Chapter 6
بسم الله الرحمن الرحيم
Babban lamarin da ya faru ɗazu a garinnan shine ita dai wannan yarinya wadda za'a ɗora ma ta arme da yaron wajena gobe idan Allah ya kaimu ita ce ke ɗauke da lalurar iskokai wanda basu bayyana ba sai yau da yake daren armenta, babban abin tashin hankalin bai wuce yanda iskokan suka maida kan yarinyar madaddalarsu ba, kanta cike ya ke taf da iskokai dan ko wajen aje tunani basu bar ma ta ba, zancen da nike muku ɗazu a asibiti ba karamin ɗauki ba dadi mukai ni da Audu gwangwan ba da kyar muka shawo kanta ta hanyar tohe ta da addu'o'i, bayan sun bar jikinta shine suka fito fili da makaman yakinsu wai zasu gwabza da mu, da yake kunsan na yi gadon yaki a wajen kakan kakan kakana Zubairu sadauki shine na tsaya cike da jarumta muka fara fafatawa, abinka da sarkin yawa yafi sarkin karfi nan da nan suka cimu da yaki shi yasa mukai ta kanmu muka tsere."
Wa ta irin kabbara gami da hayaniya ce ta kaure a wajen, yayinda kowa ke yabawa da jarumtar me gari da kuma gasgata labarinshi, su kansu fadawan karyar da Me gari ya karkace ya shafto ta yi masu dadi dan kuwa babban abin kunya ne ace sun kasa ceton Me garinsu a hannun Zulai.
Yayinda aka shiga tattaunawa akan hukuncin da za'a yankewa Zulai a fadar Me gari ita ta na can a asibiti su na tattaunawa akan yanda za'a tabar garin ba tare da anzargi wani abu ba, dan jin labarin da Fadeel ya bata ya harzuka zuciyarta matuka inda fushinta ya bayyana muraratan sanan tai alwashin ɗaukar fansa akan yanda ake cutar da rayuwarsu shi da dan uwanshi.
Zulai ba ta ankare da dare yayi ba sai bayan da suka cimma matsaya sannan ta tashi da niyyar tafiya gida nan ne ta ga duhu ya mamaye wajen asibitin sannan babu kowa a ciki sai majinyata waɗanda suka jiggata basu iya ko tashi bare su gudu, Fadeel da sam ba wani karfin kirki a jikinshi ne ya taso suka fice a tare.
BAYAN AWANNI UKU
Zulai ce tafe a gaba hannuwanta rike da fitila mai tsananin haske, fuskarta a cunkushe babu walwala ko kadan yayin da Fadeel ke biye da ita a baya jikinshi a kasalacen ga alamun gajiya sun tabbata ɓaro-baro a fuskarshi, tafiya suke ba ummm babu umumm kowa da tunanin da ya addabi zuciyarshi.
Sai da suka yi tafiyar awanni biyu cir sannan suka fita daga kauyen YAGAWA suka isa babban titi wanda ya ke tsit babu kowa, haka suka yanki wannan titi su na bawa kafafuwansu wahala ta hanyar tafiya babu tsayawa hutawa, yayin da suke tafiya a kafa Zulai sam tunaninta baya tare da ita abin da ya faru ne tsaye cak a ranta musamman kaifafan maganganun da Maman ya fada ma ta, shuuuuuu maganarshi ta gifta a kunnuwanta.
"Allah wadai da halinki Zulai bazan iya ci gaba da cakuɗaki da iyalina ba alhalin bakin hali ne da ke, tun da nike a garinan kaf ban taba jin ko da a labari wani ko wata sun aikata irin abin kunyar da kika aikata ba, kamar yanda Me gari ya ce, ki tattara inaki ya naki kibar mana ƙauyenmu bamu buƙatarki."
Tsugunnawa ta yi a ƙasa tare da dafe kunnuwanta da tsananin karfi ta saki ƙara ta na faɗin.
"Mamman! a'a Mamman a'a a'a."
sai kuma kuka me ƙarfi ya kwace ma ta irin wanda ke fitowa daga ƙasan zuciya.
Fadeel da jikinshi yai sanyi ya ja sanyayun kafafuwanshi ya zauna a kusa da ita ya shiga rarrashinta duk da shima ya na cikin damuwar, sam hankalin Zulai ba ya tare da ita dan bakin cikin abin da iyayenta suka aikata ma ta agaban jama'a ya dameta, izuwa yanzu ta fara tunanin cewa ita din ba diyar Mamman ba ce.
Yayinda Zulai ke rizgar kuka babu tsaitsayawa wata dalleliyar mota ƙirar benz c class ta nufo inda suke a zazzaune, ƙiiiiii lafiyayyar motar ta taka burki yayinda aka ɓalle murfin motar da tsananin karfi, wani dogon kyakkyawan matashi ne me cikar kamala ya fito daga bayan motar, fuskarshi a ɗaure tamau ya nufo inda Zulai da Fadeel ke zazzaune, zuwanshi bai yi wata-wata ba ya ɗago kafadar Fadeel ya miƙar da shi da karfi sannan ya saka shi cikin jikinshi ya rungume shi tammm kamar zai mayar da shi ciki jikin shi sai faman sakin numfarfashi ya ke a jere.
Ƙanƙame shi Fadeel ya yi tare da sakin tagwayen ajiyar zuciya cikin farin ciki ya ce.
"Broth yaushe ka dawo? kuma ya akai ka san inda nike?."
Dago da Fadeel matashin ya yi tare da sakin tattausan murmushi sannan ya kama kunnen fadeel ya murɗa da ƙarfi tare da dungure ma shi kai sannan ya ce.
"Bana da isashen time zo muje kawai."
Yana fadin hakan ya juya wajen Zulai da izuwa yanzu kukanta ya daina fita da sauti sai hawaye da ke zuba kamar an kunna fanfo.
YANZU LABARIN ZAI FARA DA ZAFI-ZAFIN KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZA TA KAYA.
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐