A DAREN AURENA

Chapter 5

by @maryamstar248

Sauke jin Sarkin aska bai idasa faɗin abin da zai fada ba, ƙuri kowa yaiwa Me gari su na son jin karshen jawabin sai de shi da Audu gwangwan sun hana hakan faruwa.

Sai da duhuwar magrib ta fara sannan Bala mafarauci ya ce ya gane hanyar komawa gida, cike da murna suke bin bayanshi har suka fito daga dajin suka kamo hanyar cikin kauyensu, a gajiye tubus suka iso kowa ka gani a harmutse saboda azabar wahalar tafiyar kasa da kuma uban gudun da suka tika.

Bayan kowa ya je gida yai wanka tare da cin abinci da sallah Mau gari ya aika a yi shela akan ya na son kowa ya zo fada akwai muhimmiyar magana, dayake kowa a ƙage ya ke akan san jin abin da ya faru hakan ya saka kafin Me gari ya fito fada ta cika taf da mutane, ba mazanba ba matan ba har da yara matasa kowa ya zo, a gefe guda kuwa wadannan matan da sukai faɗa ne tare da folisawa har da Auwalu da yai jage-jage da zawo, duk sun jeme sun fita a hayyacinsu kamar wasu korarri.

mutane sai kallonsu ake ana mamakin abin da ya same su musamman da aka san sune sukazo tafiya da Zulai, babu jimawa sosai Mai gari ya fito tsaf da shi sai de idanuwanshi sun zurma ciki sunyi zuru-zuru, bayan ya zauna aka gaggaisa ya fara rantabo jawabi.

"Wato dalilin da ya sa na tara ku anan shine, ina son kawo sauye-sauye da dama yayinda nike so in karrama wasu daga cikin fadawana saboda sadaukarwar da suka yi min a yau da wani iftila'i ya aukomin, sun tsaya tsayin daka wajen ceto rayuwata shi ya saka nima zan saka ma su da alkairi in nuna farin ciki da jin dadin abin da suka yi man, da farko dai ina so kowa ya maido hankalinshi akan wadannan jami'an tsaron da kuma Auwalu keya, idan kunyi duba da idon basira zaku ga sam basa cikin hayyacinsu, Auduwa ne ya tsintosu a hanyar barin gari sun zage sai ɓarza uban kuka suke su na share ciyayi da yatsun hannuwansu, shine yai da su akan su hwadi ma shi abin da ke hwaruwa amma ƙememe suka yi banza da shi sai kuka suke su na shara, da Auduwa yaga abin ya isheshi shi ne yayo waya ya sanar da sauran fadawan da suke zaune anan fada suka je suka dauko su kungansu nan zube kamar yan banza kowa a cikinsu sai nishi ya ke."

Nanfa wajen ya kaure da salati da sallallamin jama'a gami da jajanta abin da ya faru kunsan mutanen kauye da kara da karamci.

Mai gari ne ya sake katse surutun mutanen wajen da fadin.

👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️

WRITE BY

MARYAM STAR ⭐⭐⭐