Chapter 3
Zuciyarta na tsitsinkewa gami da dokawa cikin tsananin ƙarfi ta durƙusa a gaban matashin tare da fara zubar da hawayen masu tsananin zafi ta na fadin.
"Ban san wace hikima ce Ubangiji ya ɓoye a tsakaninmu da har ya sanyoka cikin rayuwata A DAREN AURENA daren da nike fata da mararin zuwanshi tsawon shekaru, daren da nai alkawurra da dama tare da cin manyan burika da alwashi a cikinsa, daren da nike fatan ya zama dare na ƴarshe da zan sake wayuwar gari a cikin wannan ƙauyen mai cike da mabanbantan mutane ma su mabanbantan al'adu, A DAREN AURENA da sanyin safiya kaddara ta hada ni da kai, kuma kaddarar aure za ta raba mu rabuwa ta har abada, daga lokacin da nai tozali da kai lissafina ya kwance, burukan da na daɗe ina ginawa suka tarwatse a ciki kuwa harda burin mallakar muradin zuciyata, lokacin da na fara tozali da kai yashe a ƙasan gona a gefen hanya cikin mawuyacin hali a lokacin ne burukana suka fadi kasa wanwar tare da rugujewa gaba dayansu, A DAREN AURENA na hadu da kai kuma A DAREN AURENA zan rabu da kai ba tare da nasan koda sunanka ba, zan tafi imbarka a hannun likitan birni Abdul nasan zai kula da kai sosai ina maka fatan alkairi da samu lafiya ya kai wannan kyakkyawan matashin ni ce ZULAIKA wacce ake kira da Zulai Mamman a makaranta a gida kuma ana kira na da Zulai yayinda Habu saurayina kuma mijina na gobe ya ke kira na mai lof ya ce wai sunan ƴan birni ne wanda suke kiran masoyi da shi."
Shiru ta yi tare da goge hawayen idonta ta tashi da zummar ta tafi caraf ta ji an damki hannunta wanda sai da tai baya tsabar tsoro kamar zata fadi amma aka kuma fizgota da tsananin karfi wanda hakan ya saka ya fada ruf da ciki akan wannan matashin mai kama da turawa tai flat akan shi, yayin da hakan yai daidai ta rafka salatin Iya Abu da sauran jama'ar da suka shigo wajen a tare sukai tsaye cirko-cirko sai zare idanuwa suke uwa na mujiya.
"La'ilahwa ilallahu, inna atuni minal tone-tone yau ni Audu gwangwan na ga abin da ya ishi uwata Salame, wato dama labarin da ya karade gari cewa kina can yawon iskanci A DAREN AURANKI, to wallahi uban kuturuma yai kadan yau sai munga ubanda ya tsaya maki a kauyen nan yar iskar yarinya mai halin ban...."
Bai idasa fadin abin da zai fada ba Zulai ta taso da dukkan karfinta tare da yin girgiza ta wancakalar da ɗan kwalin kanta ta barbaza gashinta ya zubo gaba da baya sannan ta fasa gigitacciyar ƙara tai kan Audu gwangwan da yai suman tsaye lokacin da yai tozali da juyayun idanuwanta, daram Zulai ta makale akan Audu gwangwan da ya ke yana da jiki ma sha Allah, siraran hannuwanta ta daga ta dinga tallare sontaleliyar keyar Audu gwangwan wacce ta sha askin kwal da kobo sai sheki ta ke gami da walwali, cike da tsananin tashin hankali Audu gwangwan ya shiga kiciniyar yanda zai sauke Zulai daga jikin shi ya kasa, kyarma su mai gari da sauran mutanen wajen suka shiga yi jin yanda Zulai ke wani irin gurnani mai ban tsoro, sai da ta rantali kan Audu gwangwan san ranta sannan ta kyale shi ganin har ya fara kukan azaba, direwa ta yo daga kan shi ta nufi inda me gari ya ke tsaye ya na sallati gami da addu'o'in neman tsari daga sharrin shidanun aljannu, bai yi aune ba ya ji hannun Zulai akan gemunshi ta janyo da iya karfimta, wani irin gigitaccen ihu mai gari ya saki jin yanda aka wani fizgi dogon gashin gemunshi, cike da azaba ya ke neman agajin mutanen da ke wajen amma babu wanda yai koda motsi bare akawo mai dauki, kuka mai gari ya saka kashirɓan tare da bawa Zulai hakuri tare da yi ma ta alƙawurrra da yawa.
Ita ko Zulai yi ta yi kamar bata san abin da ke faruwa ba dan kuwa dama can ta na jin haushin mai gari da tawagarshi saboda yanda suka saka ma ta ido
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪