka kwantar da majinyata maza, dakin sai ƙarni ya ke ga masu jinya sai surutai da hayaniya su ke babu ruwansu, ba ta tsaya kula kowa ba ta wuce fuuuuuuu ba tare da ta bawa kowa damar ganin fuskarta ba, sai da ta kai karshen dakin ta buɗe wani yalolon mayafi da aka rufe aka raba wajen da sauran majinyatan da ke dakin sannan ta tsaya ta jingina ta na maida numfashi, takai minti uku a tsaye kafin a hankali ta karasa gaban gadon ta tsaya tare da rankwafawa daidai saitin fuskar kyakkyawan baturen matashin da ke kwance idanuwansa a kulle alamar barci ya ke.
KAR KU MANTA WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, IYA BOOK ONE NE KAWAI FREEE.
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRUTERS 💪.
***