Chapter 4
بسم الله الرحمن الرحيم
Idanu suka hana ta rawar gaban hantsi ga wani bin diddiƙinta da suke saboda kawai wanda za ta aura ya na dan mai gari, sai da Zulai ta tabbatar da ta wajiga mai gari sosai dan shima sai da ya yi kuka sannan ta kyale shi, haka ta bi mutanen mai gari da su kadai suka rage a wajen dan kowa ya watse dan tsira da lafiyarshi, su ma fadawan duk sun tsure ganin yanda ake azabtar da mai gari, babu halin tserewa ne saboda muddin mutum ya gudu idan wani abu ya faru to fa ancire shi daga matsayinshi.
Zulai na sakin gemun mai gari tai baya-baya ta fada luuuuu a jikin wannan matashin tai daidai abinta, a zuciya ta ke fadin 'Wai dama wannan baturen haka jikinshi ke da laushin tsiya wallahi sai na mori wahala ta akan shi, sabo da ceto ranshi yau nai gwagwarmaya harda sadaukarwa sai da nai wallahi, ina dalili gwara in bararraje in more laushin wannan fatar.'
Yayinda a fili kuwa ta shiga yin murkushe-murkushe tare da sakin numfashi ta koma tai lakwas alamar ta dawo hayyacinta, mai gari tun da ta saki gemunshi ya tattare babbar rigarshi tare cire takalmanshi ya saita hanya ya kwasa a mugun guje, fadawanshi ma ganin oga ya tsere su ma suka rufa ma shi baya kamar masu gudun tsere dan kuwa kowa fata ya ke ace ya wuce dan uwanshi, gudu suke bakin rai bakin fama ga rigunansu sai cika suke da iska, babu inda suka ci birki sai a fadar mai gari, nan kowa ya zube ya na maida lumfashi, ko gama sauke numfashi basuyi ba suka hango zugar mutane da wata irin kura na tashi, da mugun gudu mutanen ke tafe wani azakwakwuri ya dage sai ɗaga murya ya ke yana fadin.
"Jama'a kowa yai ta kanshi yau gari ba lafiya, mata ko wace ta shige gida ta kulle yau garin nan babu lafiya."
Aifa su me gari jin haka ya saka su saurin tashi tare da bin ayarin wannan tawagar aka shiga tiƙar gudu da su, kafin kace mi kowane gida an garƙame shi babu wanda ke buɗe hatta masallatai duk an kulle su, haka wannan tawagar ta mutanen suka shiga tikar gudunsu babu gajiyawa, abin ka da mutan kauye dama ansaba aikin karfi hakan ya saka basu gaji ba sai da suka tabbatar da sun fice daga kauye sun nausa cikin jeji sannan suka ankara suka zauna maida lumfashi.
A bangaren Zulai kuwa sai da tai kusan minti goma ta na morar dadin jikin baturen matashinan sannan ta buɗe idanuwanta da suka canza launi, karaf idanunta suka sarke dana wannan baturen dan kuwa ya kure ta ne da kaifafan fararen idanuwansa ya na kallonta, cike da basarwa kamar ba shine ke kallonta ba ya ce, "saukarmin a jiki".
Saurin direwa Zulai ta ui daga jikin shi zuciyarta na tsalle kamar me shirin buɗe kirjinta ta fito, idanuwanta kememe babu wa ta damuwa ta fara rantabo jawabi
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪
"Malam ya da haka, kasan irin kasadar da na ɗauka kuwa wajen ganin na taimaka ma ka, shine dan na ɗan hau jikinka shine zaka wani buɗe tsatstsaman bakinka ka...."
Ɗif ta yi jin yanda ya fizgota da ƙarfi ta faɗo jikinsa, cikin ƙaramin sauti mai cike da amo ya ce "Indai jikina ne zo ki kwanta ki yi birgima akai yanda ranki ke so babu mai hana ki, ni ɗan halak ne bazan mance alkairinki a gareni ba, ba dan kin taimakeni ba da yanzu bana cikin wannan duniyar ke ɗin ta musamman ce a wajena dole ne in baki dukkan abin da kike so damma dai ni ina tsoron mace mi aljannu musamman irinki mai rantalar ƙeyar maza."
Waro ido Zulai ta yi sannan ta ce.
"Wa ya ce maka ina da aljannu, Malam bari janyo min bala'i ni lafiyata ƙalau wallahi na yi abin da na yi ne dan inyi maganin waɗanan shaiɗanun mutanen baka san halinsu ba ne tsaf zasu ƙullamin shari a garin nan fita ma ta gagari iyayena da ƴan uwana, kuma dama na daɗe ina jin haushi me gari da Audu gwangwan shi yasa nai masu laga-laga ƴan kwal uban."
Zulai ta katse wannan matashin daga maganar da ya ke.
Wani tunani ne ya bijiro ma matashin, jinjina kai yai alamar na'am da zance zucin da ya ke hakan ya saka ya nutsu sosai sannan ya fuskanci Zulai ya fara magana a bisa umurnin zuciyarshi.
"Na ji maganganun ki kuma na fahimce ki sosai, sannan kin burge ni da kika tsaya kika ɗaukarwa kanki mataki har hakan ya saka na ji ina sha'awar saka ki cikin rayuwar ɗan uwanah wanda ya ke fuskantar matsaloli masu sarƙaƙiya, idan za ki amince da ni zan saka ki aiki a kanshi sannan zan biya ki miliyoyin kuɗaɗe, na yi maki alƙawarin cika ma ki dukkanin burukan rayuwarki muddin za ki amince da buƙata ta ni sunana Fadeel ina zaune ne a garin ABUJA ɗan uwana na sunanshi FAHAD...."
Nan ya shiga zayyano zance tare da fatan samun amincewar Zulai dan ya hango maganin matsalolinsu a tare da ita.
Yayin da ya ke magana fuskarshi caɓa-caɓa da hawaye, haka Zulai ke zabura tare da nuna tashin hankali, wata maganar kuma idan yai sai kaga ta tashi ta na ɓurme-ɓurmen zaki, wa ta maganar kuma sai ta ciji yatsa ta jinjina kai, bai gama kai ƙarshen maganar ba Zulai ta katseshi da faɗin.
"Ya isa haka Fadil barni hakanan kar zuciyata ta buga inmutu a banza saboda baƙin cikin wannan labari na ka, ai tsaya ka ji zuwana birnin tarayya dole ne, dole inshiga cikin ahalinku dan inhidda baragurbi sannan inci uban munahwukai da ƴan iskan masheranta, amma wani hanzari ba gudu ba, yauɗin shine daren aurena bazan iya tsallake wannan ranar me daraja ba, kuma bazan iya barinka ka tafi kabarni anan ba yanzu minene abinyi?."
A ɓangaren su me gari kuwa, su na can cikin daji a zazzaune kowa da abin da ya dame shi, ga ƙishirwa ta addabesu ga shi sun kasa gane hanyar gida bare su dawo, wasu daga ciki har sumfara kuka saboda gabatowar kiran magrib, ya yinda me gari yai tsuru-tsuru kamar tarko ya kama kura, zuwa can Audu gwangwan ya buɗe baki ya yi tambayar da ta saka kowa kallon ɗan uwanshi dan jin mi zai ce.
"Wai dan Allah jama'a minene ya yo bi ake kwasar wannan gudun haka?."
Babu wanda bai faɗa tunanin akan abin da ya faru ba, zuwa can wannan jibgegen matashin da ya kware baki ya dinga shela akan kowa yai takanshi ya zabura ya ce.
"Wallahi Allah me gari za ku tambaya dan shi da fadawanshi muka gani sun zage sai tiƙa gudu su ke shine muma muka buyo sahu dan tsira da rayuwarmu."
Kasaƙe me gari ya yi zufar wahala na yanko ma shi, idan tunaninshi ya bashi daidai lokacin da Aljannun Zulai suka tashi ne aka gansu su na gudun ceton rai, kafin ya ce wani abu ya jiyo muryar Sarkin aska na faɗin.
"Wallahi Zulai ce ƴar gidan Mamman Aljanunta suka tashi shine ta...."
Saurin daɗe bakinshi Audu gwangwan ya yi tare da girgiza ma shi kai alamar kar ya faɗi, ajiyar zuciya me gari ya
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪